Complete Hausa Novels

A Mafarki Nasanta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Mafarki_Nasanta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 14 of 24

EPISODE1️⃣
FREE PAGE1️⃣7️⃣

WANENE DR.AMMAR(AA)
cikakken sunansa Abdulrashid Aliyu Ahmad,haifaffen garin Gusau,jihar Zamfara,Dane Ga sarki Aliyu Murai,sunan mahaifiyarsa hassana hamza wadda suke kira da unni,mama kenan ayaren (korea) mahaifinsa da mahaifiyarsa Auren soyayya sukayi,kuma auren zumunta,Mahaifinsa sarki Aliyu murai rikakken Dan kasuwa ne,wanda yake da kaloli kuma manyan kamfanona akasashen daban daban a duniya,A yanzu haka shine yake rike da sarautar ta zamfara A babbar masarautar murai ta Gusau'Ammar shine d'aa na farko ga iyayensa,sai mai bimasa hamza wanda yaci sunan kakansa na uwa,ana masa lakani da mahir,sai Auta yuhanisa inda taci sunan yayar kakarta ta uwa,suna kiranta da nisa,Ammar yana da shekara ishirin da takwas aduniya,mahir kuma yanada shekara goma sha biyar,sai nisa tana da shekara goma sha takwas aduniya,Mahaifiyar sa gimbiya hassana "yace ga wan mahaifin su sarki Ali Sarki,Hamza murai kenan,takasance yan biyu ita da mahaifiyar aj,sai autar su laila,sunan mahaifiyar su fateema suna kiranta Ammie,Ammar yaci sunan k'anin mahaifinsa Abdul rashid wanda shine autan su sarki Ali su uku ne maza,suna da mace daya mai suna khadija,suna kiranta mama dije wadda ke aure agarin kano tana auren wani custom,tana ya guda sunanta umaimah,wadda ita kadaice rabonta,tun rasuwar yan biyun ta na fari,sai kuma umar shine ke bima sarki Ali murai,Sai Abdul rashid ,sannan khadija,sunan mahaifiyar su sadiya suna kiranta hajiyar safkare,a takaice hajia,dukkanin su sunyi aure,..........Dr.Ammar yayi karatunsa tundaga secondry har tertiary a kasar india inda kuma kuma yasamu aiki achan shida aj,Dr ammar mutun ne mai tsantseni ga tsandar tsiya duk da yana da laziness bai yadda yasaka ma kansa kanzanta ba,baida daukar raini,dan gayu ne na asali,baida daukar raini,kuma bai da wulakanta talaka hasalima shi mai tausayinsune,mutun daya ne yake iya wa da halinsa shine dr aj kuma shine babban abokin sa,domin sun kasan ce kamar yan biyu kamar yadda iyayensu suke,dr ammar dai kyakkyawa ne na karshe,har yanzu bai da budurwa duk da harin da yan mata suke kawo masa,natayin soyayyarsu,mutun daya ce tazame masa kamar cingum itace dr malini,domin Allah yasanya mata wani sonshi duk d yana kokarin nuna mata bata cikin tsarinsa hakan baisa tayi sanya ba wannnan kenan...
SAI DR.AJ
Cikakken sunansa dr Al amin jabir muhammad soja,dane ga leutenant jabir muhammad wanda yakasance army ne na nigeria,shine shugaban sojojin arewa,sunan mahaifiyarsa husaina inda suke kiranta ummi,Aj yanada kanne uku inda namijin dake bimasa yarasu tun yana karami mai sunan mahaifinsu jabir ,sai mai bima margayi jabir sunanta sumayya,sai Auta Asma'u suna husnat,wadda taci sunan kakarta su ta wurin uba,Aj sa,a ne da dr. ammar kwana arba'in ne tsakaninsu,Sai sumee wadda take da shekaru sha tara sai auta husna nada shekara goma sha uku,aj da sun taso komai sunayinsa atare,Aj shima baida wata tsayayyar budurwa har yanzu Wannnan kenan...

