Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel.docx
Chapter 10 of 28
Chapter. 1️⃣0️⃣ Zafin Gaskiya 🔥💔
“Ki bishi kinji,Aleena.” Mommy ta fada da murmushi mai kwantar da hankali. “Ku biyu ya kamata ku yi magana.”
Aleena ta daga kai kadan tana nuna kamar tana tunani. Kamar tana bukatar kwarin gwiwa. Kamar ba da gangan take jan lokaci ba.
Omar bacin ransa ya karu haƙoransa su ka matse jijiyoyin wuyansa na fitowa da kowane jan lokaci da take yi. Daga karshe sai ta daga kai ta mike motsinta a hankali tana gyara rigarta da gangan ta saki murmushi mai ladabi ga Mommy da Papa amma ban da Omar. Aleena ta wuce ta gaban Omar jikin su ya dan gogi juna kadan kamar tana sane da abin da take yi. Ya Allah…Omar ya kai hannu yana shafa gashin sa cikin huci da takaici yasan tana sane.
Omar yaji kamar jinin sa yana tafasa, Kafin ya iya hana kansa kawai yaji yana tafiya da sauri ya wuce ta ya nufi hanyar library dakin karatu kofar ya bude, kuma ba tare da tunani ba ya kama hannun Aleena ya ja ta ciki Ƙofar ta rufe a bayan su. Aleena tayi tuntube tana fadawa a kan kirjin Omar saboda tsananin jan da yayi mata babu zata.
Aleena ta zabura numfashinta ke fita da sauri cikin rashin kwanciyar hankali. “Ka Sake Ni.” Ta fada cikin murya mai sanyi da rawar jiki yatsunta suna ture shi daga rikon da yayi mata. "Kada ka sake taɓa ni." Ta fada tana danna masa harara.
Omar ya yi dariya ahankali da gangan ya matso kusa da ita sai ya hangi bugun jijiyarta a kasan wuyanta, Alamun ta firgita sosai kuma tana cikin fushi. Ya sake dariya yace, Da kyau. Don yana son tayi fushi sosai. “Kina ta wani sauti kamar irin jaruman nan masu arha a film.” Ya fada cikin sanyi murya, “Kuma abin takaicin, Baby. Ni ba jarumin soyayya bane.”
“Arha? Kai kuma fa?” ta mayar masa da martani, muryarta ta tsaya daram duk da yatsunanta suna rawa kafin ta haɗa hannuwanta a kirji. “Har yanzu ina da allergy din rashin iya jure shakar numfushi waje daya da kai. Maganar me zaka yi?”
Omar ya kara jan numfashi a hankali ya ja hannun sa cikin gashin sa kafin ya sake kallonta. Amma a wannan karon, Omar ya ɗan ja baya, yana sanya tazara a tsakaninsu; Don riƙe haushin sa.
“Kada mu bata lokaci,” ya ce da muryarsa a tsaye kowace kalma tana ɗaukar nauyin haushin sa. "Kawai saboda iyayena sun ce na amince, hakan ba yana nufin na yi ba ne. Na ce musu eh saboda dole ne. Saboda ina mutunta sunan iyalina. Ba saboda ina so ba."
Wani mugun murmushi hankali ya fito akan lips din Aleena. Sai tace, “Auu, Allah? Hmm…” Ta ɗan karkata kanta, tana barin shirun ya cika sararin tsakaninsu kafin ta ci gaba. "Ina tsammanin na gane yanzu dalilin da ya sa iyayenka suka tilasta maka wannan auren." Bata barshi ya ce uffan ba, ta ci gaba muryarta na cike da sanyi da gangan. "Wataƙila wannan auren yana da kyau a gare ka, Omar." “Zai kare ka daga cutar HIV."
Omar yaji kamar numfashin sa ya bar huhunsa cikin sauri da sanyi.
Amma Aleena bata gama magana ba. “Yawan canza mata sau da yawa kamar yadda kake yi… ba abin mamaki bane Idan iyayenka sun damu. Yaya magana ta tayi ma'ana, ko?" Aleena ta sake yin wani murmushi. "Player mafi shahararre a Turkey.”
