Akan Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 20 of 21
Page 76&77
Wani irin kyau me had'e da sirrika kala² Mumtaz ta yi kamar ka d'auke ta gaba d'aya,tun jiya na ke kuka don idan na tuna ayanzu haka na zama Matar Mumtaz ba k'ara min tashi hankali na ya ke yi ba,don gaba d'aya yanzu tsoron Mumtaz na ke yi don na dad'e da sanin ba k'ara min mugu bane.
Tun k'arfe 4 y'an d'aukar amarya suka zo muna ta kuka nida Amal,don tun safe muke kukan rabuwa ni da aminiyata Hajjo kuwa sai masifa ta ke Wai min isheta da kuka kamar wad'anda za'a yanka kukan ya yi yawa.
Hajjo CE ta shiryani da kanta da wata had'addiyar tamfa super me Golding ta yi kyau sosai sannan aka d'oramin wata lafiyayyiyar Lifaya fara Sol sai ratsin gold ajikinta aka fesheni da turare exsense ne k'amshin gaske.
Har aka gama shirin kuka na ke yi aka shigar dani babban farlon Mlm ya yi min nasiha sosai me ratsa jiki nan fa kuka na ya k'ara k'aruwa da k'er Mlm ya rarrasheni don shima kukan zuci ya ke yi.
Wata sabuwar mota muka shiga wadda Muta'z ya yimin kyautarta yau bayan d'aurin Aure motar sai k'elli ta ke yi.
Muna shiga Gidan Sarauta ya d'auka a ko ina bakajin komai sai tashin kid'a da tambura ta ko ina,Muta'z kuwa yana d'akinshi shida abokansa suna ta yimai tsiya Mijin Meemi da Mumtaz abin shi kanshi burgesa ya ke yi sosai.
Meemi kuwa tana sashenta lokacin da aka shigo da Mumtaz ji ta ke kamar ta kashe kanta tsabar kishi,Baby kuwa sai kuka ta ke yi baiwar Allah Amman tak'i kulata da ta dame ta ma har dungure mata kai ta yi ai kuwa ta ringa tsala kuka.
"Don ubanki ba ubanki bane ya janyomin wannan fitanar ba ina zaman zamana yarinya ta lik'ewa mijina ai kuwa duk sai sun gane kurensu don wallahi bazan yarda wacce mace ta had'a shimfid'a da mijina ba.
B'angaren Fulani aka fara kaini ta karb'eni hannu bibbiyu sannan ta kaimu b'angaren mai martaba shima ya yimin nasiha sosai ta zaman hak'uri agidan miji,sannan ya mik'omin wasu mukulli na kyautar wani Gidan shak'atawarsa Har kuka saida Hajjo ta yi na ganin irin kyautar da Mai Martaba ya yiwa jikarta ta dinga saka mai albarka.
Sashen Meemi aka nufa dani Amman muna zuwa Masu yi mata hidama wato bayinta suka CE mana ta fita,Hajjo kuwa cewa ta yi "Uban ta fita ba bata fita ba🥴wallahi sai tadawo munanan muna jiranta ko in shigo d'akin tafito ja'ira,da k'er aka bata hak'uri ta hak'ura ammanfa tana ta sababi.
Sashena aka kaini aka ce in shiga da bismillah,ai kuwa na shiga da addu'oi a bakina gwanin sha'awa,sai da na CE alhmdh don wani dad'i da nishad'i na dinga ji sosai.
Akan faffad'an gadona aka ajjeni Amal ta rungumeni tana ta kuka y'an kai Amarya suka fara watsewa daga ni sai Amal sai Hanan ita kuwa sai murna ta ke yi ta samu k'awa ni kuwa kaina yana cikin had'addiyar lifaya sai k'amshi na ke zubawa ana cikin haka mukaji ana bud'e k'ofa.
Da sauri Amal ta tashi tana share hawayenta,Muta'z ne shi kad'ai yasha wata d'anyar shadda fara Sol abin sha'awa kyaunsa da nutsuwarsa da haibarsa duka sun fito gwanin ban sha'awa.
Gyaran murya ya yi Amal da Hanan suka gaishesa sukayi mana sai da safe,anan naji hanjin ciki na sun kad'a K'uuuu tsabar tsoron Muta'z, shima ya fuskanci haka don haka ya zauna abakin gadon yana me godewa Allah akan kyautar mata da yayi masa.
Matsowa ya farayi ni kuma ina ja da baya don kunyarsa na ke ji ba kad'anba kawai sai naji ya kamo hannuna cikin nasa,yana shafawa ahankali da sauri na janye hannuna ina Jan zuciya.
Dariya ya yi sannan yace ina yiwa Allah godiya da ya kawo mu wannan rana Dana mallakeki a matsayin matata,sosai na juyo numfashinsa gab dani ya yaye min mayafina a hankali sannan ya CE"Masha Allah ina yiwa Allah godiya da ya bani wannan babbar kyau ta,Mumtaz da ban Aureki ban San yadda rayuwata zata zama ba sonki Allah ne ya d'arsa min shi a cikin zuciyata,ki bani dama in koya miki sona kuma in shayar dake dad'in da baki tab'a ji ba arayuwarki.
Ummu Maher CE
Vote
Share
And
Comments
*_AKAN AIKI NA_*
Rubutawa✍🏻₹₹₹₹₹
*_(Ûmmu Mâhér)Míss gréén☘️_*
Wannan shafin naku ne masoyana Allah yabarmu tare.
*Mmn Teddy*
*Y'ar Kaka*
*Nabila Dikko*
*Nabiha Aminu*
*Ruky Gawata(My suruka)*
*Hadiza Barau Gidan Iko*
*Amina M Baso*
*Ummu najma*
*Dr Amira*
*Khaltum Khanna*
*Zahra'uu Naseer Aliyu*
*Nersmer*
*Momin Shukura*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.