Akan Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 17 of 21
*Shafi na 33&34*
Dariya Murat ya yi sosai irin dariyar basawa d'innan,sannan ya janyo Mima jikinsa i'ta kuwa ta kanne mishi ido d'aya alamun nasarar da ta samu na shiga tsakanin aminan juna Murat da kuma Muta'z.
*Muta'z*
Kuka ya ke yi kamar k'ara min yaro yana mai kallon yarinyar da aka b'atawa rayuwarta yarinyar da bata wuce shekara takwas zuwa Tara.
Da sauri Mumtaz ta fad'a d'akin tana d'aukar rahoto da sauri Muta'z ya juyo don ganin mai d'aukarsa hoto domin ya hango hasken camera.
Ido hud'u sukayi da Mumtaz a dai dai lokacin da Mohd ya shigo gidan,shak'a Muta'z ya kaiwa Mumtaz Wanda sai da taji ajikinta sannan ya fara magana da kakkausar murya Ya ce".
"wallahi kika sake kika yad'a wannan abin to na lahira sai ya fiki jin da d'i,muguwa masharanciya kawai dai dai lokacin shi kuma Mohd yana k'ara d'aukar rahoto.
Alokacin kuma y'an sanda sukayi wa gidan k'awayenya,har lokacin Muta'z bai saki Mumtaz ba ya shak'eta sosai don Muta'z ya fita daga hayyacinsa gaba ki d'aya.
Mohd kuwa yana ta k'ok'arin kwatar Mumtaz yayinda Muta'z ya saki Mumtaz ya wancakalar sa i'ta gefe ya koma kan Mohd.
Tunda Mumtaz ta ke ba'ah tab'a yi mata makamanciyar wannan shak'ar ba.
Saboda yadda iyayenta suke sonta da k'aunarta kuma ga ta yarinya mai biyayya basu tab'a dukanta ba,sai yau gashi wani abanza ya shak'eta AKAN AIKINTA.
Da k'er aka b'an_b'are Mohd daga jikin Muta'z don Muta'z k'arfi ne dashi kamar na doki.
Ankwa y'an sandan suka mak'alawa Muta'z yana ji yana gani suka tafi dashi Office i'ta kuma yarinyar su Mumtaz suka kaita asibiti don duba lafiyar yarinyar don ba k'aramar wahala Tasha ba don har yanzu a sume ta ke.
*****
Labarai Fulani da mai Martaba suke yayinda gidan ma acike ya ke da y'an uwa saboda bikin d'an gata Muta'z.
Da sauri Fulani da Mai Martaba suka tashi hannun su dafe da k'irjinsu suna kallon Muta'z yadda y'an sanda suka yiwa d'ansu jina jina da duka,don har ga Allah basu San Muta'z d'an sarki bane saboda shi bai fiya shiga Media bama ballanta na har a ganeshi.
Salati suke suna sallallami ya yinda kowannensu ya rasa sukuni nan da nan Suka fita a mota don zuwa ganin d'an nasu Hanan ma kuka ta ke yi kamar ranta zai fita don ganin yadda a kayi wa d'an uwanta tilo rauni.
Sara masa y'an sanda suka shiga yi har sai da ya shiga babbar headquarters d'in,ranshi a b'ace ya zauna gaban babban Inspector y'an sanda.
Ran Mai Martaba ta gama b'aci kuma har lokacin ya kasa bayani,sai Fulani ce ta fara bayanin tana kuka"Akan wani daliline zaku kama mana d'an mu kuyi mishi wannan babbar illar"?
Sai asannan ne inspetor ya gane wa take nufi domin ya hango kamar da Yaron da suka kama d'azun Akan hukuncin fyed'e.
Sunkuyar da kai Inspector ya yi domin har ga Allah kunya ce ta kamasa,saboda bai San d'ansa bane Amman koma menene a dokar k'asa hakan shine dai_dai.
Nan fa Inspector ya fara yi musu bayani Akan abinda ya faru.
Alokacin kuma Inspector ya saka aka fito da Muta'z kuma alokacin Iyayen Fiddausi suka zo wato yarinyar da aka yi wa fyed'e.
Kuka suke sosai kamar ransu a game da lalatawa y'arsu rayuwa da a kayi suna tsinewa Muta'z tare da aibata shi,don tun jiya da'aka turata talla ba'ah sake ganin ta ba.
Kan Muta'z a sunkuye yana zubar da kwallar bak'in ciki a game da wannan jarabtar da ta same sa,ko kuma ya ce sharrin da aka yi mai.
Iyayen Muta'z sun san halin d'an su tun daga girmansa har yarintarshi don haka basu yadda d'an su ne ya Aikata haka ba.
Cikin Kakkausar Murya Mai Martaba ya kirawo sunan d'an nashi Ya ce"Muta'z ka fad'a min gaskiya duk da nasan kai mai gaskiya ne"Waye ya yiwa yarinyar nan fyed'e"?.
Kallon iyayen yarinyar Muta'z ya yi sannan ya fashe da kuka cikin kuka Ya ce Ka gafarceni Mai Martaba Wallahi Ni ne".
*Real Ummu Maher ceโ๐ป*
๐๐ค๐
๐คต๐ปโโ๐คตโโ๐คต๐ปโโ
*AKAN AIKI NA 2021*
๐คต๐ปโโ๐คตโโ๐คต๐ปโโ
๐๐ค๐
Which means๐๐ป๐๐ป
*ABOUT MY WORKโ๐ป*
Na
*๐นRabi'atu B/Abdullahi*
(Ummu Maher)Miss green๐โ๏ธ
*_๐ซ๐JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐ช๐ป_*
*MURAT FANS*
Yana godiya bisa bashi hadin kai da kuka yi Fans๐ฉ๐ฅฒ
*MUMTAZ FANS*
Tana godiya bisa yadda kuka bata hadin kai wajen d'aukar hoto da kuma rahoto๐ธ๐ฒ๐ฒ.
*MUTA'Z FANS*
Yana bak'in cikin yadda kuka bawa Murat da Mumtaz goyon baya.๐ญ๐ญ
__,,,,,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.