A Wata Masaurautar Complete Hausa Novel
Reading file: A_Wata_Masaurautar_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 28 of 39
page 4⃣1⃣ 4⃣2⃣
WANNAN PAGE D'IN NAKUNE DOMIN JIN DAD'INKU MEMBER'S OF PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S, ALLAH YAK'ARA HAD'A KANMU YATSAREMU DA SHAIRRIN MAHASADA🙏🏻🙏🏻
Gimbiya Bilkisu Sunshigo garin Kano lafiya tareda fadawanta,
Gosulun motoci ne ya tsayardasu a kan titi sun d'auki kusan minti 10 sannan sukasamu gosolun ya tsagaita sukawuce,
Tafiya sukeyi saigani sukayi wata mota na biyarsu a baya,
Fadawa sune suka lura da hakan
Suka fad'awa Bilkisu, domin tambayi umurninta su tsaya suga kowaye ke biyarsu?" kosu cigaba da tafiyar da sukeyi?"
Tabasu umurni da karsu tsaya,
Watak'ila basu yakebiyaba.
Harsuka k'ara masaukin Bilkisu, suka tsaitsaya."
Shima wadda kebiye dasu ya tsayar da motarsa a daidai wurin da suka tsaya,
Fadawa sukanufesa da alamar tambaya a fuskarsu, Bilkisu ce ta dakatardasu,
Dacewa "kubarshi ya k'araso muji abunda ke tafedashi.
K'arasowa yayi dai dai a kusa da ita, Fuskarsa kan Bilkisu yana murmushi,
Kallon mamaki tabishi dashi tana tunanin a ina tasan wannan fuskar?"
Cigaba yayi da kusantota da murmushi a kan fuskarsa,
Ganin hakan dayakeyi,
Fadawa basujira umurninta ba sukayi saurin dakatardashi,
Suka had'a baki gaba d'ayansu, suka
Dakata d'an talakawa.
Mundad'e muna sanyamaka ido kana bibiyarmu tun a kan hanya,
Meke tafe dakai?"
Bilkisu tayi saurin dokawa fadawa tsawa, tace "banason hakan banason ana wulak'anta d'an adam a gabana,
da talaka da mai kud'i duka Allah ya haliccesu, indai ina taredaku karna kuma jin kunyiwa kowanne mutun wannan kalamin,
Kubarshi ya k'araso nace, domin naji abunda ke tafedashi,
Bilkisu na magana amma kallonta yakeyi cike da sha'awa, bedamu da abunda fadawa sukayimasa ba,
Ya k'arasa kusa da ita yace "gimbiya Bilkisu halayarki suna burgeni suna kuma bani sha'awa,
Saboda kyawawan halayarki yasanya nake bibiyar rayuwarki domin ganin nacinma burina a kanki na aurenki,
Da farko sunana Zaharandin Mansur nid'an minister garin nanne,
Tun lokacinda nad'ora idona a kanki Allah yasanyamin sonki a rayuwata,
Bilkisu kyawawan halayanki sune suka kuma dasamun wutar sonki a rayuwata,
Harnakai bana iya ganin kowace mace a duniya sai ke,
Pls Bilkisu ki amshi soyayya ta wlh nayimaki alk'awarin bazan tab'ata wulak'antakiba
Zankula dake zanriritaki a cikin Mata,
Zaki zamo tauraruwa a cikin taurari,kuma nayimaki alkharin bazan tab'a yimaki kishiyaba, pls Bilkisu ki amshi soyayyata.
Bilkisu kallo tabishi dashi cike da mamaki ganin yanda ya katse sai zuba zance yakeyi,
Tajuya ta kalli fadawanta take tsaye suna kallonsa,
Tayi masu nuni da suyi tafiyarsu saitanemesu, suka shiga motarsu sukayi tafiyarsu.
Ta maida kallonta a xaharandin tayi murmushi tace "nagode da k'aunar da kanunamin,
Hak'ika naji dad'in soyayyarka gareni,
Domin inason mai sona a duk inda yake,
Ta kalli agogon da ke hannunta, tace kayi hakuri sai wani lokaci domin yanzun lokacin cin abincina yayi,
Gashi kuma yanzun nadawo daga tafiya,
Tajuya zata shige gida kenan,
Sai hango Prince tayi a tsaye a bakin motarsa tareda Abdullahi
Adanunsa sun kad'e sunyi jajir, jikinsa wani cincira yakeyi yana rawa, saboda b'acin rai,
Abdullahi ne rik'edashi yana lanlashinsa had'ida bashi magana,
Bilkisu ganinda tayimasa a tsayen saida gabanta yafad'i, domin tasan ba alkhari bane yakawosa,
Ya k'arasa wurin zaharandin yarik'emasa kwalar riga yana fitar da huxuci kamar wani zaki,
Yanafad'in " meyakawoka wurin matata?"
Wani dalili zai sanyaka zuwa neman aure cikin aure,
Domin Duk maganganunda kake furtamata a kan kunnena yake.
Ya kuma cacumo masa riga, saida idanun zaharandin suka firfito waje, akan jinzafin rik'on da Adnan yayi masa,
Yace gargid'i nake maka ba umurniba,
Duk lokacinda nakuma ganinka a k'ofar gidan nan,
Ko kuma na kuma ganinka tareda Bilkisu saina b'atarda kai daga lokacin ba mai kuma ganinka."
Ganin rik'on da prince Yayiwa zaharandin yana neman kashesa,
Cikin yanayin tashin hankali tak'arasa kusa dashi
Tasanya hannunta tabuge hannun prince daga wuyan rigar xaharandin
Tace "sakesa Adnan waime hakan?"
Idan ka kashesafa?"
To bari kaji zaharandin shine Mijin da zan aure, kuma shi nakeso a rayuwatah,
Kuma kasani daga yau duk wani abu yasameshi,
Kaima baza'abarkaba sai anhukuntaka,
Domin furucin dakayi yanzun shi zai d'aureka har lahira.
Da kuma kake i'k'irarin ni matarkace waye ya d'aura mana aure dakai,
Allah ya tsareni da aurenka dana aureka k'ara na tabbata banyi aureba,
Domin babu komai ataredakai sai tsabar mugunta,
Da kuma wulak'anta talakawanka."
Ta juya wurin zaharandin da yayi tsaye yana kallonsu idonsa yayi jajir d'in wahala,
Tace "my love yi hakuri shiga motarka kayi tafiyarka, sai munhad'u a makaranta gobe saimu iyar da maganarda mukeyi,
Tabud'e masa murfin motar
Tayimasa nuni da hannu da yazo yashiga
Yaji dad'in irin karamcin da tayimasa a gaban Adnan,
Murmushin dole ya k'ak'aro yazo zaishiga motar yace "my one and only kikulamun da kanki,
Naji dad'in kulawarki a kaina luv u
Tace "luv u 2
Yashiga motarsa yayi tafiyarsa yana mai d'aga mata hannu
Itama hakan.
Duk abunda sukeyi a kan idon Adnan, jiyake kamar ya had'iye zuciya ya mutu saboda bak'in ciki.
juyawa yyi yanayiwa Bilkisu magana yana fad'in "Bilkisu tsaya kiji abunda ke tafedani alkhairi ne wlh ba muguntace taka woni wurinki ba.
Ko sauraransa batayiba tayi tashegiwarta gida."
Writing by Fareeda Bashir✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
A WATA MASARAUTAR......
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
Writing by
Ummu
Safwan
PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.