Complete Hausa Novels

Akan Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 10 of 21

*BABI NA 17&18๐Ÿ“*

_____๐Ÿ–Œ๏ธ Hakan da mai marta ya ganine ya sa yafi fita Murat sosai sonda yake yiwa d'an shi Mutaz sai ya shafi Murat saboda haka aka saka Murat makaranta i'ri d'aya da ta Muta'z, Hatta kaya tare ake musu komai dai i'ri d'aya sai suka zamo kamar y'an biyu.

Tunda Murat ya taso yaga son da I'yayen Muta'z suke yimai da yadda suke narkar mai da dukiya sai abun ya tsaya masa aranshi yake jin cewa kamar son DA suke nuna mai na k'arya ne Saboda gaba d'aya yaga i'rin dukiyar da suke nar karwa akan d'an nasu.

Don haka Murat ya rik'e cewa tabbas sai yaga bayan Muta'z sai dai ya rasa ta inda zai Fara A'ikata b'ar narsa,Har Allah ya kawo lokacin DA suka shiga jami'ah alokacin ne kuma rayuwar Murat ta k'ara samun ta waya,Saboda gaba ki d'aya Murat ya canza hali,ya kuma canza abokai musamman ma da yaga acikin turawa yake,A'ikuwa Ana cikin haka ya had'u da d'an wani attajiri a makarantar nan danan suka k'ullah abokan taka dashi ya Fara koya masa harkar bin Mata,Muta'z kuwa koda ya gane abunda Murat ya keyi ba k'aramun tashin hankali ya shiga ba saboda aduniya banda i'yayenshi da k'anwarshi babu mutumin da yake so irin Murat yake kuma fatan rayuwarshi tayi kyau sai gashi ya b'ata rayuwarshi tun kafun aje ko'ina.

Har kullum Muta'z fad'a yake yiwa abokinshi akan yaji tsoron Allah Amman sai ya nuna mishi cewa ya fishi tsoron Allah don haka Muta'z ya cigaba da yiwa abokinshi addu'ah akan Allah ya shirye shirin addinin islama๐Ÿ™๐Ÿป.

Koda lokacin exam yazo Murat baiyi wani abun azzik'i ba don saka makonshi baiyi kyau ba Sam,Muta'z kuwa saka makonshi yayi kyau sosai da sosai,saidai daga lokacin da ya duba na Murat sai Murna ta koma ciki don ganin irin saka makon da abokin nashi ya samu.

Mai martaba yaji haushi sosai don duk abunda Murat ya keyi babu Wanda bai sani ba,saboda akwai masu kula da duk wani motsinsu sai dai su d'in basu sani ba don ya nemi kada su sani.

Allah ya taimaki Muta'z ya samu A'iki da gaggawa,shi kuwa Murat babu abun Arzik'i don haka Mai martaba ya d'aukeshi manager a company d'insu Amman lokaci d'aya Murat ya lalata Company ya zama gaba ki d'aya babu wani abu mai tsada cikin Company.

Hakan ne yasa Muta'z ya bud'ewa Murat Company na kanshi Wanda zai dun ga juya kud'inshi da kanshi I'dan ma ya cinye ruwanshi tunda Allah ya gani yayi mishi abunda yake ganin ya dace.

*Cigaban Labari*

Wani i'hu Mumtaz tayi tare da tsalle sai gata a tsakar gida,Umma tace ke Mumtaz wai meye yake damunki kina wani i'hu kamar zaki fasa mun Kai,Mumtaz tace Umma yanzu naji a radio Ana cewa Ana Neman masu son gurbi a jami'ah kuma harda ni acikin wad'an da aka suka samu gurbi a jami'ar.

Umma dariya ta Fara yi tana cewa Allah mun gode maka da ka amsa Addu'ar mu Allah ya taimaka,Allah ya baku sa'ah baki d'aya Allah ya sa i'dan kunyi karatun nan Allah yasa ku taimaki junanku Amin ya Rabbi.

Muna cikin murnar mu sai ga Mahaifina ya shigo shima ya ta yamu Murna sosai,Da daddare yace inzo muje kasuwa dashi,Bayan munje ya siyo min hija bai sun Kai biyar da ta kalmi da dogayen riguna masu kyau da kamala.

*Washe gari*

"Umma tace Kai Y'annan kinga yadda kika yi kyau kuwa cikin kayannan kinyi kyau sosai Wallahi,Dariya nayi lokacin da nake saka hijabina da yasha guga k'alk'al dashi gwanin ban sha'awa,simple make_up nayi ban shafa wani Jan baki ba hoda na shafa da lipstick na saka kwalli fuska ta tayi fayau nayi kyau gwanin ban sha'awa.

Rayuwar makaranta rayuwa ce mai dad'i kuma rayuwa ce mai sauk'i Amman idan ka d'au keta da sauk'i kuma idan baka nuna Kai d'an wani bane zaka zauna lafiya DA kowa,mutane da dama suna d'auka ta y'ar mai kud'i ceni saboda yadda lau nina yake,Nidai farace niba doguwa ba niba gajeriya ba ma'ana tsaka-tsaki.

I'na da dogon hanci Wanda ya k'aya ta fuska ta,ga d'an baki na k'arami mai kyau da tsari idanuna manyana masu wani i'rin launi mai kyau gwanin sha'awa,Hmm kyau da tsari saidai Wanda yaga Mumtaz.

