Akan Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 16 of 21
*Shafi na 30&31*
_______ποΈ"Yanzu Mukhtar saboda na hana ka Auren wannan matsi ya ciyar yarinyar shi ne ka ke ga ba dani,saboda na ce to ka daga halaka shi ne ka ke ne man ka bijire mun to wallahi tallahi ko kaso ko kada kaso na ne mo maka matar da ta da ce da kai"...
Tun ka fun ya ce wani abu Hajiya ta kashe wayar ba tare da ta ji me zai ce ba,kallon wayar ya cigaba da yi da tunani fal acikin zuciyarsa.
Yana cikin wannan tunanin Musa ya kirawo shi a kan maganar Mumtaz don yanzu an gama komai har ta fara zuwa Aiki Amman ba da sanin Mukhatar ne ya ne mo mata Aikin ba.
Godiya Muktar ya shiga yi wa Musa sannan ya k'ara tura masa wasu kud'in,sannan ya ce ya cigaba da kula masa da Ajiyarsa wato Mumtaz don shi har yanzu bai fitar da ran Auren Mumtaz ba.
***
"kai Allah mun gode maka da ka kawowa Mumtaz wannan Aikin a wannan lokacin,Allah ya kare ki Mumtaz da karewar ubangiji da mala'ikunsa Allah ya baki ikon yin gaskiya aduk inda ki ke.
Malam ne ya ke ta shararowa Mumtaz Addu'ah da fatan samun da ce wa aduk inda ta ke.
Malam kenan akwai ilimi da sanin ya kamata y'ar d'aya tilo a duniya wato Mumtaz a kullum cikin Addu'ah ya ke mata Allah ya kare masa i'ta a duk inda ta ke.
Sai a san Nanne Mumtaz ta d'ago kanta Ta ce"Malam Na gode da addu'arka kuma Insha Allah Zanyi ki ya ye A kan AI'KINA zan yi k'ok'arin Kare duk wani hakkin Dana San ba nawa ba ne."
"Allah ya yi miki Albarka Mumtaz ya Albarkaci Rayuwarki Mamana".
" Amin Malam".
"Na gode".
******
Hajjo Ta ce"Ai wannan albishir da ka yi min ya yi mun da d'i Allah sanya Alkhairi ya ba su zaman lafiya".
Mai Martaba Mahaifin Muta'z Ya ce" Amin Hajjo ni zan ta fi."
Nan fa Hajjo ta fa ra shi mai Albarka tana jin da d'i da haka har ta raka sa tana k'ara shi mai Albarka don ya cika Alk'awarin Mahaifinsa.
Daga inda Mimee ta ke tana jiyo Hajjo wato kakarta tana murnar Aurensu da aka d'aura i'ta da Muta'z,tsalle ta daka a cikin d'akin ta fa d'a kan gadonta tana dariya da kukan da d'i.
Hajjo ta ce"ke kinji min y'a saboda an d'aura miki Aure da wannan mai murtu kekkiyar fuskar shi ne ki ke dariya harda tsalle,to kya yi kya gama indai wannan ne ni ka d'ai Ce agabansa.π
Ni kuwa Ummu Maher na ce"oh Hajjo kin tsufa me Muta'z zaiyi da ke kykkyawan d'an gayu mai ji da ilimin addini likita_ likitan likitoci.
***
"Haba Fulani kina sane da Auren da mai maitaba ya d'aura mun da wannan ja kar yarinyar wai a matsayin matata."
"Yarinyar da kwata_kwata bata San mutuncin mutane ba ballan tana sanin darajar d'an Adam,yana maganar yana Jan numfashi don shi hayaniya ma bai i'ya taba Asalima shi ba ya son surutu sam ..."
"Haba Muta'z me ka ke so in ce akan wannan maganar kafi kowa sanin halin mahaifinka,ba'ah yi mishi ja yayya kuma me ye ai binsa don ya yi wa d'ansa Aure,kuma ya za b'a masa matar da ta da ce da kai."
"So ka ke yi in yi mishi musu don ya yi maka Aure ko me?to ba zan iya ba domin mijina shi ne Aljanna ta."
"Kuma Hajjo Mahaifiyarsa ce don haka ba by abinda za ta umarce sa ya k'i yi Mata shi matuk'ar bai sa b'awa Allah ba,kuma matuk'ar inason ya rabu da mahaifiyarsa lafiya to dole ne in ta ya sa ya rabu Mahaifiyarsa lafiya".
