A Mafarki Nasanta Complete Hausa Novel
Reading file: A_Mafarki_Nasanta_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 4 of 24
EPISODE1️⃣
FREE PAGE5️⃣
TYPING📲📲📲
Kawar da shirun nasu tayi ta hangar ta hanyar furtawa Halee kitashi ki watsa ruwa bari indebo muna ruwan zafi tana gama fadar haka ta cire hijabin uniform dinta tayi waje.
Bayan fitar ta daga dakin Halee ta tashi daga kishingid'en datake tacire hijabinta ta nad'esa Sa tasanya acikin acikin sip dinsu wadda Khady bata ya mutsa ba,sannan ta jawo zanen da take wanka dashi tayi tadaura bayan ta cire kayan jikinta tasanya acikin basket na Tara datti Dan karamin hijabinta Wanda take wanka dashi tasanya ta cigaba da gyara kayan da duk suke ahargitse acikin sip dintasu Wanda Khady ce ta ya mutsa su dazu da zataje makaranta..
Tana cikin gyaran sip d'in ne sai ga khady tadawo da ruwan acikin small bucket bayan ta amsa mata sallama ne
Ta Tsinkayi Muryar Khady Tana Furta nidai Halee kibar gyara kayan nan kinga baki da lafiya duk da naga yau jikin naki da sauk'i nazata sai munje asibiti ~takai karshen maganar fuskarta da alamar damuwa
Hararar wasa wasa Halee tasakar mata tana idasa lankafe hijab daya daya rage saura ta gama,Ahankali ta juyo ta dauki ruwan zafin da Khady ta ajiye mata tare da furtawa Khady karki damu Sisi nah nafara zama strong women tayi maganar ne cikin sanyin muryarta da yazame mata jiki takai karshen maganar tana sakar mata kayataccen murmushinta mai Sa maza👨 had'ari atiti😎
----------------------------- 💫fa'eeh bungudu💫
Itama Khady murmushin ta mayar mata dashi bata k'ara cewa komai ba ta kama hangar da zata sadata da d'an madaidaicin toilet dinsu dake cikin dakin har ta kusa isa ta tsinkayi muryar Khady na furta "Halee kibari inzo in had'a miki ruwan tunda naga baki da karfin jiki tafiyar taki takara. Zama slowly"
Ko ayanzun ma murmushin Halee tasakar mata Wanda har kyawawan hakora ranta farare Tass suka bayyana gwanin burgewa,itama Khady Murmushin tayi tana furta ohh! Yau su Anty Halee yan sarautar sun motsa kenan girgiza kanta tayi tana kara sakin murmushi na mamakin halin Yar uwarta na rashin son yin magana.
Itama cire uniform din nata tayi tadaura zanen da wankanta tayafa katon mayafi tana ficewa daga dakin
-------------
Tun akofar dakin nasu tafara magana cikin farin ciki take furtawa Baba Adee sannu da zuwa saboda tajiyo muryar shi lokacin suna magana da Khady.
A bangaren Halee kuwa tana shiga toilet din ta fara gudanar da wankanta cikin natsuwarta da tazame mata jiki duk da yadda ranta yake ba dadi....
"Dady sannu da zuwa" ya hanya?Muryar Khady ce ta ratsa tsakar gidan nasu har zuwa barandar da wannan dattijo yake azaune.
Murmushi wannan dattijon yi har takara so inda yake dattijon kirki Wanda sunan shi yake Abdul rashid Amma anfi saninsa da Baba Adee Wanda akalla zai kai shekara hamsin aduniya.
(wannan suna Khady ce tafara sanya masa shi alokacin tana karama bata iya fadin Dady kamar yadda Halee ke fadi sai ta mayar dashi Adee Wanda ganin haka yasa itama Halee ta mayar dashi Adee jin Yar uwar ta na kiransa haka)
Sai kuma sunan yabisa har na waje suka kara masa da Baba wannan kenan..
Har ta durkusa agabansa Murmushi ne kwance akan fuskar Sa ganin yadda ta turo baki gaba nak'in amsa mata sannu da zuwan da ta masa,Baba Asabe ce dake tahowa da amadaidaicin kofin silver domin kawo masa yasha ta furta kekam dai Hadiza meyake damunki ehhh!daga dawowar Sa sai fara turar masa baki kamar wadda aka daka tana magana tana tsiyaya masa ruwa akaramin cup shima na silver mai kyau
Kurb'a ruwan da Baba Asabe ta mikamasa kurba guda yace rabu da ita kinji dije,aiko ida rufe bakinsa baiyi ba Khady takara turekke bakin nan gaba....
Dariya yayi wadda take fitar da suffar shi ta magidantan kirki yace ke koh:khadija Dan Ankiraki da dije ai bawani abu bane suna ne mai dadi koh! yakai karshen maganar yana Dan yin murmushi,ganin tayi shiru batace komai ba,yace nasan fushin da like yi nafarko ban karba miki sannu da zuwan ki ba na biyu na kiraki da sunan tsofaffi yakai karshen maganar yasa cikin yin Yar karamar dariya wadda har far in hakorinsa na Makkah ya bayyana sannan yacigaba da magana kin san Khadija nace kibar yimin sannu da zuwa tundaga nesa shiyasa na kyaleki na biyu kuma ayi hakuri laifi nane shalelen Laure....yana murmushi
Baba Asabe dake gefe itama murmushinta yi,Itama Khady murmushin ta saki jin ankira ta da shalelen Babarta cikin dariya ta furta hard a ta dadynta dukan su dariya suka sanya.
Maganar Baba Adee ce ta dakatar da da riyar su Wanda maganar bata yima Baba Asabe dadi har fuskanta ya nuna,inda yake furta "yake cewa ina Shalele ".................
Yawan likes dinku da comment shahizai Sa Ku samu page biyu arana
*A mafarki nasanta *📒
Daga Alkalamin
💫fa'eeh bungudu💫
Mu hadu next page✌✌
Dan jin cigaban maganar ta Baba Adee
Dakuma jin Amsar da Khady zata bashi, nasan kun matsu kuji asalin Halee
------------------
Kucigaba da bibiyata ahankali zan warware muku duk wani sashe na littafina....
WASAN YANZU AKA FARA👏
Kuyi hakuri ba editing domin dazu sai da nagama wahalar typing gaba daya ya goge.
Pls like share and comment.
💫A MAFARKI
NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍
💫Fa'eeh Bg 💫
Dedicated to my lovely sis Laila Almustapha
Murai💔
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of perfect essential writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S📚🖊️*
Pen 🖊️is mightier than the sword🗡️*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.