Akan Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 3 of 21
*BABI NA 3&4*๐
Mumtaz ta taso da wata irin baiwa wadda take bawa kowa mamaki saboda yarinyar akwai gaskiya bata tab'a yin abu ta nuna rashin gaskiya kosa zaka kashe ta sai ta fad'i gaskiyar lamari,Ana haka Malam ya samu Aikin nik'a ya nayi albashinshi na farko ya saka Mumtaz makaranta da shi Mumtaz kuwa ta ringa murna saboda mahaifin nata ya cika mata burin ta nayin karatu,Kullum Malam i'dan zai tafi wajen nik'ansa tare suke tafiya da Mumtaz ya sauketa amakaran ta ya siya mata biskit da alawa sannan ya tafi wajen Aiki yana mata Bye bye i'tama Mumtaz bata tafiya sai taga Mahaifin nata ya tafi sannan take shiga aji.
Karatu sosai Mumtaz ta keyi don bata wasa a makaranta sam,ga ta bata surutu a'aji kawai i'ta karatu ta saka a'gabanta.
makarantar Mumtaz tayi nisa gashi Allah ya taimaki Malam yana biya mata kud'in makarantar ta akan kari baya bari lokaci ya k'ure bai biya ba kuma yana jin dad'in yadda take karatunta tana mayar da hankali,Mumtaz duk cikin ajinsu babu wanda ya kaita k'ok'ari da mayar da hankali wajen karatu gata da k'ok'ari don duk term ita take zuwa na d'aya ko Na biyu A'ajinsu haka duk Malam man makarantar sun san cewa Muntaz tana da baiwa sosai gata tun tana k'aramarta akwai ta da hankali da hangen nesa.
Mumtaz tana dawowa daga makaranta ta ajje jakarta ta cire unifoam d'inta na makaranta ta fito tsakar gida don taya Umman ta Aiki,ta gumin da taga Umman ta tayine tace Umma lafiya me yafaru kike ta gumi me akayi miki?ta jerowa Umman tata tambayoyi lokaci d'aya,Umman tata tayi saurin cire ta gumin da tayi tace Mumtaz kin dawo ne?Eh Umma na dawo Amman meya faru naga kin rik'e kunkuminki?Umma tace Mumtaz nasan kina jin yunwa ko?Eh Umma inajin yunwa sosai me kika dafa,Umma tace Mumtaz babu abunda na dafa shiyyasa ki kaga nayu tagumi kuma na buga na buga ban samu ba,Mumtaz tace to Kuma Umma shine kika saka kanki cikin damuwa ki daina damuwa kinji,Indai na girma na samu Aiki zaki huta indunga siyo miki kayan dad'i,Umma tayi murmushin da yafi kuka ciwo tace to Mumtaz Allah dai ya cika miki wannan burin naki,Mumtaz tace Amin Ummana.
Umma tace yanzu ki tashi akwai wata y'ar sauran kamu da na dama miki da kwad'on k'anzo ki tashi kici kinji Umman ta kalleni tana mai jin tausayin d'iyar tata.
Akwana atashi asarar mao rai wataran asamu aci wataran kuwa Iyalan Malam mahaifin Mumtaz basa cin abun abinci wataran haka suke kwana abunsu,gashi Allah ya basu yarinya mai hankali da tausayi ko ta samu ko kar ta samu bata tab'a d'agawa iyayenta hankali wai don tana jin yunwa ko wani abu haka take hakura taci koda bai mata ba haka ta ke hak'ura taci.
Har Allah ya kawo lokacin da su Mumtaz suka zana jarrabawar fita daga primary Mumtaz da iyayenta sunyi murna sosai gashi ta fito da saka mako mai kyau.
Mumtaz tace Malam ina Addu'ah Allah ya cika mun burina na zama y'ar jarida sai dai bansan aikin da zanyi ba in taimaka muku ba kuna shan wahala kaida Umma,wajen biya mun buk'atu na,Malam yace babu komai uwata Allah zai taima kamana matuk'ar ba muyi bacci ba muna rok'on Allah ya kawo Aikin da zai zi mun na sakaki makarantar gaba da Primary kinji ki daina da muwa,Mumtaz tace to Baba na Allah ya tai ma keka yacr Amin uwata.
โขโขโขโขโขโขโขโขโขโขโขโขโขโขโขโขโข
Ranka ya dad'e har yanzu Mu'taz d'in bau kira ka ba Allah dai yasa lafiya mai martaba inajin tsoro kada wani abu ya samu yarima,Mai martaba yace gaba Fulani babu abunda zai sameshi kinsan yace i'dan ya dawo baya buk'atar muje d'aukoshi motar haya zai shiga kinsan halinshi don haka kada ki damu,Fulani tace haba Mai martaba yanzu haka zamu zubamai idanu gamu da motocin agidanmu wasu ma saidai mu bayar Anma d'anmu yana shiga motae haya so yakeyi duniya ta zagemu ace mun kasa kula da d'an cikinmu ballanta na Al'umma gaskiya nidai banasan wannan halin nashi Ai ba sai yayi haka ne duniya zata san cewa shi mai tausayi ne ba.
Fulani bata gama rufe bakin ta ba,Jakadiya tayi iso k'ofar d'akin tace gafaranki dai Yarima yana neman i'so,Fulani tace anyi mai iso ya shigo Yana shigowa ya gaida mai martaba da mahaifiyarshi Fulani,tace ikon Allah kaidai yarima kaji tsoron Allah wallahi duk yawan motocin gidannan kace wai kai bazaka hau ba sai motar haya zaka hau wannan wacce irin rayuwa ce haka.
*UMMU MAHER CE*
Please share
And
Commentsโ๐ป
*Tyiping*๐๏ธ
ABOUT MY WORKโ๐ป
๐๐๐
(แฆหโฃหแฆ)(แฆหโฃหแฆ)
*AKAN A'IKINA 2021*
(แฆหโฃหแฆ)(แฆหโฃหแฆ)
๐๐๐
*Labarin gaske*โ๐ป
Na
*Rabi'atu.B.Abdullahi*
(Ummu Maher)
Miss green๐๐
ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
_________________
______
๐
๏ธ๐ฎ๐ฟ๐๐บ๐ฎ๐ถ ๐
ฆ๏ธ๐ฟ๐ถ๐๐ฒ๐ฟ๐ ๐
๏ธ๐๐๐ผ๐ฐ๐ถ๐ฎ๐๐ฒ๐ฑ๐๐
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_
๐๐ ๏ธ๐ ฆ๏ธ๐ ๐
*WATTPAD LINK*
https://www.wattpad.com/?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends.
__________________๐๐ป๐๐ป
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.