Samari kuwa ta ko'ina zuwa suke wai suna sona Don takai i'dan naje makaranta bana fita daga class saboda yawan da samari suka yimun,A lokacin da nafara zuwa Makaranta na had'u da wata k'awata mai suna Zainab Bashir,Zainab mutuniyar kirki ce sosai don tana da d'abi'u masu kyau gata DA k'ok'ari sosai shiyyasa komai tare muke yi a cikin aji sai muka zamo abun sha'awa agun kowanni d'an ajinmu dama wad'an da ba y'an ajinmu ba .

Mun k'ulla k'awance mai k'arfi da Zainab,alokaci k'an k'ani y'an gidanmu suka Santa nima y'an gidansu suka sanni don kuwa watarana DA k'er muke rabuwa.

**********

Akwana a tashi asarar mai rai a yanzu muna lavel 3 inda muka k'ara dagewa a game da karatunmu na y'an jarida wato Mass Com,Allah yana bamu sa'ah a cikin karatunmu,Saidai ayanzu babu abunda yake da muna sai talaucin DA muke ciki nida i'yaye na.

Daman shagon da Baban su Amal ya bawa Babana shagon haya ne kuma asannu y'an unguwa suka karya mishi jarinshi da bashi don tsaba gen mugunta duk kud'in mutum sai kaji yace a bashi bashi toda i'rin wannan ne fa suka karyawa BABA na jari.

Shi kuma Mahaifina yana kunyar ya bugawa Alhaji waya ya sanar dashi halin da yake ciki,Saboda haka yaja bakinshi yayi shiru kuma ayanzu ya Fara Neman A'ikin da ya dace dashi Amman har yanzu Allah bai kawo ba.

Watarana ma haka nake tafiya makaranta ba tare da naci komai ba,Zainab kuwa kullum sai tazo da abinci makaranta duk saboda ni saboda tasan ni ba ma'abociyar cin abincin makaranta bace saboda haka take zuwa da abinci.

Duk itama Zainab ba kud'ine dasu ba Amman sun fimu rufin Asiri tunda Mahaifin ta yana A'ikin gwam nati sannan kuma yana da makarantar Islamiyya ta kanshi saboda haka yake samun kud'in da zai biyawa y'ay'anshi dukkanin buk'atunsu na yau da kullum.

Duk yadda Zainab za tayi Dani akan inci abincin da nazo dashi bana ci,don duk yadda muke dakai matuk'ar ba abincin mahaifiyata bane bana cinshi duk da d'inshi kuwa.

***********
Mai babban d'aki i'tace Mahaifiyar Mai martaba kyakkyawar tsohuwa mai farar Aniya,kamar kullum Muta'z da k'anwarshi sunzo gaishe da mai babban d'aki wacce suke Kira da Hajja,bayan sun gaishe ta suka zauna suna tsokanarta wai ta fiya cin goro gashi bakinta ya duk yayi ja.

Hajja kuwa tana jinsu ba tare da tace komai ba tayi dariya don ta shirya Rama i'ya shegen da suke yi mata,don haka ta kishin gid'a da filo Sannan ta k'ara gutsirar goronta ya bada k'araras sannan tace.

Hmm Ni kuwa Hanan i'na Saurayinki kuma yayanki Murat i'na yake?kwana biyu ban ganshi ba kada dai ace haryanzu bai daina rashin d'a Arshi ba?.

Sosa kai Hanan ta farayi tana cewa wallahi tsohu warnan matuk'ar mutum yazo wajen ki sai kin nemi b'ata mishi rai,yanzu meye laifinmu don munce kina cin goro A'i lafiyarki ake kare miki.

Hajja tayi dariya sannan ta kalli Muta'z tace Hmm wallahi Muta'z na kusa in gayawa ubanka ya nemo maka Mata kowa ya huta so kake kazama tuzuru agida KO to wallahi da Meemi Zan had'aka y'ar wajen Hajara wallahi kuwa kaji narantse daman irinku take so kyawawa.

Tuni Muta'z ya gimtse fuskarshi don yasan halin tsohuwarnan yanzu ta had'ashi da mai martaba,don duk abunda tace shi yake yi baya tab'a tsallake maganar Mahaifiyarshi Hajja.

Cikin Fushi Muta'z ya tashi zai fita don baya son hirar tasu tayi nisa don in akwai abunda ya tsana bai wuce zamcen Aure yanzu ba don babu yadda zai yi da Hajja ne shiyyasa,Karo yaci da wani Abu kamar mutum don haka ya d'ago kanshi don ganin waye?Meemi ya gani taci uban make-up tayi kamar y'ar tsana daman gata kamar zata karye,tsaki Muta'z yayi wuce warshi ba tare daya kalle ta,don haka Meemi ta juya tare DA cewa zaka sani yanzu Zan had'a maka muna finci kawai saita Fara kuka ta shiga wajen Hajja.

*Ummu Maher ce*
*Tyiping๐Ÿ–Œ๏ธ*

ABOUT MY WORK๐Ÿ“š

๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š
(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)
_*AKAN A'IKINA 2021*_
(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)
๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š

*NA*
*RABI'ATU.B.ABDULLAHI*
(Ummu Maher)Miss green๐Ÿ’š๐Ÿ“—

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…
_________________
______
๐Ÿ…™๏ธŽ๐—ฎ๐—ฟ๐˜‚๐—บ๐—ฎ๐—ถ ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ๐—ฟ๐—ถ๐˜๐—ฒ๐—ฟ๐˜€ ๐Ÿ…๏ธŽ๐˜€๐˜€๐—ผ๐—ฐ๐—ถ๐—ฎ๐˜๐—ฒ๐—ฑ๐Ÿ“š๐Ÿ–Š
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa _

๐Ÿ”๐Ÿ…™๏ธŽ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ๐Ÿ…๐Ÿ”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.