Complete Hausa Novels

Akan Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Akan_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 11 of 21

*BABI NA 19&20*๐Ÿ“

Hajja tace"Meemi me ya faru kike kuka gayamun Wanda ya bugeki yanzu in sab'a mishi?,Sai kuwa Meemy tace"Wallahi Hajja Yaya Muta'z ne ya ringa rankwashi na har saida wajen yayi ja saboda wai na biyo hanyar daya bi.
Hajja kuwa tace"Ni nasan daman wannan yaron yana da mugunta don kawai kinzo gidansu saiya nemi ya dinga takura miki toko ubanshi bai isa ya hanaki zuwa gidannan ba,ballan tana shi d'an yau.
Meemy kuwa da ta b'oye a bayan Hajja ta fito tana yiwa Muta'z gwalo alamun ta samu nasara,Muta'z "yace Haba Hajja wanman yarinyar muna fukace babu abunda ta iya sai dai ta ringa had'amu fad'a dake,Sai kuwa Hannan ma "tace wallahi Hajja kinfi son Meemi damu i'ta ko fad'a bakya yimata amman mu kullum cikin yimana fad'a kike ko kunyar Mai martaba bakyayi.
Hajja "tace inyee wato ma inji kunyar ubanku ko saboda shine ubana to ba ranji kunyar ba y'ar mara kunya,kuma Aure babu fashi indai ina raye Meemi Muta'z zata Aura ko yana so ko baya son hakan.
Cikin fushi Muta'z ya tashi ya fita,Hajja tayi kwafa tace kaji dashi dai Aure babu fashi,d'an nema kawai Hannan ma "tace Nifa Hajja kidaina had'ani da Murat saboda wallahi ni bana sonshi kwata kwata kinfi kowa sanin mugayen halayenshi amman kike cewa wai shi zan Aura to wallahi da in Aureshi gwara in mutu banyi Aure ba,tana fad'in hakan ta tashi ta fita tana maijin haushin kakar tata da take had'a ta da fasik'i mai neman mata tabbas tasan tana son Murat saboda babu macen da zaice Yana sonta tak'i amince mai saboda yana da kyau kud'i ga iya magana ga iya soyayya sai dai ba shida hali ko kad'an.

*MUMTAZ*

Mumtaz"tace wallahi Baba sun ce idan ban kawo da wuri ba zasu rufe Exam din da zamuyi yanzu itace ta k'arshe kuma zuwa jibi duk wanda bai kawo ba bazai zana Jarrabawar ba.
Mahaifina"yace babu komai uwata zan nemo kud'in yau Insha Allah kada ki damu Insha Allah sai burinki ya cika na zama y'ar jarida.
Dariya nayi "nace Allah ya amsa Baba,Mahaifina da Umma suka had'a bakinsu wajen cewa Amin Allah ya amsa,Tunda Babana ya fita tun safe sai yamma ya dawo yana cen yana ne marmin kud'in da zan samu shiga jarrabawa.
Umma ta kalle ni taga nayi ta gumi," tace haba Muta'z babu kyau ta gumi fa,Insha Allah Malam zai samo kud'innan kidaina damun kanki da tunani kinji"Nace to Umma...Ban gama rufe ba kina ba mukaga Malam ya shigo da sallamarsa muka amsa mishi,koda ba'ah gaya maka ba kasan babu nasara afitar da Malam yayi duk farar fatar Malam saida ta nuna alamun yasha wahala.
da sauri na tashi na d'au komai abincinshi da ruwan wanke hannu,ya kalle ni yace sannu Mamana Allah ubangiji yayi miki albarka nace Amin Baba.
Yace Mamana wallahi ban samu kud'innan ba andai samu rabi da k'er shima faskare nayi mai yawan gaske to anan nema na samu rabona,kuka na fashe dashi na tausayin Mahaifina hanna yenshi sunyi jajir abunka da farar fata,Malam yace haba Mumtaz kidaina kuka mana ko idan kika kai musu baza su amshi rabin bane?.
Da sauri na goge hawayena nace zasu amsa Baba amman don Allah kadaina wannan faskaren akaina jibi fa yadda hannayen ka fa sukayi jajir,Malam"yace babu komai ai Y'ay'a amanane a gurin iyayensu hakk'i ne akanmu mu kula dasu shiyyasa kika ina yin duk ai kin da zanyi don in kula daku.

