Complete Hausa Novels

A Mafarki Nasanta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Mafarki_Nasanta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 8 of 24

EPISODE1️⃣
FREE PAGE🔟

TYPING 📲📲📲

Dora wayar,yayi abisa laps din Dr Ammar a hankali Wanda ke jingine da sit dinsa ya lumshe da idanunsa yayi tsif kamar Wanda ruwa yaci ko kwakkwaran motsi,ba abunda yake tunani face maganar da mahaifiyarsa tamasa wadda kusan bayan dan lokaci takan yimasa maganar taji ta bakinsa ko yajanye nasa Ra,ayin bisa ga na mahaifinsa,fatan Sa kawai A wannan karon Allah yasa batayi fushi dashi ba,dan bazai iya jure fushinta ko na second ne abun yawa zai masa azuciya

Wayar Sa da Dr Aj ya aje masa ce tadawo dashi daga tunanin zucin da yaje a hankali yasa hannu yadauki wayar ya tsura mata lumsasaun idanunta kamar mahaifiyar tasa ce agaban sa,Ajiyar zuciya yasauke mai nauyi,yana kara lumshe idanunsa tare da budesu

Maganar da Dr Aj yayi ce tasa yadago idonsa daga kallon da yake yi ma wayar tasa,inda yake furta masa kar ka sanya damuwa aranka nasan awannnan karon batayi fushi mai zaifi ba kai inaji bazata tayi fushi dakaiba saboda daga yanayin yadda muka yi magana da ita na tabbatar da hakan,Wata katuwar ajiyar zuciya Dr .ammar yakara saukewa,baice furtawa Dr. Aj komai ba,Dai dai sun kawo katafaren asibitin da take Babba afadin India wadda mutane da dama ke yowar tattaki India domin samun ingantacciyar lafiya,Asibiti ce da tayi shura a fadin duniya,Babbar asibiti ce da ta Tara many an likitota ta sassa da ban da ban kama daga likitan kwakwalwa,na zuciya,likitan mata kai ko wanne fanni akwai

Su Dr Ammar da Aj suna dai daga cikin manyan likitotan dake taka rawa ta kowanne fanni acikin asibitin shiyasa sunan su yayi fice musamman Dr.Ammar.

💫 A mafarki nasanta 💫
Daga Alkalamin
💫Fa'eeh Bg💫

MAHARASTRA 24 HOURS HOSPITAL MUMBAI INDIA

...... Asibiti ce Babba wadda ta tsaru iya tsaruwa taji kayan aiki a ko ina,da kayan more rayuwam,musamman ita wannan asibiti su suke jinyar marar lafiyar da kansu,kudi kawai zaka zube kagama naka aikin....

Bayan wangale musu gate da mai gadi yayi tare da nuna farin cikinsa na zuwan su,duk da yadda yake cike da mamaki naganin wadannan manyan likitota sukadai batare da masu tsaron su...Kunsan indiawa akwai bada kariya ga wayenda suke musu hidima dan ko kare ne tsaf za,a sanya mashi bodyguard bare manyan likitota wayenda india take ji dasu dama kasa baki daya.

Haka dai ya rufe gate yana mai tambayar kansa lafiya ?suka zo sukadai ganin kamar suna risking rayuwarsu ne tafiya su kadai, abunka da turawa..nima dai ohon nace dan bangansu tun chan gidan ba,ashe dama suna sa body guard to amma lafiya?na tambayi kaina,bani da mai bani amsata haka nayi shiru abuna.

Wurin da yaksance na musamman dansu wato parking lot nasu wanda suke motocinbsu suda sauran colleques nasu,gashi nan kowa anyi tagging din sunansa akan board din mai kya.

