Complete Hausa Novels

A Wata Masaurautar Complete Hausa Novel

Reading file: A_Wata_Masaurautar_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 25 of 39

Page 3Γ’Ζ’Β£3Γ’Ζ’Β£ 3Γ’Ζ’Β£4Γ’Ζ’Β£

Dedicated to my lovely sister NA'IFA YAHAYA Allah yasauki lafiya mutafo garin Kano mukwashi shokiΓ°ΕΈΛœβ€žΓ°ΕΈβ€˜Β―Γ°ΕΈβ€˜Β―Γ°ΕΈβ€˜Β―Γ°ΕΈβ€˜Β―

Gudu yake akan titi yana motsa jininsa,
Dama haka al'adarsa take, dazar yayi sallar asuba tunkafin safiya tawaye, kafin mutune sufara firtuwa,
Prince yake gudun a kan titi domin motsa jininsa,

Yauma hakan takasance gudu yake a kan titin, saiji yayi mota ta bangajeshi, tayi sama dashi ta yafar akan titi,
Tundaga lokacin Be kuma sanin inda kansa yakeba,

Mai motar kuwa Yakama gabansa yayi tafiyarsa, yabar prince kwance cikin jini kota ina zubar masa yakeyi,

Gimbiya Bilkisu tareda fadawanta a kan hanyarsu ta barin gari,

Sun iso daidai wurin da abun yafaru,
Ganin mutane sunyi cincirindo a tsaitsaiye yasa ta kai dibanta a wurin taga mutane sun tsaitsaya alamar wani abun suke kallo,

Tayi saurin d'agawa fadawa hannu alamar su tsaya."
tabasu umurni sufita suga meke faruwa?" taga mutane tsaitsaiye a kan titi?"

Wasu daga cikin fadawan suka fito, suka nufi wurin da abunyafaru,
sukaga mutum a kwance cikin jini, anrasa mai taimakamasa."

Sukayi saurin nufo Bilkisu dake cikin mota a zaune, suna shaida mata, da cewa
Hatsarine ne yafaru ranki ya dad'e, wadda kuma abun yafaru a kansa yana buk'atar taimakon gangawa domin duk mutanen dake wurin tsoron tab'asa suke.

Tayi saurin bud'e murfin mota tafito, tana bada umurni da a d'aukeshi a nufi asibity dashi,

Nan take fadawa suka tallebesa a kasanyashi a mota suka nufi asibity dashi,
Asibitin kud'i suka nufadashi,
Bilkisu tabada ATM CARD d'inta akaciro mata kud'i ta dank'awa d'aya daga cikin fadawan kud'in, tabashi umurni duk abunda ake buk'ata yayi amfani da kud'in asaya.
Takoma warta mota tayi zamata tareda jakadiya."

Likitoci suka kawowa prince taimakon gangawa, suka tallabesa suka nufi d'akin da za'a dibashi.

Prince kwance cikin jini kamar bayada rai saiwani numfashin wahala yake fitarwa,
Likitoci tsaitsaye a kansa domin ceto rayuwarsa,

Babban likitan yabada umurni da akiramasa d'aya daga cikin wad'anda suka kawosa,

Fadawa suka nufi ofishin likita yake shaida masu majinyacinsu yana buk'atar asanyamashi jini da gangawa,
Idan ba hakan ba yana iya rasa rayuwarsa a kowane lokaci, domin jininsa yakusan k'arewa ajikinsa,

Dan haka aje cikin 'yan uwansa a nemo wasu daga ciki wad'anda jininsu yayi daidai danasa sai a d'ebeshi a sanya masashi,

Fadawa suka fito suka nufi wurin gimbiya Bilkisu suna shaida mata abunda likita ya fad'amasu, jini ake buk'ata asanyawa mutumin da suka kawo,

A razane tafito a motar tana kallonsu, d'aya bayan d'aya tace, to Ku meye amfaninku da bazaku bada jininku a sanyawa musulmi d'an uwanku domin ceto rayuwarsa ba?"

Kallo suka bita dashi cike da jin tsoro,
Fahimtar haka da tayi daga garesu yasa,
Tarab'asu tawuce cikin sauri tanufi ofishin likita,
Tura k'ofa tayi tashiga tareda yimasa sallama, bata jira amsawarsa ba, ko kuma ya bata umurnin zama ba,
Taja kujera ta zauna,

Likita saibinta yake da kallon mamaki,
Yace malama lafiya?"
Daga ina haka?"

Takai dibanta a wurin likita tace " yi hakuri docter banyi maka bayanin koni wacece ba, wlh duk a rud'e nake,

Marar lafiyar damuka kawo yanzun,
wadda ke buk'tar jini cikin gangawa, shine nazo domin a d'ebi jinina a sanya mashi, domin idan akatsaya Neman 'yan uwansa zai iya rasa rayuwarsa,
Don Allah docter kayi Sauri ka auna jinina idan yayi daidai danasa a sanyamashi.

Likita yatsora mata ido cike da mamaki, yace "idan son samune munfi buk'atar asanya masa jinin namiji a kan na mace,
Saboda mace tana haihuwa kuma tana zubarda jini duk k'arshin wata,

Mik'ewa tsaye tayi cike da b'acin rai, tace "dakata Docter Òœ‹ðŸ¼ kaifa kace yana cikin mawuyacin hali mutuwa ko rayuwa?"
Amma kakeyimun wani dogon zance, magana d'aya nakeso kafad'amun,
Ana iya d'ibar jinin mace a sanyawa wani koba'a d'iba?"

Docter yace ana d'iba amma idan mace ta jima bata haihuba,

Bilkisu tace "toni bantab'ayin aure ba bare na haihu,
Docter sanyamun abun d'ibar jini, kad'iba kak'arawa bawan Allah karya rasa rayuwarsa.

Da Sauri likita ya d'auko kayan aiki ya kwantar da ita kan gado yashiga d'ibar jininta.

Bayan minti talatin ta tashi daga kan gadon, fadawa sai sannu suke jera mata.

Ganin likita tayi a gabanta yana mata sannu had'i dayimata tambayoyi,
Babu abunda kikeji a jikin?"

D'aga masa kai tayi tace "banajin matsalar komai docter.

Yace "Alhamdulillah mund'ebi jininki roba biyu,
Asanya masa wadda insha Allahu munasaran farkawarsa nan da awa d'aya,

Tace "Allah yabashi lafiya."

Likita ya amsa da "Amin."
Ya kuma kallonta yace "amma ke matarsa ce ko?"

Domin a zamanin damuke ciki babu wadda zai iya taimaka maka da jini sai mahaifiyarka, ko kuma matarka, kodai wani d'an uwanka koshi d'an uwanka najini,

Bilkisu tayi murmushi tace niba matar sabace, ba kuma 'yar uwarsa bace,
Asalima bansan koshi wayebane,
Domin har yanzun banga fuskarsaba, tsoho ne, ko yarone, bansaniba, taimako nayimasa saboda Allah domin duk wadda ya taimaki wani Allah zaitaimakesa."

Pls 'yan uwana kutaimakamun da addu'a idanuna ciyo yakemun sosai

Writing by Fareedah bashir
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1Γ’Ζ’Β£
AND
Cool novel, makeup and kitchen2Γ’Ζ’Β£)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜

A WATA MASARAUTAR....

Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜Γ°ΕΈβ€˜β€˜

Writing by
Ummu
Safwan

PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.