A Wata Masaurautar Complete Hausa Novel
Reading file: A_Wata_Masaurautar_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 5 of 39
Page5Γ’ΖΒ£
A fusace yakoma gida, duk inda ransa yake yabaci, fadawa sai kwasar gaisuwa sukeyi amma baya kulasu,
Dakinsa yafada kai tsaye, a kan makeken gadonsa ya kwanta sai faman ajiyar xuciya yakeyi, xumut yamike tsaye kamar wadda wani abu tsunkulesa, sai safa da marwa yakeyi, yana tunanin irin abunda bilkisu tayi masa, a rywarsa babu wani wadda yatabayimasa irin wulakancin da bilkisu tayimasa, tabbas xan dauki mataki a kanki xan nunamaki cewa kin tabo jinin sarauta, domin sarauta bawasa bace,
Tafe take cikin farin ciki da annashawa, sai murna takeyi domin rayuwarta tayimata dadi, domin tarama wulakancin da prince yayi mata sai bawa safeena labari takeyi tana dariya.
Saiji tayi anjanye mata mayafi a bayanta wai gawatayi a fusace, sai ganin fadawa tayi kowanensu da katuwar bulalarsu a hannunsu, suna kallonta yarima yace axomasa dake yar matsiyata.
Kallo tabisu dashi cikin mamaki, batada alamar motsawa daga inda take, ganin batada alamar tafiya suka suma yunkurin daukarta.
Wata irin tsawa takatsamasu wadda kowane daga cikinsu saida yashiga hankalinsa, domin suma sun fahimci wani abu atareda ita,
Kallonsu takeyi sama da kasa, duk wanda ya kuskura yataba mun jiki to wlh kusani duk sai kungane kurenku, ta kuma dallamasu harara
Duk abun nan dayake faruwa a kan idon yarima, shima mamaki tabashi, ta yanda take iya katsawa fadawa tsawa, shidai a iya saninsa duk wadda yayi ido biyu da fadawa sai hankalinsa yatashi musamman idon ba'a gidan sarauta yakeba, shiyasa yaturomata su domin sutafi da ita, mamaki yakeyi to ita wacece?
A fusace yafito motar yaja hannunta da karfi tana kokarin kwacewa amma takasa, ya bude murfin motar ya turata ciki yamayar yarufe yaxagaya maxaunin direba yashiga yaja motar da kafi yabar makarantar da ita
Luv allΓ°ΕΈΛΛΓ°ΕΈΛΛ kuyi hkri da wnn
Γ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββ
A wata masarautar....
Γ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββ
Writing by Ummu Safwan 07066214433
Page6Γ’ΖΒ£
JINJINA GAREKI QAUWATA TAKAINA, BILKISU MUSA MAISAMARI, ALLAH YABARMUNKEΓ°ΕΈβΒΓ°ΕΈΒΒΌ YANUNAMUN RANAR AURENKI RANAR ZANKWASO
SHOKIΓ°ΕΈβΒ―Γ°ΕΈβΒ―Γ°ΕΈβΒ―Γ°ΕΈβΒ―
Tafiya sukeyi mainisa, bbu wadda ya kula dan uwansa, prince sai huci yakeyi kamar wani xaki, tuki yakeyi kamar xaitashi sama
Ganin bayada niyar tsayawa, gudu yakeyi sosai, duk tsoro ya lunlube bilkisu, juyawa tayi ta kallesa idanunta cike da hawaye,
Cikin yanayin kuka take magana, malam wai ina xaka kaini ne?
Menatare maka a rayuwa kakeson kaga kamusgunawa rayuwata?
Mekake takama dashine?
To wlh kasani duk abunda yasameni kaima baxa a barkaba,
Kuma saikayi dakasani a rywarka, idon sarauta kake takama da ita, sarautar wata masarautar tafi sarautar ku, ina mai tabbatar maka da kajuya da akalar motarka kamayardani a inda kadaukeni,
Duk masifar da takeyi be kulataba be kuma fasa gudun dayakeyiba, idanunsa sunkade suyi jajer, duk maganganun da takeyi jiyakeyi kamar tana watsamasa ruwan xafi a jiki, musamman da takecewa Sarautar wata masarautar tafi sarautarsu. Metasani a sarauta, datake fadamasa haka, tabbas xan nunamata kalar tamu sarautar, domin ta tabbatarda bbu wata sarautar da tafi tamu masarautar mulki.
