Akan Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 18 of 21
Shafi na 38&39
Wani wawan Mari Mai Martaba ya kaiwa d'ansa Yarima,hannunsa yana kakkarwa ya nuna sa da yatsansa sannan ya ce"Muta'z sakayyar da zaka nuna min kenan?"na tarbiyyar da na yi maka,to daga yau na cireka daga cikin y'ay'ana kuma daga kar ka k'ara kirana a matsayin ubanka".
Inspector ga shinan duk wani hukunci da ya kamata a yi mishi a yi mai,tunda duk tsun_tsun da yaja ruwa shi ruwa kan duka.
Fulani kuwa kuka kawai ta ke yi tana Ce wa"Muta'z kada ka d'orawa kanka abinda kasan ba Kaine ka yi shi ba,don Allah ka fad'i gaskiya."?
"Fulani idan ki ka k'ara yi wa wannan yaron magana to sai dai a kulle Ku tare babu ruwana".
Da k'er Fulani ta fita tana kuka tana me Amman tana ji tana gani aka Tisa k'eyar Muta'z zuwa d'akin ajje masu laifi.
Koda suka i'sa gida kowa da abin da ya ke sak'awa acikin zuciyarsa Mai Martaba kuwa k'arfin hali kawai ya ke yi don babu yadda zaiyi ne shiyyasa ya d'orawa d'ansa laifi son gudun zagin talakawa,don yasan Muta'z bazai tab'a aikata hakan ba.
To wanene ya yi wa Yarima Muta'z sharri haka"? Koma wanene nan ba da dad'ewa ba Allah zai tuna asirinsa don Allah baya basin zalunci a doron k'asa.
*******
Mumtaz
" wai me ye yake damunki tunda kika dawo kin k'i cin abincin na ki gashi kuma yau kun dad'e."?
Shiru Mumtaz ta yi don sarai ta San dole sai ummanta ta yi mata wannan tambayar don tunda ta shiga d'aki bata fito ba sai yanzu don ta tsorata sa ganin abinda ya faru.
Sai ta samu damar ce wa umman nata"Wallahi babu komai kawai sai na gaji ne Aiki ya yi yawa,kuma kinga ban samu Damar zuwa bikin gidansu Hanan ba saboda Aiki."
Umman ta ce
"Ayya Allah sarki Allah ya bada abinda ake nema".
" Amin Umma"waini har yanzu banga Malam ya dawo ba".?
Dariya Umma ta yi sannan ta ce"Ai d'azu ya dawo ba kyanan Malam ya je k'auye saboda an yi musu rasuwa."
Allah yajik'an rai na ce sannan na koma d'aki na kwanta ina tunanin irin wannan rayuwa, har yaushe ne za'ah daina yi wa y'an mata da yara fyed'e a k'asar Hausa.?ki dubi yadda aka lalatawa wannan yarinyar rayuwa,Amman koma menene iyayenta sune da laifi.
Don rashin kulawa sa yaranmu yana saka irin wannan abin ya faru dasu.
******
Babu yadda Fulani bata yi ba akan mai Martaba yasaka baki akan asaki d'ansu Amman ya k'i dolen doliyarta ta hakuri,kuma gashi tana gadon asibiti saboda tunanin d'anta,shima Mai Martaban kawai dauriya ya ke yi shi kad'ai yasan yadda ya ke ji.
Mimee da Hajjo sunsha kuka har sun hak'ura gashi yanzu an d'aura Auren su.
A b'angaren Murat kuwa yaje sau biyu ya duba aminin nashi,agaban Muta'z ya nuna ya damu dashi yana fitowa kuma ya fara dariyar mugunta saboda ya hango nasara k'arara a game da abinda yasa a gaba.
An yan kewa Muta'z hukuncin zama na shekara sha hud'u14 tare da yanke mishi tara mai yawa.
Fulani da Mimee da Hajjo suna zuwa duba Mutaz akai akai Duk sanda sukazo sai sun tasa Mutaz suyi ta kuka,abin tausayi Mimee kuwa akwai sanda ta suma bayan sunje,Mutaz yana tausayawa Mimee yadda zata dad'e da Aurensa akanta don Hajjo ta ce babu wanda ya isa ya raba Auren matukar tana raye.
*******
"Kai Gaye gaskiya nifa zanje in Tina abinda ya faru saboda ko yanzu idan muka mutu sai Allah ya tambaye mu don mun cuci bawan Allah".
By
*Real Ummu Maher ce*
💚🤍💚
🤵🏻♀🤵♀🤵🏻♀
*AKAN AIKI NA 2021*
🤵🏻♀🤵♀🤵🏻♀
💚🤍💚
Which means👇🏻👇🏻
ABOUT MY WORK✍🏻
NA
*🌹Râbî'âtû ß/ Âbdûllahî*
(Úmmú Máhèr)Míss gréén💚☘️.
💫💫
*_🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION_📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.