Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel.docx
Chapter 18 of 28
Chapter. 1ï¸âƒ£8ï¸âƒ£ Gargadi Na Ƙarshe âš ï¸
SHARE SHARE SHARE 💃💃💃💃💃
Emir and Aleena.
Suna zaune su biyu kan wani table kadan daga nasu, sun yi nisa cikin magana da waiter.
Amma ba wai maganar su da waiter bane ya tada wa Omar hankali ba —
Sai yanda Aleena ta zauna kusa da Emir, kanta na gogar kafadarsa, yanda suka yi very close sosai... kamar masu hakkin juna.
Kuma har bayan waiter din ya tafi, Aleena bata matsa ba.
Sun zauna ne kamar masoya.
Kamar suna cikin relationship wanda duniya zata yi alfahari dashi.
Kafin Omar ya kai ga kyafta ido, Emir ya kamo hannun Aleena...
Ya manna mata kiss a bayan hannun ta, sannan ya dora kiss a goshinta.
A nan. A gaban restaurant. A gaban jama'a.
A gabansa Omar.
Da gaske tana ganin ya dace ta yi haka? A gaban jama'a? Idan wani ya gan ta fa? Inda wani ya gane wace ita fa? Worse, tashin hankalin inda iyayena suna nan fa?
Na tsani wannan halinkin naki na munafurci Aleena Khan. Omar ya ja dogon tsaki. Bama ta dauki maganar da mukayi serious ba kenan. I can't believe ina ganin wannan rashin hankalin da idona.
Wani irin wuta ya taso a kirjin Omar, jijiyoyin wuyansa suka matse, hade da bacin rai da yake hura zuciyarsa. Ya juya ya kalli Hasan, muryarsa ta yi sanyi amma cike da wani abu mai ban tsoro wanda shi ma bai san asalinsa ba.
"No," Omar ya ce, yana takura kalmomin su fito daga bakinsa. "Ba budurwarsa bace."
Hasan ya daga gira, rashin fahimta ya bayyana a fuskarsa.
"Taya ka san hakan? Ka san ta ne?" Hasan ya tambaya cikin muryar da ta yi kasa.
"Eh, na san ta." Omar ya fada a hankali yana gyada kai. Muryarsa tsaye, duk da wutar da ke huruwa a kirjinsa. "Na san ta... sosai ma."
"Oh, really?" Hasan ya ce yana dariya. "Amma ka tabbata ba sa soyayya kuwa?" Ya kara juyawa yana kallon table dinsu. "Seriously... look at them, Omar. Yadda suke kallon juna—ido baya karya, bro." Hasan ya ce yana kara dariyar da ke kara hura wuta a zuciyar Omar. "Kalli fa, ba wai gulma nake ba, amma babu yadda zan yarda wadancan ba masoya bane."
Omar ya kama karshen bakin table din da yatsunsa a hankali. Ya ji kansa yana juyawa, ya sake satar kallonsu ta gefen ido. Amma kallon da ya yi sai ya kasa iya cire idonsa daga kansu.
Lallai Hasan ya yi gaskiya, Omar ya furta a ransa.
Aleena ta zauna kusa da Emir, bata taba shi ba, amma yadda suka bace cikin kallon idon juna babu mai cewa ba masoya bane. Sun juya musu baya, da gefe na fuska. Omar ya girgiza kai yana kokarin korar duk wani abu da yake ji, wanda shi kansa bai san me ya sa yake ji ba. Yanzu, da ace iyayensa sun ga wannan, tabbas stroke zai kamasu saboda bakin ciki.
A cikin wannan lokacin, Aleena ta juyo. Sai idonsu ya hadu. Kamar tana iya jin wutar da ke feshi ta cikin tsananin kallon Omar. Idon Aleena ya faÉ—aÉ—a sosai. Na wasu sakanni kaÉ—an, hannuwanta suka sankare suka kasa motsi. Idanunta da na Omar suka makale cikin juna. Fuskarta tayi sanyi, idanunta suka kad'e, tashin hankali ya bayyana karara.
Kirjin Omar ya matse, wani irin zafi yana neman cinye shi. Ya yage kallonsa daga nata, ya mayar da hankali kan Hasan, yana kokarin controlling numfashinsa. Ya daga glass din vanilla ice juice dinsa, a second ɗaya ya kurɓe shi har ya zuba cikin makogwaro. Amma duk da hakan, sanyin juice din bai kashe wutar da ke cikin sa ba.
Omar ya sake jan dogon tsaki, nauyin ɓacin rai yana ƙara zama a kirjinsa. Ya yi kokarin shanye shi, ya basar, ya nuna cewa shi babba ne mai tunani. But damn it, ya kasa. Akan idonsa Aleena ta tsinka duk wani layi da rules da ya zana mata akan cewar kar ta karya. Kuma yanzu bai ji zai iya controlling kansa.
