A Mafarki Nasanta Complete Hausa Novel
Reading file: A_Mafarki_Nasanta_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 15 of 24
------------------------------------------------------------
EPISODE 1️⃣
FREE PAGE1️⃣8️⃣↔
TYPING📲📲📲
*TUSHEN MASARAUTA*
"Ali murai shine Asalin wanda yarik'a masarautar yana da mata kwaya d'aya tal,sunan ta Hajiya lubah (iyami) da "ya "ya maza biyar,d'an sa nafarko sunan sa bello,sai nabiyu sunan sa Haruna,na ukun Abdul aziz,sai na hud'unsu Isma'il,sai Autansu yahaya..
Bayan rasuwar sarki Ali murai sai aka nad'a d'ansa na farko Bello wanda shi yacigaba da kula da masarautar yana da mata d'aya da y'a y'a hud'u namiji biyu mace biyu,Bayan wasu shekaru shima Bello yakwanta dama,wanda mutuwartashi ta kowa ya jita A Masarautar saboda sak halinsa irin na mahaifinsa sarki Ali murai,Mahaifiyarsa takoka da rashinsa da y"an uwansa da ma Alummar Masarautar.
Bayan gama zaman makoki Aka nad'a d'an uwansa Haruna,Haruna yak'arb'i mulki cikin salama ,Sai bayan shekaru sittin sannan Allah yakarbi ransa..
..Abdul Aziz Yakarb'a shi kwata kwata ma bai ka shekara hamsin ba akan karagar mulkin saboda ciwon daya ci k'arfin sa na k'oda,sai aka nad'a Isma'il,Bayan Nad'in Ism'el,Sarki Abdul aziz yakwanta dama....
Isma'el ya cigaba da mulkin masarautar Bayan shekara saba'in bisa karagar mulki yakwanta dama,wanda bayan rasuwar sa,Anyi rigima sosai da Yahaya danshi kwata kwata bayason sarautar,acewar sa kayan wahala ce da takura,bai karb'a har sai da mahaifiyar su iyami ta kwanta ciwo akan hakan,ciwon zuciyaar ta yatashi wanda yasameta tun bayan rasuwar mijinta sarki Ali murai,sanadin bak'in cikin
Yahaya da yakafe bazai k'arb'i masarautar ba,masarautar da mijinta sarki Ali murai yasga gwagwarmaya wurin ginata,daga k'arshe dai yakarb'a ganin yadda ran mahaifiyar sa ya b'aci gashi harda kwantawa ciwo....
'Anyi bikin nad'in sarauta da ba'a tab'a yin irinsa ba alokacin kowa kaga fuskar sa da annashuwa da farinciki kamar sauran lokutta domin sun san cewa ba su shiga mugun hannu ba dan duk cikin ya"yan sarki Ali murai babu wanda yamusu mugun riko,Yahaya yakarbi mulki cikin aminci tare da alkawalin kula da Alummar masarautar,yana da shekara talatin akaragar mulki matar shi tahaifi namiji wanda shikad'ai ne rabonta har tabar duniya,yaron yaci sunan margayi tsohon sarki Bello,bayan wasu yan shekaru,Kwatsam ranar aka wayi gari da mutuwar sarki Yahaya murai,wanda mutuwar sa ta girgiza kowa musamman yaronsa sa Bello,Bayan rasuwar sa da kwanakki itama tsohuwa Iyami mai ran k'arfe ta kwanta dama,tana da shekaru D'ari da hud'u a Duniya.
Wanda kowa yaji mutuwar wayen nan bayin Allah Acikin Masarautar da ma wajen Masarautar..
Bayan rasuwar yahya Anyi rigima sosai A fada akan wayenda za,a dora akwai d'an wajen margayi bello da yace yanaso sai kuma d'an wajen magaji wanda yaya ne ga Sarki Ali murai,daga k'arshe dai Muhammadu bello D'an wajen sarki Yahaya shi aka bawa bisa ga chanchantarsa duk da akwai k'aranta atare dashi dan duk sun girme masa.
Anyi nad'in sarauta tareda Daurin Auren Sarki Bello Alokacin yana da shekara ishirin da hud'u A duniya,Bayan hawansa akaragar mulkin yana d'a yan uwansa manyan muk'a man masarauta,domin cigaban Alumma .
Ya Auri yar wajen sarkin zazzau na hud'u alokacin mai suna Gimbiya Ruk'ayya bayan shekara gimbiya Rukayya ta haihu ta samu yan Biyu maza,Alokacin ne kuma matar tsohon sarki margayi yahaya uwar muhammadu bello tabar duniya,Anyi taron suna cikin alhinin wannan rashi,tacigaba rainon yan biyu dinta,Bayan wasu shekaru tasamu wani cikin inda tahaifi Namiji yaci suna Aliyu,sunan tsohon sarki...
