A Wata Masaurautar Complete Hausa Novel
Reading file: A_Wata_Masaurautar_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 11 of 39
Page1β£2β£
Kowa kallon mamaki yabita dashi, musamman prince Abdull, da ya sheryamata kwarya kwaryar walimar dawowarta.
A nan me martaba yabada umurni da akawowa Gimbiya Bilkisu,
Abubuwan motsa baki, a nan take a kacikawa gimbiya gabanta da abubuwan ciye ciye. Gaba dayansu sarki yabada umurnin duk su sauko a'ci abinci gaba d'aya.
Kowa ya sauko, a ka xunxuba abincin, kowa ya faraci, amma bnda gimbiya Bilkisu,
Maimartaba ya maida kallonsa gareta.
"Yace gimbiya meke faruwa ne? Ko abincin ne bakyaso? Ynxun nasanya akawomki wadda kike bukata.
"Turo Baki tayi, tana shagwaba, ni Abba lkcin cin abincina baiyi ba, tadiba agogon dake daure a hannunta na gwal, a shagwab'e tace Abba dibafa kagani ynxun 6:30 kuma Abba kasan sai 7:00 nakecin abinci.
Maimartaba yayi murmushin jin dadi,
" yace tabbas gimbiya hakane. na manta,Allah yayimaki Albarka. tayi dariya tace amin Abba nah.
Ta maida kallonta ga Bahijja "tace Anty Bahijja dake da yaya Abdull naga kunyimun k'iba dayawa, gaba dayansu suka sanya dariya.
Sannan tamike tace "Ammi bara nayi wanka kafun nashirya lokcin cin abincin nawa yayi.
Gaba dayansu, Kallo suka bita dashi, suna mamakin tafiyarta makaranta be canza mata rayuwa ba.
Kai tsaye d'akinta tanufa, mamaki tashiga yi, ganin ancanza mata komai na d'akin, murna tashigayi a Zuciyarta tana godewa maimartaba domin tasan shine yasanya ai'mata komai, domin yafison a koda yaushe yasanyata farin ciki.
K'arewarta wanka keda wuya, yyi dai dai da lokacin cin abincin nata, a gurguje ta shirya cikin wani matirial, pink&blu. Yaimata kyau sosai.
Sankowa takeyi sannu a hankali kan bene, domin ta halarci wurin cin abinci, ta taran da Bahijja, da kuma maimartaba zaifita fada,
Kallonsu tayi gaba dayansu tayi murmushin jin dadi da farin ciki, yau gata a gida, a gaban iyayenta da kuma 'yan uwanta.
Maimarta ne yayi gyaran murya yace "gimbiya Bilkisu anfito?
Murmushi tayi, ta sunkuyar da kanta k'asa, tace Allah yakara maka lfy, nafito domin naci abinci, na
huta,
Ganin fitowarta yasanya maimarta komawa ya xauna, yafasa fita fada.
Sai kallon gimbiya yakeyi yana murmushi, domin duk a cikin 'ya 'yansa Allah yafi d'ora masa son gimbiya Bilkisu, ga biyayya, ga kuma kyauta, bata kyamatar talakawanta.
Bahijja tayi kyaran murya, tace "yauwa Bilkisu, jiya a masarautar kano sun aikowa da Abba sa'ko, akan cewa matar sarki Bashir, tanada ciki har natsawon wata bakwai.
Bilkisu batace komaiba, face ya mutsa fuska da tayi. tace "mamansu fadila? Ko kuwa wannan jarabanbar matar tashi?
Gimbiya Bahijja ta kalleta tayi murmushi, tace "ba mamnsu Fadila ba. d'ayar.
"Kice jarabanbar kenan.
Ita dai gimbiya Bahijja komai batace ba, domin idon da sabo, tasaba jin irin wad'an magan ganu, a bakin gimbiya Bilkisu.
domin tuntana k'arama, idon sukatafi da ita can, kusan kullum saitasha doka a wurin Hajia Nafeesat, tana dukanta tana xaginta, tana cema mai bak'in hali irin na mahaifiyarta.
Shine mafarin tsanarda tayiwa Hajiya nafeesat.
dalilin da yasa batason xuwa gidan kenan.
Don ita harga Allah ta manta dasu.
Koda taje kano karatu gaba d'aya ta manta da sunada wata alak'a a tsanin masarautarsu.
Gimbiya Bahijja tace "har Abba nafad'in muje tare dake, kinga Idon hutu ya k'are, kinfuta da zuwa da jakadiya sai dai kawai ki xauna can gidan.
Tunkafin tarufe baki,tace " taf. Allah ya kiyaye ni.
Tana fad'in hkan, kamar tayi kuka, a nan kowa yasanya dariya harda maimarta, yace karkiyi kuka gimbiya bbu wadda zai tilasta maki abunda bkyso, Karkiyi kuka share hawayenki.
