Complete Hausa Novels

Akan Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 8 of 21

BABI NA 13&14πŸ“

_________Murat ya dawo daga tunani da yakeyi don gudun kada Aminin nashi ya gano halin da yake ciki,yace to Aminina Allah yadawo dakai lafiya Allah ya k'ara Arzik'i kuma ina godiya da i'rin Alherin da kake turomun Allah yasaka da Alheri.
Azuciyarshi kuwa cewa ya keyi wannan d'an kud'in da yake turomun ko Mima ta cinyesu shine yake wani iyayi waishi gashi mai kud'i,insha Allah na kusa cika burina akanka don huta da bak'incikin da kake d'oramun.
Hanan tana fitowa ta kalli Murat ta watsar dashi batare da tace mai komai ba tayi tsaki tayi wucewarta eajen yayanta suka cigaba da hirarsu shi kuma Murat ya fita yana maijin haushin abunda Hanan take yimai saboda tasan yana sonta shiyyasa take yimai kowani i'rin tashin mutunci,kuma insha Allah saina Aureki don tabbatar da Akina ya tafi daidai batare da wani ko wata sun gane ba.

************
Washe gari da safe Mumtaz ta shirya don biyawa k'awarta makaranta Amal saidai abunda ta ganine yayi mugun razana ta,ta k'arasa wajen Dadynsu Amal da yafito ta gaisheshi inda ta kalli Maigadi yana zuba musu kayansu a boot d'in motar ga Amal ma tafito i'tada Hajiyar ta daman Yaya Ibrahim yayi tafiya tun watan jiya.
Mumtaz tace Dady tafiya zakuyi ne bamu saniba kuma?sai kuwa Hajiya tace yauwa sannu uwar Alhaji da i'dan zamuyi tafiya sai mun gaya miki uwar kinibibi kawai,to transfer akayi mishi zuwa Legos zamu koma cen idan kuma zaki hanamu ne to bismillah tayi wucewarta ta shiga mota abinta.
Amal ta dafani tace Mumtaz ban tab'a sabo da wani mahaluk'i ba kamar yadda nasaba dake ba kuma inajin dad'in zama daku saidai hakan bazai yiyuwa jiya daddare aka turowa Abbanmu cewa anyi mishi transfer zuwa Legos, sai ta fashe da kuka ta rungumeni tana kuka kamar ranta zai fita.
Nima dakaina ban tab'a tunanin sabon da mukayi yakai haka ba saboda son Amal ajinina yake don ko bacci ne kawai yake rabamu shima Hajiya ce ke hanani kwana tare da Amal saboda masifar ta.
Muka rungume junanmu kamar baza mu saki junanmu ba,Dadynsu Amal yace Mumtaz kuyi hak'uri babu yadda zamuyi don nima banason rabuwa da Malam don nasaba dashi sosai Amman babu yadda zanyi Aiki nane haka daga wannan haka daga wannan jihar sai wannan.
Share hawaye na nayi nace to Dady Allah ya kaiku lafiya Allah yahad'a fuskokinmu da Alkhairi ina fad'in haka na fito da gudun gaske na shiga gidanmu alokacin Umma tana yanke farcen ta.
Umma tace ke Mumtaz kedawa ye da kika shigo gida kamar wadda tayi gamo da Aljani?dai dai lokacin Malam ya shigo yana fad'awa Umma cewa su Alhaji motarsu ta tashi yanzu za'ah kaisu tashar jirgi zasu koma Legos.
Umma tace Legos kuma Malam Allah sarki kai amman kuwa munyi rashin makwab ta nagari kai amman banji dad'i,Malam yace ya barmun shagon da nake ciki halak malak wai inyi ta sana'ah acikinshi Sannan ya biyawa Mumtaz kud'in jarrabawar da zasuyi ta fita daga Secondary sannan yabani jari na dubu Hamsin.
Umma tace Allah sarki Alhaji Allah shima ya bashi masu yimishi Allah kuma ya tsareshi da sharrin mak'iya Malam yace Amin dai don i'rin Alhaji acikin mutane k'alilan ne kam.

Bayan Sati 1
Rayuwa nakeyi ayanzu mara dad'i don nasaba sosai da Amal don Amal mutun ce mai kirki da mutun ta mutane don duk yadda Mahaifiyarta taso ta rabamu Allah baiyi ba k'arshe ta saka mana ido.
Umma tace haba Mumtaz wai haryanzu baki daina tunanin Amal ba tatafi sai watarana idon da rabon ku had'u da'ita ammsn kidaina sakawa kanki damuwa har tazo tayi miki illa.
na kalli Umma nayi dogon numfashi sannan nace Umma nasaba da Amal sosai don Amal mutuniyar kirki ce inajin dad'in zama da'ita sosai amman tashi d'aya ace wai munrabu, saina fashe da kuka Nan dai Umma tayi ta lallashi na har Allah yasa nayi shiru.

