Complete Hausa Novels

Akan Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 19 of 21

*Shafi na 40&41*

Gaye ya ce"kai Morris ba ka da hankali ne zaka je ka tona mana asiri to karka soma wallahi don ni fyed'ewa yara yanzu na fara,kai kanka kasan idan Aure muka ce za muyi ina Mike da kud'in Auren?"Aure ya zama tamkar wani ciniki ka ga ai gwara mu more sosai kafin mu samu kud'in Auren tunda ga yaran nan ana sakinsu kamar wasu dabbobi.

"Kai Morris wallahi jiya Dana je wata unguwa naga yara mata suna ta wasansu a unguwa wasu da wando basu kuma babu wallahi baka ji yadda naji tausayin yaranba shin iyayensu kuwa suna sonsu kuwa?" Gaskiya ni dai bazan bar y'ay'ana a titi ba Wallahi,kuma indai iyaye basu daina barin y'ay'ansu saka_saka ba ba za'ah daina yi musu fyed'e ba"ya fad'i hakan yana kunna sugari yana zuk'arta kamar ya samu wata alewa.

Dai dai nan ya gama d'aukar video din su sannan ya yi gidan yayansa don kai mai rahoton wad'anda suka yi wa y'ar yayan nasa fyed'e.

"Innalillahi wa inna Ilaihi Raji'un"

"Yanzu daman ba yaron nan ne ya aikata wannan fyed'en ba?kai Amman mun cuce shi kuma sai Allah ya saka mishi."

Mahaifin Fiddausi ne ya ke fad'ar hakan yarinyar da aka yiwa fyed'e.

Shamsu wato k'anin Mahaifin Fiddausi ya ce"wallahi Yaya Allah ne ya toni asirinsu na taho zan tafi Aiki na hangosu a kusa da wani kango,daman kuma da ta mu dasu saboda mu y'an cumity da y'an Daba bama shiri so shiyyasa na taho don ganin abinda ke faruwa don ansha kawo mana k'ararsu i'sa ta ke da wuya na ji suna irin wannan maganar babu b'ata alokaci na fara yi musu video."

"kai Masha Allah yanzu saimu d'unguma muje police station don mu gudanar da wannan hujjar shima a sakesa a kama wad'annan azzaluman muna fukai masu

"Kai masha Allah" Allah ya k'ara tsare mana yaranmu".

Amin.

★<><><>★
"Haba Fulani wannan wani irin kuka ne da ya zama na kullum kada ki k'ara jawa kanki wata matsalar fa"?.

Shiru Fulani ta yi tana kallon mai Martaba ba tare da ta ce komai ba ta tashi ta koma d'akinta sannan ta cigaba da kuka yanzu sai d'anta ya yi shekara sha hud'u a gidan yari bai mori k'uruciyarsa ba?kai ko wanene ya yi wa d'anta sharri Allah ya Toni asirinsa da gaggawa.

Mai Martaba kuwa kallon Fulani ya yi sanda ta tashi ta koma d'akinta,Hawaye ne ya fito a idanun Mai Martaba ya goge idanunshi harga Allah shi yasan abinda ya ke damunsa akan wannan abin Ya Allah ya bayyana duk Wanda ya yi wa d'ansa Sharri har saukar Ak'urni mai girma yasa a ke yi wa Yarima akan Allah ya toni asirin ko su wanene suka yi wa d'ansa sharri,tunda aka kulle Yarima Mai Martaba baya bacci saboda tunanin d'ansa.

Ya kalli gefensa ya tuno sanda gidansu yana cike Ga Hanan ga Muta'z sun saka Mai Martaba a tsakiya ga kuma Fulani da Mahaifiyarsa Hajjo kullum farlon cike ya ke da Iyalai, amman yau babu kowa,yana cikin wannan tunanin yaga kiran wayarsa yasa hannu da k'er ya d'auka.

"Iye..iye..iye to gani nan yanzu zanzo Allah na gode maka ganinan zuwa yanzu kuwa".

Da k'er Mai Martaba ya gama wayar yana had'a kalamai da k'er,kirawo Fulani ya yi awaya ya shaida mata abinda ya faru da gudu Fulani ta fito har tana had'a hanya da karun gidan suna ta kallon ta suna tunanin me yasa Fulani gudu haka Amman koma menene abin babba ne.

<><>,>,

Muta'z ya rasa farin ciki ya ke ko bak'in ciki Allah ya wanke shi cikin ruwan sanyi,da gudu ya rungume Fulani da Mai Martaba yana kuka,Fulani ta kalli d'an nata yau wata d'aya kenan da faruwar lamarin Amman gaba ki d'aya d'an nata ya canza gashin kansa duk ya cukur_kud'e abin tausayi.

An kamo su Gaye da Morris tambayar duniya suka cw ba wani ne ya saka suba sune suka aikata hakan da Kansu,Ai kuwa aka k'ulle su Suna Nadamar abinda suka Aikata.

Ban hak'uri Iyayen Fiddausi suka rink'a yiwa Mai Martaba duk da Basusan Muta'z d'an sarki bane sai yanzu,nan fa suka ringa yabawa Mai Martaba k'ok'arin shi na sakawa a kulle d'an shi duk da kud'in da ya ke dashi.

Nan fa y'an jarida suka cika wajen kafin ka ce me harda su Mumtaz a wajen suna mamakin yadda abin ya faru,Mumtaz ta yi k'asak'e tana kallon Muta'z duk daman kowa ya fad'i irin halin shi Mai kyau.

Ko wanni d'an Jarida ya saka lasi fik'arsa wajen bakin Muta'z don jin abinda zaice,Kawai sai kallonshi Ya kai kan Mumtaz wacce ta fara yad'a labarin Fyed'en da aka ce ya yi wa wata yarinya.

Kallon Banza Muta'z ya aikawa Mumtaz sannan ya zari lasifik'ar hannunta da k'arfin gaske Wanda har ciwo sai da ya jiwa Mumtaz, abinka da farar fata sai ga wajen ya yi jajir harda jini.

Sai da ya k'ara yi mata kallon banza kallon alamar zamu had'u sannan ya fara magana kamar haka..........."

Kash! naso inji abinda zai faru Amman idan na ga ruwan sharhi gobe zan k'ara Rubuta.

Daga
Ak'alamin

Ummu Maher

Vote
Share &Comments
*🪦✨AKAN AIKI NA✨🪦*

Book 2 sabon salo📖✍🏻

Na
_*Rêãl🌹 Oum Maher*_
(Mîss gréén💚)

*MATAR BASH💎*

📲MINAL MULTIMEDIA
https://youtu.be/NCrdsZmuh6E

Dan Allah kushiga ku danna Mana subscribe

_*📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION*✍🏻_

42/43

Jikin Mumtaz ne ya yi wani irin sanyi ganin kallon da Muta'z ya ke yi mata.

Harya gama jawabinsa bata k'ara sanin me ake tattaunawa ita dai taji tashin motoci,sai da kowa ya watse sannan taja k'afafunta da k'er ta bar wajen.

Har taje gida bata daina tunanin irin kallon da Muta'z ya ke yi mata shin d'aukar jawabin da ta ke yi ya zama laifi? Ko kuwa d'aukar jawabin da ta yi ne alokacin da a ka kirawo su zuwa gidanshi shine laifi?

"Ke Mumtaz lafiyarki kuwa ki ka zauna kina tunani haka?kuma me ya samu hannun ki harda jini?".

" Wallahi Umma bugewa na yi to shine wajen ya ke yi min zafi Amman yanzu zanje chemist d'in Sale ya yi min treatment d'in waje babu komai kada ki damu Umma wajen ya yi sauk'i".

Ta fad'i hakan ne don ganin yadda Umman ta damu sosai don tafi kowa sanin halin da iyayenta suke shiga a duk sanda suka ga wani Abu yana damunta.

★<><>★
Wani sabon biki a ka k'ara yi agidan mai Martaba don dawowar Shalelen d'ansa kuma Magajinsa,Murat kuwa yak'e kawai ya ke yi don yadda ya ke jin zuciyarsa kamar zata fashe duk shirinsa akan Muta'z ya war_ware to waye ya lalata mishi shirinsa yasan dai Morris da gaye Mimaa ce ta had'a su akan ce wa Suyi mishi sharrin da za'ah d'auresa har igiya ta yi rara Mimaa ce ta shirya duk wani shirin da aka yi shidai na shi taimakon kawai nuna b'oyayyen gidan Muta'z Wanda ya ke hutawa a ciki sannan ya sace mukullin gidan ba tare da ya gani ba.

Har aka gama shahararren bikin na Muta'z da Mimee,Murat bai iya ce wa k'ala ba daga baya ma sai ya sulale ya bar wajen tsabar bak'in ciki.

Shi kuwa Muta'z a yanzu nunawa Mimee so ya ke kamar me don ya yi matuk'ar tausaya wa yarinyar alokacin da aka kulleshi don da k'er Hajjo ta ke lallab'asa su ta fi gida don yadda ta ke matuk'ar rike cewa Hajjo wataran ma har suma ta ke yi.

Ita kuwa Mimee koda taga yadda Muta'z ya ke nuna mata sai ta dinga wani karai Raye kamar wata Kifi,shi kuwa har dariya ya ke mata don yadda ta ke siririya kamar wata silindium yadda kasan ba ta cin Abinci.

*Bayan buki*

Ko irin kunyar nan Mimee ba ta ji ba ta zage ta ringa yi wa Muta'z soyayya kamar ba Amarya ba kuma ranar farko,Shi kuwa kallon ta kawai sai ya fara tausayinta don matuk'ar ta shigo hannunsa ba za ta ji da d'i ba.

Hakan ce kuwa ta faru don a ranar Muta'z ya nuna mata ba maza bane kuma ba d'aya suke ba a fannin k'arfi da nuna Iko kiran sunan Hajjo kuwa ta yishi babu adadi shi kuwa ko a jikinsa don ita ce ta kawo kanta.

Duk da yadda tasha wuya bai hana ta k'ara son Yayan nata ba don yadda ya iya da ma ce babu dama zaka rantse da Allah daman ya saba harkar Amman ba haka bane kawai dai hallitarsa ce haka.

Koda safiya ta yi Mimee ba ta ga Yaya Muta'z ba koda ta kira wayarsa ma bata same sa ba,ta tashi daga ita sai rigar bacci ta lek'a ta Window ta hango fitar Motarshi daga gidan, kamar taje ta tsayar da motar Amman ya Riga da ya fita haka ta hak'ura ta nufa fridge don nemawa cikinta abin tab'a wa ba tare da ko Sallah ta yi ba ballanta na wankan Tsarki.

★<><>★
Sai da Muta'z ya zauna a Office d'insa sannan ya d'auki wayarsa rai a b'ace ya fara kiran wata number.

"Atiku wai har yanzu bata fito daga gidan bane don wallahi idan wata matsala ta faru akan harkar nan to Ku kuka sa kanku".

Ya fad'i hakan cikin tsawa" Oga ka d'an k'ara jira yanzu ne lokacin fito warta daga gida don haka kad'an k'ara jira.

Cikin fushi ya kashe wayar domin ya shirya komai a lokacin da ya shirya amman suna son b'ata mishi lokaci,Don ya shirya nuna wa Mumtaz kuskurenta na yad'a abinda bata da masaniya akai.

