Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel.docx
Chapter 3 of 28
Chapter.3️⃣ Wasikar Sirri ✉️
Na ɗan runtse ido na, sannan na lumshe su da gajiya, na saki wani ƙaramin numfashi cike da kunci. Na jingina da kujerar bayana kamar wadda ta gaji da rayuwa.
“Ta yaya kuke sa ran za mu iya kera raka’a dubu sittin cikin wata biyu?
Injinanmu, ma’aikatanmu—ba su da ƙarfi fiye da raka’a 300 a rana.
Wannan ba zai taɓa yiwuwa ba.”
Leila ta jingina gaba, fuskarta cike da kwarin gwiwa da murmushi mai kwantar da hankali. “Zamu nemo mafita. Complaining won't solve anything. Karki manta kefa ba irin wacce ke wurgar da towel kafin faɗa ya kai kololuwa bace. Zan wuce factory yanzu, in tattauna da ɓangaren samarwa, in ga yanda za a iya gyarawa.”
“Na haɗe hannayena da ƙirjina, ina gyada kai a hankali. “Kiyi hakan, Leila. Let's hope there's a way to make this work. A halin yanzu zan fara neman wasu madadin hanyoyi.”
Mariam ta ƙara da cewa, “Zan soke wasu abubuwa daga jadawalin ki na ’yan kwanakin nan, domin ki maida hankalin ki kacokan akan wannan batu.”
"Good," I said simply, na miƙe tsaye tare da ɗaukar jakata. Na gyara rigata, sannan na kalle su da ɗan murmushi. “Zan wuce asibiti yanzu.”
Suma suka miƙe tsaye, suna gyada kai da fahimta.
“Ki tafi,” Leila tace da murmushi mai dumi. “Ki gaishe min da granny. Ki faɗa mata zan zo gobe da labarai masu dadi. Wanda take matuƙar son su.”
Na yi murmushi kaɗan, ki daure kizo kam. “Because tana yawan tambayarki. Wai akwai wani labari daga kasar Ingila da kika fara yi mata. Tun daga lokacin take jiran cigaban sa.”
Yayinda na juya zan fita, Mariam ta dafa hannuna a hankali.
“Aleena, ki sanar damu halin da take ciki idan kin je, don Allah. Kuma ki kwanta ki huta. Kina matuƙar bukata.”
Na gyada mata kai a hankali, na fice daga office.
Motar da ke kai ni asibitin tayi shiru sosai, sautin injin ɗin yana tafiya daidai da kukan tunanina. Wannan tafiyar ta koma kamar al’ada ce gare ni yanzu — tafiya ta kullum zuwa wajen da ya fi kama da gida fiye da masaukinmu na alfarma.
Kakata mai shekaru 81 tana asibiti yanzu haka kusan wata uku kenan.
Komai ya fara ne da faɗuwarta a banɗaki bayan bugun zuciya (stroke) da ta samu. Faɗuwarta ta daɗa ta’azzarar lamarin, amma abinda ya biyo baya yafi muni.
Lokacin da akayi mata tiyata don cire jinin da ya taru a kwakwalwar ta, likitoci suka gano musabbabin hakan: ciwon daji (cancer) a cikin IV pancreatic cancer wanda ya riga ya bazu har zuwa hantar ta. Bugun zuciya bai zo ne da kansa ba — jikinta ne kawai yake kiran agajin taimako.
Lokacin da muka fahimci cewa ciwon daji ne, ya riga ya yi nisa. Kwayar jinin da ta taru a kwakwalwa ta lalata wasu sassan kwakwalwarta. Yanzu kuma, baya ga dawowa daga stroke, ana yi mata maganin ciwon daji (chemotherapy).
Amma koda akeyi mata magani, likitoci ba su ɓoye gaskiya ba: bata da sauran lokaci mai tsawo.
Sai dai kakata — Mutum ce mai ƙarfi da juriyar zuciya — taci gaba da fuskantar komai kamar lokaci bai naurce ba. Tana shan magani da fahimta, tana karɓar jinya da natsuwa da kwanciyar hankali wanda yake jan hankali kowa da kowa da ke kusa da ita.
Ni kuwa? Ban da wannan ƙarfin.
Yayin da take faɗa da ɗoki da aminci, ni kullum ina cike da tsoro da raunana — kowace rana tana tuna min da raunin rayuwa da yanda komai ke iya canzawa cikin ɗan lokaci.
Motar ta tsaya. Na fito a hankali, ƙafafuna na kai ni ƙofar shiga asibitin kamar yadda suka saba — a kan autopilot.