Bayan wasu watanni Mumtaz na hango sanye cikin after dress tayi mata kyau sosai tayi rolling d'in gashin ta abun gwani sha'awa hannyen ta sunsha lalle ja abun kamar kad'au keta tazama taka.
Mumtaz!Mumtaz!!Mumtaz!!!kira najiyo har sau uku ta bayana wanda na tabbatar da nasan mai muryar amman naman ta inda nasan ta,Hanan ce cikin ran tsattsiyar mutar ta sai k'elli takeyi kamar ka d'auke ta.
Da sauri na k'araso ina cewa to yau Hanan ce agarin to yaya gidan,Hanan tace normal amman saidai nazo wajen Amal akace sun tashi ina suka koma?nace Allah sarki sun tashi yanzu haka suna Legos anyiwa Abban ta transfer.

Hanan tace oky Ai babu komai naji dad'i ma da muka had'u dake don idan naganki kamar naga Amal ne,nayi dariya nace Allah sarki Hanan yanzu duk matsayinku agarinnan kike zuwa unguwar nan tamu ta talakawa duk da dai wajen k'awarki kika zo kada fa ki manta Mahaifinki shine Sarki fa.

Hanan tayi dariya tace Mumtaz kenan Ai don munada kud'i bawai yana nufin muna k'in talakawa bane,i'dan kika ga mutum yana k'in talakawa to gaskiya bashi da imani da tausayi,Kuma kinga ni da kike ganina a Mota ta nazo to Broz d'ina amotar haya yake yawo idan ya shigo Nigeria.

Abun ma dariyawa ya bani don tunda nake ban tab'a jin ance wani yarima ya hau motar haya ba sai akanshi,Hanan tace kin ganni ko bayanan bai yarda wani ya kaini unguwa ba ko kuma da karu su biyo ni ba,wai saboda mudaina d'aukar kanmu wani abu ba .

Nace gaskiya kunada mutunci da mutunta mutane don wasu masu matsayin basa i'ya shigowa cikin talakawa don basu da halak'a mai kyau dasu shiyyasa wasu da sun fito sai kiga ana jifan su,Amman ku kam kunada son mutane da son talakawa.

Hanan tayo dariya sannan tace shiyyasa yau nayi basaja nasaka nik'ab da kikazo kusa dani na bud'e don kiga fuska ta,saboda da mutane sun ganni yanzu zakiga Ancika wajen nan saidai a karb'eni da k'er,Nayi dariya nace au kuwa gaskiya ne kam don mutane suna sonku.

Hanan tace mu shiga gidan mu ta gaida Umma ta don basu tab'a gaisawa ba,Nace to nan nayi mata jagora zuwa gidan mu amman azuciya ta har kunya nakeji don kada taga gidanmu amman dana tuna cewa gidan ubanane ba gidan haya ba kuma ko akan kashi muke zaune zan nuna gidanmu donni ko a makaranta bana nuna cewa ni y'ar gidan wasu ce duk da daka ganni zaka d'auka cewa mud'in masu kud'ine saboda hallitar da Allah yayimun kamar y'ar shugaban k'asa.

Muna shiga gidan na hango Ummana tana tuk'a tuwo,Hanan tayi Sallama Umma na ta jiyo muka k'arasa Hanan ta gaishe ta,Sannan na d'aukowa Hanan kujera ta zauna suna k'ara gaisawa.

Nace Umma kinsan wacece wannan kuwa?Umma tace A'ah bansan ta wacece?Nace Umma wannan gimbiya Hanzn kenan y'ar gidan sarki,Umma ta rik'e baki tana cewa oh Allah yau manyan mutanane agidan namu sannunki y'annan ya mutanen gidan?Hanan da tunda muka shigo gidan take ta kallon Ummana ko k'ifta idanu babu.

Tace Umma lafiya klau duk suna gaisheku daman nazo wajen Hanan ne k'awata ce amman a Chart muka had'u da'ita har tazama kusan aminiyata so shiyyasa har muka saba to nazo sau d'aya kafun su tashi muka gaisa.

Umma tace Allah sarki sai kuma kikaji sun tashi?Hanan tace wallahi kuwa Umma kuma naga baya hawa online kwata kwata kuma wayarta ma bata shiga shine nace ko lfy bari inzo inji?sai kuma akace mun sun tashi.

Umma tace wallahi kuwa y'arnan sun tashi amman Allah yasa lafiya dai wayarta bata shiga? Muka had'a baki wajen cewa Amin ya Rabbi.

Hanan tace Umma tunda muka shigo naga kina mun kama da Mahaifina mai marta ba?Umma tayi dariya tace ke y'annan mai marta ba dai saidai kama Umma ta fad'i hakan tana dariya.

Idan kunda d'a Comment sai zan k'ara tyiping.

*More Comments*✍🏻

*More tyiping*✍🏻

*Ummu Maher ce*
*Tyiping*πŸ–ŒοΈ

ABOUT MY WORK✍🏻

πŸ’šπŸ’šπŸ’š
(αƒ¦Λ˜βŒ£Λ˜αƒ¦)(αƒ¦Λ˜βŒ£Λ˜αƒ¦)
*AKAN A'IKINA 2021*
(αƒ¦Λ˜βŒ£Λ˜αƒ¦)(αƒ¦Λ˜βŒ£Λ˜αƒ¦)
πŸ’šπŸ’šπŸ’š

*NA*
*RABI'ATU.B.ABDULLAHI*
(Ummu Maher)Miss greenπŸ’šπŸ“—

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.