Omar ya matso kusa, numfashinsa yana fita a hankali amma haƙurinsa ya gushe. Aleena ba ta motsa ba, ta tsaya daram hannunta har yanzu a haɗe a ƙirjinta murmushinta bai girgiza ba.
“Me kika ce?” Muryarsa a kasa cike da hadari.
Aleena ta dan karkatar da kanta, tana nuna kamar tana tunani. “Oh? na taɓa jijiyar zuciya ne?” Ta saki ƙaramar dariya, tana nuna rashin laifi. "I mean, come on, Omar. ’Mata nawa ka kasance dasu a rayuwar ka? Baka ma sani ba, ko?”
Muƙamuƙinsa suka damƙe, haƙora suna ta gogayya, Aleena ta tsaya cak idanunta cikin nasa tana masa kallan rashin kunya da murmushin rainin wayo. Yatsunsa suka shiga girgiza, sha’awar share ta da mari ta kama sa kusan ba zai iya jurewa ba. "Kina tunanin kin sanni?" Muryarsa ta fito da ƙarfi fiye da yadda yayi niyya. "Kina tunanin kin fahimci wane ni kawai saboda wasu kananun labarai da tsegumi?"
Ta sake sakin wata dariya kamar fushinsa ba komai ba ne illa abin nishaɗi a gare ta. “Omar, don Allah. Ba na bukatar jaridu su gaya min abinda a bayyane yake. Na girma ina kallonka. Kullum kai ne mai rashin hankali wanda bai taɓa ɗaukar mace abu mai daraja ba.
Omar ya kama gefen table da ke kusa da shi idanun sa sunyi dubu cike da wani abu mai hadari. "I'm warning you, Aleena-"
"Or What?" eh Omar? Nace, Me za ka yi?” ta katse shi tana karkatar da kanta idanun ta masu haske da ba’a acikin nashi. Zaka gudu ne wajen iyayenka ka gaya musu cewa Aleena mummunar munafuka ta yi maka rashin kunya? Kamar yadda koda yaushe kake yi lokacin da muke yara? Korafin akan abin da banyi ba?”
Muƙamuƙinsa suka damƙe sosai har seda sukai masa zafi.
Wannan yarinyar.
Wannan yarinyar mai dan banzan rashin kunya, mai shegen kaifin harshe, mahaukaciya kawai. Omar ya fada cikin ransa.
“Kasan bana son wannan auren” Muryar Aleena tayi sanyi yanzu, “Kana tunanin zan taba iya kasancewa cikin jin daɗin tare da kai har karshen rayuwata?”
Kalmominta na gaba suka kara sanyi, amma saukar su kamar naushi a ciki.
“Ba na son auren ka Omar,” Aleena ta ce, “Ba na son in kasance cikin aure da wanda ya dauki mata kamar abun wasa. Wanda nake ƙyama.”
Omar ya shaki numfashi da ƙarfi ta hanci yana tilasta kansa ya kasance cikin nustuwa da kin nuna kalamanta suna hura shi.
Wannan kalmar.
Wannan kalmar; ƙyama?
Amma bai ce komai ba.
Amma Aleena bata gama ba.
“Kai ba komai bane face dan iska kuma mai girman kai,” ta ci gaba, kowane kalma yana tafiya straight cikin zuciyar Omar. Ka saba samun duk wani abu da kakeso, koda yaushe kana kewaye da matan da suke jefa kansu a gare ka. Amma yanzu? A karon farko a rayuwarka, baka da zaɓi.” “Wannan dole ya kasance yana cin ka rai.”
Omar jikin sa ya hau girgiza da bukatar yin wani abu don ya karya shirun da bazai iya jurewa ba.
“Kina ganin wannan abin dariya ne, Aleena?” Omar cikin taku daya ya rufe tazarar da ke tsakaninsu. “Kina tsammanin zan tsaya a nan ina kallon ki kuma ki faɗi duk abin da kike so game da ni?”
