Complete Hausa Novels

A Wata Masaurautar Complete Hausa Novel

Reading file: A_Wata_Masaurautar_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 3 of 39

Page3⃣

Motocine na tsaitsaya a nesa da makarantar, prince abdull ne tareda gimbiya bilkisu da kuma jakadiya, suka fito, suka nufi mkrantar, kai tsaye offishin shugaban mkranta suka nufa, kasancewar prince abdull yasan offishin basu sha wahalar tmbyaba, kaitsaye sukayi sallama sukashiga, dama yasan da xuwan nasu, maimartaba yakirashi a waya yyimasa bayanin komai, ya kuma turamasa da kudi domin a sayawa gimbiya bilkisu gidanda xata zauna tare da jakadiya.

Nan suka kareyin komai, suka dunguma gaba dayansu, suka tafi gidanda gimbiya bilkisu xata xauna tareda jakadiya.

Gidane karami naxaman mace daya madaidace, prince abdull yajuya ya kalli gimbiya bilkisu, sai ya merebaki, yace, ynxun kinfi bukatar xama a irin wnn rywar? Kina ganin gatane kikayiwa kanki daxaki xauna a irin wannan gidan, Kibaro masarautarku dagatanki da komai kidawo inda ba a sankiba, ba a san koke wacece ba kice anan xakiyi rywa.

Gimbiya bilkisu ta sunkuyar da kanta kasa, tace yaya katayani da addu'a Allah yabani abunda nafito nema, domin ynxun addu'arku nake nema.

Ya kada kafada, a lamar ita tasani, yyi mata sallama yatafiyarsa.

A nan take jakadiya tanufota, tafadi kasa alamar girmamawa, tana fadin, Allah yajadaran gimbiya mekike bukata, a girka maki?

Saita bata fuska, banaso, a matsayin ammi ta nadaukeki banason wasu sugane wani abu a taredamu,

Jakadiya ta kuma runsunawa tana fadin ayi hakuri idon nabata ran gimbiyaπŸ‘πŸΌ

Kinga irinta ko, ni kidaina cemun gimbiya, kikirani a bilkisu naπŸ‘ŒπŸΌ

Jakadiya tace gaskiya ranki ya dade baxan iya kiran sunankiba, domin idon nayi hkan sainaga kamar naxubar da darajar masarauta, amma daga ynxun zandinga kiranki da diyata,

Sai lokacin gimbiya tayi murmushi, tace bakomai na fahimceki jakadiya,ko hkan kika kiranidashi yayi.

Nan tawuce daki domin tayi wanka, dakin ba laifin angyarashi kuma yyi kyau dai2 gwargwado, tafada toilet tayi wanka, koda tafito jakadiya hartakare masu abinci, nan tafaraci suna fira, tana kammalawa, ta haye gdonta takwanta, tareda tunanin gobe xatafara daukar darasi

Gimbiya bilkisu ce cikin shirinta na xuwa makaranta, tasanya atamfarta pink and yellow, da hijabinta shima kalar pink tayi kyau, dama gata farar mace kuma kyankyawa.

tafito ta iske jakadiya takaremasu abinci ta xauna taci, Saida ta koshi sannan tace jakadiya saina dawo,

Jakadiya ta ajeye abunda takeyi tanufota tanafadin, Allah ya tsareki gimbiya takawarki lafiya yar sarki jikanyar sarki gaba sararauta gefinki mulki, Allah yadawo dake lfy gimbiya.

Bilkisu tayi dariya tace jakadiya baxaki dainaba kenan.

Tafiya takeyi kamar batason taka kasa, waya ta takeyi da antynta bahijja tana fadamata ynda sukayi missing dinta a family nasu, bataji horn din motaba saidai jitayi anbugeta da ita har saida tafadi kasa,

Saijitayi anja motar da karfi kowaye yyi tafiyarsa, saibiyar motar tayi da ido tana mamakin shi kuma wnn waye da xaibugeta da mota kuma yyi tafiyarsa,

Safeena ce taxo wucewa ta wurin taga abunda ke faruwa, ta sauri ta karaso wurin takamata, ta Taiyida ita tsaye, tana kakkabe mata jikinta, sannu kinji, ina fatan bakiji ciyoba?

Taiyi murmushi banji ciyoba yar'uwa nagode

Safeena xata wuce kenan sai kuma tasawo tana tmbyarta, don Allah yar'uwa meye sunanki?

Bilkisu tayi murmushi tana kallonta, sunana bilkisu abdulrahaman yola.

Safeena tace in kuma sunana safeena Ahmad Kano, dafatan zamu zama qawaye.

Bilkisu tayi murmushi tace, ba matsala Allah yabarmu tare.

Writting by Ummu safwan luv u all😘😘😘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

A wata masarautar....
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

Writtin by Ummu safwan 07066214433

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.