Mumtaz kuwa baiwar Allah tana cen bata San what going on ba.

"Kai Uwata kinga yadda kuwa Abayarnan ta yi miki Kyau kamar wata Balarabiyar Asali".
Malam ne ya ke fad'in hakan ya yinda ya ke kai k'osai bakinsa Ita kuwa Umma tana k'ara sa sakin K'osan.

Dariya Mumtaz ta yi Wanda ya ke k'ara fito da ita, ya yinda ta ke jin fad'uwar gaba sosai aranta ta ce"Malam Amman yau da wuri zan dawo don Aikin babu yawa."

"To uwata Akula da hanya Allah ya bada sa'ah".

" Amin Malam sai na dawo" ta fad'i hakan tana d'aukar k'osai guda d'aya tana ci,Mumtaz kenan akwai zuciyar kula da iyaye d'aukar Albashinta 4 kenan yanzu,da k'er Mlm ya ke tilasta mata don ta siya sutura saboda sutura itace mutum babu yadda za ta yi dole ta ke siya don itama ta yarda sutura ita ce mutum. kuma tana siya musu kayan abinci sosai harda mai da magi Lipton madara kai harda au kwai.

Ni kuwa Ummu Maher na ce muma Allah ya bamu y'ay'a masu son mu Amin👏🏻👏🏻.

Tana fitowa daga gidan ta kalli hannun dama da hagu sai ta hango wani d'an adaidata da alama tafiya zaiyi,da Sauri ta tsayar dashi ta alama da baki.

Tsayawa ya yi sannan ta shiga ta fad'a mishi inda zata je.

Sunyi nisa sosai a cikin tafiyarsu kawai sai taga ya juyo ya shek'a mata Abu a hancinta tun daga nan bata k'ara sanin inda kanta ya ke ba.

*Oum Maher ce*

_*don Allah ku ta yani da Addu'ah akwai wani Abu da ya ke damuna na keson in samu,Allah ya bamu duk abinda muke nema na Alkhairi Amin.*_
*_✨AKAN AIKI NA_ ✨*

✍🏻Ummu Maher(Miss green)💚
44/45

*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION*

Tunda Mumtaz ta tashi daga dogon baccin da ta yi sai taji gaba ki d'aya an d'aure ta akan kujera,ko iya motsi ba ta yi, gashi d'akin gaba ki d'aya duhu ne,ko hannunka ba zaka iya gani ba hankalin Mumtaz ya kai matuk'a a tashi saboda batasan ko ina aka kawota ba.

Ta dad'e acikin wannan hali sannan taji k'arar bud'e k'ofar d'akin,wani k'amshi ya daki hancinta wanda ta ke tunanin ta tab'a jinshi amman bata san a inda ta sanshi ba.

Tsoronta ne ya k'aru a lokacin da taji mutumin yana takowa har zuwa inda ta ke,amman kafin yazo Wani irin haske mai wuyar gani ya haske d'akin,da d'ewar da na yi acikin duhu sai yasa idanu na suka zama kamar na makauniya,na rintse idanuwa naji gaba ki d'aya so nake in bud'e idona inga a i'na na ke,wata kakkausar Murya na ji,muryar namiji wadda itama na ke tunanin kamar na tab'a jin irin muryar,da k'er na bud'e idona don in ga waye wannan.

"İnna lillahi wa İnna İlaihi Raji'un."

"Na san za ki yi mamakin ganina ko?to ba abin mamaki bane don kinga haka ta faru da ke,kuma ki daina mamaki domin yanzu zaki gane tsakanin aya da tsakuwa."

Wasu hawaye ne masu zafi suka fara ambaliya a kyakkyawar fuskata murya ta na rawa Na ce"Don Allah kada ka cutar dani saboda nasan ahalin yanzu iyaye na suna cen suna nema na,don Allah kada ka lalatamin rayuwata kamar yadda ka lalata rayuwar yarinyar.........

Wani ruwan sanyu me kamar k'ank'ara Muta'z ya watsamin har cikin bakina,abinda ban k'arasa maganar kenan ba,wani numfashi mai wahala na furzar sannan na fasa wanu irin kuka.

"A'i ba ki yi kuka ba har yanzu domin kuwa keda farin ciki har abadan abadan,sabida baki isa ki shiga rayuwata ki gurb'ata min ita ba sannan ki ce zaki zauna lafiya".

" Zan cen iyayenki kuma kada ki damu domin inason in d'an d'ana musu yadda nawa iyayen suka ji alokacin da sukuma na ki iyayen suke cikin farin ciki,kinga kuwa dole kema yanzu na ki iyayen suji a jikinsu."

Ya fad'i hakan yana mai janyo dogon gashina da ya warware ya fad'o a gadon baya na,K'ara jan gashin nawa ya yi da k'arfin gaske yana magana da kakkausar murya.

"Kinyi gangancin shigowa rayuwata har ki ke ganin ce wa ya kamata ki yi min sharri,to wallahi tallahi sai na koya miki hankali ta inda ba zaki yi tunanin k'ara yi min sharri ba nonsence kawai".

Ya saki gashin na wa sannan ya fita daga d'akin ya kashe hasken, da k'arfin gaske ya rufo k'ofar ji ka ke gammmmmm....tsabar rufe k'ofar da a ka yi da k'arfi sai da na kusan sakin fitsari a wando.

Sai da na kwana a zaune babu ci babu sha,har lokacin sallar asuba ya yi ban yi bacci ba,tsanar Muta'z na ji a raina da kuma mummunan halayensa,na shiga tsinemai ina magana da k'arfi don so na ke yi ya ji,don duk muguntar da zaiyi min na saka azuciyata baki na bazai tab'a rufuwa ba.

A b'an garen su Mlm kuwa sunyi neman duniya amman ba suga Mumtaz ba, har wajen Aikinsu sai da Mlm ya je amman babu wata maganar da aka samu akan Mumtaz,hankalin Mlm da Umma ya yi matuk'ar tashi sosai,yadda suka ga dare haka suka ga safiya Mlm na kuka Umma na kuka,haka suka kwana suna Sallah suna kaiwa Allah kukansu Akan b'atan y'arsu Mumtaz.

Har Police station Mlm ya je ya kai report amman shiru ka ke ji abin har mamaki ya ke bawa Su Mlm yadda y'ar tasu ta b'ata kamar b'atan d'an mutum ba.

Tun asuba Umma da Mlm suka k'ara fita yawon neman y'ar tasu Hamma har yamma har dare babu labari,Akan dole suka hak'ura zuciyoyinsu kamar zasu fashe don tsabar bak'in ciki,amman da ya ke masu tawakkali ne sai suka fauwalawa Allah tare da rok'onsa akan ya bayyana musu y'arsu abar sonsu wato Mumtaz.

Sai da yamma ta yi alokacin na fara gajiya har na suma tsabar yunwa,na ji an watsamin ruwa, gaba ki d'aya kayana suka jik'e sharkaf ni kuwa sai haki na ke ina kiran sunan Allah.

Haske ya k'ara kunnawa a d'akim wnda yasa na fara tunanin ko a lahira na ke,saboda abin ya yi min yawa ga ruwa ga idanuna da suka koma kamar na makauniya.

Kallona ya shiga yi yana dariya,acikon zuciyarshi kuwa kawai tausayani ya ke ji na d'auko yarinya har gidansu,ganin irin tuanin da ya fara zuwa zuciyarsa kawai sai ya yi saurin ba sarwa,sannan yazo ya kin ceni daga mugun k'ullin da na sha.

Gaba ki d'aya na fad'o jikinsa yarab,tsabar galabaitar da na yi,wani yamm ya ji ajikinsa tsigar jikinsa ta fara ta shi,da sauri ya saki mumtaz ta fad'i ajikin bango,na fara wani irin nishi mai wahalarwa..

_Kuyi manage saboda jikin nawa da sai a hankali._

*Ummu Maher ce*
*AKAN AIKI NA*

Book 3

Ummu Maher(miss green)

46/47
Yanzu Mlm haka zamu saka idanu muna kalllon Y'ar ta b'ata an rasa gane wad'anda suka d'auke mana y'armu,gaskiya yau har Gidan radionsu saina koma don su naga kamar basu damu ba,Umma CE ke ta sababinta tana yi tana share hawaye da gefen zaninta,Malam kuwa yana gefe ya saka handkacif yana goge hawayenda suka zamar masa sabo.

Iya wahala Mumtaz tana Shanta awajen Muta'z Wanda yake jin har yanzu baiyi ramuwar da yake son yi ba,don haka yau ya shirya muguntar da zaiyi mata Wanda baza ta tab'a manta irin muguntar da ya yi mata ba har ta mutu.

Yau ma kamar kullum da kanshi ya kawo mata abinci,Mumtaz ta d'aga idonta da k'er wad'anda suka yi mata nauyi tsabar wahala ta Kalli abincin sai dai duk da yunwar da ta ke ji ba zata iya cin abincin ba saboda wani mugun yaji da Ake zubawa acikin abincin don sai ka kusa zuba fitsari saboda azabar yaji.

Cikin tsawa ya fara yi mata magana "d'auki abincin kici ko kuwa yanzu na gana miki mummunar azaba Y'ar jaridar k'arya mai d'orawa mutane sharri, yau sai kinyi Dana sanin had'a min sharri domin muguntar yau tafi ta kullum.

Tun kafin ya gama maganarsa Mumtaz ta fara cin abincin tana kwallah don sai taga yajin ma yafi na kullum,kai Muta'z ya karanci tsabar mugunta,har ta gama ci yana kallon fuskarta tare da k'ara tsanarta tunda ta kunya tashi a idon duniya dole ne shima ya kunyata ta.

Bata Ankara ba ya fizge kwanan tare da turo mata ruwa nan ta d'aga ta fara kwankwad'a sai da ta shanye sannan ta ajje jarkar a nan ta fara wani bacci mai wahala,shi kuwa Muta'z wani mummunan kallo ya bita da shi tare da yin wata mik'a kamar zai yi aikin k'arfi.

Mumtaz kuwa baiwar Allah sai baccinta ta ke yi a d'akin baccin wahala,shed'an yafara bugawa Muta'z ganga nan fa ya fara aiwatarwa da Mumtaz mummunan k'udurinsa akanta.

Cikin baccin wahala ta fara jiyo wani bak'on lamari yayinda ta fara jiyo wata irin azaba a k'asanta,wani yunk'uri ta yi don ta tashi taga menene?

Abun da ta gani ne yasa gabanta wani mummunan fad'uwa tana rintsa idanunta jin kamar zata mutu saboda azaba,wani irin kuka ta saki mai ban tausayi tana son tashi Amman ta kasa,Muta'z kuwa baima son aduniyar da yake ba don yayi nisa baya jin kira,don tunda yake bai tab'a zuwa wannan duniya mai matuk'ar dad'i ba.

Kuka Mumtaz ta ke tana tausayin kanta dana iyayenta,tun tana k'arama suke kula da ita tare da bata tarbiyya dai_dai gqargwado Amman yau gashi wani abanza ya lalata mata rayuwarta wajen amfani da kud'in da ya ke dashi wajen yi mata fyed'e.

