Complete Hausa Novels

A Wata Masaurautar Complete Hausa Novel

Reading file: A_Wata_Masaurautar_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 18 of 39

page2⃣1⃣

Gidansu Abdullah yanufa, yaci kiran number wayarsa amma a kashe, aika yaro yayi domin yakira masa shi."

Yaron yafito yake shedamasa ance yana makaranta bedawoba."

Godiya yayiwa yaron, yashiga motarsa, yanufi makarantar."

Shigarsa makarantar d'alibai sai nunashi akeyi suna fad'in gashi nan yadawo."

Bedamu da hakanba shidai burinsa yayi ido biyu da Abdullah." ya tabbatar da lafiya k'alau yake basuyimasa illah ba."

Kai tsaye group d'insu yanufa mazaje group suna ganinsa sukashiga yimasa dariya suna fad'in sai mazaje."

Ya d'aure fuska, kamar betab'ayin dariya ba."
Yace ina Abdullah."?

Suka had'a baki gaba d'ayansu sukace, "Abdullah Bilkisu tasanya an tafidashi."

What."? Tasanya antafi dashi."? Wai Metake nufine?
To wlh duk tasanya akayimasa illah,
Itama bazan bartaba."

Yakoma Yashiga motarsa yafigeta da k'arfi, ya bar makarantar."

Gimbiya Bilkisu yanzun hankalinta ya kwanta, sunshiga weekend, gaba d'aya ta manta da wani Prince can."

Hidimar komawarsu samun gidansu sukeyi, ita da jakadiya."

Wadda Abbanta ya turomata kud'i a account d'inta tasaya."

Wancan tsohun
gidan nata kuwa, tayiwa liman magana tana buk'atar a mayardashi makarantar islamiya."

liman yashiga yimata godeya da sanyamata albarka."

Gida yayi kyau dai dai gwargwado, Wadda Abbansu Safeenat ne, yazab'armata shi."

Abban Safeenat yaso ta zauna taredasu, domin a d'an zamanda sukayi tareda ita, ya fahimci yarinyace mai natsuwa da hankali." kuma batada girman kai kamar ba jinin saurataba."

Ita kuma Tayi tunanin idan prince ya fahimci a nan gidan tadawo da zama, to tabbas bazai barsuba zaisanya ayimasu wulak'anci, mai tsanani wadda ita bazataji dad'in hkanba."

Shiyasa takafe ita bazata iya zama dasuba sai dai asayamata gidanta ita da jakadiya su zauna a tare." tafi buk'atar hkan."

Sunkoma gidansu, wadda tareda ummie mahaifiyar Safeenat, da kuma Safeenat, sukaimasu rakiya, sukadinga yimasu fatan alkhairi."
Suka rabu da Safeenat acewa sai ranar monday idon sunhad'u a makaranta."

Kwana biyu kenan babu labarin Abdullah, prince duk inda yasan zaiji labarin babban Abunkin nasa kalmar d'ayace ba'a ganshiba."

Ga mahaifan Abdullah kullum sai damunsa sukeyi da yataimakesu yasanya adibo masu Abdullah wlh shikad'ai suka mallaka a duniya."

Prince bayada kwanciyar hankali, kullum tunaninsa d'aya wace hanya zaibi yadawo da Abdullah gida."

Domin ba iyayen Abdullah kad'ai sukayi rashinsaba, hardashi kansa yayi rashinsa damin bayada abokin ko amini da yawuce masa Abdullah."

kuma gashi duk halinda yahiga a sanadinsa yashigeshi."

Duk hanyarda yasan zaibi yaga Bilkisu ya bita." amma har yanzun besamu ganintaba."
Kuma yarasa a wace unguwa takoma da zama yanzun."

Har unguwarda yasanya aka karesu yatafi, amma zancen d'aya ne basusan Inda takomaba."

Sai dai yatsinci labarin tama bada gidan gabad'aya a mayardashi islamiya."

Hakan yajuya yakuma gida cikin bak'in ciki da b'acin rai."

Sai a can wani tunani yafad'o masa a rai." to ai gobe Monday
kuma yasan Bilkisu da son karatu duk inda take gobe Monday zatazo makaranta."

Yayi dariya jindad'i Yakoma gida cike da tunanin, wace hanya zaibi da ita wadda zata dawo masa da Abdullah."

Abdullah kuwa bayan fadawa sun yankemsa hukuncin da gimbiya ta umurcesu."

Sai da yayi jinya ta kwana d'aya yana mai tsinewa prince domin duk shine sillar sanyashi a wannan masifar."

Haka yacigaba da zama da fadawa tun suna azabtardashi harsuka koma tausayamashi."

shima ya kuma bayarda kansa kalar tausayin biyarsu yakeyi sauda k'afa."

ganin hakan dayake masu, yasanya suka jashi a jikinsu." sukasaki jiki dashi.'

Shi kuwa ya kwantarda hankalinsa yakashe kunne ya kwashe sirrin gimbiya
Bilkisu a bakin fadawanta."

Sabda dasun zauna basada wata fira saita gimbiya Bilkisu da irin kyawawan halayanta."

A nan Abdullah yasan ko 'yar wace masarautarce yakuma fahimci matsayinta awurin sarki."

Yau Monday Bilkisu tak'are shirinta tsaf."
Domin zuwa makaranta."
afterdress ce sanye a jikinta, ta yafa mayafinta, tayi kyau sosai kamar balarabiya."

Wayarta tad'auka takira Safeenat tace "hello sister kinshirya nabiyo tanan mutafi."
Safeenat dake kwance cikin yanayin ciyo, tace "sister banasamun zuwa makarantar nan banada lfy daciyon ciki nagwana jiya."

Bilkisu ce "subhanallah, sister Allah yabaki lfy idon nadawo zanbiyo nadiba jikin naki, sukayi sallama Bilkisu tafito tanufi makaranta."

Prince zaune a kan motarsa, yasha bak'in glass a fuskarsa."

kallon duk wadda keshigowa yake d'aya bayan d'aya."
duk wadda keshigowa makarantar a kan fuskarsa yake." fatansa Allah yahad'ashi da Bilkisu, shikad'ai yasan irin abunda yashirya mata a rayuwarsa."

A can ya hango shigowarta.'
tafiya takeyi cikin natsuwa da k'asaita da littafai rik'e a hannu ta."
Yana hangota ya duru a kan motar, ya zagaya, yashiga mortar, yafige motar da k'arfi yayi cikin Bilkisu , saida yazo gaf da ita sannan ya faka motar yafito."
Bilkisu tsaye tayi takasa tafiya sai kallo tabisa dashi."
bata ankaraba saiji tayi and'aure mata baki anturata a mota."

Writing✍🏻by
Fareeda
Bashir😘😘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

A WATA MARAUTAR..

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

Writing by
Ummu
Safwan

PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.