*MUDAWO LABARI*
------------------------------------------------------------------
*~~NIGERIA ZAMFARA~~*
*~~ BUG~~*
*~~UNGUWAR SABON GARI~~~*

...........Bayan fitowar Baba Adee daga wanka Ya shiryawar sa cikin shiga ta kamala dai dai rufin asiri cikin yadinsa mai kyau black,bayan fitowar sa wanka wanda da taimakon Bba Asabe ya shirya wanda kuma shine dalilin saukarsa da wuri dama shi ba mutun bane mai riko..
" A bangaren su Halee kuwa bayan kammala shirin su na zuwa islamiyyya suka dauki jakun kunansu,sunfito rass dasu cikin uniform ash colour hijab har kasa masu kyau sai sheki sukeyi,dukannin su sun amshe su musamman ma Halee wadda farar fatar ta tak'ara haskawa, kyakkayawar fuskar ta ta fito rass doguwar fuskar ta kara yin wani shaf mai kyau cikin dogon hijab dinta gwanin burgewa,sunata zuba kamshi mai dadi,wanda sai ka matso su zakaji shi,ba mai cutarwa ba kamar dai yadda aka annabi ya siffanta turaren mata,
'Dan Baba Adee akwai son kamshi domin mafi yawancin tsarabarsu ta turare ce,shiyasa koda yaushe zakaji su cikin kamshi....

Sallama sukayiwa Baba Adee da Baba Asabe Dake zaune a barandar gidan suna dan taba fira jefi jefi...

Miji da mata sai Allah..

ficewa Gidan sukayi bayan amsa addu,o'in da yasaba yimusu inyana gida...

Bayan wucewar su Halee islamiyya,shima Baba Adee yaficewar sa zuwa masallacin unguwartasu dan gabatar da la,asar kan lokaci.....

*~~GUSAU,ZAMAFARA~~*
Gusau ta sambo mai dimbin al umma noma shine abun alfaharinku,Gusau Babban birni ne na jahar Zamfara wanda yatara dubbanin Al umma ta kowane sashenn yarukka da yan kasuwa,musamman manoma,da ma aikatan gwamnati da manyan yan siyasa,Babban Abunda yake abun burgewa agaresu shine yadda sukayi riko da aladunsu,da addini da kuma sarautunsu,sai kuma abun da yake mai mahimmanci da suka rike shine Bin shari'ar musulunci,gari ne daza kasamu suna bin dokar musulunci wanda ko gidan karuwai zai yi wuyar samu a jihar...

*MASARAUTAR MURAI*
Babbar masarauta ce dake cikin jihar zamfara gusau wadda gaba daya nigeria suna alfahari da ita domin kafaffiyar masarauta ce tun zamanin Sarki Ali murai wanda shine sarki nafarko wanda yafara yin sarauta ajihar tun zamaninsu shehu usman dan fodiyo Na sokoto,shiyasa takasance mai mai dimbin tarihi...

'kuma shine yayi ruwa yayi tsaki gurin kafa wannan masarauta mai tarin Al ummah ,wadda tazamo abar alfahari a idon al ummar nigeria jin irin kokarin da sarki Ali murai yayi gurin kafa masarautar..

Mutane daban daban daga cikin ya yan Ali murai sun rike sarautar wannann masarauta har izuwa yanzu da ake k'ara samun cigaba...

Tattab'a kunnen Ali murai a yanzu shiyake mulkar masarautar,inda take samun kulaawa dakuma Al.ummar dake karkashin ta,Ahannun d'an d'an sarki Ahmad..

WASH TYPING AKWAI WAHALA...KUYI MANAGE DA WANNAN....BANJIN DADIN JIKI NANE.....

GOBE IN SHA ALLAH ZAKU SAMUN KARIN PAGE

Kuyi sharing,
Sannan ku danna min like akasan page din....

Ina godiya sosai masoyan amafarki
Halee tace agaishe ku...

💫FA'EEH BG💫

💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream i know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫

Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔

------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️

💫P.E.W.A.💫

Home of perfect essential writer's together we stand🤝

ESSENTIAL WRITER'S📚🖊️

Pen🖊️*is migthier than the sword🗡️*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.