Akan Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 12 of 21
*BABI NA 21&22*π
Nayi kamar banji abunda Umma ta fad'a ba don haka nayi shiru nak'i tashi Cikin zuciyata kuma tunani kawai na keyi wannan waye ya turo a kirawo ni?to koma dai waye ba zanje ba Don ni anawa tunanin bazan Fara zance ba har sai na gama makaranta sannan Zan Fara zance ,don ba Zan had'a makaranta da soyayya ba.
"Umma tace Mumtaz dake fa nake magana ki tashi kije waje kinyi bak'o," Nace to Umma Bari in k'ara sa yanke farce na"Umma tace to kiyi sauri dai ki tashi kije babu dad'i wulak'anci.
Wata kyakkyawar Mota na hango a k'ofar gidanmu irin mai bak'in glass d'innan,kuma ba'a hango mutumin da ke cikin motar,don haka a hankali na'isa wajen cikin murya ta mai dad'i"Nace Assalamu Alaikum,Wanda ke cikin motar ya amsa ba tare da ya fito ba.
Don haka nima sai naja na tsaya awajen ba tare Dana sake magana ba, Saboda ni arayuwata babu abunda na tsana aduniya sama da girman Kai,to idan ba girman Kai ba to menene?Nayi sallama ya amsa Amman bai fito ba nufinshi ni Zan bud'e motar in shiga kome?to A'i kuwa in dai haka ne zai dad'e don ni babu abunda na tsana irin zance a mota.
Cikin fushi nayi hanyar gidanmu saboda bazai yiyu yazo har k'ofar gidanmu ba sannan kuma yace zai raina mun wayo ba.
"Mumtaz don Allah ki tsaya kiji da abunda nazo miki da Alkhairi nazo miki,Muryarshi ce naji tazo mun a bazata koda ba'ah fad'amun ba nasan cewa Sir Mukhtar ne na makarantar mu,to meye ya kawoshi gidan mu kuma?.
Juyowa nayi Sannan "nace Sir sannu da zuwa ba tare da na had'a ido dashi ba,Saboda wani irin kwarjini da yayi mun ga wani irin kunyarshi da naji lokaci d'aya.
" Sannunki Mumtaz ya gida yasu Mama da Baba?"Nace duk suna lafiya Sir"Oky to Masha Allah wato Mumtaz nasan zakiyi mamakin zuwa na gidanku, Amman ba abun mamaki bane Saboda sone yaja Hakan.
"Mumtaz tun ranar da na Fara ganinki naji zuciyata ta aminta dake kuma zanso ki zamo Uwa awajen y'ay'a na,Ayanzu inada shekara 35 Amman tun ban Kai haka ba iyaye na suka damu inyi Aure,Saboda ni kad'ai ne d'ansu da suka mallaka arayuwarsu,don haka suke son inyi Aure suga Matata da Y'ay'ana.
Sai dai haryanzu banga matar da ta kwanta araina irinki ba ina sonki Ina k'aunarki Wallahi Mumtaz tun Ranar da na ganki naji Ina matuk'ar sonki so mai wuyar fassaruwa,Amman Ina fatan kema zaki Soni kamar yadda nake sonki?.
Shiru Nayi sa kama kon jin furucin Sir Mukhtar,Tabbas babu macen da zata ga Sir Mukhtar tace bata sonshi,Saboda yana da abubu wanda duk mace zata soshi,Yanada ilimi arabi da boko,yanada kyau,kud'i Da kuma hankali,kusan dai ya had'a dukkanin wani Abu Wanda mace zata soshi,Sai dai A i'nda gizo yake sak'a Shine kwata kwata ban shirya yin Aure yanzu ba Saboda inason inyi karatu in samu A'iki in taima kawa iyaye na,Sannan kuma bana son in had'a Soyayya da kuma karatu,don mafi akasarin y'an matanda suke biyewa Samari suyi ta soyayya k'arshe sai kiga babu abun arzik'in da suke shukawa A'cikin ajinsu.
"Mumtaz kina jina kuwa naji kinyi Shiru? kodai abunda nazo miki dashi ne ba kiyi a munna dashi ba?
DA k'er na bud'e bakina" Nace kayi hak'uri Sir Mukhtar bawai nak'i aminta da abunda kazo mun dashi bane A'ah kawai dai ni banason had'a Makaranta da Soyayya kawai shine matsala ta,kuma inason inyi karatu in samu Aiki don in taimakawa Iyaye na.
Sir Mukhtar "Yace babu komai Mumtaz kada ki damu indai kin amince Dani ni bazan zalin ceki ba,Ba kuma Zan ta kuraki ba Zan jira har lokacin da zaki gama karatunki sannan kuma in samo miki A'iki.
Kunya ce ta kama Mumtaz tayi saurin yin hanyar gidansu tana rufe fuska,tabbas tasan Son Sir Mukhtar ya Fara Kama ta don gashi tun daga yanzu ya Fara yi Mata kwarjini kuma ta Fara jin kunyarshi.
