Complete Hausa Novels

Akan Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 14 of 21

*Shafi na 25&26📝*

"Kai ko kunya ma baka ji ba zaka zo ka ce mun wai wannan y'ar matsiya tan ka ke son ka Auro mana gida,ba bu wanda bai san yadda tsiya ta yi musu k'a tutu ba,Shi ne ni zaka Auro mun Y'ar matsiya ta."

"Wallahi ba zai tab'a yi yuwa ba,saboda duk gidannan ba bu matsiyaci ballan tana matsiya ciya,don haka ka bud'e kunnu wan ka ka ji ni ba zaka Auri wannan yarinyar ba na za b'a maka matar da ta da ce da kai."

"Kuma ko tai makonsu ka k'ara yi Allah ya i'sa ban ya fe maka ba,don kud'inka ba a taimakon matsiya ta zai k'are ba don mu kullum ba ma son mu ragu sai dai kullum ar'zik'inmu ya yi ta k'a ruwa.

"Don haka sai su bi wani sarkin ni dai na hane ka da Auran y'ar matsiya ta jikan matsiya ta,Msssst kuma wallahi tallahi naji labarin ka fad'a wa Alhaji abin da ya faru ni da kai ne,sakarai kawai lusarin Namiji....."

Shiru Mukhtar ya yi kamar zai yi kuka,zuciyarsa na ta farfasa kamar zata fasa k'irjinsa ta fito,don yana yi wa Mumtaz son da bai tab'a yi wa wata d'iya mace ba.

Tun da ya ke bai tab'a soyayya da wata y'a mace ba ko kuma ya ce yana son ta ba,Tun y'an gidansu na yi mai magana har sun gaji sun k'e lesa saboda ko maganar mace ma ba ya so.

Sai ga shi lokaci d'aya ya sa ba da Muntaz ga wani mahaujacin son da ya ke mata,Kash!sai ga shi yanzu Mahaifiyarsa ta raba shi da abar son sa Mumtaz.

Wai me yasa iI'yaye su ke shisshigi a rayuwar y'ay'ansu wajen raba su da abin da ya ke so?,kuma ya ke muradin Rayuwa da i'ta har abada.

Tambayar da Mukhatar ya ke yi wa kansa? i'ta ce da wani i'do zai du bi Mumtaz kuma?Kuma da wani i'do zai du bi i'yayen Mumtaz da sunan ya dai na son Y'arsu.

Wasu hawaye ne suka fara zarya a idanunsa yana nemarwa kansa mafita,ya yanke shawarar Tafiyar da ya yu niyyar yi tun kafun su had'u da Mumtaz don k'ark karatunsa a England don haka yanzu ya zamar masa dole ya ta fi.

Saurin ta shi ya yi ya fita don fara shiri do a gobe ya ke son tafiya,Amman a daren nan zai je gidansu Mumtaz don ya ba ta sak'o y wuce ba ta re dasun had'u ba.

Cikin gaggawa ya d'auko bairo da ta kadda ya fara rubutu a ciki kamar haka.

_*Assalamu Alaikum*

" Amincin Allah ya tabbata akan ki Masoyiya ta Mumtaz.

Mumtaz Na so ki zama matata uwar y'ay'a na amman Allah bai yi ba,don wani mashi ya tsaya cak a cikin rayuwarmu ya hanamu rawar gaban hantsu.

Ban tab'a soyayya da wata y'a mace ba sai ke Muntaz,ballan tana ma har in samu daman Yaudarar wata y'a mace.

"Mumtaz inasonki kuma da sonki zan mutu,don Allah idan na mutu ki dinga yi mun Addu'ah kuma ki sakawa d'anki/y'arki su na na hakan zai sa koda na mutu inji dad'i.

Ki ya fe mun mumtaz don Allah,sannan ki ba wa Malam hak'uri a kan abinda ya faru.

" A k'ashe ina miki fatan Alkhairi Idan kin samu miji kiyi Aure.

Ki ya femun Mumtaz.

da ga
Sir Mumtaz_ ✍🏻.
____________________

Yana gama rubuta wa ya go ge hawayen da ya wanke masa fuskarsa yana Shesh shek'ar kuka kamar wani d'an yaro k'arami ko kuma yaron da aka hanashi Mama.

daga cen ne sa ya tsaya da motarsa ya samu yaro ys ba shi envelope d'in wato wasik'ar sannan ya bawa yaron wani Envelope k'ato sannan ya bawa yaron ya shiga gidan.

Sai da yaga yaron ya shiga gidam sannan ya shiga motarsa ya d'ora kan sa jikin sitiyarin motar yans kukan zuci,Sannan ya tafi zuciyarsa a da kushe.

K'arfe Hud'u na yamma jirginsu ya ta shi sai England yana hango ga jimari ya rufe idonsa yana kukan rabuwa da Mumtaz tare da Mahaifinsa,don Hajiyarsa ma murna ta ringa yi da tafiyar d'an na ta.

Alhaji kuwa ko da ya tambayi d'an nasa dalilin sa na k'in Auren Da ya ce a nemar mai k'in basa amsa ya yi k'arshe ma ya ta shi ya bar wajen yana kukan zuci.

Haka Alhaji ya samai ido yana taya d'an nasa addu'ar Allah ya kare mishi d'an Na sa a duk i'nda ya ke,ya kuma kawo masa mata ta gari shima ya huta da zaman gwaurancin da ya ke yi.

*************
Da gudu Mumtaz ta le k'a d'aki hannun ta yana kakkarwa ba kinta ma yana kak karwa idanunta kuwa ya yi jawur kamar garwashi.

"Um..um Umma kin ga wannan ta kaddar".
har lokacin bakin Mumtaz kak karwa ya ke yi.

Umma ta amsa cikin tsoro tana Ce wa.
" Mumtaz ta kaddar me ce ce wannan?ta fad'i hakan cikin ta shin hankali da furgici.

"Umma Sir Mukhatar ne ya aiko mun yanzu wai ya fasa neman Aure na idan na sa mu miji in yi Aure"....

*Ummu Maher ce*

*Vote*
*Share*
And
*Comments*
*🖊️Tyipin🖊️*

💚🤍💚🤍
(ღ˘⌣˘ღ)(ღ˘⌣˘ღ)
*AKAN A'IKI NA 2021*
(ღ˘⌣˘ღ)(ღ˘⌣˘ღ)
💚🤍💚🤍

Which means👇

*ABOUT MY WORK🧑‍🎓*
________✍🏻

*NA*
*RABI'ATU.B.ABDULLAHI*
{{Ummu Maher}}Miss green💚💚

Y'AR MUTAN KANAWAN NIGERIA🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.