Akan Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 6 of 21
*BABI NA 9&10*๐
Ibahim yayi shiru yana sauraron Hajiya da gaba ki d'aya i'don ta ya rufe da masifa wai yanzu an asirceshi ya zama d'an hannu.
Ibrahim ya kalli Mahaifiyar tasu yace haba Hajiya Mumtaz fa yarinya ce mai hankali da tarbiyya bata damu da dukiya ba kwata kwata haka ma i'yayen ta mutanen kirki ne.
Hajiya tace yimun shiru mara kunya harni zaka kalla kace mun iyayenta mutanen kirki ne,to waye ba na kirki ba?tambayar ka na keyi kabani amsa mana?.
Amal tayi saurin cewa kiyi hak'uri Hajiya don Allah kidaina zagin Mumtaz a gaban ta babu dad'i i'rin wannan gaskiya Momi...tun kafun ta k'arasa ta wanke ta da mari tana masifa kamar wata zautatta.
Ke dan ubanki dani kike ko da ubanki?I'na cewa yanzu kika had'ani da ubanki wai na zagi Mumtaz k'anwar uwarki ko?to bari kiji wallahi tallahi ba don yau ke y'ata ce ta cikina ba yau da kinga i'skanci muraran.
Don haka this is the last worning idan kika k'ara kai k'arata wajen ubanku saina naka saki banza mara sanin ciwon kanta.
Duk abunda Momi tayi Mumtaz na kallon ta kuma tana jinta amman ba tace komai ba,saboda yadda ta d'auki Momi kamar mahaifiyar ta don haka Mumtaz ta tashi ta koma gidansu ba tare da tace komai ba.
Amal tabi k'awar tata da kallon tausayi don tasan Duk wanda aka yiwa wannan zagin to tabbas sai yaji aranshi babu dad'i,don zagine na cin mutunci duk mai hankali idan aka yi mishi wannan zagin sai yaji a zuciyarshi babu dad'i.
to haka dai rayuwa ta dinga tafiya har kawo i'yanzu da Mumtaz da Amal suke makarantar gaba da primary wanda Alhaji Mahaifin Amal shine ya d'auki ragamar karatunsu.
*Cigaban labarin*
Mu'taz ya kira Murat yafi sau goma amman bai d'aga ba, Cen aka d'auki wayar Mu'taz yayi saurin cewa haba abokina me yasa baka d'aga waya akan kari?.
Muryar wata yarinya yaji tana cewa to A'i saika k'ara kira mai wayar baya kusa,ta d'an d'aga murya kad'an tace Honey ana kiranka awaya.
Mu'taz kuwa don haushi bai jira abunda zaice ba,ya kashe wayar saboda haushin Murat ya keji sosai ba don Murat Amininshi neba da tuni ya rabu da shi yayi yadda yakeso tunda rayuwar daya zab'arwa kanshi kenan.
Ya rasa gane kan Murat da i'rin halinshi nasiha dai i'ya gwargwado yayiwa Aminin nashi amman haryanzu bai daina tsallake 2 nashi ba.
Kullum shine d'aukar Babys amota suna yawo shine gidan Club babu wanda baya zuwa yana sha shanci da k'arawa kai zunubi.
K'arar wayarshi ce yasa ya juya ya duba Life๐ya gani ajiki,sunanda suke kiran junansu dashi kenan don tun suna k'anana shida Murat suke kiran junansu dashi saboda yadda suka shak'u sosai da juna bacci ma tare sukeyi.
Murat yace Mu'taz don Allah kayi hak'uri Na d'an shiga Band'aki ne so shiyyasa,Mu'taz yace babu komai naji,Amman Murat meyasa kullum kake tuba kake koma wa ruwa ya kamata kayi k'ok'ari kadaina bin matannan ba Kai kad'ai bama duk wani Mai bin Mata k'arshen shi na dama.
Murat yayi wani gauron numfashi sannan yace Babu komai Wallahi wannan d'in ma akasi aka samu,Mu'taz yace babu komai Amman dai kayi k'ok'ari ka daina.
Duk abunda suke yi Hanan tana jinsu awayar ta samu waje ta zauna zuciyar ta nayi Mata k'una,tabbas zuciyarta tana son kasan cewa da Murat a matsayin miji.
Amman ya zamar Mata dole ta Rabu dashi tun yanzu gudun samun matsala,Amman ta Yaya zata rabu dashi don tana matuk'ar son Murat.
*UMMU MAHER CE*
*Vote*
*Share*
*Comments*โ๐ป
*Tyiping๐๏ธ*
ABOUT MY WORKโ๐ป
๐๐๐
(แฆหโฃหแฆ)(แฆหโฃหแฆ)
*AKAN A'IKINA 2021*
(แฆหโฃหแฆ)(แฆหโฃหแฆ)
๐๐๐
Written by
Rabiatu.B.Abdullahi๐ค๐ป
(Ummu Maher)Miss green๐๐
ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
_________________
______
๐
๏ธ๐ฎ๐ฟ๐๐บ๐ฎ๐ถ ๐
ฆ๏ธ๐ฟ๐ถ๐๐ฒ๐ฟ๐ ๐
๏ธ๐๐๐ผ๐ฐ๐ถ๐ฎ๐๐ฒ๐ฑ๐๐
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_
๐๐ ๏ธ๐ ฆ๏ธ๐ ๐
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.