*Washe gari*

tun sassafe na tashi nayi shirina na makaranta naci abinci,na fito na gashe dasu Malam sannan ya mik'omin kud'in yace gashi in kai makarantar ince za'ah ciko sauran kud'in,"Nace to Baba na gode Allah ubangiji ya k'ara bud'i Babana yace Amin ya Mamana Allah ubangiji ya baku sa'ah a jarrabawar nan"Nace Amin Baba na.
Ina zuwa makaranta na had'u da Zainab itama lokacin tazo makarantar,Muka gaisa take cemun in rakata Zata biya kud'i"Nace to muna tafiya muna hira har muka iso wajen muka ga gaida mutumin sai fara'ah yake mana yana kallona, bayan Zainab ta bada nata kud'in aka bata recief sannan nima na bashi nawa.
"Nace ga nawa amman rabi ne zan ciko sauran,Kallona yafara yi kamar yana nazarin wani abu a fuska ta cen yace,Amman yadda kike d'innan abun ya bani mamaki don duk wanda ya ganki zai d'auka wata y'ar gidan mai kud'in ce.
Shiru nayi ina kallonshi don ni gani na keyi rainin wayo ne ma idan bazai amsa ba yaga yamun mana amman sai yayi mun wulak'anci sannan zai amsa.
Kallo na yayi akaro na biyu sannan yace yanzu nawa zaki ciko,nace mishi dubu biyar ne," Yace oky babu komai zan bada kud'in kar kiji komai,Shiru nayi ina kallonshi da mamaki a fuska ta ina mamakin kud'in da yace ya cikamun saina jiyo Muryar Zainab tana"Cewa Mun gode Sir Allah yasaka da Alkhairi.
Ban sanda nima na fara yimai godiya ba,Muka fito daga Office d'in yana mai k'ara kallona Cikin zuciyarshi kuwa shi kad'ai yasan abunda yake shiryawa akan Mumtaz Shiru yayi yana tuno sanda ya tambaye ta sunanta tace Sunana Mumtaz,Ahankali yace Wow Nice Name ya fara juyi akan kujerar sa ta Alfarma.
Muna fitowa"Nace Zainab Wai don Allah me mutumin nan yake nufi dani ne daya ke cewa Ya d'auka ni y'ar Maikud'i ce?Shiru Zainab tayi sannan tace to wai ke Mumtaz baki gane ba ne?,nace kwarai kuwa ban gane me yake nufi ba sam.
Zainab"Tace Hmm wato Mumtaz ked'in ta da bance ke Wallahi saboda komai naki i'rin na y'ay'an sarakai ne ko Y'ay'an masu kud'i, Saboda Allah yayi miki wata irin baiwa.
Allah ya baki baiwar kyau da baiwar Ilimi da baiwar Hankali da nutsuwa kinga kuwa Babu Wanda zai samu wad'annan abubuwan ba tare da anyi sha'awarsa ba,Dariya nayi "Nace Hmm Zainab kenen kedai kawai kice kina wasa k'awarki kawai amman ni banga wani abu dana fi kowa ba,Dariya itama tayi sannan " Tace ni kuwa Wallahi naga abunda kika fi dubbun mutane,Nan dai muka cigaba da hirarmu ta k'awaye cikin Fasaha da fahimtar Juna.

**********
Mumtaz"Tace Malam Wallahi Wani Malamin mune ya biya mun sauran kud'in,Malam yace to Mamana wani Malamin ne? "Nace Wallahi a makarantar mu yake,Malam yace to Allah ya saka da Alkhairi ,Nace Amin Baba "Malam Yace Amman Mama na kuringa kula da Makaranta zaka had'u da Mutane kala kala wala d'alibai wala Malamai don haka ki kiyaye,Nace to Malam Insha Allah.
Mun fara jarrabawa cikin sa'ah har muka gama exam,cikin sa,ah yanzu kuma mun tafi hutun sati biyu.

Ina zaune a tsakar gida ina yanke farce na,Wani yaro ya shigo yana cewa wai ana sallama da Mumtaz inji wani a waje,Shiru nayi ina kallon Yaron sai naji Umma tace kaje gatanan zuwa.

*Gaskiya kun rage tyiping Fans"*
Yawan tyiping yawan comments

*Ummu Maher ce*

Vote
Share
And
Comments๐Ÿ“
*Tyiping*๐Ÿ–Œ๏ธ

ABOUT MY WORKโœ๐Ÿป

๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š
(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)
*AKAN A'IKINA 2021*
(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)
๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š

*NA*
*RABI'ATU.B.ABDULLAHI*
(Ummu Maher)Miss green๐Ÿ’š๐Ÿ“—

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…
_________________
______
๐Ÿ…™๏ธŽ๐—ฎ๐—ฟ๐˜‚๐—บ๐—ฎ๐—ถ ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ๐—ฟ๐—ถ๐˜๐—ฒ๐—ฟ๐˜€ ๐Ÿ…๏ธŽ๐˜€๐˜€๐—ผ๐—ฐ๐—ถ๐—ฎ๐˜๐—ฒ๐—ฑ๐Ÿ“š๐Ÿ–Š
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa _

๐Ÿ”๐Ÿ…™๏ธŽ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ๐Ÿ…๐Ÿ”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.