Complete Hausa Novels

A Mafarki Nasanta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Mafarki_Nasanta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 20 of 24

EPISODE1️⃣
FREE PAGE2️⃣4️⃣

TYPING📲📲📲

*INDIA*.....

wata kyakkyawar yarinya ce mai zubin asalin larabawa fara tass da ita ta isko sa zaune abakin ruwa,itama sai ta zauna akusa dashi,ba yanzu ne yafara ganinta ba bare ya damu Akullum tana zuwa wurinsa suyi fira wata rana ma fad'a,ta bud'a bakin ta kenan Tana furta D'an uwanah sai ga wasu mutane masu bak'ak'en kaya sunzo wurin da zuwansu suka yi kan wannan yarinya suka daddafeta tana kuka tana rok'on karsu cutar dashi,wanda shima wasu sun rirrik'esa kasancewar su majiya karfi sai yaakasa kwatar kansa agaresu bare itama yataimaketa,haka suka sanya bindiga suka harbeta yana kallo ga kukanta da yake ji har tsakiyar kansa zuciyarsa har wani b'al b'al take na tashin hankali,suna gamawa da ita duk sai suka gudu har wayenda suka rik'esa suna masu furta masa kaima zamu dawo kanka,baibi takansu ba sai yadda zai ceto ranta yakeyi, sai ma Rungume wannan yarinya da yayi wadda har yanzu baian sunantaba Amma yasaba da ita sosai har sonta yashigesa baisani ba duk da yana kokarin b'oyewavzuciyarsa hakan

Kuka yake kamar wani k'aramin yaro yana jijjigata wanda take mayafin dake kanta yazame wanda yabbayanar da lallausar doguwar sumar ta har yarufe mata rabin fuskarta saboda yadda yabarbazu,ganin ta fara nisa ne Alamar mutuwa zatayi yayi ga jininta yana ta zuba,yasanya vail dinta yad'aure mata inda suka harbetan aciki ganin jinin yak'i tsayawa ne kuma yasanya sa cikin rud'u yak'ara sanya handkerchief d'insa yana k'ara danne wurin harbin,kuka yake cigaba da yi yana girgiza kansa alamar no cikin rud'u lallausan gashin kansa duk ya hargitse,sungumar ta yayi kamar wata jaririya yana yi yana kallon kyakkwar fuskarta ganin yadda take fitar da numfashi na wahala,
Takawa yafara yi daniyar bata agajin gaggawa acikin gidan nasa sai yaga hannayenta sun saki yaraf Alamar ta mutu kenan,wata uwar k'ara yasaki yana girgizata a matuk'ar rud'e yana furta "nooo karki tafi kibarni",ganin bata motsaba yakara furtawa cikin fitar hayyaci "karki tafi ki barni" Yana kuka kamar karamin yaro ..........................

Misalin karfe 3 :00 na dare
Kwance yake akan had'adden gadonsa juye juye yakeyi akan gadon kamar wanda ke cikin wani yanayi na damuwa,ya had'a zufa duk da karfin a.c dake a bedroom din nasa da sanyin da gari yake dashi na watswar hadari Dr.Ammar kenan.......

Bayan kamar minti hud'u ya farka agigice cikin fitar hayyaci yana furta "karki ki tafi ki barni",A hankali yafara yadawo wa cikin natsuwarsa Addu'o'i yayi na neman tsari Akan mafarkin dayayi,take mafarkin da yagama yi yafara dawo masa akai kamar ayanzu abun ke faruwa duk da yasaba yin mafarkin sa da wannan yarinya,Ammana ya yau yabashi tsoro..

Tagumi Ya rafka bayan gama tunano da mafarkinsa wanda yasha banban da sauran mafarkan nasa da yarinyar,Dan shin ruwa da yaji akwar min idonsa ne yasanya shafo kyakkyawar fuskarsa da lallausan hannunsa guntun hawaye ne yaji sun gangaro suka zubo acikin idanun nasa bisa beauty face dinsa big sparkling eyes nasa sai suka kara haske da shining na ruwan hawayen da ke cikinsu curly eyelashes nasa suka k'ara cure wa waje d'aya...

