Complete Hausa Novels

A Wata Masaurautar Complete Hausa Novel

Reading file: A_Wata_Masaurautar_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 26 of 39

Page 3Γ’Ζ’Β£6Γ’Ζ’Β£ 3Γ’Ζ’Β£7Γ’Ζ’Β£

Bilkisu ta sauka garin yola lafiya,
Inda dukkanin wad'anda ke cikin gidan masarautar yayi murna da farin cikin dawowarta.

Bayan tayi wanka tashirya taci abinci, ta sauko k'asa tanufi sashen maimartaba domin taji Neman da yakemata,

Ta Tarar da maimartaba kishin gid'e a kan kujera,
Tayi sallama tashiga.
Tasamu wuri a k'asa gefen k'afarsa ta zauna, ta sunkuyarda kanta k'asa tace "Allah ya taimakeka Allah ya k'ara maka lafiya,
Gani nazo ranka ya dad'e Allah yasa ba laifi tanayiba,

Maimartaba yayi murmushin nan irin nasu na manya,
Yace "aibakya laifi Bilkisu,
Domin kina kiyaye duk wani abuda kikasan zaib'amun rai,
Dan haka nafifitaki a cikin 'ya'yana.

Wato Bilkisu wata shawara nakeso muyidake wadda maganar waya bata isa,
Saikinzo gani gaki.
Bilkisu kinsan d'an sarkin kano,
Fahad shiyakeson Bahijja,
Ta girgiza kai.
To satinda yawuce mahaifin yaron wato sarki Bashir, yazo da kansa ba aike yayiba,
yazo neman aurenku keda Bahhija.
Saida gaban Bilkisu yafad'i

Yaci gaba da cewa Kema d'ansa Adnan yaganki a makaranta, yanunamun dacewa, harkun fahimci junanku, dan hakan nayanki hukunci aurardaku gaba d'ayanku keda Antynki Bahijjah.

maimartaba magana yakeyi amma gaba d'aya hankalinta bayajikinta, musamman dataji ya ambaci yabadasu gaba d'ayansu,
Idanunta ne suka cika da hawaye tasunkuyarda kanta k'asa yadda Abbanta bazai iya ganin hawayentaba,

Maimartaba tunda yafara yin magana yake kallon yanayinta yalurada lokaci d'aya tacanza masa daga k'arshe hawaye take zubarwa,

Yace subahanallahi Bilkisu laifi?"
Meyasanki zubarda hawaye?"

Goge hawayenki kidaina kuka,
Idan maganar aure ce bakyaso daki zubarda hawayenki k'ara afasashi,
Nima abunda yak'arabani kwarin gwaiwar yimasa alk'awalin badake, yazomun da mgnar cewa kunfahimci junanku a makaranta dake da yaron.
Amma wallahi Bilkisu mundun bakyaso to alk'awari ne bazan maki auren dole ba,

Kanta a sunkuye k'asa sai zubarda hawaye take,
Gaba d'aya tausayin mahaifinta duk yagama lunlub'eta, a zuciyarta,
Wato domin ya faranta mata rayuwa yana iya ruguza alkharin dayayiwa sarki Bashir nabayardasu dayayi gaba d'ayansu,
Abba idan yayi haka kuma har abada sarki Bashir bazai kuma yarda da maganarsaba,
Sannan kuma idan yayi hkan, yaya k'auwarsa sarki bashir Amminmu zaji dad'i wadda suke uwa d'aya uba d'aya, da sarki Bashir,
Zai iya zamantuwar rugujewar zumcinsu,

Maimartaba yace "gimbiya Bilkisu kenake saurare, kukan da kikeyi nameye?"

Takuma sunkuyar da kanta k'asa tace"Abba karatuna banaso nayi aure batareda na kammala karatunaba,
Abba inaso nayi karatu sosai domin nataimaka 'yan uwana mata takowace hanya,

Abba yace "nasan kudirinki a kan karatunki, gimbiya Bilkisu,
Nayiwa sarki Bashir bayanin karatunki,
Yace zai tambayi Adnan d'in idan yaji yagani ya amince zaibarki idan akayi auren saikici gaba da karatunki
Idan kuma be aminceba to lallai bazan auran dakeba sai bayan kin kammala karatunki har lokacinda burinki yacika, gimbiya Bilkisu,

Murmushin dole ta k'wakwalo tayi, had'ida kallon mai marmarba,
Tace nagode Abba,

Yace "goge hawayen kitashi kitafi kikwanta kihuta nasan kinsha gajiyar hanya,

Tamik'e tsaye had'ida yimasa sai anjima,
Tafita daga d'akin,
Tafiya takeyi kamar wadda kwai yafashewa a cikin domin gaba d'aya batacikin hankalinta, da kyar tasamu ta isa d'akinta cikin mawuyacin hali.

Akan gadonta tafad'a tasaki wani wahalallen kuka mai tsuma zuciya,
Tana magana ita d'aya kamar wata zaranriya,
Ashe dama Adnan d'an uwanane yake wulak'antani hakan?"
Meyake nufi da turowa Neman aurena?"
Wani sabon salon wulak'anci dacin zarafi zaikuma yimun bayan ya aureni?"
Domin a bakinsa yasha furtamun bayasona, bayason ganina,
Me kama danima idon ya ganta sai ya hukuntata,
Sannan ace da wannan zanyi rayuwar aure?"😭
Takuma b'arkewa da wani sabon kuka mai tsuma zuciya,
Tana danasanin had'uwarta da Adnan a rayuwarta gashi yanzun yana neman ruguzamata rayuwa."

Adnan kuwa gaba d'aya yasusuce baya da maganar kowa sai ta Bilkisu,

Anty Bahijja ke k'ara kwantar masa da hankali akan cewa Bilkisu insha Allahu takusan zama matarsa,

Likita ya turo k'ofa yashigo had'ida yimasu sallama yanufi gadon Adnan domin ya ciremasa rubar jinin da ke hannunsa,
Doctor yakai dibansa ga Adnan yayi murmushi yace " Adnan angon Bilkisu ina fatan ba abunda kemaka ciyo domin munasan ran sallamarka nan da zuwa gobe,

Adnan kwance yake amma jin doctor ya ambaci Bilkisu yayi zumut ya mik'e zaune,
Yana murmushi yace doctor kokasan Bilkisu ne?"
Kaga mundace da juna ko?"
Gata fara kyankyanwar yarinya mai dogon hanci, ga k'aramin baki,
Yace "doctor kaga Bahijja yayi nuni da Bahijja yace kamarsu d'aya da Bilkisu na,
Amma Bilkisu tafita kyau,

Gaba d'ayansu dariya suke masa ganin yanda soyayyar Bilkisu ta kusa zautar dashi,

Bahijja tace, ayye Adnan yanzun Nice Bilkisu tafini kyau?"
To lallai bazan baka aurantaba nafasa,

Aisai ganinshi tayi durk'oshe a gabanta rik'e da k'afafunta, yana fad'in "yi hakuri Anty Bahijja ki aura mun Bilkisu wlh idan narasa Bilkisu zan iya rasa rayuwata,

Sai a kunnen maimartaba, yace bazaka rasa ranyuwarka ba Adanan indai akan Bilkisu ne domin munyi mgana da mahaifinta yabaka Bilkisu amma dasharad'in sai ta kammala karatunta."

Writing by
Ummu
Safwan
Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜

A WATA MASARAUTAR.....

Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜

Writing by
Ummu
Safwan

PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.