Sai da ya gama ne ya fara kuka da idanuwansa don tunda yake bai tab'a zina ba,yayi zama cikin turawa Amman bai saka ya watsar da tarbiyyar da iyayensa suka yi masa, yana fita daga d'akin ya kirawo wata number tare da bada umarni,shi kuma gaba Ki d'aya ya fita daga Gidan,da k'er ya kawo kansa gidansa yana had'a hanya kamar Wanda yasha wani Abu.

Taji sanda aka bud'e k'ofa Amman bata san ko waye ba don ko d'aga idonta bata iyayi tsabar kukan da taji gashi ko tafiya ba zata iyayi ba saboda azaba.

Wani Abu suka busa mata kamar ranar da suka d'auko ta har suka kawota k'ofar gidansu bata San anzo ba.

Alokacin kusan k'arfe 8na dare ne,suka ajje ta a hankali a soron gidansu,suka taho a hankali cikin sand'a suka shiga mota,alokacin Malam ya dawo daga Sallah ya hango fitowarsu daga Gidan tun kafin ya iso wajen suka shiga motar suka jata da k'arfi suka fita daga layin baki d'aya.

Salati Malam ya saka bayan ya haska soron ya ce"Mumtaz ke ce me suka yi miki,Innalillahi Wa inna Ilaihi Raji'un."

Ummu Maher ce.
*AKAN AIKI NA*

_Ummu Maher (Miss green)_

48&49

Tsananin tashin hankali ranar Mlm ya yi shi,don ganin y'arsa tilo a k'asa kamar gawa baisan yanada wani k'arfi ba, sai yau don gaba ki d'aya ya d'auki Mumtaz ya yi cikin Gidan da ita yana kwallawa Umma kira,da gudu itama ta fito har tana tuntub'e jin ya ambaci sunan Y'arsu Mumtaz,Tayashi rik'e Mumtaz ta yi tana cike da tsoro don ganin y'ar tasu kamar gawa a d'akinta ta kwantar da ita tana faman yayyafa mata ruwa Mlm kuwa yarasa tudun dafawa ga y'arsu Amman tana cikin wani hali Wanda basai an gaya maka irin wahalar da tasha ba,ta rame ta k'anjame abun tausayi wata kwallah Malam ya share yana k'ara kallon fuskar Mumtaz wadda ta ke cikin wani hali na wahala.

Wata irin ajiyar zuciya Mumtaz ta saki a hankali jin hannun Ummanta ajikinta don koda bata bud'e idonta ba tasan waye don bazata tab'a manta sanyin jikin Mahaifiyar taba,da sauri ta rungume Umman tana k'ara sautin kukanta,Malam ma cike da tausayi ya ke kallonsu.

"Don Allah Umma kada kuga laifina Wallahi d'auke ni a kayi aka kaini wani gida aka yi ta azabtar dani AKAN AIKI NA,wallahi Umma kodon samun kwanciyar hankalinku daga yau nabar Aikin Jarida don samuwar kwanciyar hankulanku keda Mlm,sai ta k'ara rungume Umma d'in tana k'ara sakin wani irin marayan kuka na tausayin kanta dana iyayenta.

Likita Malam ya kirawo ya duba Mumtaz d'in tare da yi mata allurai nan da nan sai kuwa bacci ya d'auke ta awajen,Malam yasan Mumtaz zata iya tashi tana jin yunwa don haka ya siyo mata Shayi da baredi hakan kuwa a ka yi tana tashi daga bacci cikin dare Umma ta bata shayin da buredi ta cinye tas kamar mayunwaciya,Umma kuwa tana zaune tana kallon y'ar ta cike da tausayi,koda ta gama kwanciya ta k'ara ba ita ce ta tashi daga wannan baccin ba sai k'arfe 9na safe,tana tashi Umma ta gama dafa mata ruwan zafi,ai kuwa taji dad'in ruwan zafin don ta gasa jikinta don haryanzu tana jin azaba dauriya kawai ta ke yi.

Umman ta kula da haka shiyyasa ma kafin ta fito daga wankan har ta had'a mata abin karyawa tare da ajje mata magani har ma da kayan canzawa,Mumtaz kuwa ta ji dad'in ruwan zafin don ta gasa jikinta sosai kuma Alhmdh ta fara jin dad'in jikinta don har tafiyarta ta fara dawowa dai_dai abinci ta ci sosai nanmq kamar mayunwaciya Umma kuwa tana ta kallonta har dai ta kasa hak'uri tare da cewa"İn ce dai basa baku abinci Mumtaz don daga yadda ki ke cin abinci ya isa ka tabbatar ballanta na duk wanda yaga ramarki yasan dole kinsha wuya".

"Ruwan fiyowata ta k'urba mai d'an sanyi tana jin bugun zuciyarta na k'aruwa na tsoro tare kuma da tausayin iyayenta dama ita kanta," kinyi shiru Mumtaz don wallahi ni nasan wad'annan mutanen koma su waye to basu da imani,an mayar da talaka tamkar wani banza ayi ta cutarsa ana zaluntarsa don an san babu mao tsaya masa,to Ai akwai Allah shi zai shige mana gaba,kuma koda baki fad'a ba Mumtaz daga yau kin daina aikin nan tunda abin ya soma da haka,kai duniya da mutum ya ce zaiyi gaskiya shikkenan ya zama nama awajen mutane,Allah dai ya shige mana gaba."

Har Umma ta gama maganarta bance da ita k'ala ba don ni kad'ai nasan halinda zuciyata ta ke ciki,araina kuwa ina k'ara jaddada rashin tausayi irin na Muta'z baya tunanin shima zai haihu?koma dai ba haka ba ai yana da k'annai me ya ke tunanin zai faru idan hakan ta faru y'an uwansa tabbas tasan hakan sai ta faru ko ba yauba wanda ya yi da kyau ma ya ya k'arke ballan tana wanda bai yi da kyau.

Ni kuwa Ummu Maher na ce Allah ya shiryar samu cikin shiriya madai_ daiciya Amin.

*GERMANY*

Shiri ya ke sosai na komawa gida don ba k'aramar murna ya yi ba jin Hajiyarsa ba ta k'ara yi masa magana Akan Auren da ta ce za ta yi masa ba,gefe d'aya kuma na zuciyarsa yana k'ara jin dad'i don ayau zai had'u da sanyin idaniyarsa,duk da Rabonsa da ya yi waya Manager na wajensu Mumtaz har ya manta don Aiki daya sha masa kai.

Baba megadi yana lek'owa ya hango ubangidansa wato Mukhtar ya washe baki yana jin dad'in ganinsa,sannu da dawowa ya yi mai sannan suka gaisa cikin mutuntawa don yana matuk'ar ganib darajar Megadib don mutamin arzik'ine,haka shima Baba megadin yana matuk'ar ganin darajar Mukhtar don mutumin kirki ne tsabanin Hajiyarsa da igiyar kud'i ke janta don ko gaisuwarsa bata fiye amsawa ba.

Da murna ya shigo gidan nasu don rabonsa da ganin mahaifansa da k'annansa har ya manta,shiyyasa ya ke Allah² da ya gansu sannan ya tafi wajen sanyin idaniyarsa.

Yana shiga main farlon gidan nasu ma'ana babban farlonsu ya hango Hajiyarsa cikin kwalliyar wani tsadaddan leshi mai matuk'ar kyau da tsada sam bai kula da wanda ke wajanba ya taho da sauri yana mai jin matuk'ar jin kewar Hajiyarsa ta sa,Sakinat ce ta shi haushi da bak'in ciki da suka gama cika mata zuciya don ganin ko kallonta Mijin nata baiyi ba,duk da shi har yanzu bai san da cewa Anyi masa Aure ba,Tsananin zafin da Sakinat taji ne yasa ta buga uwar k'ara don taka ta d'in da Sir Mukhatar ya yi wanda shi ba da gayya yayi ba don bai ganta ba harga Allah.

*Ummu Maher ce✍🏻.............*
*AKAN AIKI NA*

_Ummu Maher(Miss green)_

50&51

Juyowa Mukhtar ya yi da sauri don jin ihu a bayansa,sai a sannan ya kula da Sakinat y'ar Gidan k'anin Babansa da ke Abuja.

"Sakinat yaushe ki kazo gari ?haushi da b'acin rai suka taru suka yi wa Sakinat yawa don haka sai ta yi shigewarta d'akin Hajiyar Mukhtar,Y'ar dariya Hajiya ta yi sannan tabi bayan Sakinat don tana son Sakinat Sosai don ita da uwar Sakina Aminai suke tun kafin su Auri y'an gida d'aya.

Sororo Mukhatar ya d'aga kafad'a alamar ko a jiki na ya yi sannan ya wuce dining ya fara bud'e kulolin abincin tuni ya zauna ya cika tumbinsa sannan ya shiga d'akin Hajiya,Sakinat tana zaune kusa da Hajiy a ta cika fam kamar zata yi kuka.

Nuna masa waje Hajiya ta yi Sannan ta ce ina son ka nitsu kaji abinda zan gaya maka,Tun yanzu zan fad'a maka duk d'an da baya farantawa iyayensa sunansa matacce don yana Raye ne Amman kuma matacce ne.

Yanzu zamuje sama Alhaji yana nan daman don yana wani aiki ne daka dawo ban CE ka shiga ba Amman yanzu zamuje,haka Mukhtar ya din ga bin Mahaifiyarsa har zuwa sashen Babansa.

Gaishesa Mukhtar ya fara yi sannan ya tambayesa ya aikinsa ya ce komai Alhmdh,Nan dai Abba ya fara nasiha da jawabi sannan ya wuce kai tsaye ya gaya masa Auren da sukayi masa ba tare da ya Sani ba,tunda Abban ya fara magana kansa A k'asa yana jin kansa kamar zai tsage,koda Abban ya ga haka sai ya cewa Hajiya su tafi,bayan sun tafi ne Abban ya cigaba da yi masa nasiha tare da yi masa albishir d'in duk Wanda ya keso ya kawo masa ita shi kuma in dai mutuniyar kirki ce zai Aura masa,Amman sai ya kula da hakkin k'anwarsa kuma matarsa,Sannan Abba ya ce mai zai fara zama Anan Gidan kafin suga yadda zaman zai kasance,Don gidansu yana cen komai an zuva da kuma masu kula da Gidan kafin a tare.

Koda Sir Mukhtar ya fuskanci Abbansa a zuciyarsa ya CE indai zaka yadda da zab'ina Mumtaz to nima zanso Sakinat kuma zan sota tare da yi mata adalci.

Hajiya kuwa shirya y'arta ta yi sosai,suna yi Sakinat tana mita Hajiya ta mik'o mata wani turare wai ta fesa,ta amsa tana k'un k'uni Hajiya ta ce.

"Yanzu Sakinat a haka zaki mallaki mijin kina sakarci?" To bari kiji matuk'ar kinason Mukhtar ya soki to sai kin koyi abubuwa da dama don janyo hankalinsa ya soki.

Haka Hajiya ta ringa yiwa Sakinat nasiha har ta d'auka tana yiwa Hajiyar godiya,don Sakinat yarinyace shekararta19 don haka Hajiya ta bada k'aimi wajen saito ta kan Hanya,don Hajiya akwai ilimin zama da miji,kissa kisisina da dai sauransu.

