Akan Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 2 of 21
*BABI NA 2*๐
Malam kazo da sauri Mumtaz tana zubar da jini da sauri "Alhaji yace to Mumtaz d'ince babu lafiya yanzu Malam yake fad'amun bari muyi sauru mu tafi Asibiti kiyi sauri ki fito da'ita.
Umma tayi saurin komawa gida ta fito da Mumtaz suka tafi Asibiti,shan kwanarsu kefa wuya su hancin motarsu Amal ya kawo kai Amal tace Mama kamar Motar Dadyne naga yafita daga gidan kuma naga yana sauri sosai Allah dai yasa lafiya Mama tace to Amin.
Amal da zumud'inta ta nufo gidansu Mumtaz tana son ta nuna mata kayan da ta suyo akasuwa sai taga gidan Arufe an saka kwad'o ta ce Afili to yau kuma ina su Umma suka tafi dukkansu Allah dai yasa lafiya tayi saurin komawa gida don gayawa Mamanta.
Likitan tace Alhaji munyi iya k'ok'arinmu don ganin cikin jikinta ya tsira Amman hakan ya faskara sakamakon maganin zubarda ciki da tasha.
Malam da Alhaji harda Umman Mumtaz saida abun ya tab'asu sosai sakamakon jin wai Mumtaz ce take da ciki ne da'ita to waye yayi mata cikin? suka had'a baki wajen fad'ar hakan likitan kuwa har tayi tafiyarta ta barsu anan sunata sambatu su kad'ai.
Banko k'ofar da'akayi ne yasa Mumtaz bud'e idonta da k'er don jin yadda sukayi mata nauyi sosai kamar ba jikinta idon yake ba.
Umma tace Wallahi Mumtaz kin cuceni yanzu daman cikine dake kika d'aukomun abun kunya kinsan kuwa abunda kika Aika ta,yanzu duk i'rin tarbiyyar da muka baki abanza saida kika zubar mana da mutunci yanzu sai ki fad'amun waye yayi miki ciki,eyeh dake nake kike kallona munafuka,Kuka na shigayi ina cewa Wallahi Umma ban zubar muku da tarbiyyar da kuka bani,k'addarace tafad'amun Umma ta k'ara sha k'o Mumtaz tana tambayar cikin d'aga murya wanda duk wanda ke kusa zai iya jin ta.
Su Alhaji ne da Malam mahaifin Mumtaz suka shigo cikin d'akin saboda yadda suka jiyo hayaniya cikin d'akin,Alhaji yace haba Umma kiyi hak'uri ki k'eleta tayi mana bayani da kanta,Umma ta saki Mumtaz tana haki tare da hararar Mumtaz.
Alhaji yace Mumtaz ki fad'i tsakani da Allah Muntaz ki fad'a mana waye yayu miki ciki,domin idan kika b'oye mana Allah yana sama yana kallan ki don haka ki fad'ama na kinji.
Mumtaz ta share hawayen da ya b'ata mata fuska tace hak'ik'a zan gaya muku gaskiya,Alhaji yace to Mumtaz muna jinki?Muntax tayi shiru tabbas tana son gayawa i'yayenta gaskiya Amman tana tsoron Abubda zaije ya dawo domin tasan Iyayenta baza su tab'a i'ya jayayya da iyayen wanda yayi mata wannan Aika Aikar ba saboda nesa ba kusa ba sunfi duj yadda kake tunani kud'ine dasu kamar Bankin CBN saboda suna da kud'in da ko shugaban k'ada bazai had'a k'afa dasu ba,koda Kuwa Alhaji ne Mahaifin Aminiyarta Amal.
don haka sai tayi k'arya dacewa,Don Allah Umma ku ya feni hak'ik'a wadannan mutanen da suka saceni wata biyu da ya wuce har nayi tsawon wata biyu agidansu sune suka yimun wannan Aika Aikar mu biyarne y'an mata kuma duk saida suka lala ta mu.