Wani dogon burki yaja a dai dai wani katafaren gida, megadi yafito yabude masa get, yashigar da motarsa a guje yanufi farking space, yaja wani dogon burki wadda saida bilkisu tarufe idonta saboda tsoro, tashiga zubar da hawaye, tana maiyi masa Allah yasa a xuciyarta,
Fadawan dake gadin gdan saida shiguwarsa a guje tabasu tsoro, kasancewa kuma basusan da xuwansaba, domin idon xaixo yakan kirasu a waya yashedamasu da zuwan nasa domin a share masa gdan ka kankabemasa kura. sunynasamakin xuwansa domin ba a dai dai wnn lkcin yake xuwa gdan shakatawar nasa ba
Ganin tsayuwarsa lfy yasa suka runtumo a guje sunka sunkuya alamar girmamawa suna gaidasa tareda yimasa kirari,
Allah yataimaki yarima, Allah tsare gabanka ya kuma tsare bayanka, Dan sarki jikan sarki, sarauta gabanka da bayanka, Kaine xaka kaji mahaifinka, yarima mejiran gado, Allah ya taimakeka bamusan da xuwankaba,
Xagayemasa mota sukayi sunatayimasa kirari shikuwa, saiji yakeyi da qasaita da mulki, kasa fitowa yayi saida ya dauki minti 30 sannan yabude murfin motar ya fito,
Duk abun nan da akeyi bilkisu kallonsa takeyi, tana mamaki a xuciyarta ta yanda yakeji da mulki da isa
Da kuma miskilanci.
Koda yafito fadawa nabiye dashi, xagayawa yayi dai dai wurin xamanta, yabudemata murfin motar, beyi mata mgnaba ita kuma batayimasa, bata kuma fito a motarba,
Ya dauki minti 10 a hka, sannan ya maida kallonsa gareta, yace idon bazaki fitoba xansanya fadawa su daukomun ke akai, sushigomun dake,
Yana kaiwa nan yajuya yayi tafiyarsa, ganin yasoma tafiya yasanyata fitowa domin yana iya sanyawa a dauketa din tunda ba imani ke garesaba,
Tafiya yakeyi tana biye dashi. Domin ita koda xa'a kasheta batasan a inda takeba,
Wata kofa yanufa,tana biyedashi shiganta kofarke dawuya taganta cikin wani katafaren pallow na alfarma pallow yyi kyau sosai amma duk da kyau pallow baxai rudetaba domin tasaba ganin fiye da irin wnn
Tsaye tayi abakin kofar taki Shiga ciki,
Shima tsaye yyi yana kallonta, beyi mata maganaba, saifama yakeyi da mulki, sunshafe kusan minti 30 a hakan, sannan daga karshe yabude baki yyi magana, idon bazaki shigoba xansanya a fadawa su daukomun ke,
Domin yanxun kinshigo fadata, xannuna maki sarauta da mulki ba abun wasabane,
Xan mulkeki yanda rai keso, domin na fahimci a gda ba'a koyamaki yanda xaki daraja masautaba, basu kuma koyamaki yanda zakibawa yayan sarauta girma ba,
Domin xan a xabtar dake yanda kikasan ake axabtarda tsintantun bayi,
Xaki xama baiwata, kuma kiyimun aiki irin na bauta, har sai kin fahimci cewa kintaba yayan gidan sarauta,
Murmushi tayimasa tareda karasa shiga daga cikin pallon, karasawa tayi kusa garesa tana maiyin murmushin a fuskarta
Xagayesa tashigayi tanayimasa kallon sama da kasa, sai daga karshe tabudemaki tayi mgna,
Adnan kake kowaye? Baka isa nayimaka bautaba, kuma bakayi martabar da xan xamemaka baiwa ba,
Dame kake takane? Kalmarka dayace kace mulki, to kai ba yarima bane face bawa, ba kuma bawan kowabane face bawana ni bilkisu ta nuna kanta
Ko kamanta lkcinda kabudemun murfin mota nafito, to kasanya a ranka tun daga lkcin kasomayimun aikin bauta,
Writing by Ummu safwan
.Ina ganin sakon ninku masoyana nagode
Luv AllΓ°ΕΈΛΛΓ°ΕΈΛΛΓ°ΕΈΛΛ
Γ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββ
A wata masarautar....
Γ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββΓ°ΕΈββ
Writing by Ummu Safwan 07066214433
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.