*MUTA'Z*

Yana zaune idonshi Alumshe kamar yana bacci Amman ba bacci ya ke yi ba,yana tunanin yadda har ya iya rashin imani wajen ketawa yarinya haddin ta,Shin yanzu idan K'anwata a kayi wa haka yaya zanji?wani Abu ne ya tokare masa k'irjinsa tsantsar tausayin yarinyar ya ke ji Sosai,a haka har Mimee ta sameshi tana kallon yadda ya zurfafa a tunani,ko kusa Mimee irin matan Nanne da idan miji yana wani hali ta kansu kawai suke ko ya mutu ko yayi rai,Apple d'inta ta d'auka tana ci tana lumshe ido don yanzu ta zama Miss Apple.

*MUMTAZ*

Ta warware sosai ta yi Y'ar k'iba don yanzu Baba yana sana'ah Babansu Amal ya turo mai kud'i masu kauri ya tada shagonsa damk'am da kaya yana sa'ah,kuma su Amal d'in ma sun kusa dawowa.

Tunda abinnan ya faru tsakanin Muta'z da Mumtaz shikkenan ta fara zazzab'in dare ta rasa na menene ga wani uban kwad'ayi.

*MISS GREEN CE........*✍🏼
*AKAN AIKINA*

_*Ummu Maher*_
(Miss green🌱)

52&53
......Umma ta ce"yanzu Mumtaz haka zaki yi ta zama kina kwad'ayi ba zakici abinci ba sai kwad'ayi?"Umma wallahi kwad'ayi kawai na keji ki barni in samu inci faten nan don Allah,taliyarce mutum gajiya ya ke yi da ita.

"To gashi je ki siyo kifi ki saka ciki nasan zaifi dad'i,da fara'ata na amsa ina godiya ina cewa Umma ta zama Hajjaju,dariya ta yi sannan ta ce" Allah yasa Y'ar nan don maka akwai dad'i,ina dariya na saka hijab d'ina sabo Wanda Mlm ya siyomin sabo ne ruwan kalar kwanduwar kwai,kasamcewa ta ma d'an hasken fata sai nayi kyau sosai,gashi Hijab d'in irin mai facemask ne,sai yayi min kyau kamar nayi roling da man wando irin bujennan sai nayi kamar matashiyar Ba indiya.

Wani irin fad'uwa gaba na ya yi ganin Sir Mukhtar a k'ofar gidanmu yana jikin window d'in motarsa yana face d'in k'ofar gidanmu cikin wata tsadaddiyar motarsa jip mai kyau kalar bak'a.

Fara'ata na rage sannan na wuce shi sai dai harga Allah nima banji dad'in wuceshi d'in da na yi ba,don ko babu komai Sir Mukhtar bai cancanci haka agareni ba bisa yadda ya yi namijin k'ok'ari wajen kula dani da iyaye na.

Da k'er ya fara magana har muryarsa tana sark'ewa kamar wani mai jin tsorona.

"Mu.."
"Mu.."
"Mumtaz"

Juyowa na yi ya yinda na hard'e hannayena saman k'irjina sannan Na ce.

"Na'am"

Cikin siririyar voice d'ina mai matuk'ar da d'i,kallonsa kawai na ke yi yadda ya canza ya zama fari ga k'ibar da ya k'ara,da ka ganshi kasan kud'i sun zauna ajikinsa.

"Don Allah don Annabi Mumtaz ki yi hak'uri ki ya feni nasan na yi matuk'ar yi miki laifi,da abinda na aikata miki Amman wallahi hakan ba zai k'ara faruwa ba wancen ma tsautsayi ne please".

Ya had'a hannayensa kamar zaiyi kuka,ni kuwa na waskata bakina gefe tare da fari da idanu kuma har yanzu hannayena suna k'irjina.

To sak'anin Masoya babu mai shiga don matuk'ar ka shiga ma Kaine zaka ji Kunya.

To hakan CE kuwa ta faru tsakanin Mukhtar da Mumtaz biyo bayan hak'uri da Sir d'inta ya dinga bata sai ga Mumtaz har tana wangale baki,hakan kuwa ba k'ara min sanyaya zuciyar Mukhtar yayi ba duk burinsa bai wuce yaga Mumtaz da iyayenta suna cikin farin ciki ba.

Da sauri Mumtaz ta shiga gida don gayawa mata Sir Mukhtar ya dawo yana waje,yanzu zai shigo su gaisa,Umman ma ta yi farinciki sai dai har yanzu bata daina d'ar_d'ar da al'amarin Mukhtar d'in ba.

Kud'i ya ajjewa Umma sannan yayi mata albishir da zai turo magabatansa a satinnan,Umma ta yi farinciki sosai tare da sanyawa Mukhtar d'in albarka.

......Hajiyar Mukhtar taja dogon numfashi Sannan ta kalli Maman Sakina ta ce"kinga abinda nake gaya miki ko?yarinyar da ita da Matsiyatan Iyayenta sun gama da Mukhtar.

Hajiyan Sakina ta ce"kinga tunda har ya dad'e bai fito daga cikin gidanba me zai hana mutafi koma me zamu yanke idan munje Gidan ma yanke.

_*Ummu Maher ce👌🏻*_
*_Ummu Maher_*

*AKAN AIKI NA*

54&55
.........Wani wawan Mari Hajiyar Mukhtar ta wanka wa d'an nata sannan ta nuna shi da manuniyarta ta ce.

"Sha_sha"

Mara sanin darajar iyayenka wato Mukhtar har yanzu daman baka daina kula wannan matsiyaciyar yarinyar ba,y'ar matsiyata jikan matsiyata,har yaushe ne aka d'aura maka Aure da zaka dinga bibiyar wannan munafukar yarinyar,shiyyasa Dana ga ka fita na bika don ni yanzu har tsoro kake bani.

"To wallahi kaji narantse ka sake ka k'ara komawa wajen wannan tsinanniyar yarinyar saina Tsine maka!Saina tsine maka!!

Wani jiri Mukhtar ya fara ji da k'er ya kai kansa d'akinsa yana kuka wiwi kamar yaro.

Mumtaz kuwa washegari tana ta zuba idanu koda zata ga Sir Mukhtar shiru haka kawai gabanta ya dinga fad'uwa,dauriya kawai ta ke yi Amman gaba ki d'aya bata jin dad'in jikinta.

Da daddaren ta daure ta tafi Asibiti,sai dai tayi matuk'ar Dana sanin zuwanta asibiti domin kuwa an shaida Mata tana d'auke da ciki har na wata biyu.

Ihu Mumtaz ta saka a asibitin da k'er wata nurse mai suna NAWWARA ta cikin Doctor nawwara na Ummu Maher, hak'uri ta dinga bata sannan Mumtaz ta bata lbrn abinda ya faru da ita bayan wata 2da suka wuce na saceta din da akayi,sai dai bata fad'a mata kowa Nene ba.

Bayan ta dawo daga asibiti ta shige d'akinta tana tunanin rayuwarta, Umma CE ta shigo mata da indomie.

" Maza ta shi Kici abinci shiyyasa ma na dafa miki ita nasan zaki ji dad'inta.

Tausayin iyayenta ne ya kama ta kamar ta yi musu kuka.

Ciwo fa ya sako Mumtaz a gaba yau ciwo gobe lfy, Umma kuwa ta ringa zabga mata magungunan musamman na shawara don ta ce Shawara ce da ita.

Har darbejiya da lemon tsami ake mutsika mata ta sha Abu dai sai gaba ya ke yi,gashi Babu Mukhtar babu dalilinsa,abun duniya yayi wa Mumtaz yawa,a kullum kwanan duniya sai ta tsinewa Muta'z a bisa cutar rayuwarta da yayi don yana matsayin d'an mekud'i.

Sand'a_sand'a Mumtaz ke yi har ta fito waje alokacin Mlm bai dawoba,cen ta fita wani chemist da ke bayan unguwarsu.

Sallama ta yiwa likitan sannan ta amsa ta shigo ciki,Maganin ciwon ciki ta CE ta bata,ta d'auko mata sannan ta bata kud'in ta fito.

Tana shigowa Gidan Umma na fito wa daga d'akinta.

"Mumtaz!ina kika ne na lek'o ban ganki ba?"

"Eh wallahi"

Na je na siyo paracetamol na lek'o kin fara bacci shiyyasa,ta fad'i hakan tana bud'e randa don shan maganin.

D'aki ta koma ta fara bacci,Mlm yana shigowa ya rufe musu gida,sannan yayi musu albishir su Amal,zasu dawo gobe murna sosai sukayi suna addu'ar Allah ya kawo su lfy.

*Washegari*

Mumtaz ta fito daga wanka kenan taji an rufe mata idanu,koda ba,ah gaya mata ba tasan k'awarta ce Amal,juyowa tayi suka rungume junansu har kuka sai da sukayi.

Umma ta fito ta shimfid'awa Amal ta barma ana ta hirar yaushe gamo,Mumtaz tana ta kallonsu cikin so da k'auna.

Ranar dai ansha hira Mumtaz tana tunanin gayawa Amal halinda take ciki har dare yayi kowa ya kwanta.

Da daddare Mumtaz ta sake komawa chemist aka had'o mata gabje gabje waidon duk ta samu sauk'i.

Tun cikin dare mararta ke mata ciwo Amman ta kasa ta yarda kowa agidan gudun kada ta katse musu baccinsu.

Da k'er baccin wahala ya kwasheta sai k'arfe 8na safe na tashi,da k'er na d'auki buta zan shiga ban d'aki,ban lura da randar dake kusa dani ba kawai na fad'a kan randar,Salati na ke jiyowa a samana ga wani Abu yana bina a k'afafuna kamar jini.

Wannan shine Labarin Mumtaz da Tun farkon littafin muka fara da labarinta.

*Miss green CE✍🏻*
💞💞💞💞💞💞💞
*AKAN AIKI NA*
(Book 4)

WRITING BY.

UMMU MAHER.
(MISS GREEN💚🌱)

WATTPAD NAME
RABIATU222.

*DEDICATED TO AKAN AIKI NA FANS &UMMU MAHER PALACE.*

No.56to60

......Sai da na yi kwana biyar a asibiti sannan na warware har yanzu bana iya had'a idanu da su Mlm saboda har yanzu ina matuk'ar jin kunyarsu akan abin da na janyo musu Wanda nima k'addara ta ce hakan.
Amal ma tazo ita da Mamansu Amal har kuka ta yi da jin abinda ya faru munyi kuka nida ita kamar babu gobe a haka har muka bawa zuviyoyinmu hak'uri,Allah ma daya taimakeni cikin ya fita da yaya zanyi da d'an shege,wannan abin shine ya ke sakawa in k'ara godewa ubangiji tare da tsinewa Muta'z kullum.

Abinda Mumtaz bata Sani ba bayan tafiyarsu asibiti yazo Muta'z yazo gidansu yafi sau babu adadi abin ba k'ara min tada hankalin Muta'z ya yi ba,kada dai ace yarinyar nan sun tashi ta yaya za'ayi ya nemi yafiyarta son yasan ba k'aramin aik aika ya yi mata ba,kuma yasan idan har bai nemi yafiyarta ba Allah bazai tab'a yafe masa ba kuma shima wataran sai anyiwa y'ay'ansa haka.

