A Wata Masaurautar Complete Hausa Novel
Reading file: A_Wata_Masaurautar_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 9 of 39
Page Γ°ΕΈβΕΈ
Kamasa sukayi, suka sanyashi a mota, suka nufi gda dashi,
A bakin get direba yayi horn, maigadi ya budemasu get, suka shigar da motar sannu a hankali sbda kar yarima yaji ciyo, parking space suka nufa suka'ajiye motar, fadawa suka nufosa, suka kankamasa sai sannu suketa yimasa.
Nuni yayi da hannu, alamar susakesa. sakinsa sukayi, sai sannu sukeyimasa.
" tafiya yakeyi kamar wadda akayiwa kaciya, domin shi kadai yasan abunda yakeji a jikinsa.
Dakyar yasamu ya shiga gda.
Bebi takan kowaba, kai tsaye sakinsa ya nufa, yafada a kan makeken gadonsa, ya kwanta rumda ciki,
Sai a lokacin yakejin wasu hawayen wahala nafitomasa,
Tunani yakeyi, irin hukuncin da xaiyimata, tabbas xan hukuntaki, hukunci mai tsanani, xan ladab"tardake, wadda ko makiyinki sai ya tausayamki, xanunamki cewa babu wadda ya isa yataba, "yayan sarauta ya kuma xauna lfy,
Shikadai yake surutunsa, kamar wani zautance,
Bilkisu kuwa yana barin wurin, taja hannun safeenat suna dariya, tana fadamata yanda abun yafaru, sai dariya sukeyi,
"Mutane kowa fadin albarkacin bakinsu sukeyi, wa "dansu na jinjina mata, wa "dansuwa na ginta,
Mafiyawan masu xagin nata duka matane, wa "danda suka mutu a kan son sa.
Yau gdan cike yake da yan"uwa da abokanin arxiki,
Domin uwar"gida sarautar mata, wato hajiya nafeesa, ciki kegareta, wata bakwai, amma babu wadda yasani,
Domin tana ganin kamar rashin haihuwarta yanada nasaba, ga hajia maryam mahaifiyar adnan.
Gashi tadau burin duniya ta daurashi a cikin, lokacinda ta fahimci tana da cikin,sai ta tsiri tafiya garinsu, bata dawoba saida cikin yakai wata bakwai, don hka ko sarki,
bata fadama tanada cikiba, sai yau dayakai wata bakwai,
Sarki yayi murna sosai, don hka ya gayyato "yan'uwa da abokanen ar'xiki, domin atayashi murna.
Ba sarki ba, har maman su adnan tayi murna da samun cikinta,
Amma duk da hkan. hajia nafeesa, cewa takeyi, duk munafurci ne, ba"kin ciki takeyi, da cikin.
Ita dai batabi takantaba bare tabiye mata.
Shine fa, taga shiguwar, Prince cikin fushi, yana tafiya kamar wadda kwai yafashema a ciki,
Ai kuwa babu abunda tashiga fadi, sai dan "bakin ciki, mai irin rayuwar uwarsa, yaji labarin inada ciki, shine ya shigo rai "bace,
To komai ba"kin cikinka, sai na haifi muslimu a gidan nan, domin shima ya hau karagar mulki,
Masifa taketayi ita daya, kamar wata xaranriya,
Shi dai prince yana dakinsa, duk abun duniya ya damesa, sbda bakin ciki ko kayan jikinsa be cireba,
Sai mganar zuci yakeyi,
Kamar ni prince d'an d'an sarki a'ce, wata "yar matsiyata take yiwa abunda taga dama? xunbur ya mike tsaye, kamar wadda wani abu ya tsikara, sai safa marwa yakeyi,
Yana tunanin, ita wace ce?
Dame take ta'kama?
Waye ubanta a garin nan?
Dolene nayi bin cike a kanta, domin na tabbatar da ko ita wace ceΓ°ΕΈΛΒ‘
Koma yayi ya kwanta, rumda ciki, idanunsa sun rikede sunyi jajir , sai tunani yakeyi, ta ina xaifara bincin.
Sannan idon yagano asalinta wane hukunci zaiyi mata?
Wadda saitayi dana sanin, saninsa, a' rywa
Written by Ummu Safwan. Luv u allΓ°ΕΈΛΛΓ°ΕΈΛΛ
Γ°ΕΈββ Your Γ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββ
A WATA MASARAUTAR....
Γ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββ
Writing by Ummu Safwan 07066214433
Pure moment of life
Writer's (P.M.L)
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.