Aleena ta firgita gaban ta ya shiga faduwa da bugu mai karfi.
Omar ya tilasta murmushi a leɓansa.
“Kin san abin da yake da ban dariya, Aleena?” Ya dan karkata kadan, yana jin dadin ganin canjin yanayinta. Muryarsa tayi kasa sosai da gangan. “I can’t believe you are still standing here, talking to me. Kuma kina bani nishaɗi.”
Aleena ta jefa masa wani mugun kallo, tace, “Oh, don Allah.” “Ba zan taba baka nishaɗi ba koda kuwa rayuwata ta dogara da hakan.”
“Haka ne?” Omar ya tambaye ta cikin wani murya ta ba’a da tsokana.
Ya bar kallonsa ya yi ƙasa wan da ya fada akan ƙirjin Aleena kafin ya sake saduwa da idanunta, murmushi yana karkadawa a leɓunansa.
Aleena nan da nan ta warware hannuwanta daga kirji suka rabu kamar tana bukatar rufe kanta. “Kada ka kuskura.” Tace.
Omar bai yi jinkiri ba.
Hannunsa ya fito, yatsun sa suka kewaye da hannayenta, dayan hannunsa ya jingine shi akan shiryayyen littattafai a bayanta.
Numfashin Aleena ya kama taji kamar yana daukewa jikinta ya tsaya cak. A ƙarƙashin riƙon Omar, saurin bugun jijiyarta ta karu. Wani abu ya kyalkyale a idanunta, wani abu ba fushi ba, amma kamar tsoro hade da wani abu wan da bazai iya fassarawa ba.
Omar ya jingino lips in shi suna kusa da kunnenta, muryarsa haɗuwar laushi da dafi. “Gaya min Aleena,” ya rada mata. “Idan kina ƙyama ta sosai kamar yadda kikace, me yasa numfashinki yake daukewa?”
Muƙamuƙinta suka damƙe, idanunta suna kyalkyalawa da wani abu mara iyaka kafin ta tilasta shi ya tafi.
Sannan ta tura sa.
Da ƙarfi.
Omar ya kyafta ido, da kyar ya iya riƙe kan sa akan table. Yaji wani irin zafi ya harba masa cikin kashin sa, ba kawai daga fushi bane, amma daga wani abu mai duhu, mai kaifi. Bai yi tsammani ba, amma gashi yana nan zafin. Shin saboda…
Aleena Khan?
Bai taba sanin cewa zai iya jin abu haka saboda ita ba.
Me ke faruwa.
“Kada ka sake taba ni irin haka,” ta ce.
“I hate you,” ta ƙara, da numfashi mara daidaituwa. “Ina bakin cikin cewa an daureni tare da kai. Ina bakin cikin cewa granny tana tilasta ni cikin wannan auren. Ina takaicin wannan la’ananniyar wasiyyar. Ina ba-” Ta shaki numfashi da ƙarfi, kamar ba za ta iya samun kalmomin da zasu gamsar da ita ba, kamar kawai fadin su ma suna da ƙona. “Kawai ina ƙin komai game da kai Omar.”
Ya yi numfashi ya tilasta kawar da zafin da ke karkadawa a jijiyar sa yana amfani da kalmominta a matsayin tunatarwa ga ƙiyayyan da yake mata.
Ya daidaita kansa ya gyara rigarsa kowane motsi da gangan.
Sannan, a hankali, ya ɗaga kallonsa zuwa nata. Yace, "That makes two of us,” Aleena tun da nima naki jininki.
Shiru suka yi nawani ɗan lokaci, babu ɗaya daga cikin su da ya motsa.
Sannan, Aleena ta shaki numfashi da ƙarfi, ta juyo takun ta cikin sanyin jiki tafara tafiya zuwa kofa.
Oh, no, Omar ya furta, da sauri ya motsa kafin ta fita yatsun sa suka naɗe kewaye da hannunta daidai lokacin da ta kai ga riƙon kofa.