Amal ta dawo daga asibiti don d'aukarwa Mumtaz kaya tana cikin bud'e Gidan taji muryar namiji a bayanta,saurin juyowa ta yi sai taga mutum kamar balarabe a gabanta shagala ta fara yi da kallonsa,har sai da ya fuskanci hakan sannan ya yi gyaran murya yana ce wa.

"Am Nanne gidansu Mumtaz,y'ar jarida?."

"Eh nan ne lfy Mlm?"

"Daman yau kwanana biyar ina zuwa Gidan a kulle Allah dai yasa lfy?"

"Wallahi bata da lfy ne tana hospital Amman da sauk'i".

Gabansa ne ya yi wani mummunan tashi cikin in ina ya CE.

" Me.Me me."
"Me ya sameta?"

D'an Jim Amal ta yi sannan ta ce.

"Zazzab'ine".

Oky Allah ya sauwak'e muje in dubata motar Muta'z suka shiga sannan suka tafi asibitin,suna zuwa Gaban Muta'z ya ringa fad'uwa don harga Allah tsoron had'uwarsa da Mumtaz ya ke yi,kallon sunan asibitin ya yi sannan ya yi murmushi suka shiga.

Cak Muta'z ya tsaya sannan ya ce wa Amal idan ta je ta kirawo mai Baban Muta'z, hakan kuwa a ka yi tana shiga ta fad'awa Mlm ya fito gaisawa suka fara yi sannan Muta'z ya fara yi wa Mlm bayani ce wa shine Yarima mai jiran gado,ba k'aramar murna Mlm ya yi ba wai yau shine Agaban Yarima.

" Baba da man nazo ne Neman wata alfarma daman naga y'arku Mumtaz tun bayan wata 1 da ya wuce kuma naji ta kwantamin to shine na keso Ku bani Auren ta!.

Das gaban Mlm ya yanke ya fad'i,Gaskiya ne da aka CE Mahak'urci mawadaci wai yau Yarima ne ya ke son y'ar sa Mumtaz tabbas yana jin lbrnsa mutumin kirki ne sosai,kuma ya ji lbrn wannan asibitin ma nq shine n karan kanshi.

Amman sai dai kash!Mumtaz An lalata mata rayuwarta ta yadda ba za'ah iya b'oye abinda ya faru da ita ba.

*MISS GREEN CE✍🏻...💔for life*
*✨ _AKAN AIKI NA_ ✨*

By
Ummu Maher (Miss green)

_🙏🏻never put the key to your happiness in some e'lse pocket😭_

No.54&55

.......__D'akin Mlm ya yiwa Muta'z jagora suka shiga,Mumtaz tana zaune tana shan shayin da Amal ta had'a mata kawai sai taga Muta'z yana bayan Mlm ya yi kyau cikin farin yadi k'al kamar audiga,sajensa sai walk'iya ya ke kamar hasken Zerhra sai dai ya rame sosai kana ganin sa zakaga hakan,gaban Mumtaz ne yayi mugun fad'uwa ta zabura zata tashi tana nuna sa da manuniyarta sai dai kome ta tuno kuma ta koma ta zauna tana rik'e da kanta daya kusa rabewa gida biyu.

Mlm ya fuskanci akwai wani Abu don haka ya ce"Mumtaz wannan sunansa Muta'z yazo ya duba kine!"Muta'z kuwa bakinsa na rawa ya CE"sannu Mumtaz, Allah ya sauwak'e ya baki lfy ".Amin Amal ta amsa mishi yana fad'in hakan yayi sauri ya fita yana kukan zuci yana tausayin abinda ya aikatawa Mumtaz baiwar Allah.lallai babu Wanda ya cancanci ya Auri Mumtaz saishi domin kuwa ko babu komai shine ya lalata mata martabarta na y'a mace Wanda ko wacce mace indai budurwa CE ta ke lallab'ashi tare da alkintasa ko don tsira da mutuncinta.

Yana fita ya kirawo wani yaronsa mai suna Musa ya yi mai bayanin komai nidai Ummu Maher bansan komenene ba Amman naji ana zancen gini,A sati 1,da Mumtaz ta yi a asibiti har Muta'z ya sa anfara ginin Gidan su Mumtaz gadan_gadan abunka da kud'i sai gashi gini har an kusa gamawa duk da ba iya Gidan su bane,har wani kango na kusa da Gidan su Mumtaz d'in ya had'a ya siya sai gashi gida ya fito d'od'ar yayi kuma girma.

Duk abinda ke faru wa Mlm ya Sani Umma CE kawai bata Sani ba hatta Amal ta Sani,Muta'z ya nemi alfarmar a k'ara wa su Mumtaz sati d'aya akan Wanda ta yi sannan ya ware kud'i masu yawa don akaita d'akin Hutu,koda Umma ta samu Mlm da maganar jikin Muta'z yayi sauk'i kuma gashi har yanzu babu zancen Sallama,sai Mlm ya ce mata eh ai sun fad'a masa sai ta k'ara sati d'aya,daga haka Umma bata kara magana ba ta cigaba da kula da y'arta Mumtaz, don halin da ta ke ciki tana buk'atar kulawa sosai.

Har yanzu tsoron Muta'z Allah dai yasa Mumtaz bata fad'awa iyayenta abinda ya faru tsakaninsa da ita ba,sai dai har yanzu mamaki ya ke yi da yaji babu Wanda yayi masa magana koda kuwa a fuskane don kullum sai sun had'u da Mlm kuma kullum Muta'z cikin yiwa Mumtaz hidima ya ke yi kamar Wanda baisan zafin kud'i ba.gefe d'aya kuma yana k'ara son Mumtaz da ta rufa masa asiri ba tare da ta tuna masa ba.

*MURAT*
Ayanzu fa Murat da Meema abin duniya ya ishesu gashi yanzu komai ya dagule musu don har yanzu basa shiri tun akan abinda ya faru,don shi Murat gani ya ke yi laifin Meema ne ita kuma Meema tana ganin laifin Murat,tofa wannan ne ya had'a musu wata gagarumar matsala don tsakanin Murat da Meema an samu matsala,don ayanzu Murat ya koma kula wata aminiyar Meema suna lalacewarsu,don Meema ta tab'a ganin su awani hotel inda hankalinta ya tashi sosai,har ta yiwa Murat barazanar nunawa duniya vedion sharrin da a kayiwa Muta'z, hankalin Murat ya tashi sosai ya dinga Neman su shirya da Meema ita kuma Meema ta CE Indai yana son su shirya sai dai ya Aure ta,domin kuwa ta gaji da yawon duniya babu shiri Murat ya amin cewa Meema Amman zuciyarsa bata so hakan ba don dai babu abinda zai iyayine,don baiso Auren irinsu Meema yafi son ya Auri Y'ar Gidan mutunci.

*MUTA'Z*

Alhmdulillah ayanzu an kammala ginin Gidan su Mumtaz komai na more rayuwa anzuba musu d'akin Mumtaz kuwa kamar d'akin matar gwamna saboda kyau gaban mirror kuwa kayan shafa ne kala_kala,ga kayan kwalliya turare da dai sauransu gida dai masha Allah.

Mota guda Muta'z ya bada da driver don tuk'a iyayen Mumtaz da ita kanta sarauniyar Mumtaz,wadda har yanzu bata San wainar da ake toyawa ba.koda aka d'akosu daga asibiti Mumtaz kallon motar kawai ta ke yi saboda kyau da tsarinta ga A/C mai dad'i aciki,koda ta shiga motar sai da taja dogon numfashi don motar k'arshe CE ta had'u sosai.da sosai.

Mamaki da rud'a nine suka ziyarci Mumtaz ganin Gidan su ya koma kamar a k'asar waje,Salati ta farayi a fili tana kallon Umma da Mlm tana cewa"Umma kalli gidamu?wani azzalumin ya karbe ya gine mana shi don rashin tausayi.

Notice!zaku ga na bar GRP kuyi hak'uri laifin ogane don baya so,Amman zan cigaba da tyiping insha Allah nagode!nagode!dafatan kun fahimce ni🙏🏻ina missing dinku mussaman Amira da Bilkisu da Kaltum khanna masoyan littafin Akan Aikina na gode na gode,Mumtaz tana gaisheku,duk Maison magana dani sai ya turomin sak'onsa ta private domin bana cikin GRP.🙏🏻🥰

*ILOVE U ALL MY PANS🥰🙏🏻😭*

*Ummu Maher CE*
_*✨AKAN AIKI NA*✨_

By
Ummu Maher (miss green)

Ina gaida masoyan wannan littafi na akan Aikina aduk inda kuke,Akan Aikina fans GRP ina gaisheku ban manta daku ba duk da bana cikin GRP.

No.56&57

Umma ma mamaki ne kwance fal fuskarta ta kalli Mlm tana son k'arin bayani,"Muje Mlm ya CE wa Su Umma sannan ya bud'e get d'in Gidan suka shiga,Mumtaz da Umma bin Mlm kawai sukeyi kamar rak'umi da akala har suka shigo babban farlon Gidan,Mlm ne ya yi musu alamar su zauna cikin kujerun da ke farlon,a d'arare Umma da Mumtaz suka zauna suna ta faman mamaki kujerun ma kad'ai abin kallo ne.

A nitse Mlm ya fara basu labari tunda ga farko har k'arshe ya k'are maganar yana kuka,don tunda ya ke bai tab'a tunanin ko irin wannan Gidan zai shiga da aunan aiki ba,ballan tana ya zama gidansa,babu abinda zai cewa Muta'z sai dai Allah ya saka mishi da alkhairi,don da Mlm ya so yayi taurin kai wajen amsar Gidan Amman kuma daga baya yaji babu dad'i mayar da hannun kyauta baya.

Wani Abu ne ya tsaya wa Mumtaz azuciyarta wai yau Wanda ta tsana arayuwarta wai shine ya Gina musu gida irin wannan?ta kalli Mlm tana matuk'ar jin tausayin iyayenta don tasan basu San munanan halayensa ba da basu amshi wannan Gidan da ya yi musu ba amatsayin rufe musu baki sai dai tasan Mlm bashi da kwad'ayi ko kad'an kawai dai ya amsa ne don ko babu komai yasan filin Gidan sane kuma bayan hakan tasan Mlm baya maida hannun kyauta baya.

Umma ma ta yi murna sosai tana ta saka mishi da alkhairi,Mlm ne ya raka Mumtaz d'akinta a saman bene Wanda ya gaji da had'uwa don irin benen nanne mai rawn kafin ka isa saman,bata gama mamaki ba sai da ta shiga d'akin nata,d'akin ya gaji da had'uwa ta CE"wow so nice"Amman da sauri ta rufe bakinta tuno da cewa Muta'z ne ya saka mata komai ba d'akin sai taji duk bak'in ciki ya kewaye ta.koda ta bud'e sip d'in da ke manne acikin d'akin taga kaya sun kai set hamsin a shirye a goge acikin Sip d'in masu matuk'ar kyau Riga da siket dogayen riguna da k'anan kaya maau kyau da tsari,ga gaban madubi kayan shafa kala_kala.

Da daddare suna zaune kan Dining suna cin abinci suka ji nocking, Mlm ne ya CE Mumtaz ta je ta duba,a hankali ta tashi ta bud'e k'ofar farlon,gabanta ne ya yi wani irin bugawa ganin Muta'z a tsaye yana kallon ta da rinannun idanunsa,yana sanye da wata d'anyar shadda coffee, kasan cewarsa mai haske ba k'ara min kyau suka yi masa ba.