Tambayar kansa yayi shin yanzu dagaske sun kashe masa ita?kuma suwane ne wad'an nan mutane da har suka yi masa barazana?,me ta musu?meye had'inta dasu,?yana jin badadi aransa zuciyarsa tayi d'aci mafarkin nasa na yau abun yatab'a shi duk da yasan mafarki ba gaskiya bane,Amma yasaba da yarinyar tana tayashi fira abakin swimming fool nasu shiyasa akodayaushe yake yawan zuwa bakin ruwan ko zai ga koda fatalwartace ....

Tambayar kansa yak'ara yi wacece ita da har ta iya kiransa da D'an uwanta? duka wayen nan tambayoyi suna tayawo ne acikin kwakwalwarsa,rasa mai basa Amsoshin tambayar sa ne yasanya shi tashi yayo alwallah,ya zura jallabiya fara mai taushi,akan short d'insa,ya shimfid'a sallaya ya raya darensa sannan yayi karatun alqur'ani mai girma acikin zazzakar muryar sa domin kuwa Dr ammar akwai kira'a yana da hizif talatin akansa ne,
Addu'o'i yayi na Allah yasa mafarkinsa ba gaskiaya bane,sannan yanemawa kansa kariya da wannan baiwar Allah da haryanzu ko sunanta baisani ba,sannan yayi Addu'a ga k'anen mahaifinsa da nora da na Allah yajik'ansu da rahama,yakuma bayyanar da takwaransa lafiya,sannann kuma yana Addu,a da fatar Allah mahaifinsa yasauko daga fushinsa,sannan yayiwa Al ummar musulmi addu,ar zama lfya, ire iren wayen nan Addu'o'in sune yayi sannnan yacigaba da kira'ar sa har yaji ankusa tada sallar asuba,fitowa nasa d'akin yayi yana k'wankwasa ma Aj kofa A lokacin shima Aj ya shirya suka d'unguma sai masallacin unguwar su....

*NIGERIA*
*BUNGUD'U ZAMFARA*

Halee ce ta mik'e zaune daga barcin da take yi tana furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un,khady ce itama ta mik'e zaune tana tambayarta lfya?,

A hankali ta bud'a bakin ta cikin rashin kuzari da tsoro ta furtawa khady cewa "mafarki nayi",dafa ta khady tayi tana tana furta kamar wane kalar mafarki kenan..Shiru tayi mata tana jin zuciyar ta ba dadi,sai kuma ta fara bata labarin mafarkin nata 'wasu mutane ne suka zo kasheta sai ga wani mutun mai kayan sarauta ajikinsa yazo yataimake ni sai dai banga fuskar sa ba saboda rawanin dayarufe fuskartasa,ahaka yayi iya kokarin yakare ni sai dai Allah bai nufa ba sai suka kasheni,sannann kuma kafin in mutu naji suna furtamasa saura shi shima zasu dawo kansa,dukkaninsu jikinsu yayi sanyi musamman Halee dake bada labarin tanaji kamar abun zai faru dagaske ne,kasheta d'in da maganar da suka furtama wannan bawan Allah,Khady ce cikin kwantar ma Halee da hankali ta furta karki saka damuwa Halee mafarki ba gaskiya bane,ni wai ma kinyi Addu,ar kwanciya kuwa?ta tambayeta ne duk da tasan Halee bata wasa da Ibada,tasan awasu lokuttan ma ita ke shafeta da Addu, a in bacci yadauke ta batayi ba,ta tambaye ta ne kawai domin kawar mata da tunanin da ke shirun addabar ta,d'an kallonta Halee tayi cikin damuwa tana langab'e wuyanta kyakkaywar fuskarta takara kyau,kara furta mata khady tayi ganin bata bata amsa ba,aikin shed'an ne kawai may be kinyi kuskure awurin yin Addu,ar ne musakeyin Addu'ar ta furtama Halee da ke ta Kallonta,murmushi tayi tana furta mukawana lafiya bayan gama Addu,ar tasu suka gyara kwanciyar su,Amma ita kam Halee har Asuba tayi bata runtsa ba,tunani ne barkatai ke zomata...

