Akan Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 1 of 21
๐๐๐
(แฆหโฃหแฆ)(แฆหโฃหแฆ)
*AKAN A'IKI NA 2021*
(แฆหโฃหแฆ)(แฆหโฃหแฆ)
๐๐๐
*Labarin gaske*โ๐ป
Na
*Rabi'atu.B.Abdullahi*
(Ummu Maher)
Miss green๐๐
_BISMILLAHIR_ _RAHMANIR RAHIM_
GABATARWA:dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah(S.W.T)Salati Mara Adadi Zuwa ga Manzon Rahma(S.A.W)
Tsokaci:Wannan littafin Ban rubuta shi don cin mutuncin wani/wata ba duk wanda yayi dai dai da rayuwarshi to yayi hak'uri akasi aka samu,Wannan littafin gaske ne ma'ana ba labari ne k'irk'irarre ba.
Sadaukarwa:Ga dukkanin mosayana Ummu Maher,Mu samman๐๐๐
Nabila dikko
Nabiha Aminu
Ummu Najma
Zahara'u Nasir Aliyu
Amina .m.Baso
duk ina godiya,da dukkanin mutanen da ban ambato su ba to suyi hak'uri.
Abbakar.Ak saraki
da
Ahmad isah Koko
Inq godiya sosai da kulawarku gareni๐
*Babi na d'aya๐*
Malam!Malam!!Malam!!fito kaga i'kon Allah yarinyar nan ta suma,Malam ya fito da gudu yana kallon yarinyar ya kalli Inna Majaifiyarta yace maza ki d'auki Mumtaz ki ku fito bari in kirawo Alhaji mu tafi asibiti,Sunan yarinyar kenan Mumtaz.
Kafin Malam ya dawo Inna ta kalli k'afar Mumtaz sai taga jini yana malala kamar ruwa da gudu ta fito k'ofar gida tana kiran Malam.
*Wacece Mumtaz*
Mumtaz dai shine asalin sunan ta wanda Mahaifinta ya saka mata saka makon sunan Mahaifiyarshi ne ya saka wa Mumtaz, Asalin Malam Abdullahi Mahaifin Mumtaz y'an jihar Bauchine wanda sun kasance y'an kasuwa ne sosai gidansu suna siyar da kayan masa rufi ta hanyar ne suke samun na cin abinci kuma i'tace hanyar abincin su.
Kwatsam sai karayar Arzik'i ta samu mahaifinsu Malam Wannan abun ba k'aramin tada musu da hankali yayi ba.
dalilin da yasa karayar Arzik'i ta same shi shine Mahaifinsu su Malam Wato Alhaji Jibrin shine yanada wani aboki d'an asalin Maiduguri Alhaji Bukar kusan ma Amininshi shi ne sana'ar Alhaji Bukar shine siyar da dabbobi daga wannan gari zuwa wannan gari.
Kwatsam sai wataran Malam Bukar yakawowa abokinshi Alhaji Jibrin ziyara yaga yadda ya bunk'asa da kasuwancinshi na siyarda kayan masa rufi.
Abun ya tsayawa Alhaji Bukar har yaushe Jibrin zai zama haka a kasuwanci bayan ya fishi tunda ga nan Alhaji bukar ya kafawa abokinshi Jibrin tsana mai tsanani Ya fara bin bokaye don ya raba shi da dukiyarshi,Har yayi nasarar rabashi da komai nashi ya zamo duk abunda ya tab'a sai yayi asararshi tun daga wannan lokacin Alhaji jibrin Mahaifin Abdullahi ya shiga wani mummunan talauci ya zama na koda kayan da zaisa ma sun fara lalacewa sai ya shiga wanka sun bushe sannan ya saka su.
Ana haka wataran Alhaji jibrin ya fita neman tai mako gidan wani mai kud'i kawai sai ya jiyo kukan wata jaririya cikin bolar kusa da k'ofar wani gida kamar zai wuce kuma sai ya dawo ya duba yaga jaririya ce aka yar kyakkyawa da'ita kamar y'ar larabawa ya d'auketa hannunshi yana kakkarwa ya nufo gida,yana zuwa gida ya nunawa matarshi Adama mahaifiyar Abdullahi da yake ita kad'ai ce matarshi kuma Abdullahi shi kad'ai ne D'an ta don haka koda Alhaji jibrin ya kawo mata wannan jaririya ba k'aramin jin dad'i tayi ba sosai don haka ta rik'e yarinyar da hannu bibbiyu.
Abdullahi kuwa duk duniya ya nuna ba shi da wacce ya keso sai Wannan yarinya wacce Alhaji ya saka mata suna Maryam,Tun tana k'arama yake sonta duk abunda ya samo to na k'anwarshi ne Maryam koda ta girma sai abun ya koma soyayya sosai koda iyayen suka gani sunyi murna sosai.
don haka da taimakon y'an uwa da mak'ota aka hahhad'a akayi musu Aure.
Ranar bikinsu ne wani mummu nan labari ya samesu'cewae Mota ta buge Alhaji Jibrin ya mutu Har lahira.
Sunyi kuka sosai da mutuwar mahaifin nasu mai son Su da nuna musu k'auna.
Koda akayi Auren Inna Adama mahaifiyar Abdullahi tace su zauna agidan tunda gidan yana da girmanshi haka kuwa akayi suka zauna agidan.
Ana haka wataran Inna adama ciwon ciki ya kamatq cikin dare ko kafin a kaita asibiti tace ga garunku nan ta mutu har lahira tashin hankali sosai Abdullahi da Matarshi Maryam suka shiga,Ana hakane kuma Maryam ta samu Ciki watanshi biyar ya zube saboda rashin kulawa don har yanzu suna cikin talauci sosai.
Saida Maryam tayi shekara Goma sannan ta haifi Mumtaz wannan shine labarin Mahaifan Mumtaz.
*Ummu Maher ce* Miss green๐
*Vote*
*Share*
And
*Comments*๐
*Tyiping*๐๏ธ
ABOUT MY WORKโ๐ป
๐๐๐
(แฆหโฃหแฆ)(แฆหโฃหแฆ)
*AKAN A'IKINA 2021*
(แฆหโฃหแฆ)(แฆหโฃหแฆ)
๐๐๐
*Labarin gaskeโ๐ป*
Na
*Rabi'atu.B.Abdullahi*
(Ummu Maher)Miss green๐๐
ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
_________________
______
๐
๏ธ๐ฎ๐ฟ๐๐บ๐ฎ๐ถ ๐
ฆ๏ธ๐ฟ๐ถ๐๐ฒ๐ฟ๐ ๐
๏ธ๐๐๐ผ๐ฐ๐ถ๐ฎ๐๐ฒ๐ฑ๐๐
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_
๐๐ ๏ธ๐ ฆ๏ธ๐ ๐
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.