" Don haka nima Ina mai u martarka da ka yi hak'uri kabi zab'in da iyayenka suka yi maka ko ka sa mu da ce wa,kuma ka cigaba da yi wa iyayenka biyayya wataran sai labari".
Fulani tana kaiwa ta tashi ta koma b'an garenta tana tausayin d'anta abin k'aunarta a kullum.
Bayan kwana biyu aka fa ra bidirin biki A yi wannan a yi wan can Amman ba bu k'eyar ango don tun ranar ya koma sabon gidansa da ya Gina saboda hutawa.
Har gida Hanan ta kaiwa Mumtaz Invitation na biki,ranar ta da d'e i'ta da Umma suna hira ka fun daga bisa ni Mumtaz ta dawo daga wajen Aiki i'ta da wani abokin Aikin ta mai suna Mohd Lawan,jininsu ya had'u sosai don haka kullum sai ya rakota har gida bayan sun dawo daga Aiki.
Ko kafun Mumtaz ta dawo kallon Umma Hanan ta ringa yi tana hango fuskar mai martaba a kan fuskar Umma,don har Mumtaz. Ta dawo Hanan bata daina kallon Umma ba tana mamakin irin wannan kamanni ya yi ya wa.
Daga Alk'alamin
*Ummu Maher*
*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*
*TypingποΈ*
ππ€π
π€΅ββπ€΅ββπ€΅ββ
*A KAN A'IKINA 2021*
π€΅ββπ€΅ββπ€΅ββ
ππ€π
Which Meansππ»
*A BOUT MY WORKπ€΅βββπ»*
Na
*Rabi'atu Bashir Abdullahi*
(Ummu Maher)Miss greenππ.
π«π«
*π
οΈARUMAI π
¦οΈ WRITERS π
οΈSSOCIATIONπποΈ*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausaπͺ*_
*π«(π
οΈ.π
¦οΈ.π
οΈ)π«*
*Shafi na 32&31*
Sosai Mumtaz ta yi murna da zuwan k'awarta Gidan su Wato Hanan sunyi hira sosai sannan ta ke fad'a mata bikin Sweet brother d'in ta sannan ta bata gate pass d'in wajen.
Har bakin motar ta Mumtaz ta raka ta sannan ta dawo gida,har sai da Mumtaz ta shiga gida sannan Hanan ta ja motarta ta tafi,har zuciyarta tana jin k'aunar Mumtaz tana ji da ma Mumtaz ta zama y'ar uwarsu tana kwad'ai tawa a zuciyarta da ma matar Yayan ta ce da wannan tunanin ta fara driving zuwa gida.
*MUTA'Z*
"Yanzu don Allah Abinda ka ke yi Mu'taz ya da ce kenan ace tunda aka saka rana har yau da za'ayi dinner ba kaje kun dai dai ta da yarinyar nan ba."
"Fulani ki yi hak'uri duk yadda ki ke so haka za'ayi insha Allah idan na fita zan shiga wajen Hajjo insha Allah".
Da d'i ne ya kama Fulani don dama tasan d'an na ta mutun ne shi mai girmama iyayensa shiyyasa ma a kullum ta ke k'ara son d'an na ta.
*MUMTAZ*
" Kai Masha Allah Mumtaz kin ga kuwa yadda ki ka yi kyau kuwa?".
Dariya Mumtaz ta yi sannan ta kalli Ummanta ta ce "sai na fara zuwa Aiki don yau ni ce da duty zan d'auko wani Aiki sannan sai na biya wajen Dinner d'in".
" to Mumtaz ki kula da hanya Allah ya ki ya ye".
"Amin Umma".
*****
Sosai Mimee ta sha kwalliya ta alfarma sannan ta fito don su gana da Muta'z don kiranta kawai ya yi ya ce tazo ta same shi yana son yin magana da i'ta, haka kuwa a kayi yana zaune wajen shak'atawar Hajjo sai ga Mimee tazo.
Tun daga nesa ya hango ta yana sanye cikin shadda blue ya sanya hularsa zanna bukar ya yi kyau sosai shaddar sai walk'iya ta k'eyi da shek'i alamun shaddar mai tsada ce sai wane da wane zasu saka ta.
SLM
Kawai ta ce sannan ta samu waje ta zauna idonta k'uri akansa tana yi mishi kallon tsaf,ta da d'e tana son yayan nata sai yau ne Allah ya kawo mata ranar da za ta malleke sa a matsayin Mijinta don an Riga da an d'aura Aure tare wa kawai za tayi.
Shafa sajensa ya yi Wanda yasha gyara ya kwanta luf abin sha'awa da k'er ya fara juya lulu eyes d'insa zuwa fuskar Mimee.
