Complete Hausa Novels

A Mafarki Nasanta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Mafarki_Nasanta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 23 of 24

EPISODE1️⃣
FREE PAGE2️⃣7️⃣

TYPING📲📲📲

Bayan dukkaninsu sun samu natsuwa sai Sarki Ali yatambaye su daga ina suke gida ko schl

YAr bak'ar wadda take kama da Dr.Ammar sosai ce ta furta" Abba muntaso daga school ne shine muka ce driver yakawo mu nan muganku.

Murmushi sarki Ali yayi yana furta" su sumayya uwayen yawo",sumayya datake d'an satar kallon mahir tad'an kawar da kanta gefe cikin jin kunya tana furta

"Allah Abba bana da yawo,Nisa ce tace sai munzo nan kuma gashi bamu ma gaya wa Ummi ba".

mugun duka Nisa takai mata Abaya Bayan jin kazafin da tayi mata, cikin shagwab'a Nisa ta furta Allah ni Abba ba ruwana itace tace muzo zata karbi sako gurin yaya mahir.

Abbah da jin wannan magana ta Nisa sai yayi murmushi irin nasu na manya dan dama dazu yaga yadda Sumy ke satar kallon Mahir Din sai dai bai kawo komai ba aransa,Murmushi yakarayi irin na jin dadi,sannan A hankali ya furta"Sumayya wani irin sako ne halan?sumayya dake cikin zullumi dama tana tsoron hakan tafaru dan tasa halin nisa wani lokacin bakinta baida sayi,shiyasa tun amota sai data kwatse ta,Dan ta girme ma nisa da shekara daya kuma tafita wayau ita nisa surutu ne dai bai wani sha mata kai ba kamar sumy d'in.

Gabanta ne yafad'i da jin tambayar da sarki Ali yayi mata in ina tafara Alamar rashin gaskiya sai kuma ta donar da kanta kasa,tayi danasanin cewa nisa gurin yaya mahir zata karbi sako dama cemata tayi suje sugaida Unni da duk haka bata faru ba,Kwadayin ganin mahir din take shiyasa tace sako zata karba awajensa,saboda yakwana biyu baije gurin Ummi ba saboda schl data rikesa.

Shiko mahir duk da yana kusa kuma yana jin komai dake wakana bai nuna ko a fuskarsa ba Alamar dasunan shi azancen..

'''''''ganin taki basa amsa,sai ya juya akalar tambayar sa ga mahir shiru mahir yayi duk da yaji tambayar da mahaifinsa yamasa "wane sako ne halan zaka bata"itace tambayar da yamasa,da gayya sarki Ali ya furta masa tambayar,kara furta masa yayi cikin raha kodai sakon sirri ne yana d'an kallon sumy dake gefensa,Ai dasauri ta mik'e cikin jin kunya tayi hanyar Babban falo,Dariya sarki Ali yayi irin tasu ta manya yana girgiza kansa.

Shiko mahir tunjin furucin mahaifinsa na karshe ya sunkuyar da kansa yana mai turar labb'ansa yana furta " nifa Abba bawani sakon sirri bane kawai dama yaya Aj ne yace zaiyi magana da ita ne"

"Touh itakuma wayar Umminku fa,ko bata da amfani ne " inji sarki Ali,bakinsa yakara turowa jin k'aryar tasa bata hauva,Amma akarfin hali irin nasa sai ya furta Abbah inaga ta lalace ne,Murmushi Unni tayi kawai ita da sarki Ali suna girgiza kansu ganin soyayyar ta yaran zamani.

Ahankali Unni ta furta tashi kaje Babana kasha magani ka kwanta tunda kaki cin abinci,Hararar Nisa Yayi dake jinhgine da kafad'ar mahaifinsu tana dariya kasa kasa na muguntar da tayiwa Sumy.

Ahankali mahir ya furta " Unni kinganta koh,wallahi yarinyar chan bata jin magana duk Abba da yaya Dr A suka sakanta ta "murmushi Unni tayi tana mai fad'in kyaleta kaji ai kaima unni ta sakantaka koh,Murmushi sarki Ali yayi ganin ydda zuri'ar tashi suke cikin farinciki yana jin ina ma Akwai Ammar dinsa akusa.MganarUnni ce data furta wa mahir ai kai Autan Unni Ne,ta tsayar masa da maganar zucinsa..

Autan Unni din da Unni ta furta ne yasanya yuhanis ta taso da sauri tana ita wallahi bata yadda itace autar Unni har Da Ummi ma tana maganar tana matso hawayen shwagwaba,tana mai zaunawa a d'ayan gefen Unni Sarki Ali murmushi yakarayi yana furta kyaleshi maji dadi na kinji ai ni ke kadaice AUtanah bada yaya dr ba bada yaya mahir ba,kivar Unni chan danata tarkacen kidawo nankinji yakai karshen maganr cikin wani yanayi dalilin saka sunan Dr Ammar,sbd haka suke kiransa yaya dr,Ita kanta Unni wani yanayi tashiga mai dadi jin karo nabiyu yakara sanya nur d'inta cikin zancen sa.

