Complete Hausa Novels

Akan Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 7 of 21

BABI NA 11&12๐Ÿ“

Hanan ta kalli Yayan ta Muta'z"Tace Bros meyasa haryanzu Murat bazai daina wannan halin nashi nason mata ba?Kullum sai yace ya daina amman gobe sai ya koma.
Wallahi Bros yanzu kaf duniya babu mutumin da na tsana i'rin Murat kwata kwata shi baisan mutuncin Alk'awari ba.
to Wallahi bros badon kaiba da tabbas sai nayiwa Murat wulak'ancin da harya mutu bazai manta dani ba,saboda na lura ma badon komai yake sonka ba saidon kud'inka shiyyasa yake sonka don ya cuceka.
Hanan!Hanan!!Hanan!!!ki bud'e kunnuwanki kijini kada ki sake zagin aminina kuma d'an uwana a gabana don yace yana sonki bawai yana nufin ki ta gayamai maganar da tayi miki bane don haka ya rage naki ki soshi ko karki soshi don haka ki b'acemun da gani nonsense kawai Muta'z yayi mata wata tsawa da gudun gaske ta fita daga d'akin tana kuka Kai cin rai.
Tana fita Kai tsaye d'akin ta tanufa tana wani i'rin kuka mai cin rai,haryanzu d'an uwan ta yakasa gane halin Murat Sam don Murat mutum ne mail wayo DA son abun duniya don shi Murat irin mutananne masu k'emar mutane musamman ma talakawa don i'dan yaga talaka tamkar yaga wani Abu mummuna.
Bayan haka kuma gashi DA son mata don duk inda yaga mace musamman ma y'ar bariki i'donshi yana kanta don shi haka Allah yayi shi DA masifaffen son y'an Mata.
Lallai ya zamar Mata dole ta samarwa kanta mafita DA yayanta Mutaz don gudun fad'awa halin Azzalumin mutum i'rin Murat Mara imani.

*Mumtaz*
ta kalli Umma mahaifiyar ta tace haba Umma wannan matakin DA kika d'auka bai dace ba saboda Mahaifiyar Amal bata mutunta d'an Adam KO kad'an.
Amman yanzu kice zaki fara Aiki agidan don Allah kiyi hak'uri Umma mu tsira DA mutuncin mu please,Umma ta dafa y'arta tace Mumtaz kiyi hak'uri kada kidamu DA yadda take wulak'anta mutane saboda ko badon komai ba saboda zaman nan da nakeyi haka bbu wani neman nakai babu dad'i saboda koda Mahaifinki yana yi dole nima inyi.
tunda ba komai zamuce yayi mana ba,Nace amman Umma kinsan halin matarnan kuma kikeso kiyi aiki agidanta ina laifi ma kije wani gidan tunda kin matsa dole sai kinyi aikin.
Umma tace Mumtaz matarnan fa dakan ta tazo gidannan tace i'dan babu damuwa tanason inringa A'iki agidan ta amman idan hakan ya b'atamun rai inyi hak'uri.
Mumtaz tace yanzu Umma wannan matar ce tace zaki ringa yi mata A'iki tana biyanki yanzu tayiwa Dady adalci kenan gaskiya Umma kada kiyi Aikin nan don Allah saboda bata da mutunci ko kad'an.
Umma tace kai Mumtaz yaushe kika zama haka mai manta Alkhairi Arayuwarki yanzu duk abunda matarnan take miki saikin zageta tunda kika fara zaginta bance miki komai ba shine kika samu bakin cin mutuncin ta haka.
to bari kiji nayi shawara dake ne saboda ina ganin ko babu komai ke y'ata ce kuma kina da hakk'i akaina kamar yadda nima nake da nawa hakk'in akanki amman ba don haka ba da saidai kiji nafara A'iki na, wawiya kawai Umma tayi wani tsaki mai k'arfi tayi wucewar ta abun ta.
Mumtaz tabi bayan Umman nata da kallo tabbas batason wacece mahaifiyar Amal ba shiyyasa,domin duk k'iyayyar da take yiwa Mumtaz bata yimata gaban Umma shiyyasa, saidai ma agaban Umman ta ringa nunawa tafi ta son Mumtaz d'in.
Tana cikin wannan tunanin taji sallamar mahaifinta da sauri taje ta'amshi kayan hannunshi tayi mishi sannu da zuwa.
tana kai kayan ta dawo zata wuce Mahaifin nata yace Mama na zo mana,Nace to Baba nadawo nazauna ina jiran abunda zaice don nasan tunda ya ganni acikin damuwa saiya tambayeni abunda ya sakani damuwar.
Yace Mamana meya faru?ko bayan fitata wani abu ya faru waye ya tab'amun Mamana ta kaina?shiru nayi babu amsa don bansan ma abunda zance mai ba don tabbas mahaifina baisan cewa Mamana Zata fara A'ikatau gidansu Amal ba yanzu kuma matuk'ar nafad'a mishi to tabbas kashi na ya bushe don tabbas mamana cewa zatayi nice na fad'awa Abba na.
don haka na k'irk'iro k'arya ta nace Baba na d'an zazzab'ine yake damuna shiyyasa amman yanzu yayi sauk'i.
Baba yace to kuma shine baki fad'awa mahaifiyar taki halin da kike ciki ba saiki zauna da ciwo?Nace ai Baba yanzu ya fara yimun shiyyasa ban gayawa Umma ba.
Umma dai tana kusa da Babana batace mana cikanku ba hasalima tashi tayi ta fara k'ok'arin d'aura tuwon dare,Baba na yace to bari inci abinci sai in kaiki chemist d'in Tasi'u.
Ai da sauri nace A'ah Baba wallahi kabarshi ma naji sauk'i Wallahi,Baba yace ayi haka Mamana ai gwara abaki magani ko kada kuma yadawo miki,Nace wallahi ya daina yanzu Baba.
Yace to shikkenan Mama na,Umma kuwa kallo na tayi tace Hmmm dama kindaina k'aryar ciwo don kada na gasken yazo don i'don na gasken yazo baza kiji dad'i ba.
Baba Yace haba ke kuwa kinsan Mamana bata k'arya ballan tanama k'aryar ciwo kema A'i sheda ce ko?don Mamana bata k'arya sam.
Umma tace yaudai tayi maka don yanzu na shiga d'aki kafun infito wai har kanta yafara ciwo saboda i'ta ta i'ya k'arya mai lasisi,Baba na yace kai haba ya zakice haka naga Allah yakan kawo wa mutum ciwo yanzu anjima kuma ya sauwak'e mai.
Ko kuma yanzu yana numfashi anjima ya daina don haka ni yanzi na yarda da ciwon Mamana don nasan ba halin ta bane k'arya.
Baba na yace zo Mamana nasiyo miki wani abu mai kyau๐ŸŒปdasauri na kalli Babana da shima ni yake kallo,na fad'ad'a fara'ata don ganin me yasiyomun.
Hijabi ne mai kyau da sandal na makaranta mai kyau sai sabulun wanka mai kyau harda man shafawa,godiya na ringa yiwa Mahaifina ina maijin k'ara sonshi har zuciya ta.