Inda naga an rubuta Dr.Al amin dr aj yanufa dan nan ne nafarko kafin na Dr ammar Wanda shima sunan sa arubuce yake cikin tsarin burgewa,Bayan sun parker motar tasu kowa yacire sit belt dinshi Dr.Ammar dayajawo karamar bag din shimai kama da school ba,wayarsa dake ajiye atsakanin lap dinsa yadauka,A hankali yadora kafarsa ta dama wadda take sanye hadaddun takalmansa yana mai kara gyara zaman stethoscope dinshi da labcoat dinshi yana ida fitowa da gangar jikinsa baki daya,futowar sa keda wuya yaci karo da wasu garadan maza kirar america atsaye agefenn motar tasu kowannensu fuskarsa ba Annuri,Shima Dr aj haka ce takasance dashi bayan yafito yaci karo da irin garadan mazan da Dr Ammar ya ci karo dasu ,Murmushj kawai Dr.Aj yayi,nasan arina ya furta domin dama ya hango motocinsu pake agefen titi kirar hilux da wasu daga cikin motocin da gwamnatin ta bada masu kyau,Amma baiyi tunanin zasu cikin hospital din ba,ashe dama suna ciki.

Abangaren Dr ammar kuwa bayan cin karo da yayi dasu take yakara murtuke kyakkkyawar fuskar sa kamar bai taba koda murmushi ba.

Daya daga cikinsu ne ya furta sorry sir! duk sauran suka hada baki suna maimaita abun da ya furta,wannan umurnin gwamnati ne mutumen yaci gaba da magana,mukare ku tako wani hali yanzu idan yanzu idan akaji ka koremu zamu iya rasa hanyar samun cin abinmu,wannan aikin shimuka dogara dashi kayi hakuri bazamu kara ba,ko wacchan ma matsala akasamu we are sorry sir haukat suka kara hada baki atare suna maimaitawa,yana maganar ne cikin harshen indianci

Sassauta fuskar sa yayi tun bayan jin bayanin d'aya daga cikin su wanda yake shine tsoho acikinsu.

Dalili kuwa shine bazaiso ace ta sanadinshi baa sun rasa hanyar samun abincinsu,danshi yakasance mai tausayi ne ga nakasa garesa,ma'ana talakawa wayenda yafi su arziki,A hankali yak'are musu kallo sannan yadauke kansa,su kam daganin yanayin fuskar ta boss dinsu sai suka yi calming na zukatan su ,maganar da yayi ce tasaka su furta thank you sir ,duk sai suka juya gefen da Dr aj yake,bayan ya d'aga musu hannu kawai,alamar ya isa, Cikin hada baki suka furta ma Dr. aj Goodmrnng Sir! mrnng fn ya furta cikin sakin fuska ya cigaba da magana dama yaji maganar da Dr.Ammar yayi nacewa suje wurin sa inyace su dawo kan aiki shikenan,shine Dalilin godiyar da suka ma Dr. AA din Dan sun riga sunsan inta tashine bama zai koresu ba kan dan karamin laifi,Murmushi yasaki Bayan tunawa da duka wannan case din akanshi ne, A hankali ya furta dasu karku k'ara irin haka kunji,cikin yaren na indianci domin acikin su akwai wayenda basa jin turancin, Amsa masa sukayi da yes sir atare duk da yasan komai tsarinsa ne,tunanin da yafaru ne yadawo masa masa arai.......
Fitarsa ce keda wuya a cikin gari sai motar sa ta tsaya,inda tayar motar tayi faci gashi kuma babu spare tyre a cikin motar wanda basu san da hakan ba sai da ta tsaya musu kuma adai dai inda ba Al umma,tafiya ce zaiyi domin wakiltar su taro shida Dr.Ammar,A wani taro da zasu gudanar na likitota,dole haka samu gefen titi shida bodyguard dinsa suka parker motar,anbuda booth ko za,a samu spare amma babu,domin motar tamusu bazata ne,sai an duba lafiyar mota ake fita da ita,yau saboda urgently meeting ne sai basu tsaya dubawa ba ashe tayar motar na bukatar iska.