Shi kuwa Sir Mukhtar shafa kanshi ya Fara yi yana kallon Mumtaz cike daso da k'aunarta,ya shiga motar shi ya d'auko wasu kaya,sannan ya fito ya samu yaro yace ya kaiwa Mumtaz yana ganin yaron ya shiga saiya shiga motarshi ya tafi yana mai farinciki.
Mumtaz kuwa tana shigowa gida ta wuce d'akin ta da sauri tana fara'ah don bata kula da Umma dake tsakar gida ba tana yi Mata magana,Umma kuwa Murmushi tayi tabi Mumtaz da kallo Saboda idan kaga Budurwa tana farin ciki irin wannan to ta fad'a cikin soyayya,Umma bata gama rufe bakinta ba taji sallamar yaro,Yaron"Yace wai gashi inji wani a waje a bawa Mumtaz wannan.
Umma ta amsa tana cewa to An gode, Umma ta fara bud'e wani kwali kamar na wayar Hannu,ta bud'e shi me zata gani?wata dan k'areriyar waya ce mai kyau da tsari,Hannun Umma kuwa kakkarwa kawai ya keyi,sannan ta bud'e wata envelop β kud'i masu yawa aciki ga wata zungureriyar ta karda aciki,da k'arfi Umma ta Fara kiran Mumtaz cike da tashin hankali.
Da sauri Mumtaz ta fito ta tsugunna"Tace Umma gani,Mumtaz waye wanda yazo gurinki yanzu? "Umma Sunanshi Sir Mukhtar Malamin mune a makaranta Shine wai yace yana sona.
Umma tayi shiru kamar baza tayi magana Cen kuma" Tace shikkenan tashi ki tafi Bari Malam ya dawo zamuyi magana dashi, a hankali Nace to Umma.
********
Meema ta kalli Farida"tace kinsan Allah Farida bazan fito bariki a banza ba in koma a banza,kina ganin Murat sai binshi na keyi ya Aureni Amman sai wulak'anci ya keyi mun Saboda yaci moriyar ganga yanzu saiya zubar Dani.
Farida"tace A'i ni wallahi mamaki ma kike bani da kika lik'ewa Murat meye amfanin son Wanda bai damu da Kai ba,Saboda haka kawai gwara ma ki hak'uri dashi kawai,ga maza nan y'an bariki sai binki su keyi kina wulak'an tasu ke kince sai Murat kuma har kina maganar ya Aure ki,kada ki manta fa kunyi bariki dashi koda kin Aureshi ba lallai bane kuzauna zaman aminci da kyau na ba.
Haba Farida meyasa kike fad'in haka Kinsan cewa matuk'ar ban Auri Murat ba komai zai iya faruwa dani,Nidai don Allah Farida ki samomin mafita don Allah.
Farida"tace Meema Zan baki wata y'ar shawara da kuma wata dabara irin tamu ta y'an bariki,Meema tayi y'ar fara'Ar da tunda suka Fara magana ba tayi ba,"Tace ina jinki Farida nasan ba zaki bani banzar shawara ba,Farida tayi dariya sannan "Tace A'i dole in baki shawara tunda Ina cin banza, don Meema idan ban baki shawara ba ma sai Allah ya tambayeni don duk kud'in da muke samowa tare muke cinye romon kinga kuwa dole ne in baki shawara don a cigaba da samo mana d'an abun b'atarwa.
Farida" tace Meema yanzu zamu Fara tun tub'ar Murat akan maganar Aurenki i'dan yak'i yarda saimu had'a mishi gadar zare Wanda ba zai i'ya tsallakewa ba.
Meema"tace k'awata wani i'rin gadar zare ne Wanda ban San dashi ba?Farida"tace Meema tambayar da nakeso inyi miki wani mutunne Murat yafi tsana aduniya saboda da haka ne zamu had'a mishi gadar zare.
Meema tayi shiru cen Kuma "tace kwarai akwai hallitar da Murat yafi tsana aduniya don kuwa ko zancen Muta'z kika yiwa Murat sai kunyi fad'a.
*Yawan Comments*
yawan tyipingβπ»
*Ummu Maher ce*
*Vote*
*share*
And
*Comments*
*Tyiping*ποΈ
ππ€π
(α¦Λβ£Λα¦)(α¦Λβ£Λα¦)
*AKAN A'IKINA 2021*
(α¦Λβ£Λα¦)(α¦Λβ£Λα¦)
ππ€π
ABOUT MY WORKπ©π»βπ«
*NA*
*RABI'ATU.B.ABDULLAHI*
{{Ummu Maher}Miss green
π}
*π
Shalelen Jarumai writers Assπ
*.
____________
Y'AR MUTAN NIGERIAπ³π¬ππ€π
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.