Nisa kuwa da sauri takoma inda Abban tana dariya tare furta yawwa Abbana ni kadai bada yaya rigammenme ba,ganin mahir na kokarin yimata rankwashi akai jin takirasa rigamamme.

Kyafci mahir yayi yana mai mikewa tsaye sallama yayi musu,sannan yayi ma Nisa Alamar zamu had'u,yayi fucewarsa yana murmushi.

A b'angaren sumy kuwa bayan ficewarta daga dakin sai tayi zamanta afalon jin zaman y isheta kuma tana jin nauyin komawa ciki ganin tabada kanta,dan taji kunya sosaiii,sai tayi ficewarta daga sashen fitar ta kenan ta hango motarsu Abdallah da yusuf tashigo Jikokin fulani,Abdallah d'an gurun yaya mustapha shikuma yusuf d'an wurin malan,Yayyen su Unni.

A hankali suke firarsu ta yan uwa shida sumy bayan gama parkng motar A chan achan Babban parking space dake a fadar yusuf ya wuce nasu sashen bayan gaisawa da sumy,shiko Abdallah yatsaya domin su gaisa kwana biyu basu had'u ba...

A bangaren Mahir kuwa bayan fitowarsa daga dakin yaduba falo baiga sumy sai yafito gaba d'aya cikin sashen ckin mamakin ina ta tafi kuma,a compound din sashen nasu yahango su ita Abdallah Akan wasu chairs suanat firarsu gwanin burgewa kamar wasu masoya,wani kololon bakin cikin ciki ne ya ziyarci mahir daganin Babban Abokin nasa da sumy zaune sunata raharsu,takawa yayi zuwa inda suke yayi,ya yyi tsaye,Abdallah ne yafara lura da tsayuwarsa Abayan sumy dake ta maganarta hankali kwance,lura da yanayin fusakarsa ne yasanya Abdallah tambayar bros lafiya dai koh?sai alokacin sumy ta gansa dasauri ta mike ta fara kame kamen rashin gaskiya... cikin "sanyin muryarsa ya furta lafiya qlau".Unni ce tace inkira mata wannan yarinyar,ohk Abdallah yafurta yana fadin" big girl sai anjima ko dan nasan dakyar mukara had'uwa kila.. inkoma gida kigayar mun da Ummi da husnat"toh tace tana mai rab'a mahir tawuce cikin gidan..

Abdallah ne yakara furta ma mahir yakannaka bros?kasha magani?eh kawai mahir ya furta wucewarsa cikin jin haushin Abdallah,bai tab'a jin haushin big girl din da Abdallah ke kiran sumy dashi ba sai yau,sauri sauru yacimmata Sumy da har tashiga falon..

Ke yadakatar da ita daga kokarin bude kofar second falon datake kokarin yi A hankali ta juyo suka had'a ido dashi yana mai kafeta da dara daran idanunsa masu yanayi dana da Dr ammar,Saurin duk'arcda kanta ta tayi kasa ganin irin kallon dayake jifarta dashi,wanda bazata iya jurewa bah,muryarshi ce tadaki dodon kunnenta,yana furta "wane sako ne zaki karba hannu na"? rass gabanta yafadi nan tafara kame kame duk da bata furta komai ba,ganin yanayin da tashiga yasanyashi dauke kansa,yana kawar da wanchna zancen ta hanyar tambayar ta maganar me sukeyi da Abdallah?

niko nace mahir kamanta da yan uwata kai ne 😄

Kanta tayi saurin dagowa danjin tambayar da yayi mata ido suka kara had'awa dashi tayi saurin janye nata ganin uwar hararar da ya sakar mata,murmushi ne ya subuce mata wanda ganin irin hararar da yayi mata sai taga yakara yimata kyau,Amsa masa tayi A hankali "yaya mahir gaisawa ce mukayi sai kuma firar school din mu danake basa,"ke uwar bada labari koh"shiru tayi jin abunda abunda yafurta girgiza masa kanta kadai tayi tana kara sakin murmushi a fakaice,Bata san cewa yaganta ba,shima ana bangaren murmushin gefen baki yasaki yana mai furta "meye na murmushi"kai takara girgizawa tana kokarin bud'a bakin ta kenan taji tafi abayanta raff raff ....

Waye kuke tunani kenan ya musu kutse suna tsaka da shan love 😍?shin ko dai mahir ya fad'a ne?

Like,share and comment pls.

Idan kina bukatar daga farko zaki iya tuntuba ta....
https://chat.whatsapp.com/IjZCle5c6V3BGRlnZ0yKim
💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫

Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔

*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,na episode two*!!!✌️✌️💥💥
*masu son a tallata musu hajarsu should contact me via*
*call +2348069059746*
*chat +2348066995473*

------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️

💫P.E.W.A💫

Home of perfect essential writer's together we stand🤝

ESSENTIAL WRITER'S📚🖊

Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.