Agogon hannun sa ya duba yaga lokacin su yana yana ta yin gaba kawai sai ya yanke shawarar kiran Dr.Ammar.......
Kwance yake a cikin k'aton swimming pool din ya nutse aciki kamar ba mutum aciki ko ina tsit sai kamshin flowers da kukan tsuntsaye ke tashi, ko ina yanata walkiya sama tayi sky blue ga ruwan dake cikin swimming full din gwanin burgewa....

💫Fa'eeh Bg💫

Tunani yake yi akan maganar da duk mahaifiyarshi ta kira sa,sai ta tunatar dash,kuma aduk lokacin da yanuna kamar bai fahimci maganar ta ba sai tayi fushi dashi,wanda damuwar ce ta zame masa biyu gata mahaifinsa wanda duk akanta ne mahaifiyar tasa take yin fushi dashi,ga kuma mafarkin sa dayazame masa jiki,wanda duk wani shaki ki nasa yasan da wannan mafarkin nasa saboda tun yana D'an shekara bakwai yafara yinsa,ko mafarkin mene ne ?oho!

K'arar kiran da yasanyawa Dr. Aj ne a waya ke amsa kuwwa akunnensa cikin sauti mai dad'i,A hankali ya katse tunanin da yake Bayan D'agowa daga Nutsen da yayi..
A hankali ya fara takowa har yafito cikin ruwan lemar ruwan ta kwanta ajikinsa cikin burgewa,kyakyawan gashin kirjinsa yakwanta luff,da sumar kansa,k'aramin short ne ajikinsa,wanda yadaura towel akai da wani karamin towel ahannun sa yana goge kansa da shi,wanda wani d'ai daga cikin yaran sa suka miko masa,wayarsace bai bada damar tab'awa ba.

A hankali yasanya zarazaran ya tsunsa yadauki hadaddiyar wayar tasa wanda zuwa wannnan lokacin har kiran yakatse,wani yasake shigowa a wayartasa picking call din yayi.

A bangaren Dr .aj kuwa tsaki yake ta faman bugawa har sai da bodyguard nasa suka furta yallabai ko d'ayan mu yakoma yadauko wata motar tunda bakayi reaching nasa ba,Domin suma bodyguard nasa mota biyu suka je da fito da ita kuma duk irin budaddun nan masu kama da hilux,tasa ce kawai Audi,cigaba da magana bodyguard din yayi yana furta tunda naga ka kira sa har sau uku bai daga ba,ko baya kusane

Shiru Dr aj yayi yana sauraren maganar ta yaron nasa dan yasan halin kayan sa yanzu haka yana chan yana laziness dinsa gurin daukar kiran yana dialing numban again.... picking din call din yaji anyi shi yasanya shi kara wayar akunnen sa kirar i phone 15 pro max irinta da Dr aj,yana mai jan dogon tsaki

Abangaren Dr ammar kuwa A lokacin da yaji saukar tsukin acikin kunnensa sai da yajanye wayar akunnen nasa sannan yakara mayarwa tare da d'an kallon wayar tasa inda naga an rubuta blood line b'aro b'aro ajikin wayar tasa,tab'e dan karamin bakin sa yayi bayan ya ya dan kalli wayar sai kuma yasa ki kayataccen murmushinsa mai kara wa fuskar sa annuri,dan yafahimci mutumin nasa har yanzu akai yake dama koda yafita fushi yakeyi dashi,Dan yace bazai je taron ba sai dai shi ya wakilcesu,tunawa da yadda yafita ne yakara saka shi sakin murmushinsa wanda ke kara bayyanar da kwarjininsa,
A hankali yafurta man lafiya ?kai da ke cikin meeting ya akayi kuma kake kokarin damu na da kira,haushine yakara turneke Dr aj Bayan gama sauraraen furucin nasa,cikin jin haushin sa ya furtama Dr aj ka turo mun dai daga cikin body dinka da wata motar,motar da nashigo tasamu matsala tayan yayi faci ne kuma babu spare yana gama maganar ya katse kiran ....

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.