Complete Hausa Novels

A Wata Masaurautar Complete Hausa Novel

Reading file: A_Wata_Masaurautar_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 7 of 39

Page8⃣

NAGA SAKONKI INA GOSIYA UMMULKHAIRI NIGER ALLAH YABAR KAUNA,
INASONKU MASOYANAH A DUK INDA KUKE😘😘

A guje fadawa suka fito, kowane daga cikinsu, kansa a sunkuye alamar girmamawa,

Allah ya taimaki yarima gamu,
kallo yabisu dashi ya kuma mayarda kallonsa xuwa gareta
Yana murmushin mugunta, yacewa fadawan suyi tafiyarsu,

Yace daya daga cikin abunda xan axabtar dake dashi kenan yunwa, xan horaki, horo mafitsanani, domin sai kinyi danasanin taba yayan sarauta,

Kisani bbu wani abu daxaki nema kirasa a gdan, babu bawanki dakika ajiye daxaki sanya aiki da harkika iya bude baki kinafadin lkcin cin abinci yyi

Mekikasani najin dadin rywa?
Da harxaki iya bude baki kifadi hakan,

Tokisani abinci baxaki cishiba har sai lkcinda naga dama😎

Murmushi tayi tana kallonsa, tadaga masa hannu ya isah βœ‹πŸΌ yarima, kasani bakowane irin kazamin abinci nkeciba, musamman wadda yafito ta hannunka,
Nafadamaka lkcin cin abincinane yayi ina bukatar a maidani gda,πŸ™„

Kallonta kawai yakeyi, bayada niyar motsawa daga Inda yake,

Ganin hakan yasa itama tanemi wuri a kan kujera ta zauna,tashiga dan ne Dan nen, wayarta dake hannunta,

Can dai yaga xaman baya masa, tashi yayi, yafada dakin barcinsa a kan makeken gadonsa yayi kwancensa yana waya, da abokaninsa yan group dinsu maxaje grp ynadariya,

Bayan yakare wayar,da abokanensa, sai yyi kwance rubda ciki, yana murmushi koba komai yasan yau ya rama abunda bilkisu tayimasa, koda yunwar da yabarta yasan tahoru,

Tsayin minti 30 yana kwance, ko meyatuna? oho xumut yamike daga kwaciyar, yanufo pallon inda bilkisu take xaune rywarta a bace, domin ynxun 12:30pm lokacin tashinsu daga makaranta yayi,
Jakadiya xatayi sauraren dawowarta mkrtar

Ta kallesa sama da kasa daniyar tayi mgna, amma kuma tafasa,

Kallonta yakeyi yana murmushin mugunta, nufota yayi yana kallonta, malam kitashi mutafi.

Kallonsa tayi da niyar tayimasa mgna, amma kuma tafasa, takara dibun agogon hannunta taga 1:00pm hankalita yatashi domin tasan jakadiya xata shiga damuwa, narashin dawuwarta,

Batayi masa maganaba bata kuma kallesaba, domin zaran tabudi bki tayi mgna kukane xai biyo baya.

Mikewa tayi, tabi bayansa suka nufi mota,

A bakin mota taja tayi tsaya, shikuwa har yaxauna a maxaunin direba, yana jiran tashigo sutafi, taja tayi tsaye, ta dauki tsawon munti10 a hka, ganin batada niyar shigowa tanason batamasa lkci, yabude murfin motar da karfi yafito,

Don Allah malama idon baxaki tafiba kijaye kibawani hanya na wuce, tunda ke bkitashi tafiyaba, ni inada abunyi,

Kyalesa tayi kuma bata matsa daga inda takeba

Kallonta yaci gaba dayi, yace kodayake gdan ne bakyason fita, sbda kinga gda mai kyau, kuma kinsha esee ko? To saikinbar gdan nan koda ranki bayaso.

Fisgar hannunta yayi da karfi yabude murfin motar ya jefata ciki
Ya mayar da murfin yarufe
Ya xagaya yashiga maxauninsa ya tada motar yajata da karfi suka fita gdan.

Tafiya sukeyi bata kulashiba harsuka kusan zuwa mkrta, gabda xai shiga mkranta sanan tabude baki tace ajiyeni nan
Da karfi tayi mgnar yaja wani burki da karfi ya tsaya domin saida tabashi tsoro

Mude murfin mutar tayi tafita, snn ta sunkuya tayimasa mgna,
Ngd da bin umurnina da kayi na ajiyeni a nan, amma kasani bana barin bashi,

Mukama da kai wani likacinβœ‹πŸΌ

Writing by Ummu Safwan
Luv u all😘😘😘😘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

A wata masarautar.....
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

Writing by Ummu Safwan 07066214433

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.