Complete Hausa Novels

Akan Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 15 of 21

*Shafi na 27&28πŸ“*

______Wani k'u lulun ba k'in ciki ne ya tsaya wa Umma acikin ranta,wai Mukhtar ya fasa Auren y'arta Mumtaz to a k'an wani dalili?Zai Rabu da'ita menene laifin Y'arta Mumtaz?.

Kukan da Mumtaz ta Fara yi ne ya dawo da Umma daga cikin tunanin da ta ke yi,tayi saurin zuwa ta rufe bakin Mumtaz tana Cewa"Kiyi hak'uri Mumtaz komai ya yi farko yana da k'arshe Da man Allah ya yi Mukhtar ba mijin ki ba ne don haka ki fauwa lawa Allah komai shi zaiyi miki maganin komai Allah kuma ya ba ki miji nagari Wanda ya fishi.

Nan dai Umma ta ringa rarrashin Mumtaz tayi shiru sai dai ciwon kan da ya da me ta don har yanzu son Sir Mukhtar yana Nan a ranta,har yanzu tambayar da Mumtaz ta ke yi wa kanta shi ne ?wai me yasa Sir Mukhtar ya rabu da i'ta me ta yi mai da har zai d'auki wannan mummunan mata kin a kanta?.

To koma dai menene bai kamata ta rabu dashi ba,ya zama lallai ta nemi gidansu ta je ta sa mesa don ta ji Da hir abinda yasa Sir Mukhtar ya daina son ta.

Koda Malam ya dawo yaji abinda ya faru shima addu'ah ya din ga yiwa Mumtaz tare da yi Mata nasiha a kan rayuwa,Sannan Umma ta nuna wa Malam kud'in da Sir Mukhtar ya ba yar a bawa Mumtaz.

Shiru Malam ya yi sannan Ya ce"Shi Mumtaz d'in ne ya bayar a bawa Mumtaz d'in?

Umma "ta ce eh Malam shi ne ya ce a ba ta Amman Malam wannan kud'in ya yi yawa?.

" Kada Ku da mu Zan samu Mahaifinsa tunda na San gidansu Amman mu ba za mu amshi kud'in sa ba don munfi k'arfin a siye mu da kud'i."

*ENGLAND*

Sir Mukhtar Ya ce"Hello kana ji na I'na son ne ma Mata A'iki ne anan wajenku to i'nason ka turo mun number Shugabanku don muyi magana dashi don yarinyar tana da buri a Rayuwar ta na zama cikakkiyar y'ar jarida saboda ta kare mai gaskiya kuma yarinyar tana da jajir ce wa........
A hankali Sir Mukhtar ya ke maganar lokacin da wasu sa babbin hawaye suka zubo masa ya yi saurin go ge su,sannan ya ce"Rabi'u sai anjima ka turo mun da number.

Rabi'u ya ce"Ba b komai Mukhtar Insha Allah kada kaji komai Zan turo maka Nagode oga Allah ya ba da abinda a ke nema."

"Amin"
"Na gode"
"Rabi'u"

Suna gama wayar kuwa Rabi'u ya turowa Sir Mukhtar number,Mukhtar ya yi mai godiya Sannan ya kirawo ogansu Rabi'u.

Hamdala Mukhtar ya yi bayan sun gama wayar Sannan ya turawa Ogansu Rabi'u kud'i naira na gugan naira har dubu d'ari uku cuf Akan d'aukar Mumtaz da sukayi A'iki a gidan radio har Dana TV.

Sannan yaja musu kunne a kan kada su yadda su gaya Mata ce wa shine ya ne ma mata A'iki saboda ya San yanzu suna cikin fushi dashi sosai,shiyyasa ma ya fito da wannan hanyar don su rage zafin abinda ya yi wa Mumtaz.

Allah ya gani har yanzu yana son Mumtaz kuma bai fidda ran Auren ta ba,don gani ya ke yi matuk'ar bai Auri Mumtaz ba komai zai i'ya faruwa da shi.

