Complete Hausa Novels

A Wata Masaurautar Complete Hausa Novel

Reading file: A_Wata_Masaurautar_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 16 of 39

page1⃣9⃣

A haka barci b'arawo yayi awun gaba da ita."

Shiri takeyi domin tafiya makaranta, domin tunda asuba Abba yakirata a waya yake shaida mata, fadawan da yaturo mata sunkunsan k'arasowa ."

Shiri take a gurguje, saiga Safeena takawo masu breakfast dinsu, kallon agogon hannunta tayi, tace "sis kinsan lokacin cin abincina beyiba sai zuwa anjima zanyi breakfast,
Kifito kawai muk'arasa makaranta karmu makara.

Safeena tace "to bara na d'auko mayafina, ta ajiyewa jakadiya abincin tajuya tafita."

Tafiya sukeyi suna fira ita da safeenat, d'alibai sai nunata sukeyi suna magan ganunsu, bata kulasuba, class tanufa domin d'aukar karatu,

Fitowarsu kenan daga class, Bilkisu tasamu wuri tazauna, tare da safeenat a kan wasu fararen kujerun roma,
Suna diba littatafansu, sai ganin prince tayi a gabanta tareda Abdullah sai wani huci yakeyi,
Kallon tsana yabita dashi yace "ke 'yar matsiyata waye yabaki izinin zama a kan wad'an nan kujerun."?

Nakoreki a garin nan ashe bakitafi bako?
To yau zanyimaki kurar kare,
sai anrakamun ke kibar garin nan saboda na tsaneki banason ganin fuskarki mai kama da aljanu, muguwa kawai,
yakai dibansa a k'afarsa data kumbura yace kinyi nasara kinyimun illah to kisani kafin nasanya ayimaki rakiya kibar garin nan kema sainayi maki illah wadda ko mak'iyinki sai ya tausayamaki."
Abdullah yace " bazaki tashi a kan kujerar anamaki magana ko kallon mutane bakyayi,mai sunfar muna fukai,
ya sanya hannu ya zame kujerar da take zaune saida tafad'i k'asa."

Ranta idan yayi dubu ya b'aci idanunta cike da hawaye ta d'aga kai ta kallesu, samada k'asa bata tankamasu ba, saima sunkuyarda kanta ta kumayi k'asa tana zubar da hawaye."
Safeenat ce kejan hannunta, alamar subar wurin, amma tayi tsaye tak'i d'agawa daga inda take."

Sai jiniya suka jiyo a bayansu, da bushe bushe irin na sarakuna, motocine keta shigowa cikin makarantar sunfi talatin, aikuwa kallo yakoma Kansu kowa mamaki yakeyi, ko bak'i sukayi a makarantar ne."? wasunsu na fad'in wanan sarki wane garine yakawo masu ziyartar bazata,
Prince kuwa naganinsu yabisu da kallon burgewa yanda suke busa da jiniya, yasan ko gaba da gabanta a sarauta."

Gimbiya Bilkisu na ganinsu tayi murmushin jin dad'i, sun iso a dai dai lokacinda take da buk'atarsu.

Prince sai kallon motocin yakeyi yaga sunk'i k'arewa sai shigowa sukeyi gwanin ban sha'awa."

Be ankaraba sai ganinsu yayi a gabansa sun tsaitsaya mamaki yashigayi,

Gimbiya Bilkisu tashi tsaye tayi tasamu wuri ta zauna a kan kujera, ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya mulki da sarautar ya motsa, Safeenat sai kallo tabita dashi tana mamaki,

Fadawan kowanensu yafito a mutarda yake a guje suka runsunawa Bilkisu suna kwasar gaisuwa had'i dayimata kirari, "Allah yataimake, Allah ya tsaremana lafiyarki, hak'ika masarauta tayi rashinki, ranki ya dad'e gamu, sarki ya turomu kina buk'atarmu a kusa dake,

Bilkisu dake kan kujera ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya, ta maida kallonta agun prince da duk yawani rud'e sai mamaki yakeyi,yana tunani a ransa to ita wanan wacece?
shi kuwa Abdullah sai goge zufa yake, domin yafita hanyacinsa gaba d'ya.