“Ka bar ni natafi, Omar.” Ta fada cikin wata murya mai tsawa.
“A’a.” Omar yace.
Yatsunta suka dunƙule ƙirjinta ke tashi da saukowa da fushi mara iya jurewa. Aleena tace, “Ba na son in ci gaba da magana da kai akan wannan.”
“Too late,” Omar yace, yana mayar mata da martani, muryarsa mai zafi. “Kin rasa ‘yancin yanke shawarar abin da kike so a lokacin da kika din ga jefa min kowane mummunan zagi, Aleena.”
Ta juya, kallonta yayi kasa…. Tace, “Me kuma kake so daga gare ni, eh? Kana son in yi farin ciki da wannan auren? In yi godiya? In karɓi cewa rayuwata ba tawa bace ba yanzu?”
Muryarta tana rawar jiki tana girgiza.
Kawai sai Omar, ya sake ta.
Aleena ta kyafta ido, kamar ba ta yi tsammanin zai sake ta da gaske ba.
Wutar da ke idanunta ta ragu, ta mamaye da gurbin gajiya. Tace, “Ba na son in aure ka, Omar,” ta ce, a hankali yanzu. “Ina da wanda nake so. Ina da saurayi na, Ina son yin rayuwa tare da shi. Ba tare da irin ka ba.”
Omar ya karkatar da kansa, yana nazarinta, baya son ta ji kamar kalamanta suna da rinjaye.
“Did he propose already?” Muryarsa mai laushi da gangan, ta lullube da sanyin ba’a. “Kode keda shi kun fara shirye-shiryen aure ne? Yaron ne dalilin da yasa kike kokarin gudu daga wannan auren?”
Aleena numfashinta ya kama wan da ke bugar jijiya.
Wannan shi ne duk wani tabbaci da Omar yake bukata. Wata yar gajeriyar dariya ce ta fita daga lips in shi. Yace, “Wow. Ashe lamarin ya fi duk yadda yake tunani muni.”
Yatsunta suna girgizawa a gefenta, kamar tana hana kanta daga sharara masa mari. "Shut up, Omar. Baka san komai ba. Taja wani dogon tsaki.
“Ban sani ba?” Omar ya fada yana matsowa, idanunsa suna kallan yadda hakoranta suke matsewa. To menene plan in ki? Ki gudu? Ki roki kakarki ta canza ra’ayin ta? Ko kuwa kina fatan za ki ci gaba da jan saurayinki har sai kin samo hanyar tserewa daga wannan?”
Hancinta ya yi ja. tace, Gwanda ni, i respect my relationships. Ba kamar kai ba.
Omar, ya saki dariya, ya karkatar da kai da gangan yana ba’a. Yace, “Haka ne? Respect? Idonsa yana bin ta da kallon da yake so ya raunana ta da zafin raini. “To gaya min Aleena, shin kin shirya jiran invitation card in biki ya je har ƙofar gidansa ne? Ko kuwa zaki bar shi ya gano hakan da kansa?
Aleena ta gyara tsayuwarta, ta danne tsoronta da nuna nutsuwa. Tace, “Ka san me, Omar?” “Za ka iya fadin duk abin da kake so, amma a ƙarshe, baza ka taba samun abin da nake dashi ba.”
Kallon sa ya sauka akan lips in ta sannan ya koma kan idonta. “Go on, Aleena. Fada min mene shi?.”
Aleena ta saki murmushi a hankali da gangan, "Gwara ni, ina da wanda yake sona da gaske."
Omar, bai firgita ba, bai motsa ba, bai ja da baya ba amma kuma yaji kalmarta ta soke shi daidai in da takeso. Ya dan daƙe ya saki wani dan murmushi amma ya zama mara amfani. Ya juya don tafiya yatsunsa suna murza hannun kofar. Amma sai muryar Aleena ta sake yanka shirun. Wanda yasa Omar ya tsaya cak cikin wani sanyin jiki.
“Kana jin tsoro, ko?”Omar.
Omar bai motsa ba.