'A Daren sunan Aliyu ne wani Babban tashin hankali yafaru inda wuta ta kama ad'akin su hassan da husaini duk suka k'one k'urmus sanadiyyar wutar lantarki suda mahaifiyar su gimbiya Ruk'ayya wadda taje dubasu daga nan ta musu Addu,ar kwanciya bacci duk da tasan cewa bazasu kwanta hakan nan domin takoyar dasu,alokacin suna shekara shidda A duniya,Mutuwar data girgiza Sarki Bello da kuma masarautar wanda sai da sarki Bello yasuma alokacin da aka sanar dashi,Bayan jimamin rashin Sarki Bello yaci gaba da rainon D'an sa Ali....
**Bayan shekara guda sarki Bello yayi Aure ya Auri wadda take baiwa ce Amasarautar, ya Aureta ne saboda ganin irin kulawar da take bawa Aliyu wanda kuma ita kad'ai yake yadda da ita,Sai ya " yenta ta kuma ya Aureta domin samun farin cikin D'an sa tilo daya.
Lafiya lau masarauta take tafiya tareda cigaba mai yawa,Bayan wasu shekaru Sarki Bello na Biyu yabar Duniya yana da shekaru hamsin akan karagar mulki,inda yabar Aliyu cikin maraici mai yawa duk da wannan yentacciyar Baiwa mai suna Nana Asma'u tana sonshi tana bashi kulawa mai kyau saboda yadda take jinsa kamar d'anta na cikinta..
BAyan gama jimamin mutuwar sarki Bello na || biyu aka nad'a d'ansa Aliyu alokacin yanaa da shekaru ishirin da hud'u a duniya.
Bayan na d'insa da shekara guda yayi Aure ya Auri yar masarautar sokoto jikar yar sarkin musulmi na ||| na uku;mai suna ummulkhairi ana kiranta gimbiya (umma),Bikin yatar dubbanin Al umma takowace masarautun nigeria da manyan yan siyasa,masu kudi..Ankawo Amarya lafiya cikin fada acikin sashen ta mai kyau,suna cin Amarcin su lafiya lau tare da zaman Amana....
Komai yana tafiya dai dai ta b'angaren mulki yadda yakamata.
Bayan shekara d'aya gimbiya umma tahaifi santalelen d'anta namiji ranar suna yaro yaci sunan sa HAMZA ALIYU MURAI,Anyi taron biki lafiya,inda tacigaba da rainon yaronta,Bayan haihuwar Hamza da wata takwas tasake samun wani cikin alokacin gimbiya ummulkhairi taso zubarda cikin ganin Hamza ko shekara bai had'a kar yasha ciki,sai dai mai martaba sarki Aliyu yahana zubar da cikin sai dai yasa aka cire Hamza daga nono...
Taraini cikinta lafiya lau batare da tasha wuya ba,watannin haihuwar cikin nayi nak'uda ta motsa amma yaro yaki fitowa ak'arshe dai CS akayi mata aka ciro santalelen d'anta mai kama da uban sa sak,yaron yaci suna Ahmad...
.....Bayan wasu "yan shekaru sarki Aliyu D'an Bello jikan Yahaya D'an Sarki Ali Murai yabar Duniya alokacin,yabar Duniya da shekaru arba'in akaragar mulki,Mutuwar sa tagirgiza y"a yansa guda biyu a duniya da matar sa ummulkhairi,inda tacigaba da kula da yayanta cikin kulawa,Bayan Rasuwarsa da yan watanni Nana Asma'u matar margayi sarki Bello na || tabar duniya...
Sarautar dole aka bawa magajin gari rik'on kwarya kafin ya'yan sarki Ali su kai lokacin iya rike sarautar,domin dukkaninsu bazasu wuce shekara goma sha biyar Alokacin ba.
Bayan wasu shekaru Ahmad yayi aure ya auri matarsa Bafullatanar Adamawa itama yar gidan sarautace sunanta Haleematu sadiya suna kiranta hajiyar safkare wanda sunan da kakarta ta lakamatane,ya Aureta yana da sheakara ishirin da shidda aduniya sunyi Auren soyayya da gimbiya halimatu,kuma aloakacin ne aka damk'a sarauta hannun Ahmad duk da sai da akayi rigima dashi dan yace bazai karb'a ba sai dai abawa y"a yanshi tunda shine Babba,Dakyar aka samu yakarba bayan ya yan nasa ya sanya da mahaifiyarsu gimbiya ummulkhairi suka tasoshi gaba....
Anyi bikin nad'in sarauta lafiya cikin annashuwa da salama,ta fannin zaman takewarsa da matar sa masha Allah za,ace gwanin burgewa.
****Bayan shekara daya gimbiya halimatu sadiya ta haifi santalelen d'anta mai kama da ubansa sak jinin fulani,farin cikin wannan masarauta bazai boyu ba musamman sarki Ahmad da D'an uwansa hamza,wanda ke ji kamar shi akayiwa haihuwar...
