Complete Hausa Novels

Akan Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 4 of 21

*BABI NA 5&6๐Ÿ“*

Nan Fa Fulani ta dage tanawa Mu'taz fad'a akan me zai dinga hawa motar haya,Mu'taz dariya ma Mahaifiyar tashi ta bashi Ya kama kunnenshi yace Allah yabawa Fulani hak'uri Allah yaja da ranki Uwargida Awajen Mai marta ba takawarki lafiya,Ai bai gama Rufe bakinshi ba Mai martaba Sarki Mahaifin Mu'taz ya k'elk'ele da dariya yace kaimu son i'rin wannan kirari haka nida kwanannan Zan k'ara Aure in Auro Baturiya Mai jan bakii,A'i Fulani k'ara har zuk'a tayi tana cewa daman Kai da d'an ka haka kuke da anfara magana sai kuyi sauri Ku Fara wayan cewa,Kai kuma da amfara magana sai kace zaka Auro baturiya ka Auro Agwa ma.
Dariya Mu'taz yayi shida Mahaifinshi Mu'taz yace haba a kwai wata baturiya da ta Kai Fulani wani Abu ai babu shi ya fad'a yana dariya,Fulani tace kwaji da shi dai.
Oyoyo Bros Wata y'ar budurwa ce da baza ta wuce Sha shida ba ta rungume Yayan Nata tana yimai sannu da zuwa cikin so da kulawa na y'an uwan taka.
Da ka ganta kasan k'anwar Mu'taz ce saboda yadda sukayi matuk'ar Kama da juna,Oyoyo My sister shima ya fad'a Mata yana Mai Jan hancin ta.
Bros ya naji kuna tsokanar My mom d'ita,Hanan Ashe kinji i'rin tsokanar da suke yimun KO?Hanan ta rungume Fulani tana cewa K'elesu My mom zamu rama,har wata baturiya ce za'ah had'a ta da my Mom d'ita Tauraruwar Mata kyakkyawa acikin kyawawa.
Fulani tace yauwa gaya musu dai suji?Hanan ta fakaici idon Fulani suka tuntsire da dariya i'tada yayan nata.
Fulani tace waifa akan na fad'a mishi gaskiya akan hawa motar hayar da yake yi shine Mahaifinku ya goyi Bayan shi,Hanan tace gaskiya My Bros kadaina hawa motar haya don Allah.
Mu'taz yace to Fulani kiyi hak'uri na daina,Fulani tace yau d'ana haka nakeso shiyyasa kullum nake k'ara sonka saboda kanajin magana ta.
Sarki Abubakar wato Mahaifin Yarima Mu'taz yayi dariya yace mu kuma da ba'ah sonmu sai ajefar damu ko?kuma tunda abun haka ne kwanannan Baturiyar nan zata shigo tunda abun haka ne.
Fulani tayi dariya tace Hhhh Mai Marta ba kenan Ai kaga y'ay'annan nawa sun isheni duniya da lahira don haka ba Baturiya ba ka Auro Balarabiya.
Mai martaba yayi dariya tare da cewa Hhhh Fulani kenan kishi KO?to naga ne miki kwantar da hankalinki Akwai wata mace da zata kaiki ai babu ita,Ai kuwa yaran nasu suka tun tsire da dariya .
Nandai suka ci suka sha suna maijin dad'in dawowar d'an nasu daga America,Bayan sun gama ne Mu'taz ya d'auki wayar shi ya kirawo Amininshi kuma d'an uwanshi Murat.
Kiran farko Murat ya d'auka yana jin muryar Abokin nashi ya ture Mima daga kusa dashi don yadda ta mak'alk'aleshi sai kace wata mayya ta kalli Murat cikin takaici daga zuwanta gidan za'ah Fara wulak'antata.
don Mima irin mutannan nan ne masu son Kansu matuk'a shiyyasa take mafarkin ace Murat ya zama Nata i'ta kad'ai,saboda yadda Murat yayi Mata yanzu ya tabbatar Mata da cewa Wanda ya bugo yanada wani bugire tare da wani matsayi arayuwar Murat.