Babu laifi Mimee kyakkyawa ce fara ce irin fau d'in nan k'irar jikinta kamar na silindium don tana da siranta sosai jikinta dai kamar irin ma asalin turawa.
" Yaya Muta'z gani an ce kana kira na,so ana yimun Make_up ne shiyyasa banzo ba"...
D'aga mata hannu ya yi alamun ta tsaya da maganarta sannan ya ce",daman nazo ne don in gaya miki bazan samu damar zuwa wajen dinner ba,idan ke za kije to ga hanya nan Amman ni bazan je ba,kuma kada ki kuskura ki fad'a wa rigimammiyar tsohuwar nan idan kika gaya mata in kika shigo hannu na ba zakiji da d'i ba,tunda ba tsohuwar ce za yi miki zaman Auren ba."
D'aukar glass d'insa ya yi irin me Skye d'innan yasa ka sannan ya yi wucewarsa yabarta da shak'ar dadda d'an k'amshin turarensa.
Bin bayan shi Mimee ta yi da kallo yana k'ara shiga ranta ji ta ke yi kamar ta janyo dare don ta ganta ga ta ga Yayan ta abin sonta.
Shi kuwa gogan bayan ya fito Gidan hutawarsa ya tafi don yaje ya huta kuma akwai wasu abubuwan da ya keso ya yi saboda haka ne yasa yazo Gidan don baya son hayaniya.
Saida ya yi sadaka sosai da kud'i,tsoffi sai addu'ah suke masa yana amsawa har ya shiga gidan.
Bai samu mai gadi a bakin gate d'in ba don haka da kanshi ya fito ya bud'e gate d'in sannan ya shiga,don yana tunanin ko yana ban d'aki ne.
Koda ya shiga gidan numfarfashi ya dinga ji acikin gidan yana bin lungu da sak'o na gidan yana dubawa.
Abinda ya gani ne yasa shi k'amewa awajen saboda abinda ya gane wa idanunshi.
*MURAT*
"Murat Aiki ya kan kama an gama komai yanzu burinka ya kusa cika ko kuma in ce ya cika ma."
Juyowa ta yi rik'e da wayarta a hannu tana dariya kamar mahaukaciya,sannan ta ce"babu abinda bana ganin bayanshi idan ya ce zai shiga rayuwata don haka mutane suke tsoro na.
Mima ce ta ke fad'in haka ya yin da ta kewayo da hannu ta kan sajen Murat cikin kissa da kisisina."
Janyo hannunta ya yi da k'arfi sannan ya ce"My Mima kin gama min komai dole ne ki zama ta hannun da ma na,dariya ta yi sannan ta d'auki glass cup tana shan lemo,tana jin zak'in lemon har can cikin zuciyarta sai da ta yi kurb'a biyu sannan ta ajje cup d'in ta d'auki wayar ta tana Neman wata number.
*__MUMTAZ___*
"Mohd yaushe zamu tashi ne saboda inason zuwa wata dinner ne?".
Ya bud'e bakinsa zaiyi magana wayar sa ta kama ruri,da sauri ya d'auki wayar yana cewa" hello waye.
Murmushi Mima ta yi sannan ta saita muryarta ta ce"Assalamu Alaikum. "
"Don Allah kutaimaka kuje gidan Muta'z Abubakar yarima Wanda ya ke titin gidan Radio d'inku,mun ganshi ya d'auki wata yarinya da gudu aka yasaka ta acikin motarsa Amman yanzu don Allah kuje kada ya cutar da i'ta."
"Hhh hhh hhh"
Dariya Mima ta yi sannan ta cire sim d'in ta saka shi a kwandon shara,Murat shima dariyar ya ke yi Sannan afili Ya ce".
*_MUTA'Z THE LIFE ISπ₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯_*
*Real Ummu Maher ceβπ»*
Vote
Share
&
Commentsβπ»
*Typing*ποΈ
ππ€π
π€΅π»ββπ€΅ββπ€΅π»ββ
*AKAN AIKI NA 2021*
π€΅π»ββπ€΅ββπ€΅π»ββ
ππ€π
Which Meansππ»
ABOUT MY WORKπ€΅π»βββπ»
Na
πΉRabi'atu B/ AbdullahiπΉUmmu Maher
(Miss green)πβοΈ
π«π«
*π
οΈARUMAI π
¦οΈ WRITERS π
οΈSSOCIATIONπποΈ*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausaπͺ*_
*π«(π οΈ.π ¦οΈ.π οΈ)π«*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.