Complete Hausa Novels

A Wata Masaurautar Complete Hausa Novel

Reading file: A_Wata_Masaurautar_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 19 of 39

Page2Γ’Ζ’Β£2Γ’Ζ’Β£

Tafiya sukeyi, bakinta a d'aure, idanunta sai zubarda hawaye sukeyi."
Saida suka shiga wata unguwa wadda babu hayaniyar mutune a cikinta." Unguwar tsit kakeji kamar babu bel'adamar dake rayuwa a cikinta."

Parking yayi a dai dai wani katafaren gida, wadda babu kowa a cikinsa."fitowa yayi ya bud'e get dakansa sannan Yashigar da motarsa a ciki."

A guje yanufi wurin ajiye motoci."
Tsayawa yayi yabud'e murfin mota ya fito."
Ya zagaya wurin zaman Bilkisu sai zubarda hawaye takeyi."
Ya finciko hannuta da k'arfi yafito da ita, jaye yake da hannunta, harsuka k'arasa shiga cikin gidan."

Wani d'aki yanufa da ita, wadda yake ya motse.
kaya ne ko'ina a watse."
A ranta tace turk'ashi yau dai Allah kad'ai zai fissheni a hannun mugun mutumin nan."
Gashi k'azamin banza, duk k'asaitarsa, dawani kwalliya tasa, ashema gidansa babu komai a cikinsa sai k'azanta."

Ya katsemata tuninta dayace zaki fad'amin inda Abdullah yake ko saina aikata abinda nayi niya a kanki."?

Inkasheki inkashe banza." Domin babu wadda yaga a lokacinda na d'aukoki, bare kiturowa mutane banzayen fadawanki masu kama da samudawa."

Magana yakeyi idanunsa sunkad'e sunyi jajir, cikin b'acin rai yace bazaki bud'i baki kiyi magana ba bare kifad'amun a 'inda kika kaimun Abdullah."

Bilkisu sai kallonsa take sama da k'asa, domin ita a yanzun Allah ya ciremata jin tsoransa a rayuwarta."

Shima ita yake kallo cikin mamaki,
Tace "karyane wlh baka isa kakashiniba sai dai idan lokacina ne yayi."
Abdullah bazan fad'i inda yakeba harsai ka d'an d'anni bak'in cikin daka sanyani na tsawon wani lokaci."

don hka kabani hananya nafita nayi tafiyata, tunkafin warin wannan d'akin yayimun illah."

Cikin b'acin rai yanufuta a fusace, ya had'a bayanta da bango hannunsa a kwalar rigarta ya matseta yana ce mata.
"Ina Abdullah? Iyee ina Abdullah nace?"

Tafita hanyacinta don tsabar tsoro da firgitar abunda yayimata a rayuwarta babu namijin daya tab'ayi mata abinda yayi mata yanzun."
Ta runtse idanunta hawaye na fita daga idanunta,
Ya k'ara matseta ya kuma matso da fuskarsa daidai tata yana wani huci, zakifad'amun inda Abdullah yake ko saina kasheki?"

Ta katse shi dacewa, "hannunka a k'irjina!" Ta fad'i hakan cikeda shagwab'a kuma cikin sanyin murya wadda ke k'unshe da wahala."

Besan lokacinda ya saketaba, dashima ya gano hannunsa a kan k'irjinta yake."
Ya ciji leb'ensa na k'asa a ransa kuwa haushinta ya k'ara kamashi so take tayi suducing d'inshi?"
Tambayar da yakeyiwa kansa kenan,
Lallai yarinyar nan tayi nisa, ganinta zata iya jan hanlinsa ne kome take nufi?"

Duk Kansa yakeyiwa wad'an tambayoyin, a zahiri kuma yanunata da yatsa yana Jamata kunne kokifad'i inda kikai Abdullah ko na d'aukar maki kwankwaran mataki a kanki yanzun nan."

Karfin hali tayi domin ta tsorata da ganinsa cikin wannan yanayin, idanunsa sunkad'e sunyi jajir
Tace "malam kabud'emun k'ofa nafita bana iya k'ara minti d'aya a cikin wannan k'azamin d'akin.
Tanufi wurin k'ofar da niyar tabud'e tafita, saiji tayi ya fisgota ya had'ata a bango ya matseta gam ajikinsa, saiwani numfashi yake fitarwa kamar wani zaki."

Tuni hankalin Bilkisu yatashi, tarufe idonta, tana fad'in SUBHANALLAHI!"

Ina kikasanta? Ashe kinsan Allah?"
To wlh duk Baki fad'i Inda kika kai Abdullah ba zakiyita zama a nan gidan,
Har sai ranar da kikafito da Abdullah sannan kema nasakeki,
Muguwa kawai, aibashi yayi maki laifiba, ni ne nayaki laifin, meyasa bazaki d'auki mataki a kaina ba sai a kansa?" Kina tunin ninafi k'arfinki kenan shiyasa zaki sanya samudawan fadawanki sutafi da Abdullah

Kisakesa mana, ni sai kisanya a kamani."

Magana yakeyi amma bata tankashi,
Ya kuma kuluwa, yajaye a bakin k'ofar d'akin yaturata a kan katifa,
Yabud'e k'ofar d'akin yafita, yasanyawa k'ofar key yayi tafiyarsa ya barta nan."

Bahijja da Fahad soyayya tayi nisa domin har ansanya ranar da maimartaba zaitafi yola neman auren Bahijja k'arshen watan nan."

writing
By
Fareeda
BashirÒœðŸ»
Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜

A WATA MASARAUTAR.......

Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜

Writing by
Ummu
Safwan

PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.