**********
Murat yace abokina duka duka kwananka nawa da dawowa zakace zaka koma k'asar waje Ai yakamata kad'an dad'e saidai i'dan bakason ganinmu to shine Murat ya fad'i hakan yana mai b'ata fuskarshi kamar da gaske.
Muta'z ya dafa Aminin nashi yace kayi hak'uri life A'iki nane yake buk'atata awanannan lokacin shiyyasa saboda Ina matuk'ar alfahari da Aikina saboda nasamu alfanu sosai dashi.
Kaga ayanzu inada asibitina mai zaman kanshi ak'alla yakai biyar ayanzu haka a k'asashen waje,so shiyyasa kaga nakeso inga nakoma don cigaba da Aikina.
Tunda Muta'z yafara magana kallonshi kawai Murat yakeyi gaskiya indai hakane yanada A'iki babba agabanshi saboda yadda abokin nashi ya bunk'asa haka.
Ace kanada Asibiti har 5 outside country lallai kuwa bak'aramun kud'ine da aminin nashi ba kuma bai tab'a gaya mishi cewa asibitinshi ya kai har biyar ba sai yau.
to kodai ya gane manufarshi akanshi ne?to indai kuwa hakane dole ya canza takunshi don yazamar masa dole yaga ya cimma nasara akan Aminin nashi.

Don Allah ina baku hak'uri abisa rashin jina kwana biyu da bakuyi ba saboda ina Exam ne shiyyasa,ku tayamu da Addu'ah please nasamun nasarar cin jarabawar.๐Ÿคฒ๐Ÿป

*Ummu Maher ce*โœ๐Ÿป
(Miss green)๐Ÿ’š
*Tyiping๐Ÿ–Œ๏ธ*

ABOUT MY WORKโœ๐Ÿป

๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š
(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)
*AKAN A'IKINA 2021*
(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)
๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š

NA
*RABI'ATU.B.ABDULLAHI*
(Ummu Maher)Miss green๐Ÿ’š๐Ÿ“—

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…
da sunan Allah mai rahama mai jin k'ai
_________________
______
๐Ÿ…™๏ธŽ๐—ฎ๐—ฟ๐˜‚๐—บ๐—ฎ๐—ถ ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ๐—ฟ๐—ถ๐˜๐—ฒ๐—ฟ๐˜€ ๐Ÿ…๏ธŽ๐˜€๐˜€๐—ผ๐—ฐ๐—ถ๐—ฎ๐˜๐—ฒ๐—ฑ๐Ÿ“š๐Ÿ–Š
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_

๐Ÿ”๐Ÿ…™๏ธŽ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ๐Ÿ…๐Ÿ”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.