“Ba nawa ba. Ba na wannan aurenba. Amma na abin da zai biyo baya. Kana tsoron rasa iko.”
Wani dogon numfashi ya bar lips in Omar, Yayin da ya juyo ta gefen kafadarsa ya hadu da kallon ta. Yace, “Naga alama da gaske kina jin daɗin waɗannan ƙananan wasannin, ko?” Ya kara da murmushin sa mai kaifi kamar reza, Amma sede "Ina tsammanin zaki ci gaba da wasan yanzu ke kadai."
Aleena ta katse shi, tana cewa, "Ina tunani ne, Omar... bayan duk abin da ka yi, bayan duk matan da ka kasance da su-" Ta bar kalmomin su dade, tana jin dadin kowannensu. "-akwai wacce ta rage da gaske take son ka fiye da dare daya kawai?"
Rikonsa a kofar yayi karfi, bugun zuciyar sa ta tsaya, yayi shiru sannan ahankali yaja numfashi ya tilasta murmushi a gefen lips in shi kafin ya juya gaba daya ya fuskance ta. Yace, "Barin fada miki abu daya Aleena, kuma bazan maimaita miki ba. "Ki ji dadin karamar soyayyar ki da saurayin ki kafin ta kare." Ya kalle ta ya lura da damuwar da ta bayyana lokaci daya a fuskarta, sai ya kara da cewa; "Idan kina alfahari da rayuwar ki ta soyayya, to ki fahimci abu daya anan, muryarsa a tsaye ko girgiza babu. "Ban taba bawa ko wace mace damar hakan ba, saboda soyayya? bata cikin tsari na bawai don na rasa su ba. Saboda kowannensu sona suke kuma zasu kawo kansu ko ban nema ba, So, don haka bana bukatar soyayya. Ya kara da wata karamar dariya ya fice ya bar ta anan tsaye cikin sanyin gwiwa.
*******
Sati daya kenan yanzu da canzawar rayuwar Aleena, gaskiya ta fado cikin zahiri ta sauya komai cikin kiftawar ido. Cikin satin kullum Aleena zata hospital kamar yadda ta saba. Amma lafiyar granny ta kara muni Kwana huɗu da suka wuce—bayan chemotherapy na ƙarshe—doctor ya sanar dasu cewa jikinta baya karɓar duk wani abu da ake mata yanzu, Ciwon cancer ta bazu cikin gaggawa bisa sakamakon gwaje-gwaje.
Doctor ya bada shawarar ta rage damuwa. Amma sai Granny ta yi murmushi ta ce, bata taɓa jin damuwa ba koda da rana ɗaya ba a rayuwarta. Amma Aleena ta san ba gaskiya bane - kuma abin da ya fi daka mata zuciya shi ne sanin cewa itace silar jawo mata wannan damuwar.
Granny da Aleena basu taɓa zama sun tattauna batun maganar auren ba sosai, amma a wasu lokuta takan kawo zancen. amma Aleena sai ta datse ta da cewa; “Na amince, don Allah kada mu sake zancen yanzu.” Haka kuma kullum take cewa iyayen Omar idan suka zo hospital din idan har aka kawo batun auren, wani lokacin ko tayi shiru, ko kuma ta maimaita kalma ɗaya.
Wannan ya zama sabon waƙarta.
Rashin yin zancen auren yana taimakon Aleena wajen yaudarar kanta tunanin cewa auren bazai faru ba ko — aƙalla ba nan kusa ba. Kuma a cikin wawancin mafarkinta tana addua cewa idan ta cigaba da banza da zancen watakila sararin samaniya su manta, ko wani miracle zai zo ya hana auren faruwa tsakanin ta da Omar Thorne.
Amma ko jin sunansa kadai yana sa bugun zuciyarta ya tsaya bacin rai ya cika duk wani jijiyoyi a jikinta. Ta yaya zata iya rayuwa da mutumin da sunansa kaɗai ke sa taji rayuwarta ta yi mata duhu?
Ya Allah, this is too much.