*Ranar suna yaro yaci sunan kakan sa sarki Aliyu Bello jikan yahaya d'an Ali murai*yaro yasamu gata ta kowanne fanni,Alokacin shima Hamza yayi Aure ya Auri Gimbiya Hauwa'u yar masarautar Fulanin Bungud'u ana mata lak'ani da fulani,fulani macece mai fadin rai da rashin son talaka,da mugun son kanta,ba kamar gimbiya halimatu ba mutuniyar kirki mai mutunci,BAyan Aurensu da Hamza sai tafara nuna mishi ai sarautar dashi ta dace domin shine Babba yace abashi sarautar,ai shine dana farko ga sarki Ali Bello,sai ya rik'a nuna mata baida buk'ata,kullum haka suke rigima da ita,har zuwa lokacin da tasamu cikin Mustapha A lokacin kuwa matar sarki Ahmad Halimatu tasamu ciki na biyu ta haifi umar,sunan mahaifinta kenan,tana kiransa da emir,Bayan kamar wata takwas sai ga wani cikin na ukku inda ta tahaife sa lafiya,tasamu Abdul rashid,tacigaba da rainon ya yanta cikin kwanciyar hankali.
Daga cikin abin bak'in cikin da yafaru Akwai rasuwar gimbiya ummulkhairi matar tsohon sarki Ali,Mahaifiyar sarki Ahmad da Hamza,sunyi rashin mahaifiyarsu abar kaunar...sai dai muce Allah yajikanta da al ummar musulmi baki daya.........
*Yaa Allah Duk wata mahaifiya 💔💔dake kwance akarkashin k'asa,Allah kajik'anta da rahaama,da musulmi baki daya,Yaaa Allah wayenda suke raye kuma ka k'ara musu lafiya mai amfani tare da tsawon rai mai albarka*🙏
Rashin uwa rashine 😭Babba Arayuwa
Allah yabar mu dasu 🙏
--------------------------------------------------------------
Matar Hamza Fulani tak'ara samun wani cikin nabiyu ta haifi d'anta namiji mai suna Muhammad ana masa lak'ani da Malan,tana da ya"ya biyu kenan.
Itama sarauniya halimatu taka'ara samun wani cikin bayan shekara uku inda ta haifi yarta mace mai suna khadija inda daga gareta haihuwar ta tsaya mata chak......
Sarauniya Halimatu yaranta sun taso cikin soyayyar junansu Da yan uwansu yan gurin magaji hamza,domin shi d'an uwansa ya nada magaji bayan rasuwar wanchan magajin.....
Duk da tsangwamar da Fulani take nuna musu amma hakan bai hanasu jan yan uwansu ajiki bah.
Ta b'angaren magaji Hamza kuwa yana shan matsin lamba gurin Hauwa'u (fulani )kan karbar mulki alokacin takara samun ciki tahaifi ya mace mai suna ummulkhairi suna kiranta (khairiyya) dan taci sunan kakar ta ne wanda daga gareta haihuwar ta tsaya ma fulani chak..
A lokacin Duk fulani tana masa matsin lamba wanda har tafara cin galaba akan sa,dan bata tsaya haka nan ba,sai da talek'a gurin malammaan tsibbo (bokaye) Wal iyazubillah....
bokaye mana domin tahakan ne wasu suke amfani dashi sai suce ai malami ne shi bokan,ana amfani da sunan malamman ana shirka ana cutar Al umma..ALLAH YAYI MUNA TSARI DASU...Masu zuwa gurin bokaye Allah yashiye su🙏
MU HADU GOBE IN ALLAH YAKAIMU
YAU KAM KUNSAMU LONG PAGE,DAN KONI NAJI AJIKI NA,KUNGA NA GOGE LAIFINA NA JIYA,DUK DA BANI DA LAFIYA NE
NAGODE SOSAI ALLAH YABAR KAUNA🙏
KUFARA SHIRI ANKUSA GAMA FREE PAGES,DAN BATUN SAMBAD'O KUD'INKU......
Kucigaba da bibiyar Alkalamina
Yau duk sai A hankali typing din domn page d in yatado mini da rashin da mukayi...Allah yajik'anku da rahama Baba Bello,kakana Baba Yahaya,Alhajin Auki,Mariya,gwaggo yar sarki, Allah yasa Aljannna takasance makomarku da dukkan musulmi baki daya..AMEEEN...
💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream i know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,Na episode two*!!!✌✌💥💥
*TALLAH!!! TALLAH!!! TALLAH*
*Ina yan kasuwa masu son tallata hajarsu,ga dama tasamu domin Muna tallata kowace irin hajace daga jihohi daban daban harda ma k'asashe,akan farashe mai sauk'i,zaku iya tuntubarmu ta lambobin waya kamar haka*......
+ 2348069059746
+ 2349078741775
-----------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION 📚🖊️
💫P.E.W.A.💫
Home of perfect essential writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S📚🖊️
Pen🖊️*is migthier than the sword🗡️*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.