"Omar, are you okay?" muryar Hasan ta fito cike da damuwa.
Omar ya gyada kai, mukamukinsa a matse, sannan yace cikin sanyin murya, "Kasan me, Hasan? Abubuwa da yawa sun faru a rayuwata kwanakin nan... kuma ba kowa ne yasan cewa yanzu haka nayi aure ba."
Idanun Hasan suka bude cikin mamaki da rashin fahimta. "Mey? Aure?"
Omar ya sake gyada kai yana hadiye wani abu mai daci a makogwaronsa. "Yes... kuma labari ne mai tsawo. Amma point dina shine, wadancan da kake gani zaune — Emir Batuhan da yarinyar da ke gefensa — ba masoya bane. Saboda..."
Ya tsaya. Kalaman suna shake shi a makogwaro, jijiyoyinsa suna harbawa da gudu yayin da ya danna wayarsa cikin aljihunsa. "Saboda waccen yarinyar... sunanta Aleena Khan. Kuma... matata ce."
Daga nan, Omar ya mike tsaye daga kan kujera, kujerar tana yin wani ƙaramar ƙara akan tiles ɗin, abin da yasa Hasan ya firgita, bakinsa a bude, ya kasa rufewa.
"They are just good friends," Omar yace, muryarsa sanyi kamar yankar wuka. "Kaga Hasan, mu manta da abinda ka gani yanzun nan. Ina bukatar in tafi yanzu in yi magana da matata. I'm sorry, saboda bazan iya zama nan ba. And... karka manta — next visit dina zuwa club dinka, zaka iya gani na closer than you think. Ka jira kirana."
Hasan ya gyada kai da sauri, amma jikinsa yayi sanyi. "Bazan yiwa kowa wannan maganar ba, Omar... amma masha Allah, nayi maka murna. Allah ya sanya alkhairi. Ba matsala, sai mun kara magana."
Omar ya gyada kai, yana juyawa, bugun zuciyarsa na hade da wani zafin kirji. Ba zai iya barin Hasan cikin rashin fahimta ba — abokinsa ne, kuma ya cancanci sanin gaskiyar auren sa.
Zeyneb tana aiki a Batuhan Ads, kuma Omar baya son gulma da kananan magana su fara yawo. Ko yanzu ko anjima, gaskiya zata fito, kowa zai sani.
Idon Omar ya hadu da na Aleena yayin da take mikewa tsaye, idanunta sun yi ƙasa-ƙasa, cike da lissafi. Emir ya lura nan da nan, ya daga kansa ba tare da wani alamar firgita ba. Idonsa ya hadu da na Omar cikin wani silent challenge.
Omar ya yi tafiya a hankali zuwa table ɗinsu. Tension ɗin na ƙaruwa da duk wani taku da yake kara dauka. Ya tsaya kusa, sannan ya zauna, ya ɗan matso kadan — kallonsa ya tsananta akan su biyun.
"Salaamu alaikum," Omar yace da muryarsa kasa, cikin nutsuwa amma dauke da kaifi, wanda shi kadai ya isa ya yanke iskar da suke shaka. Ya ƙara da wani murmushi mara iya karantuwa.
Emir ya gyara zamansa, ya dan ja baya kadan, sannan kallonsa ya sauka kan Omar. Cikin wani murmushi na raini yace, "Wassalam, barka dai Omar."
Omar ya saki wani murmushi, sannan ya juya kallonsa kan Aleena — wacce har yanzu ta kasa komawa ta zauna balle magana. Idonta ya makale cikin na Omar, ta kasa dauke shi.
"Ko zaki amsawa saurayin ki ne? Mey ke faruwa anan, Aleena?" Omar ya tambaye ta.
Aleena ta kyafta ido sau biyu a lokaci daya, sannan ta kau da kallonta daga kan Omar zuwa kan Emir. "Emir, zamu fita waje muyi magana nida Omar, dan Allah kaji."
"No need," Omar ya katse ta, murmushinsa yana daukewa. "Bana bukatan hakan," muryarsa cikin wani sanyi kamar kankara. "Bata min lokaci kawai zaki yi. Bazaki fahimta ba, Aleena. Saboda yanzu haka kalamai na sun yi miki tsauri. So... don haka bazaki gane ba."
"Please don't try to make a scene here," Aleena ta fada a hankali tana daga gira, tana masa nuni da inda suke. "Kaga da mutane da yawa anan, kazo muje waje muyi magana."
Omar ya ja baya ya dan kwanta kan kujera, dariya tana fita da karfi daga bakin sa yayin da yake kallon ta kamar yana karantarta. Wani nishadi yaji yana dawo masa.
