Complete Hausa Novels

Akan Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 9 of 21

BABI NA 15&16๐Ÿ“

Hanan tace Allah Umma kinyi kama sosai da mai martaba sosai wallahi,don ni da naganki ba kiji yadda gabana yake fad'uwa ba wallahi don tunda nake ban tab'a ganin i'rin wannan kamar ba don ko mu da muke y'ay'anshi ba muyi kama da shi haka ba.

Dariya Umma ta kuma yi a karo na biyu don i'ta abunma dariya ya bata,tace Hanan kenan a'i ita kama haka take ba kiji ance babu wanda akayi kamanninshi shi kad'ai illa Manzon Allah(S.A.W)to bayan shi kuwa gaskiya ko wacce kama da y'sr uwarta,Amman nasha ganin mutanan da suke yi n kama sosai don wani ma in baki sani ba sai kice y'sn uwan juna ne.

Nan dai sukayi ta hira a junansu gwanin sha'awa daga k'arshe Hanan tayiwa Umma kyautar kud'i masu yawa Umma tayi ta godiya sannan na rako ta k'ofar gida ta hau motarta,ni kuma na koma gida ina jin dad'in yadda muka sha hira nida Hanan sai na tsinci kaina a mai tunanin Amal don bata bari na in zauna ni kad'ai ma ballan tana har inyi tunanin wani abu.

***************
A yau ne sakama kon jarrabarwamu ya fito na Waec&Neco don haka nayi saurin zuwa in dubo saka makona Alhmdh na ringa fad'i don jarrabawa ta tayi kyau sosai,Ina cikin murna na dawo gida don sanar da Umma cewa naci jarrabawa har nayi hanyar gida sai kuma na tuno da Malam wato mahaifina don in kai mishi yaga sakamakon jarrabawar don zan i'ya cewa Malam yafi Umma damuwa da karatuna.

Da murna ta na i'sa shagon ina zuwa na fad'a tare da Sallama alokacin yana gyara kaya akan trader d'inshi,ya juyo yace Mamana har kin dawo daga dubo jarrabawar?Nace eh Malam na dubo kuma sakamakona yayi kyau sosai,Malam yace Alhmdh Allah yayi miki Albarka Mamana kuma Allah yasa Albarka acikin A'ikin ki.

Nace Amin Malam nima ina godiya da ka sakani makaranta har nazamo yadda na zama yanzun Allah yasaka maka da Alkhairi yabarmu tare,Malam yace Amin amman fa ba nikad'aine nasha wahala wajen biyan kud'in makarantar kiba harda Alhaji Don shima ya taka gudummawa Arayuwarmu baki d'aya saidai muci gaba da yimishi Addu'ah ta samun nasara arayuwa.

Amin Malam kullum sai nayi tunaninsu ko wani hali suke ciki gashi ko number d'insu bamu dashi ballan tana in kirawo inji muryarsu,Malam yace A'i jiya yasaka wani ya kawomin wayarshi wai ya kawomun mugaisa.

Nace kai Malam shine baka kirawo niba mungaisa,Malam yace to A'i kinga wayar ba tawa bace shiyyasa amman yanzu zan sai waya sai mudinga gaisawa nace to shikkenan hakan ma yayi.

**************
Meema tace Murat kasan Allah bazaka ringa raina mun wayo ba kana cemun wai Har yanzu baka gama target d'in ba,abunda muka tsara shine kafun yayi wannan tafiyar tashi zamu A'ika ta komai don yana da kyau ace yanzu kasan inda yake maka ciwo ya mayar dakai kamar wani oganka sai abunda yace ka keyi wai shi gashi mai kud'i.

Murat yayi murmushi sannan yace Meema kenan kinsan nafiki hankali da kuma ilimi sannan na fiki Zak'uwa akan abunda zan A'ikata amman yana da kyau ace kasan yadda zaka tafiyar da tsarin A'ikin ka kinga kuwa dole saidai mubi a sannu har Allah ya cika mana burinmu.

Meema tace Hmm nifa kasan Allah Muta'z d'innan mugun haushi yake bani taurin kanshi da kuma jiji da kanshi yayi yawa,shifa ko kallon mata ba yayi ballan tana ma har ayi tunanin wani abu,nasha d'ana mai tarko ina tura masa mata gidanshi wai don suja hankalinshi amman duk abanza babu wani abu da ya cigaba.

Murat yayi dariya i'rin tasu mugaye yace Hmm A'i kuwa zaki dad'e kina ai kawa Muta'z karuwai don shifa yadda kika san ba Namiji ba haka Allah yayi shi kwata kwata baya koda sha'awar y'an mata ballan tana har asamu abunda akeso ta wannan hanyar.