Murmushi ya sakarmin sannan ya rab'a ta gefe na ya wuce ni kuma na rufe k'ofar ina binsa da wani mummunan kallo,aduk sanda naga Muta'z sai naji wata muguwar tsanarsa acikin raina don bana manta sanda ya yi amfani da k'arfinsa a matsayinsa na d'a namiji ya yi min fyed'e,har yau ban San me yake damuna ba da nake b'oyewa iyaye na abinda ya aikata min,tsoronsa?ko me na keji da na kasa fad'awa iyaye na.

Haye wa sama na yi ina sharar kwalla acikin akan kyakkyawar face d'ita,da kwallan tausayi Muta'z ya Bini har na shige d'akina na haye lumtsumemen gadona ina kuka mai cin rai,Muta'z ya cuce ni yanzu idan nayi Aure me zance da mijina matuk'ar ya Gane ni ba budurwa ba CE? Wannan tambayar kullum na ke yiwa kaina Amman na kasa samun amsa,sai dai amsa d'aya na ke bawa kaina Muta'z ya cuceni.

Tun daga ranar sai Muta'z yazo gidanmu da daddare sunyi hira da Mlm kuma ayanzu ya samowa Mlm aikin wani company d'aya daga cikin company Mai Martaba wato Mahaifin Muta'z.

Alhmdh don ko ayanzu munyi ban kwana da talauci,awani yammaci ne Mlm ya sameni a d'akina ina karanta wani novels mai suna ASANADIN ABAYAR SALLAH,na marubuciya Ummu Maher, na ji dad'in littafin sosai ina cikin karatunne Mlm ya shigo,na yi saurin sakkowa daga kan gadon ina gaishesa,ya samu waje ya zauna ni kuma ina k'asa azaune na sunkuyar da kaina,gabana sai fad'uwa ya ke yi,na jiyo muryar Mlm yana cewa.

"Mamana magana na keson yi da ke ta fahimta don nasan halin Mamana idan abin bai miki ba ki fito ki gaya min?don ba zan miki dole ba sai dai ,a irin wannan rayuwar da muke ciki Abu ne mai wahalar gaske samun namiji mai addini,nutsuwa da kuma kamala, wannan yaron Muta'z ne ya ke sonki kuma harya turo magabatansa don ayi mishi iso don ya fara zuwa zance".

Da sauri na tashi tsaye dafe da k'irjina Wanda ya ke sama da k'asa tsabar tashin hankali,Na CE" Baba bazan iya Auren saba saboda bashida hali mai kyau.....

Ummu Maher CE.

Vote
Share
And
Comments.
*_💚💘AKAN AIKI NA💘💚_*

Book 4 last

Na
Ummu Maher(Miss green🍀💚)

58&59

Ina kaiwa nan na koma d'aki da gudun gaske ina kuka,matuk'ar aka takuramin akan Auren Muta'z to babu makawa nasan mutuwa zanyi don ba zan iya rayuwa da azzalumi ba,mak'iyi na,macuci,mazinaci.

Mlm ya kalli Umma sannan ya ce"Bazan tab'a yiwa Mumtaz auren dole ba,ina ganin wannan yaron da mutunci fiye da yadda kike zato,don kafin in sanarwa Mumtaz sai da na yi bincike sosai akan yaron don,yaron d'an manya ne Babanshi ayanzu haka shine sarkin da ke mulkalmu,sarki me adalci da sanin yakamata,zanso Mumtaz ta Auri Wannan yaron badon kud'insu ko wani abuba,A'ah sai don tarbiyyarsa da nagartarsa."

"Ki rarrashi Mumtaz bazan tab'a yi mata zab'en tumun dare ba a matsayina na mahaifinta,kuma nasan wataran itama za tayi alfahari da wannan Auren,don na hango so da kuma tausayin Mumtaz a cikin kwayar idanunsa,don haka zan cigaba da addu'ar Allah ya tabbatar da alkhairi Amin.

Kullum sai Muta'z yazo gidanmu amman bai tab'a ganina ba,don da naji k'arar motarsa na ke guduwa don ayanzu ba wai son ganinsa ne ba nayi ba,a'ah kawai da naganshi sai inji gabana ya yi muguwar fad'uwa.

Ga Amal kullum tana gidanmu muna shan hira,ita ma hirarta a kullum bai wuce in Auri Yarima Muta'z ba,don a cewarta munyi matuk'ar dacewa da juna,don kullum idan yazo suna shan hira shida Amal,kuma kullum baya gajiya da bawa Amal sak'o ta kawomin,har waya sabuwa dal ya kawomin.

***
Ranar wata asabar ina zaune ina shan iska a farfajiyar gidanmu,ina sanye cikin riga da siket ns atamfa holand na tufke gashina,na siraro d'an kwalin ta tsakiya gashina ina shan iska,sai naji ajikina kamar ana kallona,saurin juyowa na yi sai da gabana ya fad'i na daburce har na yarda d'ankwalina a k'asa,na yi saurin duk'awa don d'auko d'ankwalin,sai na ji hannun mutun dab dani na sunkuya shima ya sunkuya tare muka d'auko d'ankwalin hannayenmu na gogar na juna,babu abin da na tsana irin had'a idanu da Yarima Muta'z, don wani abu na ke hangowa acikinsu wanda ya ke sakawai gaba kid'aya inji kwarjininsa ya bai bayeni,don duk tsiwar dana d'auko zanyi mai sai naji ta tafi.

Cikin voice d'insa mai dad'i ya ce

"ykk My pricess"
Saurin d'ago kaina na yi sannan na tashi zan tafi,ya ruk'o hannuna gaba d'aya naji na fad'a kan k'akk'arfan k'irjinsa,muka had'a ido ban san sanda na tashi da sauri na shiga gida ba,gaba na yana dukan³,shi kuwa shafar gashin kansa kawai ya yi yana jin kansa kamar wani sabon ango.

MURAT
______
***
"Meema wallahi kin cuceni,kin cuci aminina da kika k'ara bani kwarin guiwa wajen cutarsa da kuma cin amanarsa,Allah bazai tab'a barin mu ba,matuk'ar hakkin Muta'z yana kanmu,kuma ki sani Meema bazan tab'a auren wulak'an tacciyar mace irinki ba,wacce ta gaji da duniya,duniya ta gaji da ita......

" kai Murat sai ta zancen ka wallahi tallahi daman kai can Azzalumine macuci,don haka kada ka sake cewa wai ni ce na saka kan hanya?"kuma ka ke tatsuniyar cewa ba zaka Aureni ba,kasan abinda ma bazai tab'a yiyuwa bane?"ko kana so?ko baka so?dole sai na Aureka,domin kuwa a lokacin daka rabu dani to fa awannan lokacinne zan toni asirinka kowa yasan waye kai".

Wani kyakkyawan mari Murat ya kifawa Meema sannan ya nuna ta da yatsar sa ya ce"Wallahi Meema kinyi k'arya ki gama lalacewarki sannan ki ce wai yanzu in Aureki,bazan tab'a Auren Karuwa,fasik'a irinki ba,don haka ki nemi me Aurenki Amman ba ni ba.

Wata shewa Meema ta yi sannan ta ciro wani fefen vedio ta ce"wannan vedion Murat shine rayuwarka kuma shine Ajalinka bazan tab'a bari wannan vedion ya kufcemin ba,domin ina da irinsa yafi 100,kuma ka duba wayarka ka gani.

Kuyi hak'uri anyi min rasuwa ne shiyyasa na yi tyiping kad'an.

Taku har kullum Ummu Maher💔
Miss grèèn💚.

kunga yanzu bana grp so duk masuyin comments yana isomin.

Ku yad'a
Sannan
Kuyi comments✍️
*_AKAN AIKI NA_*

By Ummu Maher
Miss green🍀

60

....wallahi Fulani ina masifar son yarinyar tare da tausayinta,Amman kinsan wani abin mamaki?

Fulani ta girgiza kai alamar a,ah.

"Amman yarinyar nan ko ganina bata San yi bansan ko me na yi mata ba,don Allah Fulani kije gidansu ki farauto min zuciyarta ko Allah zaisa ta so ni.

Shiru Fulani tayi har ya gama maganar sa,tana mamakin Yarima Muta'z ko yaushe ya yi Auren oho?har ya ke son k'ara wani Auren Amman sai ta daure ta ce" ni kuwa wannan wata yarinya ce mai sa,ah irin wannan Yarima kamar kai a ce an samu yarinyar da zata k'i ka?ko dai wani Abu ka yi mata da bata sonka?ni dai nasan babu macen da zata had'u da kai ta ce bata sonka,don komai kana da shi na nagarta ilimi,addini,tarbiyya,kyau,nasaba,hak'uri,da kuma yiwa iyayenka biyayya.

Don haka irinku mata suke so,don haka na yi maka Alk'awarin nemo maka Aurenta kuma Insha Allah komai yazo k'arshe.

Rungume Fulani Yayi sannan ya manna mata kiss a kumatunta,don bashi da tamkar Mahaifiyarsa.

"Hajjo in zo ki rakani wajen Fulani ta damamin wannan furar ta ta,mai dad'i ke Idan mutun yazo gurinki saiki cikani da wasu magarya alhalin ba k'oshi zanyi ba,"to uwar masifa muje kisha gero ma ba fura ba".

Suna shiga sashen Fulani suka ga Murat yana zaune suna ta hira da Fulani,Mimee ta sunkuya ta gaishe da Fulani cikin shagwab'a tace"don Allah Mama ki dama min fura insha wallahi indai bansha fura ba sai inga kamar cikin jikina zai zube wallahi."

"Ah ai kuwa yanzu Muta'z ya gama shan nasa,bari akawo miki yanzu kinji y'ata,ba a b'ata lokaci ba Mimee ta shiga shan furar ta babu k'akkutawa,don tunda ta samu ciki yau kusan wata 7 kenan take masifar shan furaDon fura tana d'aya daga cikin abinda take masifar son sha tunda ta samu ciki.

....tun safe Umma da Mlm suke shiri don Muta'z ya gaya musu zuwan Mahaifiyarsa,Amman Mumtaz tana cikin d'akinta ko lek'owa bata yi ba,don wani azabar zazzab'i da ciwon kai ta ke ji.

"Mumtaz!Mumtaz!!INA kika Shiga ne tun safe kina d'aki don mugun halinki da ki ka koya to wallahi maza maza ki sakko tun safe nake aiki kina.....

Maganar ta ce ta tsaya jin Takun shigowarsu Muta'z da Mahaifiyarsa,rasa inda zata sakasu ta yi Mahaifiyar Muta'z kawai ta tsaya tana kallonta tana yi mata wani irin kallo.,.

To Ku biyoni anan gava don jin wani irin kallo Mahaifiyar Muta'z ta ke yi wa Umma,Mahaifiyar Mumtaz?shin me ya janyo wannan kallon?.

*Ummu Maher CE*

Share&cmnt.
[11/22, 15:19] 🥰Ummu Maher🏕️⛱️: *_AKAN AIKI NA_*

By
_Ummu Maher_
_*Miss green*_

Wattpad
Rabiatu222

64&65

.....Da sauri Fulani ta rungume Umma sannan ta CE"Jamila daman kina raye tun kina jaririya aka yarda ke aka nemeki aka rasa,Allah mungode maka da Bayyanarki don babu tantama Jamila ke ce don kamarku da mai Martaba har ta b'aci wallahi".