A hankali ta mik'e daga kan katifarsu zuwa toilet nasu ta dauro alwallah,raka'atanil fajr ta gabatar sannan tayi Asuba tagabatar da Addu'o'in ga wannan bawan Allah,wanda ko da ace tagansa afili bazata iya ganesa saboda rawanin da yayi k'awanya wa fuskarsa,sannan tayi Addu'ar Allah ya had'a ta da iyayen a Aljanna idan har sun mutu..
Inkuma suna raye Allah yabayyanar mata dasu,Byan tayi karatun alqur'ani acikin zazzak'ar muryar,dogon hijab dinta na sallah ta cire ta lunke,sannan tasanya d'an k'araminta na tsakar gida komawa tayi kan katifar su d'an runtsawa kafin gari ya waye taje yin ayyukkanta basai Baba Asabe tazo tashinta ba,saboda weekend ce babu makarantan boko sai ta islamiyya,gashi Baba Adee ya koma mafara gurin aikinsa tun satin da ya wuce.....

Bayan ta kwanta baccin yagagareta tunanin mafarkin da tayi take

Hawaye ne ke silala a idonta wanda bata san dalilin su ba,ko na tausayin wannan bawan Allah ne ko na tausayin rayuwarta ne,shesshekar kukanta ne yasanya khady bud'e idanunta tar akan Halee bayan jin shesshekar kukan nata,wadda tunda takoma barcin bata tashi ba saboda tana fashin sallah...

Leka kyakkyawar fuskar Halee tayi dan ta tabbatar indagaske ne kukan takeyi duk da tasan kuka bai wa Halee wahalar yi,sharkaf taga kyakkaywar fuskar Halee da hawaye batace mata komai ba tabarta tacigaba da shesshekar kukan ta sai da tayi mai isarta ko zuciyarta zata samu salama,domin yin kukan ma wata rahama ce ga d'an Adam...

Bayan ta tsagaita da yin kukan sai kuma bacci yakwasheta daga nan kishingiden da take......

Halee baiwar Allah

Koda ta farka har khady tayi wanka tahad'a mata musu abun da zasu karya dashi sannan ta gyara ko ina na gidan har jidan ruwa ma tagama A murtsatse.

Kallonta kawai Halee keyi wadda tafarka cikin zullumi tuna wa dayau batayi aikintaba,kafe khady tayi dake zaune akan d'an madaidaicin mirron d'akin nasu ta shiryawarta cikin doguwar riga ta atamfa, da manyan idanunta da tambayoyi barkatai aranta, khady lura da kallon datake mata ne yasanyata yin murmushi tana furta madam ki tashi kiyi wanka mu karya sai kiji komai,Murmushi itama Halee tayi har sai da fararen hak'oranta suka Bayyana tana mai mik'ewa tazuro fararen kafafun ta sannan takama hanyar toilet,tareda daukar flask na ruwan zafi ahannunta,har takusa kai bakin kofar toilet din ta tsinkayi muryar khady na furta Aunty na had'a miki ruwan wankan ki maido da flask din murmushi Halee tayi,tana juyowa Ahankali tasakarma khady yar karamar harara tana furtawa cikin sanyin murya "nikam banace kibar cemun Aunty ba?,harda wani rik'e habarta irin ba wasan nan,khady kuwa mezatayi in ba dariya ba ganin yadda halee tayi,"watan ma dariya nabaki tak'ara furtawa cikin d'an murmushinta mai narkar da zuciyar yan maza,har sai da dimples dinta suka bayyana,take kuma tak'ara turneke fuska irin ba wasan nan,Khady ce cikin dariyarda ke cinta gani fuskar da Halee tasha,kama kunnuwanta tayi tana kokarin hadiye dariyarta tana furta sorry shalelen dady,Itama Halee dariyar ce ta kubcemata,jinta ambaci shalelen da Baba Adee ke kiranta dashi wanda take mugun so arayuwarta tun bayan iyayenta wayendabata ko san suwaye ba.........

Wassh hannu na ai namuku kokari
Kuyi hakuri ban samu namuku editing ba.

next page tomorrow in sha Allah

Me kuke tunani game da wannan mafarki na Dr ammar?
Shin wace yarinya ce wannan?
Kucigaba da bibiyar alkalamina duk zan warware muku kowanne babi na book d'ina

Comment,like,share pls

https://chat.whatsapp.com/IjZCle5c6V3BGRlnZ0yKim

💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫

Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔

*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,na episode two*!!!✌️✌️💥💥

*MASU SON*
*TALLA!!!SHOULD* *CONTACT ME VIA*

*+2348069059746*
*+2348084504630*
------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️

💫P.E.W.A💫

Home of perfect essential writer's together we stand🤝

ESSENTIAL WRITER'S📚🖊

Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.