Fuskoki masu kyau suka tarbeni: Nurses, likitoci, ma’aikata. Kowa da murmushi. Na mayar da amsa ba tare da tunani sosai ba, na nufi lif da zai kai ni har ɗakin da take ciki.
Room 404.
Na bude ƙofar daidai lokacin da na gani — kakata na zaune a kan kujera, tana riƙe da wata tsohuwar littafi a hannunta, da bargo mai launin hoda a kan cinyarta. Tagwayen gilashin karatu suna zaune lafiya a hancinta, kuma hasken ɗakin yana lullube ta kamar itace zuciyar komai a cikin wannan wuri. Da ta daga kai ta gan ni, idanunta suka cika da farin ciki, murmushi ya bazu a fuskarta.
Akwai ma’aikaciyar jinyarta a can gefenta, tana zaune a kujera kusa da ita, ta yi min murmushi sannan ta fice daga wajen zuwa gadon, tana gyara bargon da aka shimfiɗa da kwarewa. Na nufi inda take a guje, na rungume ta da ƙarfi. Ta shafa sumar kaina a hankali, hannunta mai dumi da laushi yana ta’aziyya ta sumbace goshina.
"Darling," she asked, "you look troubled. What happened?" Ta tambaya da murya mai sanyi da damuwa.
Na jingina da kafadarta, na sauke ajiyar zuciya kamar damuwar ranan zata bar jikina.
“Omar Thorne,” na ce a hankali.
Wani ɗan dariya mai laushi ya kuɓuce mata, tana girgiza kanta. Sai ta ɗaga haɓata, idanunta suka sauka cikin nawa.
"Always," ta ce da sautin dariyar da ke ɗauke da damuwa. “Ba abin mamaki bane. Me ya kuma yi? Fada min darling. What has he done this time? Didn't you say you were avoiding him?"
Na fada cikin kujera, Kafada ta sun lanƙwashe da gajiya. tunanin fuskar Omar na cikin taron da ya wuce da murmushin rainin nan nasa yayi ta dawo mun.
“Ya kira taron gaggawa yau,” na ce da ƙunci. “Ya zo da wata buƙata da ba zai taɓa yiwuwa ba, kamar dai muna da sandar sihiri. Granny… bana iya jure shi kuma.” I just can't stand him anymore.
Kakata ta sanya hannu a cinyata, tana goge ta da ƙauna da kulawa.
“Aleena,” ta ce da murya mai laushi da kwantar da hankali, “ki sake zuciyarki daga wannan fushi. Kin san yadda na ke faɗa miki: dangin Thorne mutane ne masu kirki. Dole mu nuna musu kyautatawa kullum.”
Na lumshe ido na, ina sauke numfashi cikin ɓacin rai. "I'm trying," na ce da rauni a muryata. “But he’s always under my skin, Granny. Every chance he gets, he finds a way. I don't know how I'm going to survive three more years of this partnership."
Granny tayi shiru, murmushinta ya ɗan lafa, idanunta suka ɗauki nisa. Tana kama da wacce ta faɗa cikin wani tsohon tunani. Canjin da ya bayyana a fuskarta sai ya matse min zuciya da wani abu mai ɗaci…
”Granny? Lafiyarki kuwa? Me ke faruwa? Kina buƙatar wani abu ne?”
"I'm fine, Aleena,” ta katse ni cikin murmushi mai laushi, tana shafa gefen kumatuna da hannunta. “Amma ki saurare ni yanzu. you need to try harder to be kind, not just to Omar, but to his family as well. Akwai wani abu mai muhimmanci da nake son fada miki. Cikin watanni bakwai, zaki cika shekara 26. Wannan shekarar ce kakanki ya ambata a wasikar da ya rubuta kafin ya tafi. Kuma… wataƙila bazan kasance ba lokacin da ya kamata in gaya miki da kaina.”
Kalamanta sun buge ni kamar dutsen da ya faɗo daga sama — masu nauyi, masu raɗaɗi.
Kirjina ya cika da wani iri, na girgiza kai da sauri kamar wacce ke ƙoƙarin ƙin gaskatawa, na matse kunnena da hannuwa biyu.
“Don Allah, Granny ki daina!” na ce da muryar da take rawa. “Ban shirya jin haka ba. Ki daina magana kamar haka!”
Sai ta kama hannuwana a hankali ta janye su daga kunne na, tana kallona da idon da ke cike da tausayi amma da ƙuduri.
"Still so stubborn," ta ce da murmushin da ke cike da soyayya da taushi.