Murnushi tayi tace "ngd Abba nah
Dariya tabawa kowa, daga nan kowan nensu yatashi yanufi d'akin barcinsa.
Kwance tashi asaran mai rai. Gimbiya Bilkisu har ta kammala hutun ta.
Shiri takeyi domin komawarta mkranta.
Maimartaba ne ya aiko kiranta.
Ajiye kayan sake han nunta tayi, tanufi wurin maimartaba, domin jin kiran dayake mata.
Gurfane take gabansa ta sunkuyar da kanta, kasa "Allah yataima keka, Allah yak'ara maka lfy gani, naji ance kana nemana.
Maimartaba yayi kyaran murya, yace "Gimbiya Bilkisu nakiraki ne domin na shaida maki cewa, tareda Antynki Bahijja xaku tafi. domin zataje tadiba lfyar Hajia Nafeesat, sbda kinsa zumuntar dake tsakanin mu da sarki Bashir.
Ta d'ago kanta cikin biyayyah ta kalli maimartaba
"Abba ba wai zank'ibin umurninka bane a'a ba hakan nake nufiba. sai dai Abba kasan a motar haya xan koma, kuma ita Anty Bahijja bata shiga motar haya Abba,
Banason mutafi tare da ita a motar gida. yin hkan shi zaisanya agane koni wacece,kuma banason abunda zaisanya a gane ko ni wacece Abba kadiba mgnata.
Ta kuma durk'usawa, "tuba nakeyi Abba idon nab'ata maka rayuwa kayi hkri.ππΌ
Kallonta yakeyi, yana murmushi jina jinjinawa hali irin na Bilkisu,
Yace "karki damu 'yata. Nasan bakifad'i hkanba domin kib'atamun rywaba. Tashi kitafi Allah yayimki Albarka.
Tace " Amin Abba.
Ta koma taci gaba da shirinta domin komawa makaranta
Writing by ummu Safwan luv u allππ
ππππππππππ
A WATA MASARAUTAR..
ππππππππππ
Writing by Ummu Safwan 07066214433
PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S
this page is dedicated to my lovely doughter Fareeda shu'aibu Jos, Allah yabar k'auna, luv u so muchππππ
Sarki Bashir mahaifinsu Adnan, da Ammi mahaifiyarsu Bilkisu uwa d'aya Uba d'aya ne,"
Kada ku manta da Ammi mahaifiyarsu bilkisu 'yar sarki ce,"
da masarautar kano. da masarautar yola. suna da kyan kyawar fahimta."
da sarki Abdulraham, da Sarki Bashir abokanen junane."
don hka sarki Bashir yabawa sarki Abdulraham Auren k'auwarsa Ammi,"
Kunji alak'ar zuwan Bahijja garin kano,"
Amma Bilkisu da Adnan babu wadda yasan juna a tsakaninsu.
sabda tuntana k'arama tadaina xuwa gidansu saboda jininsu be had'u da hajia Nafeesa ba."
Motocine birjik harabar gidan, za'ayiwa gimbiy Bahijja rakiya, kwaliya tayi kalar ta gidan sarauta."
tasanya alkimba, sai tafiya takeyi cikin k'asaita da mulki,"
Fadawa kuwa sai zuba mata kirari sukeyi,"
Ammi ce a gefenta, tarakota,sai jamata kunne takeyi, tace
"Bahijja kikula da kanki, kiyi taka tsantsan da mutanen gidan, domin kinsan xaman da sukeyi da hajiya nafeesa, kiguje abunda xai kai ya komo a gdan," sannan kizama maiyiwa kowa biyayya,
musamman hajiya nafeesa daxaki tafi wurinta,"
Bahijja tayi murmushi, tace
"Ammi kada kidamu insha Allah babu abunda zaifaru. kinsan tsuhuwa mai ran k'arfe Addah tana nan bata mutuba. don hka bazan samu matsala da kowaba a gidan ba har naje nadawo,"
Ammi tayi murmushi, tace "nayarda dake Bahijja, Allah yatsareku ya kuma kaiku lfy, Bahijja tace "Amin Ammitah."
tashiga mota suka suka tafi,"
Gimbiya Bilkisu tareda jakadiya sun sauka lfy."
Saukarsu gda kedawu Bilkisu takira wayar Safeenat tafad'a mata tadawowarta makaranta.
Safeena kuwa tashiga murna da jin dadi, domin tayi missing din babbar k'awarta Bilkisu."
Ranar Monday, takasance kowa ne d'alibi sauri yakeyi domin halartar shiga Aji, gudun karsuyi latti,"
Bilkisu ce tareda Safeenat tafiya sukeyi cikin sauri, domin su shiga Aji, kar malam yariga su shiga."
