Complete Hausa Novels

A Mafarki Nasanta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Mafarki_Nasanta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 2 of 24

EPISODE1️⃣
FREE PAGE2️⃣&3️⃣

Typing📲📲📲

Gefen hijab dinta tasanya ta share hawayenta muryar Baba Asabe ce tadawo da ita daga maganar zucin da takeyi
Da masifa take furta munafuka algunguma wallahi bari kiji duk ranar da kika kara bari Hadiza tabiki in na aike ki wallahi ko na lahira sai yafi ki jin dadi sha sha marar asali kawai tsintacciya yar gaba da fatiha wadannan kalmomi da Baba Asabe take yawan furta mata suna daga mata hankali sosai fiye da zaton mai tunani duk ranar da Baba Asabe ta furta su agareta sai tasha kukan ta ita kadai alokacin kuwa Khady ce kawai ke iya lallashinta.

Har tunani take yi anya kuwa ita badaga sama tafado ba,wasu lokuttan kuma takanyi tunani kodai ita din yar gaba da fatiha ce kamar yadda Baba Asabe ke yawan furta mata,tunani barkatai dai ke shiga akanta aduk lokacin da ta tunano da kalmomin masu muni agareta sai dai kawai takori shaidan da Addu,ar neman tsari daga sharrin zuciya.

Dan tun Tashinta gidan wayennan kalmomin su suka bayyanar mata da ita din wacece agidan Baba Adee tun alokacin da ta fara mallakar hankalinta ta fahimci cewa ita din ba jinin Baba Adee bace da Baba Asabe sai dai duk da cewa ta fahimci komai akai bata taba gigin tambayar dayan su asalinta ba dan gudun maganar da zataji wadda zata iya saka ta rasa rayuwar ta wadda ayanzu take maleji da ita,Barema koda zata tambayi Baba Asabe baza ta iya sanar mata da komai ba domin koda Baba Adee ya kawo Halee gidan bai sanar da ita komai akanta ba,yadai sanar mata ya tsinceta ne akan hanyar shi takomawa gida tsakin gusau da furfuri dake jihar zamfara wannan kenan.
Cigaba....
Maganar da Baba Asabe ce keyi tadawo da ita daga dogon tunanin da tashiga na munanan kalmomin da Baba Asabe ta furta agareta Baba Asabe ce ke furta sakarya munafuka ana magana kina sunne kai kamar takwarai sha sha sha ballagaza kuma wallahi kinji narantse na kara aikarki kika dade sai kinci ubanki, mtssw taja uban tsaki tawuce warta fuuuu.

Kamar ance tajuya tahango Khady tsaye itama tana tsiya yar da hawaye kamar yadda itama Halee take zubar da nata hawayen
Yau nina naga ikon Allah inji cewar Baba Asabe wai ke Hadiza Uban me kika hada da yarinyar nan ne ehhh sha sha wuce kiban guri ko in tattakaki anan mtsww tana sanya hannu ta warci ledan kayan miyar ta shigewar ta madafa tana mitar ita kadai,Ta dora sanwar rana dan dama duka aikin gidan Halee ce keyi toh yau ma anyi lattin dora girkin ne kuma tasan Baba Adee yana nan dawowa bada jimawa ba shiyasanya ta kyaleta bata tilas ta mata yin girkin ba.

Alkalamin✍️✍️
💫💫fa'eeh bungudu💫

💫A MAFARKI NASANTA💫

Bayan shigewar Baba Asabe a kitchen Khady tayi sauri ta matso inda Halee ke durkushe tayi zukunnin rakumi cikin uwar ranar da ta bude tana ta faman zubda hawaye ga hannunta dafe da kanta dan tun lokacinda Baba Asabe ta zage ta da kalmar dan ubanta kanta yakara sarawa bayan jin wadanchan kalmomin na farkon Baba Asabe take yawan furta mata na marar asali tsintacciya bayansu babu abunda ke kona mata rai kamar azagi mahaifinta da mahaifiyar wanda ko da za,a yankata bazata iya cewa ga yadda kamanninsu yake ba ko tana da iyayen oho?Amma duk aka zagesu tana jin bakin ciki marar misaltuwa wanda bazai fadu ba,tana sonsu duk da bata taba ganinsu ba ko jin labarinsu.
Dafa kafadanta da Khady tayi ne yadawo da ita daga dogon tunaninta dakuma kara gudun ruwan hawayenta wanda zuwa yanzu kukanta yafara karfi har da shessheka dago lulu eyes din ta tayi wayenda suke dauke da zara zaran eyelashes masu tsarin kyau masu dauke da kwarjini farare tass dasu kwayar idonta har wani walkiya take yi na farin cikin idanun nata,A yanzu kuwa sunkoma jajaye saboda damuwa da ciwon kan datakefama dashi ga kuma kukan da tafara yi.
Zararan eye lashes nata sunkara curewa guri daya saboda ruwan hawen da suka jika su,Khady kuwa tunda suka hada idanu da Halee taji guiwoyin ta sun sage dan kuzarin datake dashi taji ya gushe,tausayi Babbar kawar tata kuma wadda tazame mata yar uwa wadda takejinta kamar tsoka da jininta.
Ahankali ta furta Halee! kanta ta kara dagowa akaro na biyu bayan mayar dashi kasa da tayi tana tsiyayar hawaye da idanu Khady tama alamar ta tashi suje daki tunda tasan yanzu bata bukatar wani dogon zance saboda ciwon kanta gashi taji jikinta yakara daukar zafi sannan in Baba Asabe ta iskosu wata masifar ce sabuwa wadda kuma take tunani ayanzu kwakwalwar Halee bazata iya dauka ba,Hannunta ta mikamata Halee bata ce komai ba takama hannun Khady ga gamn ta rike.
Ahankalin suke takawa kowa da tunanin da yake yi azuciyarsa harsuka isa dakin da yake chan gefe mallakinsu su biyu
Baba Asabe da duk taga komai .....✍️✍️✍️

💫A MAFARKI NASANTA💫
daga Alkalamin✍️✍️

💫fa'eeh bungudu💫
please like share & comment

💫 A MAFARKI NASANTA💫
in my dream i know her
By
Pha'eezah almustapha
Daga Alkalamin ✍️✍️
💫fa'eeh bungudu💫

Dedicated to my lovely sis laila Almustapha murai💔

*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of perfect Writer's together we stand🤝

ESSENTIAL WRITER'S📚 🖊️*
pen 🖊️ is migthier than the sword🗡️*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.