Murat shine kasan Na dawo KO kazo mugaisa shine kak'i zuwa KO?Murat ya Sosa kanshi yana cewa Haba Life kayi hak'uri wallahi wani Uziri ne ya b'oye ni Amman yanzu ganinan zuwa ya fad'i hakan yana Mai kashe wayar ya nufi inda Mima take wacce ta gwalalo idanuwa tare da bud'e kunnuwa taji me'ake fad'a.
Ganin Murat yayi hanyar ban d'aki abun ya k'ara k'ular da Mima yau me Murat yake nufi da'ita daga zuwan ta saiya nemi wulak'anta ta,koda ya fito daga ban d'aki kud'i ya watsawa Mima Wanda baisan KO nawa bane.
Ba tare da ya kalleta ba yace inkin gama ki rufemun gida bai jira me zata ce ba yayi tafiyarshi tana ta masifa tare da nadamar zuwa don ba haka bokanta yace Zai faru yace Mata matuk'ar ta kwanta da Murat to komai yazama Nata domin Murat zai dinga binta kamar wani doki da akala.
Hira ce ta kaure sosai don tsakanin Murat da Abokin nashi kuma Amininshi Murat kuwa wani Abu ne acikin zuciyarshi a game da Aminin Nashi yana rok'on Allah ya nuna mishi Ranar da zaiyi maganin shi ranarda zai cika burinshi akanshi Ni kuwa Nace KO wani buri ne Murat yake b'oyewa oho?.
Hanan ce ta fito sanye cikin Doguwar wato Arabian gown gaban rigar yasha ado gata farar fata fatarnan Tasha jan lalle Wanda zaka rantse da shi aka haifeta dashi, Murat ya bita da I do kamar maye.
tana zuwa tayiwa kanta mazauni akusa da yayan Nata,ta kalli Murat ba tare da sakin fuska ba kamar yadda ta taho tace Ina wuni tana wani yauk'i kamar ba tason yin magana.
Murat ya shafa kanshi yanajin son yarinyar har Cikin zuciyarshi don duk wulak'amcin da Hanan take yimai bai tab'a nuna Mata ba saboda tun tana k'arama yake sonta.
K'anwa ta KO Nayi miki laifine kike kame mun fuska Murat ya fad'i hakan lokacin da ya d'auko tufa ya saka abakinshi yana jin dad'in tufar har Ranshi,Hanan tayi saurin cewa Wallahi babu abunda yake damuna kawai dai Kaina ne yake ciwo,cikin tashin hankali yace Hanan kinsha magani kuwa,Hanan ta tashi tana tafiya tana cewa Eh nasha yanzu ba tareda ta sake magana ba ta fita daga farlon don kwata kwata yanzu batason Murat tun Ranar da ya nemata da wata buk'ata ta tsaneshi ba kuma wai tsanarshi tayi ba A'ah kawai dai abun da yayi Mata ne ya saka gaba d'aya yanzun bata son ganin shi,har a zuciyarta tanason Murat sosai Amman yariga da ya b'ata rawarshi da tsalle.
Mu'taz ya kalli k'anwar tashi Bayan ta fita sannan ya kalli Aminin nashi yaga gaba d'aya hankalinshi yana kan k'anwar shi Hanan,KO meye ya shiga tsakanin su Oho?.
Shidai A'iya saninshi yasan cewa Murat da Hanan suna matuk'ar son junansu to meye ya faru,to KO Hanan ta gano Aminin nashi yana Neman matan banza Oho?A kullum Addu'ah ya keyiwa Abokin nashi na Neman tsari daga halinda Murat ya fad'a.
Mu'taz yace Murat ka k'eleta zata sakko kasan Mata kaidai Ka cigaba da Jan hankalinta asannu komai zaizo da sauk'i sai Abu na gaba da Zan gaya maka Murat kayi k'ok'ari kadaina kula matan banzan nan kasani Allah bata bacci kuma yana kallon ka don haka ka kiyaye dokokin ubangiji sai shima ya kiyaye ka daga fad'awa azabarsa.
Murat yaji haushin maganar Abokin nashi don haka ba tare da ya nuna mai ba aka cigaba da hira Inda Murat ya nuna wa Aminin nashi ya daina duk wani hali na banza.

โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…
Mumtaz kiyi sauri fa mutafi makaranta kinsan fa yau Malamin nan zaizo kinsan ba shida mutunci KO kad'an Amal ta fad'i hakan tana Mai shiga d'akin don ganin Aminiyar tata bata da niyyar fitowa,Wow wata yarinya a hango wacce ba zata wuce sha biyar ba tana shafa Mai A fatarta Mai kyau da tsantsi,Mumtaz kenan yadda mak'erin budurci ya k'erata komai Nata yayi kyau masha'Allah.
Mumtaz tace daman sauri na ke tayi kafun ki fito nasan kina zuwa zaki addabe ni shiyyasa nake ta sauri,Au haka zakice KO inji Amal dake shirin fita.
Mumtaz tayi saurin janyo ta tana bata hak'uri,Amal tace to sai kiyi sauri idan ba haka ba intafi,Nandai Mumtaz ta gama shiryawar ta suka fito don zuwa makaranta inda sukayi wa Umman Mumtaz sallama suka tafi ganin sha'awa.

*Wacece Amal*
Amal dai y'ar wani mutuncr Mai kud'i d'an Asalin jihar Kano ne matar sa y'ar Niger ce Buzuwa ce Jamal su biyu ne ita da Yayan ta Mai suna Ibrahim,Mahaifinsu Alhaji Abdullahi sun dawo Bauchi da A'iki ne saboda transfer da'akayi mishi saboda haka suka dawo Bauchi da zama,Alhaji Abdullahi bata son zama cikin masu kud'i wato bata son zaman G.R.A.saboda yace baka sanin halin da talakawa suke Cikin zama cikinsu kuma zai k'ara maka I'mani tare da tausayi da jin k'ai don haka koda ya su da mak'ofta suke da su Mumtaz don haka tunda ya bud'e i'do yaga halin da suke ciki Saiya ringa taima ka musu ya bud'ewa Malam shago a Bayan gidansu yana siyarda kayan masa rufi,Mumtaz kuwa tuni sunyi saboda Mai k'arfi tsakanin ta da Amal,hakan da Alhaji ya ganine koda za'ah saka Amal Makarantar gaba da Primary wato Secondary tare yakaisu yayi musu komai tare.

*UMMU MAHER CE*

Miss green๐Ÿ’š๐Ÿ“—โœ๐Ÿป

Share๐Ÿ‘‰๐Ÿป๐Ÿ‘‰๐Ÿป๐Ÿ‘‰๐Ÿป
And
*Comments*
*Tyiping*๐Ÿ–Œ๏ธ
ABOUT MY WORKโœ๐Ÿป

๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š
(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ
*AKAN A'IKINA 2021*
(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)
๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š

*Labarin gaskeโœ๐Ÿป*

*Na*
*Rabi'atu.B.Abdullahi*
(Ummu Maher)Miss green๐Ÿ’š๐Ÿ“—

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…
_________________
______
๐Ÿ…™๏ธŽ๐—ฎ๐—ฟ๐˜‚๐—บ๐—ฎ๐—ถ ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ๐—ฟ๐—ถ๐˜๐—ฒ๐—ฟ๐˜€ ๐Ÿ…๏ธŽ๐˜€๐˜€๐—ผ๐—ฐ๐—ถ๐—ฎ๐˜๐—ฒ๐—ฑ๐Ÿ“š๐Ÿ–Š
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_

๐Ÿ”๐Ÿ…™๏ธŽ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ๐Ÿ…๐Ÿ”

*WATTPAD Link*
https://www.wattpad.com/?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends.
____________๐Ÿ‘‰๐Ÿป๐Ÿ‘‰๐Ÿป๐Ÿ‘‰๐Ÿป

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.