Tafiya sukeyi sai ganin d'alibai sukeyi suna nunasu da hannu, Safeenat bata lura da hkanba Bilkisu ce kawai talura.
maza da mata kowane nunansu yakeyi, Bilkisu ce tayi k'arfen halin yin mgna, tace
"sister lfy naga kowane sai nunamu yakeyi da yatsa.ππ»ππ»
Safeenat takai kallonta a gun mutanin taga tabbas hakane nunasu akeyi.
tacewa Bilkisu, "bara ga sister zainab a can xaune barana tambayeta kowani abu ke faruwa bamu saniba."
Ai kuwa kafin ta rufe bakinta, sai ganin prince Adnan tayi a gabansu.
Kallon Bilkisu yakeyi sama da k'asa, sannan yace mata "hiii. y'ar matsiyata, to gani naxo gabanki." xanyimki wulak'ancen da babu wadda ya isa yarama maki a makarantar nan." xan wulak'antaki wulak'anci mai tsanani."
kina tsammanin Zaki tab'a yarima d'an sarki kuma kikwana lfy?" to k'arya kikeyi 'yar matsiyata."
kinsanyani jinya ta tsawon sati biyu,ke kuma zansayaki ta shekara d'aya."
sannan daga k'arshe nayi amfani da mulkina da sarautana nasanya a koreki a makarantar. Ba kuma a hka zanbarkiba har saikin d'an d'anni azabar bauta, bauta kuma irin ta k'as k'antun bayi." Zan nunamaki babu wadda isa yaja da yarima Adnan ya kuma zauna lfy."
Kinjawa kanki, kin kuma jawa iyayen, domin harsu bazan barsuba, har sai sunyi nadamar haihuwarki a rayuwarsu."
Yana kaiwa nan, yayi nuni da hannu. a nan take fadawa suka zagayesa,"
Safeenat ce hankalinta duk yatashi, tashiga magiya tana bashi hakuri."
Bilkisu dake tsaye idanunta sun kad'e sunyi jajir, bakomai take tunaniba illah tayi lorzing din darasinta na yau, kuma gashi yau Monday.
Tajuya ta kalli Safeena sai faman bashi hakuri takeyi amma yayi beres da ita.'
su kuwa d'alibai da fadawa duk sun xagayesu, saikace wad'anda sukayi sata,"
Ai kuwa rayuwarta ta kuma b'aci, a nantake ta dokawa safeenat tsawa. Tace "ya isa Safeenat, kidaina bashi hakuri, yazo yyimun duk abunda yagadama." Tunda anfad'a maka sarauta haukace." Ko anfad'amaka, tunda kana yarima d'an sarki kataka kowa yadda kaga dama."
To k'arya kakeyi, babu wani abu da ka i'sa kayimun,"
Sanan kuma babu wata masarauta da ta i'sa nayimata bauta."
Jinya kuma bakayi komaiba". Don sai nasanyaka kayi jinyar shekara 10 kana kwance."
fadawa sukace "karya kikeyi 'yar talakawa baki isa kisanya yarima yayi jinyaba."
juyawa tayi ta kallesu sama da k'asa, ta xubar." Sannan
Tajuya ga Prince Adnan tace masa, a hkan kake tak'ama da mulki?" To tabbas baka cancanci kazama yarima ba."
Kaje ka diba kundin tsarin mulki a chapter 9067 zakaga ynda ake tafiyarda mulki, ba irin naka narashin adalciba, nason kataka talakawanka yanda kaga dama."
Kallonsa takeyi ranta a b'ace."
Tace koda yake banga laifinkaba idon nayi tunanin rashin ilimi ne da jahilci ke d'awainiya dakai,"
don hka babu abunda kake iya yimun, tana kaiwa nan taja wani dogon tsaki, ta tufa masa yawu a fuska, taja hanun safeenat
suka bar wurin,"
Kallo yabita dashi, yashiga goge yawun da ta tofamasa a fuska, yana mamakin ta yadda takecin galaba akansa."
Fadawa xasuyi yunk'urin rek'eta prince ya d'aga masu hannu alamar sukyaleta."
Tonima dai ganin hakan yasa nayi saurin barin wurin, kar prince yasa a suburbud'eππΌββππΌββ
Writing by Ummu Safwan luv u all ππ
ππππππππππ
A WATA MASARAUTAR.....
ππππππππππ
writing by Ummu Safwan 07066214433
PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S
kinwuce k'awa. Kuma kin wuce aminiya. kinzama 'yar uwa a gareni." ZAINAB ALIYU MAIRIGA (ZEETAH) ALLAH yabar k'auna. hard'iya, da jikoki." Luv u so muchπππππ
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.