Complete Hausa Novels

Akan Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 5 of 21

*BABI NA 7&8๐Ÿ“*

Wannan dalilin ne yasa Mumtaz da Amal suka taso tare komai suke yi hatta abinci tare suke cinshi,suna son Junansu sosai da sosai.
hatta bacci wani lokacin tare sukeyi,I'dan safiya tayi Mumtaz ta koma gida duk ranar da basu kwana tare ba kuwa to Da sassafe zasu had'u don har mafarkin junansu sukeyi.
Mumtaz bata da tsoro ko kad'an,Amal kuwa akwai ta da tsoro don y'an gidansu ma sun santa da tsoro kamar farar kura.
Koda fad'a Akeyi da Amal to ka tabbata sai Mumtaz ta shiga ciki anyi da'ita saboda i'ta daman tun tana k'arama bata da tsoro ko kad'an hakan ne yasa yara suke tsoron Mumtaz.
Hajiya Mahaifiyar Amal bata san Wannan alak'ar tsakanin Mumtaz da Amal,A cewar ta wai Mumtaz zata shafawa Amal gayyar talauci,Shiyyasa take ta k'ok'arin rabasu ta k'arfi da yaji.
Saidai duk wannan abun da takeyi bai saka yaran sun daina son junansu ba,Gashi kullum Ibrahim Yayan Amal ya dawo daga wajen Aiki sai ya tambayi Mumtaz I'dan kuwa bai ganta ba to sai yaje gidan.
Hakanne yake k'ara tunzura Hajiya Wato mahaifiyar Amal,don gani takeyi duk Mumtaz ta kwace mata iyalai,don Alhaji Yanzu taimakon su Mumtaz yakeyi sosai.
Hajiya fa ta dage sai ta raba,Amal da Mumtaz iyakar k'arfin ta,don wataran ma Idan Mumtaz tazo gidan korar ta takeyi ko kuma tayi ta zagin iyayenta wai matalauta matsiya ta.
Zagi dai kala kala babu wanda Mumtaz bata shanshi awajen Hajiya,abun takaicin kuwa i'dan Mahaifin Amal yana nan bata nunawa Mumtaz wani abu ballantana ma har wani ya gane meke faruwa.
ko kud'in makaranta idan Alhaji ya bawa Mumtaz fakar idon Alhaji a keyi ta karb'e,Idan Amal tayi mata magana yanzu ta zane ta wannan abun ya tsayawa Amal aranta don tsakani da Allah bata jin dad'in yadda Mahaifiyar tata takeyiwa Aminiyarta.
Don haka rannan ta shiryawa Uwar tata tsiya ta d'au aniyar sai ta gayawa Dadynta don du abunda mahaifiyar tata ta keyi bai sani ba.
Rannan suna Zaune dukkansu Afarlo har Mumtaz,sai kuwa Amal ta kar kace bakinta tace Dady zanfad'a maka wata magana,Dady ya gyara zamanshi yace to Uwata ina jinki wani abune ya faru?.
Eh Dady daman nadad'e inason in fad'a maka akan abunda Momi ta keyiwa Mumtaz ne?Ai kuwa sai Momi tace to Uwar y'an sharri kedai kamar canza mun ke akayi mai bak'in hali kawai,kuma kirufa mana bakinki anan Noncense kawai.
Alhaji yace haba Hajiya ki tsaya mana yarinyar ta fad'i gaskiyar ta Tafara magana kin tsayar da'ita meye dalilinki?to banason i'dan ina magana da yara na kina saka mana baki kina jina ko?.
Momi kuwa abunnan ya k'ona mata rai ta kasa cewa komai sai zuciyarta da take mata zafi,Ita kuwa Mumtaz batason Amal ta fad'awa Dadynta wannan maganar don zai i'ya haddasa musu rigima k'arshe a dawo da abun kanta.
Alhaji yace ina jin ki Mamana me Mamanki ta keyiwa Mumtaz yanzu in d'auki mataki akanta,sai kuwa Amal tace Dady wallahi Mama kullum idan Mumtaz tazo nangidan saita zageta wai y'ar matsiya ta y'ar talakawa,Wallahi Dady wataran ma idan ka bamu kud'in skull karb'e na Mumtaz, ta keyi wataran ma ta hanata shigowa gidannan wai ita bata gaji Arzik'e ba.
Alhaji fa ranshi idan yayi dubu to yab'aci don me Hajiya zata dunga wannan jahilcin I'ta ta manta a yadda ya Aure ta take Mahaifin ta Saran icce yakeyi Amman bai talaucinsu ba ya Aureta amman yanzu har tana da bakin zagin y'ay'an mutane.
Kwala mata kira Alhaji yayi koda tazo yaci mata mutunci sosai yace kuma duk ranar da ta sake yiwa Muntaz wani abu to Wallahi bai yafe mata ba,Hajiya kamar ta shak'e y'ar tata saboda haushi.
Nandai taringa bashi hak'uri amman ko sauraron ta baiyi ba yayi tafiyarsh,yana mai jin haushin matar tashi don ko kusa bai kawo abunda ke faruwa zai faru ba.
Ibrahim ya kalli Mahaifiyar tasu yace Gaskiya Hajiya wannan halin bai dace ba kwata kwata,don Allah yayi mutun cikin talauci ba yana nufin baya sonshi ba,A,ah sai don Allah yagwada imanin mutun amman bai kamata mutane suna k'ok'arin nunawa ubangiji izza ba.
Hajiya tace yumun shiru sallamammmu kawai sunje sun tsaface ku dukkanku bakwa ganin laifinsu,kullum yabonsu kukeyi mutanenda talauci gadonsu ne abarsu suyi abunsu mana amman wai taimakonsu sukeyi.
toni bana cikin wad'anda aka sallama,don haka ni bana cikin wadanda aka sallama.

kuti hakuri nqyi tyiping kad'an wani uzuri ne ya rik'eni.

*UMMU MAHER CE*

*Share*
And
*Comments*
*Tyiping*๐Ÿ–Œ๏ธ
_ABOUT MY WORK_โœ๐Ÿป

๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š
(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)
*AKAN A'IKINA 2021*
(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)
๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š

By Rabi'atu.B.Abdullahi๐Ÿ‘‰๐Ÿป
(Ummu Maher)Miss green๐Ÿ’š๐Ÿ“—

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…
_________________
______
๐Ÿ…™๏ธŽ๐—ฎ๐—ฟ๐˜‚๐—บ๐—ฎ๐—ถ ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ๐—ฟ๐—ถ๐˜๐—ฒ๐—ฟ๐˜€ ๐Ÿ…๏ธŽ๐˜€๐˜€๐—ผ๐—ฐ๐—ถ๐—ฎ๐˜๐—ฒ๐—ฑ๐Ÿ“š๐Ÿ–Š
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_

๐Ÿ”๐Ÿ…™๏ธŽ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ๐Ÿ…๐Ÿ”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.