Ta maida kallonta a fadawan tayimasu nuni da hannu alamar sutashi,
Da Sauri suka mik'e tsaye, Suna mai jiran umurninta.

Shikuwa Prince da Adnan saboda rud'ewa rik'e yake da hannun Abdullah suna k'okarin Barin wurin,
Dalibai da malamai duk sunzagayesu sai kallon mamaki sukeyiwa Bilkisu."

amma banda shugaban makarantar domin yasan ko ita wacece."

K'okarin barin wurin sukeyi Prince da Abdullah tayiwa fadawa nuni da hannu da su tsayar mata dasu,

Aikuwa a guje suka sha gabansu, suna fad'in gimbiya ke buk'atar mgna daku,
Prince ya kalli kansa yace wacece kuma gimbiya?
Kusan kodawa kuke magana kuwa? Yanuna kansa da hannu."

Duk abunda sukeyi akan idon gimbiya, tayi murmushin mugunta."

Gimbiya Bilkisu tace ina sarki hukunci? Yamike tsaye yace gani ranki ya dad'e."

Sanan ta kuma cewa ina sarkin gishiri."?
yace "gani rankin ya dad'e."

"Tayi masu nunu da Prince da Abdullah dake tsaye suna musu da fadawa,

Tace " kud'aukomun wad'ancan yaran masuyimawa mutane gardama."
Suka runsuna sukace angama ranki ya dad'e

Prince da Abdullah na tsaye saiji sukayi and'aukeso sama, ba'a diresu a ko inaba sai a gaban Bilkisu dake zaune a kan kujera."

sarkin hukunci yace ranki ya dad'e gasu."

tayi nuni da hannu alamar subar mata su a nan, 😊

Ta kallesu sama da k'asa tayi murmushin mugunta,
Tace prince Adnan ina mulkinka yake? Ina sarautarka take? Kana amfanida mulkinka da kuma sarautarka kana taka talakawanka yanda kakeso."
bakasan irin baiwar da Allah yayiwa wani a cikin wad'anda kake wulak'antawa ba,
To gani gabanka kana i'k'irarin zakasanya fadawanka suyimun korar kare a garinka,
Kana i'k'irarin zaka wulak'antani, wulak'anci mai tsanani.
Ba dan komai kakeyin haka ba, sai dan kana yarima d'an sarki,
A yanzun zan nunamaka ko a sarautar, gaba da gabanta,
Zan nunamaka mulkin wata masarautar yafi mulkin masarautarku."

Tace "ina sarkin hukunci yace "gani ranki yadad'e, tanuna Abdullah tace " meye hukuncin mekatsalanda a magana."?
sarkin hukunci yace "bulala hamsin,ne gimbiya

tace sarkin hukunci ayimasa bulala d'ari gamida hukunci mai tsanani."

Yace angama rankin ya dad'e."

Abdullah najin anbaci bulala d'ari saida yasaki fitsari a wando d'alibai sai dariya sukemasa, dama addu'a sukeyi Allah yakawo masu k'arshin zaluncin prince a makaranta,

Abdullah ya kalli prince dake durkushe a gaban Bilkisu, yace "aiga irinta nan saida nafad'amaka ka kyale yarinyar nan amma ka kafe saitabar garin nan, yanzun gashinan kadazamun bala'i."

Ya runsuna a gaban Bilkisu yace ranki ya dad'e kiyi hakuri natuba wlh ko kallonki baza kuma yiba, kice a sansautamun hukuncin nan, wlh bazan sakeba."😊

Bilkisu tayi masa wani kallo sama da k'asa
"Tace wai mekuke jira dashine? Kunbarshi yana damuna da suruto." aikuwa aka tungumi Abdullahi akasanyashi a mota, yana kuwa ya komai, duk yajik'e wandonsa da fitsariπŸ™Š

Ta maida kallonta a kan prince, tace "natsaneka kamar yanda kaima kake i'k'irarin ka tsaneni, bana buk'atar ganin fuskarka,
Tace ina sarkin gishiri? yace "gani ranki ya dad'e tace asanyashi a mota a tafi dashi, a horashi a koyamasa yanda ake daraja d'an adam a duk inda yake."

Ummu safwan😘😘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

A WATA MASARAUTAR....

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

Writing by
Ummu
Safwan

PURE MOMENT
OF LIFE WRITER'S

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.