Good thing, Aleena bata kara ganin Omar ba cikin wannan week din, Omar yana zuwa hospital din granny tasha fada mata amma kullum lokacin da Aleena bata nan. Omar bai taba tambayar ko ina take ba ko wani abu da ya shafe ta ba. Kamar su biyun sun san lokacin da zasu nesanci juna.
Emir da Aleena sun fita tare yau saboda Emir ya lura ta shiga damuwa mutuka bare duk lokacin da suke wayar dare ya fahimta koda yaushe hankalin ta baya tare dashi. kuma kullum ya tambayeta mene…amsa daya ce granny. Aleena ta canza masa kuma; Ba don bata son sa ba, sai dai don tsanin azabar wannan yanayi da ta samu kanta game auren da aka shirya.
Shahararren sanen restaurant suka isa, suka shiga ciki Emir yana zaune gefenta.
Ma’aikatan wajen sun kawo ruwa, abinci, da kayan sha. Wurin yayi shiru, waka a kunne mai daɗi a hankali. Glass cup ne a hannun Aleena fruit drink a ciki ta daga domin sha, sai ta ji kamar wani abu ne cikin drink din. Da sauri ta kalli Emir idanun su suka haɗu, ta zura hannu cikin glass din sai ga zoben da ta gani a motarsa. Emir zai mun proposing? Aleena gaban ta yace daras…Kafin ta iya cewa komai, Emir ya riga ya durƙusa. Ma’aikatan wajen suka ƙara sautin wakar tana fita cikin sanyi da soyayya.
Emir ya fara magana…
“Na dade ina tunanin wannan ranar.” ya ce da murya mai laushi. “I love you, Aleena. Ina son mu ci gaba da rayuwa tare. Ba zan iya hango gaba ba tare da ke ba. Na san yanzu ba lokacin da ya dace bane saboda granny tana hospital, amma hakan ne ya ƙara min ƙwarin gwiwa. I want to be here for you, To protect you. Ba zaki taɓa zama ke kaɗai ba. Ki barni in zama ginshikin rayuwarki.”
“Aleena, zaki aure ni?” Emir ya ce yana durƙushewa gaba ɗaya.
Aleena tana kallon zoben. Zuciyarta ta cika da tunani, Numfashinta ya ɗauke. Kafin ta ankara hawaye suka fara sauka a fuskarta.
Emir ya fara murmushi, yana matsowa kusa ya shiga share hawayen fuskarta. “Hey…” ya ce da murmushin sa dake kara fadadawa.
Ya kai hannu ya karbi zoben daga hannunta, ya ɗauki nata hannun domin sakawa. Sai kawai—“Emir, No!” Tace cikin sauri muryarta cike da ƙarfi ko dayake hannuwanta suna rawa. Emir ya tsaya cak idanunsa suka kada—watakila saboda yadda ta dakatar da shi kwatsam, ko kuma saboda amfani da sunansa da tayi.
“A’a. Don Allah… don Allah… kar kayi hakan.” Aleena tace cikin muryar mai rawar gaske.
“Me ya sa?” Ya tambaya, murya tana ɓari. Ya kalle ta saboda bai taɓa tsammanin hakan ba.
“Don Allah… ka tashi daga kasa ka zauna.” Ta roƙe shi muryar ta cike da rawar zuciya.
Emir ya tsaya na ɗan lokaci, sai ya tashi ya zauna a hankali, yana kallon zoben a hannunsa. Lips din sa suna rawar hawaye.
“Ki gafarce ni…” ya ce a hankali, har yanzu ya kasa iya kallon ta. “Na ɗauka kina so mu yi aure. Na ɗauka… kina jin hakan kamar yadda nakeji, Watakila na wuce gona da iri. Ki gafarce ni, Aleena.” Muryar sa ta kasa iya tsayawa idanunsa suka cika da hawaye.
Aleena hawayenta suka shiga sauka babu tarewa ko dakatarwa, Zuciyarta tana karyewa, kashi-kashi. Ciwon da take ji ya fito a fili da bugun zuciya mai ƙara da sauti.
