A Wata Masaurautar Complete Hausa Novel
Reading file: A_Wata_Masaurautar_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 13 of 39
Page 1⃣7⃣
Gudu yake kamar Zaitashi sama, sai tunanin marin da Bilkisu tayimasa a gaban bainar jama'a
kaiwa sitiyari mota duka yayi ya burxarda da wani iska mai zafi a bakinsa, idanunsa sunkad'e sunyi jajir. Sai gudu yake zubawa a kan titi, ganin gudun dayake ba'a hankanlinsa yakeyinsaba yasanya
Abdullah yayi k'arfin halin yimasa magaba, "don Allah prince katafi a hankali mana, kadiba ga yanda jini yake zuba a k'afarka, duk kawani fita hanyacinka akan wannan matsiyaciyar yarinyar, wai ynxun ina muka nufa ne kabiyo ta wannan hanyar."?
Betankawa Abdullah ba, sai gudu yake shararawa, Abdullah duk ya tsorata da ganinsa cikin wannan halin.
Sai ganin yayi.
yayi parking a dai dai k'ofar gidansu Bilkisu, waya yad'aga yakira fadawansa, yayi masu kwatancen a inda yake suzo susamesa.
Ya mayarda kallonsa ga Abdullah yace, "yau zannuna mata na i'sa nakoresu a garin nan,kora ta wulak'anci, kuma zan a zabtar dasu har saitayi nadamar marina datayi a gaban bainar jama'a,
Itama zan wulak'antata kamar yanda tayimun a gaban bainar jama'a.
Yana rufe bakinsa saiga fadawa sun iso kowanesu jira yake abashi umurni.
Runsunawa sukayi suna kwasar gaisuwa, kallo yabisu dashi d'aya bayan d'aya, yayi masu nuni da gidansu Bilkisu,
Yace "kushiga gidan nan kufitomun da duk wani abu dake cikin gidan nan, tareda bil adaman dake rywa acikinsa, duk a fitomun dasu yanxun nan."
Fadawa suka afka gidan, suka tararda jakadiya zaune tana yankan a aifa, sai ganin fadawa tayi gabanta, kallonsu tashigayi cike da mamaki, ita dai tasan ba fadawan masarautarsu bane, tomeye had'insu da wad'an nan fadawan? Tashiga yiwa kanta tambayoyi. Saiji tayi anwatso mata a kwatin kayansu a k'afa, cike da mamaki take kallonsu tana fad'in "lfy"? Meyafaru"? Me mukayumaku"? Basu saurare taba sukaci gaba watso masu kayansu a waje."
Bilkisu kuwa na makaranta, batasan abunda ke faruwaba. Kuka takeyi, safeenat sai hakuri take bata, gameda abunda prince yayi mata.
Mekewa tayi tsaye cikin yanayin damuwa tace sis zantafi gida kaina ke yimun ciyo, bazan samu damaryin test d'in nanba domin kona tsaya bazan iya rubuta komaiba.
Safeenat tace "sis Allah ya sauwak'e, idon kikaje gida kisha magani. Ynxun da munfito gani nan zuwa naga jikin naki.
Bilkisu tace "to sis ngd saikin shigo."
Tawuce tatari mai adai2 sahu yakaita gida.
da shigarsu kwanar unguwarsu ta hango mutane, sunyi cincirundo a k'ofar gidansu mamaki tashigayi tana tambayar kanta lfy"? Taka mutane haka a k'ofar gidansu?
K'arasawa tayi domin ganin me kefaruwa, sai ganin kayansu tayi anawatso masu a kofar gida,
Jakadiya sai kuka takeyi tanabada hakuri amma basu saura ra mataba,
Bilkisu nazuwa wurin gaba d'aya kallo yadawo Kanta, ganin fadawan prince tabawa kanta amsar wadda yasanya suyimasu irin wnn wulak'ancin, batabi takan kowaba sai wurin jakadiya tanufa dake durkoshe tanabawa fadawa hakuri,
Durkusawa tayi tad'ago jakadiya tsaye tace "Ammi meye abunbasu hakuri a ciki? Ki kyalesu kawai suyi abunda sukeso.