*MUTA'Z*

"Haba Hajjo ke duk sanda nazo wajenki sai kin ne mi ki b'a ta min rai?Meye laifi na don Na ce ba za'ayi min Auren dole ba?Na ce miki ba na son Meemi wannan yarinyar mai d'an Karen si ranta kamar wata horo wallahi ba Zan Aure ta ba".

Hajjo ce ta rik'e baki tare da Ce wa"Inye lallai wannan yaron wato Kai yanzu ka girma KO?to wallahi baka i'sa ba kuma Wallahi baka i'sa ka Warware Alk'awarin Barkindo ba.

Wato Barkindo shi ne Mijin Hajjo tsohon sarki Wanda ya mutu ya barwa d'ansa tilo wato Mahaifin Muta'z.

"Kuma wallahi zanga uban na ka idan ma shi ne ya ke zugaka don kayi mun rashin ta i'do" tun bata I' da maganar da ta ke yi ba Muta'z ya yi tafiyarsa da ya ke Mumtaz akwai shi da zuciya sosai.

Hajjo ta harari bayan Muta'z Ta ce" d'an ne ma wato kai ma ka yo halin Barkindo na zuciyar masifa d'an a bu k'an k'ani sai ya haddasa Zuciya to yanzu me ye abin fad'a anan.

da sauri Meemi ta fito a wajen da ta lab'e saboda yanzu Muta'z ya kafa Mata dokar matuk'ar yana waje kada ta kuskura ta fito saboda idan ta fito sai ya b'ata Mata rai,i'ta kuma a duniya tana tsoron Muta'z don ta San halinsa da zuciya kamar kuturu.

"Haba Hajjo kina jin sa wai yana ce wa da siranta ta kamar horuwa Haba Hajjo gaskiya na gaji da cin mutuncin Hamma Muta'z kullum da wulak'ancin da zai yi mun saboda ya San Ina sonsa,gaskiya Hajjo idan baki Auramun Hamma ba mutuwa zanyi.

Nan dai Hajjo ta ba wa Meemi hak'uri akan Komai ya zo k'arshe ya zama dole mai babban suna ya Aure ki ja'iri kawai.

*MURAT*

"Ke! mima na gaji da wannan Alk'awarin na ki har yanzu lokacin d'aukar fansa ta baiyi ba don wallahi na rantse na kuma rantsewa sai na d'auki fansa A kan Muta'z".

πŸ€” To fa kunji mai sauraro wai sai ya d'auki fansa kan Muta'z kamar ya yi mishi wani Abu, duk taimakon da Muta'z ya yiwa Murat Amman ya manta shi so ya ke yi sai ya cuci shi don hassada.

y'an uwa na mudaina hassada domin hassada babban ciwo ne Allah ya tsare mu da hassada Amin🀲🏻.

Mima Ta ce "Come down Murat da d'i na da Kai ragon hak'uri Amman na fad'a maka akwai plan d'in da na ke shirya wa don haka kada ka da mu komai yazo End.

Nan fa Mima ta janyo Murat zuwa d'akin masha'arsu wai duk don ta lallab'ashi don i'ta kad'ai tasan abinda ta barwa zuciyarta kuma i'ta kad'ai tasan plan d'inta.

*Miss green ceπŸ’šπŸ’ƒ*

*Share And Comments*✍🏻
*TyipingπŸ–ŒοΈ*
πŸ’šπŸ€πŸ’š
πŸ€΅β€β™€πŸ€΅β€β™€πŸ€΅β€β™€
*A KAN AI'KINA 2021*
πŸ€΅β€β™€πŸ€΅β€β™€πŸ€΅β€β™€
πŸ’šπŸ€πŸ’š

Which meansπŸ‘†πŸ»
*A BOUT MY WORKπŸ€΅β€β™€βœπŸ»*

Na
*Rabi'atu.B.Abdullahi*
(Ummu Maher)Miss greenπŸ’šπŸ“—

πŸ’«πŸ’«
*πŸ…™οΈŽARUMAI πŸ…¦οΈŽ WRITERS πŸ…οΈŽSSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausaπŸ’ͺ*_

*πŸ’«(πŸ…™οΈŽ.πŸ…¦οΈŽ.πŸ…οΈŽ)πŸ’«*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.