Mamaki da firgici ne suka kama Umma sosai don ita dai tunda ta taso a rayuwarta bata San kowa ba sai Mlm da Iyayenshi sai dai basu b'oye mata komai na rayuwarta ba,sun gaya mata cewa tsintarta a ka yi a gefen hanya.

Da sauri Fulani ta d'auko wayarta ta kira Hajja don ta shaida mata.

"Wai wani jarababben ne ya ke damuna awaya ne?idan na ce kada a siyomin waya sai an siyomin to nidai babu ruwana wallahi da munafinci"...

Maganarta ce ta tsaya cak,jin abinda Fulani ta ke fad'a hannu na rawa Hajjo ta saki wayar ta fad'i k'asa wan war, Meema ce da ke kwance saman kujerarta tana shan fura ta hango Hajjo zata fad'i k'asada k'er ta tashi don taro kakar ta.

Hajjo kuwa da kanta taje wajen
[11/22, 20:15] 🥰Ummu Maher🏕️⛱️: Mai Martaba don shaida masa abinda ke faruwa don hankalinta ya tashi sosai da jin wannan maganar,shima cikin tashin hankali ya biyo Hajjo suka fito dogarai suka biyosu don bud'e musu k'ofa,cikin sauri Mai Martaba ya fara tuk'a motar cikin gaggawa,rabonda ya yi tuk'i kusan shekara 20 kenan.

Da kwatancen Fulani Allah ya kawo su Hajjo lfy harma da Meema,kai tsaye suka shiga cikin Gidan,hankalinsu gaba ki d'aya ya karkata ga maganar Momi.

"Inna lillahi wa inna ilaihi Raji'un"

Muryar Hajjo ce ta karad'e d'akin sannan ta tafi da saurinta ta rungume Umma tana mai godewa Allah da yasa taga y'arta tun kafin ta mutu don a kullum addu'arta taga y'arta don duk duniya tana son ta tunda kuma ta haifeta aka ga irin son da ta ke yi mata shikkenan aka tsani yarinyar har sai da aka had'a baki da wata baiwa aka yardar mata da y'a,sai da aka gane kuma Allah ya Toni asirinta ta fad'i gaskiya sun had'a baki da kishiyar Hajjo don ita bata da y'ay'a,Mahaifiyar Meema ita ce ta biyu sai Kuma Mahaifiyar Mumtaz Auta kenan wadda ta b'ata tun tana k'arama.

Ko da Mlm ya ce su Hajjo su bada wata shaidar bayan kama da Umma ta ke yi da Mai Martaba,nan ta ke Hajjo ta tashi ta ce Umma ta ja hannun rigarta akwai tawadar Allah,haka kuwa a kayi tana bud'ewa kuwa sai ga tawadar Allah.

Da sauri Umma ta tashi ta k'ara rungume Hajjo tana mai jin dad'in ganin Mahaifiyarta duk da bata Santa ba sai yanzu,Addu'ah Mai Martaba ya fara yi sannan aka fara hira gwanin ban sha'awa,Muta'z ma yazo nan ya dinga jin wani farin ciki a cikin zuciyarsa don daman tun ranar da ya fara ganin Mumtaz yasan cewa jininsa ce don yadda ya ke sonta kamar rai.

Yawan maganar da akeyi ne ya tasheni daga dogon baccin Dana samu,ina tashi naji ciwon kan gaba kid'aya babu shi, daga ni sai wata doguwar rigar bacci pink colour tana da siririn hannu,gashin kaina ya bazo baya duk ya warwatse alamun daga bacci na tashi,na fara sakkowa saga upstar ahankali cike da nutsuwa na fara kiran Umma!Umma!!.

Tunda na fara sakkowa mutanen wajen hankalinsu ya dawo kaina kowa yana jinjina wannan halittar mai kyau da tsaruwa,Fulani kuwa cewa ta yi Lallai dole Muta'z d'inta ya gigice don duk yadda ya kai da kyau to fa wannan yarinyar k'arshe ce.

Ita kuwa Meema tun kafin ma tasan wacece taji tana wani matsanancin kishi da Mumtaz, don Meema da taga hankalin Muta'z duk yana wajen Kallon Mumtaz ai takanas ta taso ta zauna kusa da Muta'z Amman bai san Meema tana wani Abu wai shi kishi ba.

Ummu Maher ce

*Vote*
*share*
Comments👌🏻
*_AKAN AIKI NA_*

By
_Ummu Maher(Miss green🍀)_

Littafaina

Uwar gidana
Auren dole
Ruhi d'aya
Inayatullah
Farouk
Kaddarar rayuwa ce
Asanadin Abayar Sallah
Akan Aikina
Jameeler
Doctor Nawwara

_gaskiya ina jin dad'in yadda kuke nuna min k'auna mussam duk masu yimin post.

*Kaltum Khanna*
*Dr Amira*
*Nabiha Aminu*
*Rukayya gawata*
*Hjr L Sadiq*
*mmn teddy*
*Momin Shukura*
*Nana M sha'aban*
*Fauziyya d s*
*Autar Mama*
*Ummu najma*
*koise baby*
*Bilkisu*

Da duk masoya na wad'anda ban samu damar ambato sunansu ba.

Please nayi mistake tun a baya na page maimakon in saka 70 na saka 65har sau biyu yanzu zan tashi a 70.

70
Da sauri Hajjo ta taso ta rungumeni tana cewa"Allah Sarki jikata gakinan kamar Ku d'aya da Muta'z."

Gaba d'aya ban gane inda zancen nasu ya dosa ba sai da Mlm yayi mata bayanin komai sannan na tashi da Sauri na rungume Hajjo harda Mai Marta ba ina kuka Ashe Mahaifiyata tana da gatanta haka ta zauna cikin talauci da k'uncin rayuwa sannan ta zauna ba tare da tasan danginta ba ko kuma ta nemesu ba, sai yanzu da Allah ya kawo k'arshen komai.

Ai aranar Hajjo a gidan ta kwana ana ta hira ni kuwa kaina na kan cinyar Hajjo a haka har bacci ya d'aukeni Umma kuwa suna ta bada labarin yadda aka yi aka yarda Umma na a bola.

Ban San ya akayi Hajjo tasan abinda ke tsakanina da Muta'z ba,ai kuwa Hajjo cewa ta yi a satinnan za'ayi Auren don hankalin Muta'z ya kwanta shikkenan ya had'a Auren y'an uwan juna.

Ranar kamar in Zane tsohuwar nayi don na lura fitinanniyar tsohuwa CE,Mai Martaba kuwa ya ce Ummana ta dawo Gidan sarauta kusa dashi yana ganinta hankalinsa zai fi kwanciya,Umma ta CE yayi hak'uri soon zata dawo.

Yau kusan sati 1 kenan Muta'z baya gari,don ya kwana biyu baizo gidanmu ba,nima ban damu ba don kwata kwata baya gabana har yau idan naganshi wani irin mugun haushinshi na keji sai dai kwata kwata bana iya had'a idanu dashi don tsoron I'danunsa na keji.

Fulani kuwa sai Jana a jiki ta ke yi,na rasa me yasa nake son matar don tana burgeni sosai.

***
Duniya fa ta juyawa Murar sosai don Meema ta rikita lissafinsa don ta ce matuk'ar tana numfashi dole ne ya Aureta,a yanzu kuwa har ya kai kud'i harda sarana babu Wanda ya Sani,saboda tsabar zubar da aji Meema da kanta ta amshi kud'inta harda na sadaki kuma an saka sati2masu zuwa asha biki,bak'in ciki kuwa Murat yasha sa wannan wani Irin Aure zaiyi babu albarka manya ko kad'an a ciki,gashi don tsabar abin kunya wai amarya CE ta ke amsar kud'in Aurenta da kanta.

A yanzu kuwa wasan b'uya suke yi da Muta'z don besan abinda zai CE masa idan sun had'u ba,ayanzu yayi nadamar duk abinda ya yiwa Amininsa kuma d'an uwansa Muta'z yasan Allah bazai tab'a barin hakkin Muta'z akansa ba,ya zama dole ya nemi yafiyarsa ko Allah zai dubesa,don yasan Auren Meema k'addararsa ce don Bai tab'a tunanin zai Auri mace Y'ar duniya kuma fasik'a ba.

A duk duniyar nan babu yarinyar da ya ke so, kuma yake k'auna kamar Hanan ita kad'ai ya ke so ya mallaka a matsayin matarsa uwar y'ay'an sa sai dai yasan Hanan ta yi mishi nisa Nisan da bazai iya kamota ba,don fasik'i baya Auren wadda ba fasik'a ba,yafi kowa sanin halin Hanan yarinya ce mai ilimi,tarbiyya,da kuma biyayya,uwa uba addini,ada kafin Hanan tasan halinshi tana matuk'ar yi mai biyayya a matsayinta na k'anwarsa har Allah yasa suka fara soyayya sai gashi ya b'ata rawarsa da tsalle akaran banza,don babu wata mace mai mutunci da zata so ta Auri mazinaci ,dumu² Hanan ta kamashi shida Meemi suna aikata masha'a da Allah ya Toni asirinsa ranar Aikenta Muta'z yayi wajensa Allah yasa tayi mummunan gamo tun daga ranar Hanan ta tsani Murat kamar ta caka mai wuk'a ta kashe shi.

***
Rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya,yau CE ranar da aka kawo kud'i na baiko da kud'in saka ranar Muta'z da Mumtaz,ranar Mumtaz tasha kuka kamar ranta zai fita,don ma sauk'inta har yanzu bata ganin Muta'z har yanzu bai dawo ba da sai ta tona mishi asiri kowa yasan halinsa,ita kanta bata San yadda za ayi ta yi rayuwar Aure da Muta'z ba,mutumin da ya b'ata mata rayuwarta ya yi mata fyed'e harda kullin cikin shege,idan ta tuno da wannan abin yana matuk'ar b'ata mata rai sosai, kuma tana tunanin tona mai asiri zumuncin da ke tsakanin iyayensu ya lalaci ga Hajjo da ta shige gaba akan komai,matuk'ar ta Sani to wallahi sai ta tsani Muta'z tsana mai tsanani.

Wata biyu aka saka alokacin Meemi ta haihu,kuma har yanzu bata San halin da ake ciki ba na maganar k'arin Auren mijinta,Hajjo ta CE a k'eleta da kanta zata fad'a mata har sai ta haihu sannan za'a fad'a mata.

Ni kuwa kallonsu kawai na ke yi don abinda Muta'z ya min sai na rama Wanda yafi nashi ma,Amman ni kad'ai na barwa zuciyata don sai ya gane nima macece.

*Ummu Maher CE*
*_AKAN AIKI NA_*

By
_Ummu Maher(Miss green)🍀_

Ina gaishe Ku y'an GRP dafatan duk kuna lfy👏🏼daga Ummu Maher dinku.

Pg 71&72

....yau aka kawo lefena akwatina set12 mak'ota da y'an uwa sai tururuwar shigowa suke yi ganin lefena,kowa kuma da abinda ya ke fad'a wasu da basu San alk'armu da su Muta'z ba cewa suke munbi son zuciya munbi kud'i sauran aje a siyar damu.