Tana mgna amma idanunta sun cika da hawayen bak'in ciki.
Yau ita gimbiya Bilkisu itace ake wulak'antawa a gaban bainar jama'aðŸ˜
Tana rungume da jakadiya suna kuka."
sai tab'i taji anayi a bayanta, juyawarda zatayi ganin prince tayi tareda Abdullah sunayimata dariyar k'eta.
Kallo tabisu dashi sama da k'asa,
Prince yace " ni nasanya a yimaku hakan, domin bana muradin ganinku a k'asata, bakeba ko mai kama dake nagani saina sanya ankoreta a garin nan, bareke. Na tsaneki banason ganin fuskarki bare mai kama da fuskarki.
Kallon tsana tabisa dashi, tana mai zubarda hawaye, tace "banada niyar mugunta amma kaine mutum na farko da zansanya a axabtar dashi a zaba mai tsanani,
banada niyar amfani da damata domin wata manufa marasa kyau, amma Kaine mutum na farko dazaka sanyani yin hkan,
Kasani na tsaneka tsanawa mai tsanani. Ka wulak'antamu a gaban bainar jama'a kaima ka saurare naka hukunci gobe.
Tana kaiwa nan Safeenat tafito cikin a dai dai sahu, ganin Prince tsaye tabawa kanta amsar tambayar dazatayi,
Bilkusu tayi karfin halin yimata mgba tace sis tsayar mana da mai a daidaita karya tafiyarsa.
Tsaidashi sukayi takama hannun jakadiya tasanyata a ciki, sanan tadawo d'aukar kayansu, ba komai tad'aukaba sai jinkar takardunta, sai kuma a kwatin kayansu, tasanya a bayan adaidai ta.
Mutane sai kallonta suke suna mai tausaya mata.
Dawowa ta kuma kiyi, tanufi gefenda makwanciyarta take tsaye tana zubarda hawayen tausayinsu domin sunyi matuk'ar sabawa da ita
Cikin yanayin kuka ta nufo Bilkisu ta rungumeta tana kuka, Bilkisu tayi k'arfin halin yimata mgna, tace
"Hajjah daina kuka zandawo gareku bada jimawaba, abunda nakeso dake yanxun kisamu yara sukwashe maki duk wani abu dake wurin nan, nabaki shi kyauta, sanan ta Nuna wani k'aton frege tace wanan kuma a kai sa gidan liman nabasashi."
liman dake tsaye cikin yanayin tausayi yanufota yana godiya, domin tun zuwan Bilkisu a unguwar duk ranar juma'a saitasanya ayimasu abincin sadaka duk wanda yazo sallah a masalancin to saiyaci abincin Bilkusu yana mai sanyamata albarka, sannan shima liman d'in duk zai sallar juma'a dasabon d'unki yakeyi wadda Bilkisu take d'unka masa.
Abunda yasa suka saurarawa wadda yayi mata hkan, ganin fadawa dasukayi da kuma Prince da ke tsaye domin sunsan halin prince ba imani ke garesa ba.
Sanan tanuna wasu durum2 na ruwa tace liman a kai wad'an nan masalanci a dinga zuba ruwan alwala."
Tana kaiwa nan tajuya tanufi wurin prince dake tsaye yana kallonta sai a lokacin yafara tausayamata, tanuna masa hannu tace" kasaurare hukuncin da zanyi maka gobe dakai da duk wasu magoya bayanka."
Tabarshi nan a tsaye tashiga a dai2 ta suka nufi gidansu sakeenat."
Ummu Safwan 😘😘
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
A WATA MASARAURAR..
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
Writing by
Ummu
Safwan
PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.