Na ƙanƙame fuska, na shure hawayen da suka fara taruwa.
“Don Allah, kada ki ce haka, Granny. We will find better doctors. Should we go to the U.S.? Da akwai wani da zai iya taimakawa. Ki ce min kawai, zan shirya komai.”
Murmushinta ya kasance mai laushi amma yana ɗauke da wani nau’in karɓar ƙaddara da nutsuwa.
“Yar albarka,” ta ce da muryar da bata da rauni amma dauke da nutsuwa. Babu buƙatar duk hakan. Wane likita ne zai iya warkar da cutar IV cancer na mataki hudu? Wane magani ne zai goge abinda ya riga ya faru? Zuwa can ɓata lokacin da suka rage min ne. Ni fa kawai nafi son in yi kwanakin da suka rage min cikin lumana, tare dake.”
Na shanye kuka da ƙyar, na rungume kafadarta da dumi, na matse ta kamar zan hana lokacin wucewa. Mun taba wannan hirar a baya — kuma a zuciyata, na san gaskiyarta. Tura ta kasashen waje da sunan “fata” zai fi jefata cikin wahala fiye da taimako. Wannan dai inkarina ne — ƙin karɓar gaskiyar da take gabana.
"Fine," na furta cikin sauti mai rauni, kamar wanda ya mika wuya.
Ta shafi hannuna da taushi kafin ta miƙe a hankali, tana tafiya zuwa karamin table da ke kusa da window.
Sai na hangi wani farar bakar akwati da ke zaune cikin natsuwa. Bata jan hankali har sai da ta ɗauke shi da kulawa. Tana dawowa ta zauna dashi a cinyarta.
“Me ke ciki, Granny?” na tambaya, cikin mamaki daya ratsa cikin ɓacin raina.
Ta murmusa da kyau, idanunta na sheƙi da tsohuwar ƙauna.
“Wani abu mai daraja ne. Memories.” Ta bude akwatin a hankali.
Ciki kuwa, hotuna ne — tsofaffi masu gefen da ya fara shan lokaci. Na ɗauki ɗaya, hoton kakannina ne lokacin suna matasa, fuskokinsu na sheƙi da farin ciki. Wani hoton bikin aurensu ne, wani kuma yana nuna lokacin kafuwar Khan Electronics.
Na ci gaba da leƙen hotunan, tana kallona tana shafa gefen akwatin da yatsunta. Sai ta nuna wani hoto: mutane huɗu a liyafa, duk suna dariya da annashuwa.
“1972 ne wannan,” ta ce. “Shekarar da muka kafa kamfanin.”
Na kalli hoton da hankali. Na gane kakannina nan take, amma sauran biyu? Wata mace da wani namiji — ban san su ba.
"Who are they?" na tambaya, yatsana yana kan fuskokinsu.
Muryarta ta lafa, kamar wacce ke mafarkin wani abu mai kyau.
“Su ne Thornes. Kakannin Omar.”
Kamar iska ta tsaya — ba saboda mamaki ba, amma saboda nauyin abin da wannan ke nufi. Family na da nashi yan da suka saba da juna, suka fara tare… kuma yanzu ni da ɗan su muna cikin wani faɗa mai tsananin kiyayya.
“Kin gani kenan? Tarihinmu da nasu yana da kyau,” ta ce, tana riƙe hannuna da ƙarfi, tana kallona da mahimmanci. “Aleena, lokacin da kakanki ya rasu, kina da shekara bakwai. Amma kina iya tuna yadda Thornes musamman kakan Omar, suka kasance kusa da shi har ƙarshe. Kafin ya bar duniya, kakanki ya rubuta wasiyya, yana cewa in baki wani abu da zarar lokaci yayi. Wannan abu? Yarjejeniya ce da ya amince da ita tare da kakan Omar. Sun rubuta tare. Kuma yana da muhimmanci ki girmama hakan.”
Na murtuke fuska da mamaki.
“Yarjejeniyar me kuma?” Sai ji nayi kamar an dasa min dodo a zuciya. Me kakana da kuma kakan Omar za su iya amincewa a kai da har ya hadani a ciki?
Sai granny ta ɗauki wata takarda da aka rufe, ta daga ta a hankali daga akwatin. “Ina fatan za ki karɓa da zuciya ɗaya. Iyalin Omar — iyayensa — sun sani, amma kamar ni, suma ba su gaya masa ba. Kakanki ya ce a jira har sai kin cika 26. Lokacin,ya ce kin girma, kin isa, kuma kin fara jagorantar Khan Electronics da cikakken iko.”