"Ka fita waje kuyi magana kawai, Omar, akan ko mene yake damunka," Emir ya fada, wanda daga jin muryarsa kowa zai san kasancewar Omar nan bata gabansa. "Wannan dabi'ar taka ta mai da komai wasa da yarinta bamu da lokaci."
Omar ya daga gira yana pretending kamar ransa ya baci. "Yarinta?" Ya matso kusa, hannunsa suna bugun table din da karfi da gangan. "Look at you, Emir. Kana kiran abinda nake yarinta? Bayan kai ne kake yawo a gari da aurena, ko kunya baka ji."
"Auren yarjejeniya dai ko," Emir ya maida masa, muryarsa cikin nutsuwa da rashin damuwa ko kadan a jikinsa. Da wani mugun murmushi ya fito a gefen bakinsa. "Sannan kuma, bari in tuna maka... har yanzu budurwarta ce."
"Hakane," Omar yace. "Amma kamar kana bukatan na tuna maka shedun da suka shaida igiyata a kanta, da zoben hannunta? Ko ka manta da bakinta da nawa muka amsa muka karbi juna, wanda kaji da kunnenka a waje?" Omar ya mayar masa da martani, dariyarsa tana karuwa. "Don haka Aleena... matata ce."
"Mey hakan, Omar?" Emir ya tambaya yana daga gira. "Karka ce min kishi kake yanzu?"
Omar ya bude idonsa sosai, bakinsa a bude yana shirin mayar da martani, amma Emir ya rigashi ya sake magana. "Interesting," ya fada, muryarsa cike da jin dadin abinda ke faruwa. "Na san ka sosai, Omar. Idan har kana kishi akan wani abu, nasani... Emir ne fa ni. Omar, karka manta."
Idon Aleena ya zagaye daga Omar zuwa Emir, cike da mamaki da takaici. Da kuma ta kasa fahimtar komai — suna magana ne kamar wadanda suka san juna sosai.
"Stop it, Emir. Ba kishi yake ba. Meysa zai kishi?" Aleena tace.
Emir bai dauke idonsa daga kan Omar ba, haka kuma Omar bai dauke nasa ba. Omar ya tsaya yana kallonsa da wani kallo kamar yasan wani abu dashi bai sani ba — kuma Omar ya tsani kallon nan.
"Don't talk nonsense kamar kasan ni, Emir. Don baka sanni ba kodan," Omar ya fada, muryarsa tana kara sanyi mai kaifi. "Karka kaini bango na rasa karamin mutuncin da ya rage da nake dashi gami da kai. Zai zama abin kunya ganin cewa munyi rayuwa kusan shekaru tare, wanda na dauke ka kamar brother. Baka tunanin hakan?"
Emir ya matse mukamukinsa, idanunsa cike da haushi, jikinsa kamar yana rike kansa daga fadan wani abu da zai ladama daga baya.
Suka yi shiru, amma basu daina kallon juna ba — tension din yana karuwa.
Aleena ce daga karshe ta karya shirun. "Alright, enough. Ya isa haka don Allah. Take it easy," ta fada a hankali tana matsowa kusa da Emir, ta tsaya a gefensa tana kallonsa. Wannan tsayuwar kusa da shi ta kara wani irin haushi cikin zuciyar Omar, wanda ya rasa yadda zai fade ta.
"Come on, Omar. Come with me," Aleena ta fada, tana masa nuni da ido cewa ya biyo ta yanzu.
"Aleena," Omar yace da murya ahankali, idonsa acikin nata, sannan ya sanya hannunsa ya dannata ta zauna kan kujera. "I am warning you, karki kunyata ni ko family dina." Ya fada, sannan ya dan kwanto kasa kusa da ita. Yanzu muryarsa ta sauka cikin wani irin rada mai razanarwa a kunnenta.
"I don't care ko meye tsakaninki da Emir yanzu, kina jina? Amma ki tuna cewa ke mace ce kuma matar aure — matata. Karki ga har yanzu ina kyaleki kiyi yadda kikeso ki dauki hakan kamar bansan me nake ba. Kada ki kaini bango, bazaki ji dadina ba."
Omar ya mike tsaye yana gyara rigarsa. Idon Aleena ya biyo Omar, fuskarta ta firgice gaba daya.
"Ki dauki wannan matsayin gargadina na karshe," Omar ya fada da muryarsa mai kaifi, babu yafiya ko kadan a ciki. "Next time, bazan yi magana ba... mataki kawai zan dauka. Enjoy your lunch."
Ba tare da ya jira wata amsa ba, ya juya, ya fice daga restaurant din cikin takunsa mai nauyin izza.
💘AUREN ALEENA💘
Amal Musa âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.