Ni kuwa basu San da za'a janye Aure na da Muta'z to da tabbas da nafi kowa jin dad'i don ban San me yasa ba ?koda shigowa gidanmu yayi b'oyewa na keyi don bana son in kalli kwayar idonsa don abubuwa da yawa nake gani acikinsu.

****
Cikin dare Mimee ta fara nak'uda dak'er taje d'akin Muta'z ta tashe shi alokacin ta fara fita daga hayyacinta,suna isa emergency aka karb'esu da gaggawa aka shiga da ita.

Da sauri Muta'z ya zaro wayarsa ya kira Fulani harma da Me Martaba don ya sanar musu halin da ake ciki,Har Mumtaz ya kira sai da tayi ringing 5 sannan ta d'aga yaji muryar Mumtaz kamar sarewa don dad'i,don haka yayi gaggawar sanar mata halin da suke ciki.

Duk da k'iyayyar da ta kewa Muta'z Amman tayi matuk'ar tausaya mishi don tasan halinda maza suke shiga idan matansu suna labour.

Da sauri na sakko k'asa na sanarwa Hajjo da Umma halin da ake ciki,cikin rud'ewa Hajjo ta d'auko hijabinta mu ma muka shirya sai Hospital.

Har mukaje bata haihu ba hankalin kowa ya tashi har ana tunanin ko ayi Mata operation, sai Allah ya sauke ta lfy ta haifi Y'arta mace Ku Kakkyawa me kama da Mahaifinta,nan da nan asibitin ya kaure da murna,Amman duk da halin da Mimee ta ke ciki kallon banza ta dinga bina dashi,ina ganin haka nayi tahowa ta gida,INA fitowa daga asibitin naji an janyo hijabina ina juyawa naga Muta'z a tsaye yana murmushi,had'e raina nayi na juya amman bai bani dama ba kawai sai ya rungumeni a k'irjinsa,ban San me yasa ba na kasa hanashi saima wani irin dad'in k'amshin jikinsa da na keji abin sha'awa don tunda na ke ban tab'a jin dad'in turare haka ba.

Muna cikin wannan halin ne naji muryar shi dai dai kunne na ya ce.

"I love u"
Har cikin b'argon jiki na naji wannan dad'in Amman da nayi wani tunani da sauri na wuce parking space,da sauri ya wuce ta gaba na ya janyo hannuna ya ajjeni a kusa dashi ya figi motar sai gida.

Kallona kawai ya ke yi yana tuk'i ya kasa cemin komai saboda miskilanci don na lura Muta'z miskili ne,nima ban ce mai komai ba na juya ina kallon window sai naji yana cewa.

"Mumtaz na Sani ni me babban lefe ne awajenki to ina Neman alfarma a wajenki ki bani dama in gyara lefina don Allah", ya fad'i hakan cikin rarrashi.

Ko kallon shi banyi ba har muka iso wani tafkeken gida me rantsattsan kyau,mamaki ne ya kamani na juya zanyi magana kawai sai naga ya bud'e min murfin k'ofar motar alamar in fito.

Ko kallon sa banyi ba na fito na tsaye a waje,kawai sai naga ya tsugunna a gabana yana cewa" don Allah Mumtaz ki yi hak'uri ki yafe min nayi alk'awarin insha Allah zan gyara lefina please ya had'a hannayensa alamun ban hak'uri.

Ban sanda na had'a hannaye na da nasa ba inq cewa na hak'ura ka tashi mu tafi gida Allah ya yafe mana baki 1.

To tun daga wannan ranar ne Muta'z ya k'ara shigemin kuma ko agaban waye sai ya nuna min soyayyarsa a fili,Amal ta kan CE min na yi dacen miji me sona,kawai kallon ta na ke yi don ni kad'ai nasan me Ya yi min Amman Allah da kansa muna yi mishi lefi ya yafe mana don haka na yafewa Muta'z lefinsa Amman dole sai na gumq masa idan mukayi Aure wannan sirri na barwa zuciyata.

Ummu Maher ce
*_AKAN AIKI NA_*

Rubuta wa✍🏻
_(Ummu Maher)Miss Green_

Pg 74&75

.....ko da naje barkan Meemi ko kallona ba ta yi ba k'arshe ma ta tashi ta barmin wajen,Allah yasa Fulani tana Gidan ta amshi kayan barkan da na kawo sannan ta ringa yiwa Meemi fad'a akan wulak'an ta d'an Adam ko don ina a matsayin y'ar uwarta mafi kusanci.

Ni kuwa daman nasan hakan zai faru don ba kowacce mace ba ce ta ke da b'oye Kishin ta don haka kuwa dole ne ta yi,Amman ni dai har zuciyata bana jin haushin ta ko kad'an don ni shi kanshi mijin ba sonshi na ke yi ba ballan tana inyi kishinsa don haka tuni daga shi har ita na tattarasu na watsar.

Umma ce kad'ai ta je ranar suna Amman babu yadda ba ta yi dani inje ba Amman na k'i k'arshe ma na lafe a gado na ce ba ni da lfy.

Ina kwance a kan gadona daga ni sai wata rigar bacci Red color gashin kaina duk ya barbazu akan gadon kamar wata ba India,k'arar shigowar mota naji Amman sai ban tashi ba don nasan Mlm ne ya dawo kuma watak'il wani abin zai d'auka don haka naci gaba da bacci na.

A cikin bacci na naji wani irin k'amshin turare Wanda k'amshinsa ba ya gushewa a cikin hancina da gangar jiki na baki 1,saurin ta shi na yi don tsabar tsoro gabana ne ya yi wani irin mugun tashi ganin Muta'z a kaina yana yimin wani irin mayen kallo kamar zai cinye ni.

Da Sauri na fara Neman blanket d'ina Amman baya kan gadon,kunya ta bi ta isheni kawai sai naga ya k'araso har inda nake ya lullub'amin a jiki na sannan ya yi min wata signal ya bi hanyar fita,tsayawa naga ya yi a bakin k'ofar sannan ya ce min"ki fito Hanan ta zo ganin ki don jiya ta dawo daga mkrnt......

Ai ban Bari ya k'ara sa ba na d'auko hijab d'ina na saka na wuce ta gabansa da Sauri don zumud'in ganin Hanan,shi kuwa tsayawa yayi a bakin k'ofar yana shak'ar daddad'an k'amshin da Mumtaz ta barmai,har zuciyarsa ya ke jin wani irin tsagwaran son Mumtaz har cikin zuciyar sa so na tsakani da Allah.

A farlo ya samesu sun rungume juna suna ta zuba surutu,ya watsowa Hanan wani kallo sannan ya ce"ke Hanan ki iya bakin ki don Da amarya ta ki ke magana ehee".

Dariya Hanan ta yi sannan ta ce"Kai gaskiya Yaya ka iya zab'e fa gata k'anwarka ga ta matarka kaga shikkenan ka had'a k'annenka a matsayin Matanka".

Nan dai Hanan ta ringa bani labari,shi kuwa Muta'z sai kallo na ya ke yi kamar zai cinye ni da naga ya matsamin sai na rik'e hannun Hanan na ce muje kitchen mu d'ora girki,sannan na juyo Amman na kasa kallon kwayar idonsa na ce"ka koma gida kaga yau suna zamuyi girki."

Zama naga ya k'ara yi sannan ya CE"Wow shikkenan kinga sai inci girkin amaryata".ya fad'i hakan ya na mannemin ido alamar yaji dad'in hakan.

Hanan sai dariya ta ke tana cewa Romio da Juliet kawai,ni kuwa naja hannunta muka shiga kitchen muka fara aikin mu gadan gadan,tunda suka fara girkin Muta'z yake kallon farlon kamar ya bisu ga wani k'amshi da ya faraji Wanda ya gama cika farlon.

Naman kai muka dafa Wanda ya gaji da k'amshi ,sai jallop d'in taliya Wanda Tasha green beans, da hanta,da kayan k'amshi sai coconut&pine apple jus.

Hanan ce ta fara jerawa a dining ni kuma ina gyara wajen da muka b'ata sai da na gama gyarawa tsab sannan nafito,na d'auka gaba d'aya ya tafi baya farlon Ashe yana nan ya hard'e k'afa 1 kan 1,kallo na ya ringa yi har na fara hawa kan step a hankali kamar me tausayin tsep d'in, Muta'z kuwa kamar wani soko sai kallo na ya ke yi Hanan ta kula da hakan sai dariya ta ke yi shi kuwa gogan besan ma meke faruwa.

Yana ganin Mumtaz ta hau sama ya fara cika cikinsa da d'a amun yana santi kamar wani yaro sai da yaci ya more sannan ya tashi yana masha Allah kace na more da amarya me iya girki.

A hankali na fara sakkowa akan step d'in ina sanye da wata doguwar Riga Arabian gown blue black kasan cewa ta fara sai ta haska ni sosai na nad'a belt d'in a kaina na saka plat show me kyau, ina danna wayata har na k'ara so Amman Muta'z besan na k'ara so ba don wani mugun kallo da ya ke bina dashi kamar zai cinye ni,ni kuwa na basar dashi na zauna ina cewa Hanan idan ta gama cin abincin zamuje gidansu Amal don su gaisa.

Saurin tashi Muta'z ya yi wai zai kaimu,Amman na ce mishi ya barshi ga gidansu nan kusa da namu Amman fafur ya CE wallahi sai ya rakani.

Haka kuwa akayi har gidansu Amal ya rakamu sai da yaga mun shiga sannan ya tsaya acikin motar ya ce mu shiga zai jiramu,ina matuk'ar mamakin kishin Muta'z kamar Wanda za'a saceni.

Amal ta yi matuk'ar jin dad'in zuwanmu,Mamansu ma sai nannan ta ke damu don yanzu sona ta ke kamar za ta goyani,ni kuwa a zuciyata oh Ashe dubiyarnan sai kana dashi a ke damawa da kai.

.....Fulani da kanta ta d'auko me yimin dilka da gyaran jiki ciki da waje,ai kuwa matar tasan abinda ta ke yi don irin matan sudawan nanne don haka ta zage awajen gyarani ciki da waje,gabana kuwa ko d'an yatsa bazai shiga ba tsabar gyara kuma an hana Muta'z zuwa gidanmu don har sai an kaini Gidan shi sannan zai ganni don haka Bak'aramun kwaruwa Muta'z ya yi ba don har ciwo sai da yayi,don Ni da kaina na tsara wannan don yadda na ke ada ma Muta'z yana k'ok'arin tab'a jikina ballan tana yanzu da komai nawa ya canza Wanda ya sanni ada yanzu ba zai gane ni ba.

Please kuyi hak'uri abubuwa ne suke yimin yawa shiyyasa bana tyiping da wuri✍🏻.

Ummu Maher CE
Vote
Share
And
Comments.
*_AKAN AIKI NA_*

Rubuta wa✍🏻
_(Ummu Maher)Miss green🍀_

_*Please don Allah kuyi hak'uri fans bana samun kawo muku labarin Jamila abubuwa ne suka yi yawa*_

_(The Wedding)_

💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
To fa ranar muke jira yau gata tazooo,ranar bikin Muta'z da Mumtaz.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.