Meema tayi dariya sannan ta tashi ta bud'e fridge ta d'auko wani swan mai sanyi ta kora shi sannan ta d'aukoshi a hannun ta tana tafiya tana yanga kamar zata fad'i don i'ta Meema i'rin matan nanne sirara k'ugun ta kamar zata karye saboda sirantar tata har tayi yawa.

Murat kuwa tuni ya kwalalo mata manyan eyes d'inshi yana kallon Meema dasu donshi Gaba d'aya idan yana ganin Meema baya i'ya komai saidai duk yadda yake jin ta aranshi bata kai Hanan ba don Hanan ji yake indai bai Aureta ba komai zai i'ya faruwa.

Baisan sanda Meema ta zauna ba sai jin muryarta yayi tana cewa Murat ka kwantar da hankalinka kaji Insha Allah Akwai wata hanya da zanbi wajen naga ba ruguza rayuwar Muta'z amman ba yanzu zan gaya maka ba don nasan halinku na maza sai kayi amfani dani wajen biyan buk'atarka daga ka gama kuma ka jefar dani kan titi inda ka kwaso ni๐Ÿ˜.

Murat yayi dariya yace haba haba Meema ni na'isa in wulak'anta ki i'dan na wulak'anta ki in zauna dawa ki tuna fa duk abuna bazan tab'a mantawa dake ba don kinfimun duk sauran mata na duniyar nan.

Nanfa Meema taji dad'in wasa ta da Murat yayi taci gaba da shararomai zance tare da siyeshi da abubuwa kala kala i'rin nasu na y'an bariki shi kuma ya sakar maya hannun Aljihu ta d'ibi yadda take son kwasa.

*Wa nene Murat*

Murat dai shine asalin sunanshi wanda i'yayenshi suka saka mai,Mahaifinshi yakasance d'an asalin jihar Kano a unguwar Rijiyar lemo, Sunanshi ee'ro magini wanda babu inda baya zuwa acikin Nigeria don yin A'ikin gini kwararre ne sosai yayi Aurenshi da matarshi mai suna Maryam i'tama y'ar asalin jihar kano ce Unguwarsu d'aya da i'ta.

Sun dad'e Allah bai basu haihuwa ba saida sukayi shekara Goma da y'an watanni sannan ta haifi d'an ta Namiji suka saka mai suna Murat,Suna son Murat sosai.

Tashi d'aya Malam ya koma Bauchi don akwai wata ma'aikata ta masu gini don haka ya tattara iyalanshi suka tafi Bauchi,Kwanansu Hud'u da zuwa Bauchi aka kirawo ee'ro Aikin gini agidan sarauta Yaji dad'in Aikin sosai don ko babu komai yasan zasu samu kud'i sosai don haka yayi sallama da matarshi ya tafi.

Abu da ajali suna cikin Aiki bulo ya fad'o masa atake kuma rai yayi halinshi,don haka aka kai gawarshi hidanshi don a sallaceshi,Matarshi Maryam tayi kuka sosai kamar ranta zai fita alokacin Murat yana d'an shekara bakwai 7 amman duk da haka saida yagane mahaifinshi ya rasu.

Watan ee'ro biyu da rasuwa Maryam ma tabi mijin ta i'tama Allah yayi mata rasuwa,Shikkenan Murat ya dawo maraya babu uwa babu uba,don haka Aka kaishi gidan sarkidon a nemo y'sn uwan i'yayenshi.

Kwananshi hud'u da zuwa gidan sarki Sukayi sabo sosai da Muta'z wanda yakasance d'a tilo da sarki donko bacci Tare su keyi da Murat.

*Ummu Maher ce*โœ๐Ÿป

Vote
share
And
Commentsโœ๐Ÿป๐Ÿ’Œ๐Ÿ“ฉ
*Tyiping*๐Ÿ–Œ๏ธ

ABOUT MY WORKโœ๐Ÿป

๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š
(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)
*AKAN A'IKINA 2021*
(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)
๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š

*NA*
*RABI'ATU.B.ABDULLAHI*
(Ummu Maher)Miss Green๐Ÿ’š๐Ÿ“—

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…
_________________
______
๐Ÿ…™๏ธŽ๐—ฎ๐—ฟ๐˜‚๐—บ๐—ฎ๐—ถ ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ๐—ฟ๐—ถ๐˜๐—ฒ๐—ฟ๐˜€ ๐Ÿ…๏ธŽ๐˜€๐˜€๐—ผ๐—ฐ๐—ถ๐—ฎ๐˜๐—ฒ๐—ฑ๐Ÿ“š๐Ÿ–Š
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa _

๐Ÿ”๐Ÿ…™๏ธŽ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ๐Ÿ…๐Ÿ”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.