Ta juyo ta kalle shi. Emir ya mayar da zoben cikin aljihunsa. Aleena ta kai hannu don ta rike nasa.
Wannan shine ranar da take gudu..Za ta karya masa zuciya kenan? Zuciyarta tana matsewa, kuka yana ƙoƙarin fitowa da mugun ƙarfi. Tunanin rasa shi ya fi ƙarfin abun da zata iya ɗauka.
Kukan ta ya fito da ƙarfi. Jikin ta yana karkarwa da azabar ciwo.
“I love you Emir. Bazan iya rayuwa ba tare da kai ba… amma ba zan iya ba. Ba zan iya auren ka ba. Ina mai matuƙar baƙin ciki. Ba zan iya ba.”
Ya lulluɓo da kuka, yana janyo kujera gaba.
“Shin saboda baki shirya bane? Don Allah, ki faɗa min. Idan baki shirya ba, zan jira. Zan jira har abada.”
“A’a,” ta katse shi, tana share masa hawaye a hankali.
“Ba zan iya… kawai ba zan iya auren ka bane.”
Ya janye hannunta daga fuskarsa.
“Me ya sa?”
Ta yi shiru, kalmomi sun tsaya a makogwaron ta.
“Abu ne…last week da ya wuce.”
Ya zaro ido cikin mamaki.
“Me ya faru last week da ya wuce? Me ya hana ki faɗa min? Wani kika samu ne? Aleena, haka ne? Kin samu wani? Ko dai lokacin da kika zo office dina da idanunki ja? Shin… kina son wani ne yanzu, Aleena?”
Ta girgiza kai da sauri.
“A’a. Ba zan taɓa yi maka haka ba. Abu ne da…” ta tsaya, ta rasa kalmomin. Ba zan iya faɗa ba. Ya Allah, ba zan iya ba.
Emir ya ci gaba da shiru, yana jira.
“Ba zan iya faɗa ba,” ta ce cikin kuka mai raɗa, hannuwanta suna ɓoye fuskarta.
“Ki faɗa min,” ya roƙeta, murya mai rawar jiki. “Ina da haƙƙin sani. Me yasa ba zaki aure ni ba? Don Allah.”
Ta fara shan kuka, makogwaronta yana ɓari da ƙoƙarin faɗa.
“Sweetheart, ni—”
Kira mai kara daga wayarta ya katse ta, ta kalli screen din. Zuciyarta ta fadi lokacin da taga “Nurse ɗin granny” ce ke kira.
Ta kalli Emir na ɗan lokaci. Tace,
“I have to take this call, Nurse ɗin granny ce.”
Emir ya kalleta sai ya gyada kai, damuwa ta bayyana a idanunsa.
– Madam Aleena, da fatan za ki gaggauta zuwa hospital yanzu. Kakarki ta faɗi. Doctor tace…
Idanun ta suka ɗauke, duniya ta fara juyawa. Bata fahimci abinda Doctor ta faɗa gaba ba.
Yayin da Emir ya lura da tashin hankalin, ya taso da sauri ya riƙe ta.
“Aleena? Me ke faruwa?”
Ta kashe wayar da gaggawa, hannuwanta suna rawar jiki, ta miƙe tsaye tana ɗaukar bag din ta.
“Dole ne in je hospital. Granny… tana… tana…”
Emir ya kamo hannunta da sauri, muryarsa mai nutsuwa amma cike da damuwa.
“Eh, eh. Ki nutsu. Kin ji?” Ya kalli ma’aikatan resturant din yace karbi card dina ku cire bill din, sannan ya kalli Aleena.
“Tafi mota. Zan biyo ki nan da nan.”
Ba tare da tunani ba, ta gyada kai, ta juya ta nufi filin ajiye mota. Duniya ta zama ba komai ba a gaban ta kamar babu wani abu da ya rage mai mahimmanci.
Ya Allah, don Allah kada wannan abu ya zama gaskiya.
A/N: 💔🥺………
💘AUREN ALEENA💘
Amal Musa ✍️
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.