Alhaji yace to meyasa Mumtaz baki gaya mana ba don mu d'auki mata ki kinga yanzu gashi sun sakaki cikin wani hali muma sun saka mu tabbas biri yayi kama da mutun tabbas nasan Mumtaz ba mazina ciya ce ba bazata tab'a Aikata abunda kuke zarginta dashi ba.
Malam ya shard'e wata zufa da ta tasomai yace hak'ik'a nafi kowa sanin halin Mumtaz yarinyace kamila maijin tausayin iyayenta akoda yaushe gata da Addini,hak'ik'a mungodewa Allah da yasa cikin ma ya zube saidai muce Allah ya bata lafiya dukkansu suka Amsa da Amin.
*Asalin labarin rayuwar Mumtaz da kuma abunda ya shafi rayuwarta dan gane da cikin da akayi mata*
โ
โ
โ
โ
Tunda Muntaz ta taso da wayonta taga iyayenta suna cikin wani matsanancin talauci sosai,hakan yasa ta taso da jin tausayin iyayenta duk abunda tasan zata tai maka musu dashi tanayi indai baifi k'arfinta ba akan Aikin gida tun tana k'arama take Aikin gidansu,sannan Mahaifinta yana faskare dashi suke ci suke sha don haka duk ranarda Mumtaz taga Mahaifinta ya tashi zai tafi Aikin faskare sai ta tashi tace nima Malam zan bika,don gaskiya bazan iya bari kana shan wahala ba jibi yadda fa hannunka yake duk ya farfashe,Sai Malam yayi dariya yace Mumtaz kenan kinga duk aikinnan da nakeyi don ke da mahaifiyarki ne don hakk'inku yana kaina kuma sannan inason insakaki makaranta kiyi karatu kinji,sai Mumtaz ta wangale kyakkyawan bakinta tace Malam nidai i na girma inason inzama irin matar nan da kullum kake jinta aradion ka wadda take shiri nima inason inzama mai Aiki a gidan Radio don in taima ka muku da jama'ah baki d'aya.
Malam kuwa inda sabo ya saba don kusan kullum sai sunyi wannan hirar da y'arshi tilo aduniya wato Mumtaz ya lura yarinyar ta taso da wani ginshik'i azuciyarta wanda ta keso ta cika burinta akanshi Ma'ana tana son ta zama ma'aikaciyar gidan Radio ma'ana y'ar jarida don haka duk ranarda wannan zancen sai yaji yanason ya cika mata burinta,don haka sai yace Mata babu komai Mumtaz Insha'Allah zaki cika burinki na zama y'ar jarida don ni zan tabbatar miki da kin cika burinki don Insha'Allah zan sakaki makarantq don kema ki amfana da karatu kinji.
Suna wannan abun Kullum Umma sai ta lab'e tana jinsu cike da sha'awar y'arta da mijinta Allah ya sani suna son su bunk'asa rayuwar yarinyar wajen sakata makaranta don ta Amfana Amnan ya zamar musu dole wajen cikawa Mumtaz burinta bunk'asa karatunta har ta zama y'ar jarida kamar yadda kullum take muradi.
To fah wasa farin girki don yanzu wannan labarin ya soma kubiyoni don jin tarihin Mumtaz kachokan.
*Ummu Maher ce*
*Vote*
*Share*
And
*Comments*โ๐ป
*Tyiping*๐๏ธ
ABOUT MY WORKโ๐ป
๐๐๐
(แฆหโฃหแฆ)(แฆหโฃหแฆ)
*AKAN A'IKINA 2021*
(แฆหโฃหแฆ)(แฆหโฃหแฆ)
๐๐๐
*Labarin gaskeโ๐ป*
Na
*Rabi'atu. B.Abdullahi*
(Ummu Maher)
Miss green๐๐
ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
_________________
______
๐
๏ธ๐ฎ๐ฟ๐๐บ๐ฎ๐ถ ๐
ฆ๏ธ๐ฟ๐ถ๐๐ฒ๐ฟ๐ ๐
๏ธ๐๐๐ผ๐ฐ๐ถ๐ฎ๐๐ฒ๐ฑ๐๐
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_
๐๐ ๏ธ๐ ฆ๏ธ๐ ๐
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.