Na buɗe baki da niyyar yin tambaya, amma sai wayata ta fara vibration a jaka. Na duba, sai naga Emir ne — fuskata ta danyi murmushi.
Granny ta ci gaba, muryarta na laushi, amma mai ƙarfi:
“Saboda halin da nake ciki, ina so ki ji wannan yanzu. Idan kina so, za ki iya buɗe wasikar. It’s about you and—”
“Granny I am sorry.,” na ce da sauƙin murya, ina ɗaga wayata.
“I need to take this call. It's Emir."
"Oh, of course, darling." Ta ce, tare da zuba idonta gareni murmushinta mai cike da fahimta.
Na fita zuwa farfajiyar bene, Da zarar na dauka, muryarsa mai dadin sauraro ta sauka cikin kunnuwana kamar sanyi.
“Sweetheart,” Emir ya furta da sauƙin murya, tana da wani salo na kwantar da hankali kamar iska mai sanyi.
Na jingina da tayal din bene, hannuna ya sauka a kan igiyar gini, fuskata na daure da murmushi. A gefe ɗaya na ido, na hango Granny tana kallona daga cikin falo, idonta cike da kauna da fahimta.
“Yes baby.” na amsa da sanyi.
“Jirgi na ya samu jinkiri,” ya ce da ƙaramin kuka, “amma zan sauka a Turkey kusan ƙarfe biyar na yamma.”
Na ce da dariya, "That's still better than your last flight from Japan that was delayed almost six hours," Na lumshe ido da murmushi. “Na yi kewarka sosai.”
Emir Batuhan.
Shugaban kamfanin Batuhan Ads, daya daga cikin manyan kamfanonin talla a nahiyar Asia. Muna tare kusan shekaru biyu yanzu. Har yau, muryarsa tana da ikon sassauta damuwata. Mun hadu ne a birthday party din aminiyata Nisa, daga ranar farko muka ji kaunar juna sosai. Sai muka fara fita, har ya zamana idan na gansa ina jin zuciyata na bugawa da saurin gaske.
“He is good-looking and really tall.” da murmushin sa mai ratsa zuciya—shi ne namijin da na dade ina mafarki.
“Ni ma na yi kewarki, Aleena,” ya ce cikin taushin murya.
Na yi murmushi. Daga gefe, na hango Granny ta tashi daga kujera, tana kallona kafin ta juya zuwa gado.
“Za mu hadu yau da daddare?” ya tambaya. “Yanzu kina asibiti ne?”
“Eh, yanzu na iso,” na ce, na dan shafa gashina da gefen hannu.
“Kin fi so in same ki a nan ko kuwa?”
Na yi shiru kadan. Ban san ko ina son ya zo asibitin ba. Duk da cewa Granny tana sonsa sosai, yau zuciyata na bukatar nutsuwa. Ina bukutar ni da shi kadai.
“You don’t need to come to the hospital.,” na ce a hankali. “Why not we look for a nice restaurant? Yafi sauƙi.”
“Amma na dade ban ga Granny ba,” ya ce a tausashe. “Zan so ganin ta… Amma na bar miki zabi.”
“Ba komai,” na ce a gaggauce. “Ni dai kawai ina bukatar kasancewa tare da kai. Mu biyu…”
“Hmmmm… Da alamar kewata akeyi na sosai din gaske?” ya ce da dariyar shagwaba.
Na harare shi ta cikin wayar da dariya. Wani lokaci yana birgeni da dariyar nan tasa, sai dai yana so ya gigita ni da kalmomi.
“To yau dai bari nima in yi tsokana na fada araina. “Amma Idan kuma ka gaji, basai mun hadu ba karna takura maka.”
“A’a!” ya katse da hanzari. “Please choose and book any restaurant you like before i arrive and i will handle the payment.
“Safe flight,” Aleena said with a sweet smile. I will see you later.
“I love you, Aleena,” he said softly.
"I love you too," na amsa da murmushi, yayin da granny tazo inda nake tana kallona.
Na kashe wayar, na ajiye a jaka, sannan na nufo inda take tsaye.
“Emir ya dawo ne?” ta tambaya da murmushi.
Na gyada kai. “Eh Granny. Kuma ya ce yana kewarki.”
Murmushinta ya tsaya a fuska, amma wani abu ya leka cikin idanunta—kila tausayi, ko kila nadama ce.
“Me kike so ki gaya min kafin wayar?” na tambaya a hankali.
Ta dan tsaya kafin ta girgiza kai. Ta kamo hannuna cikin nata, sannan ta ja ni zuwa ciki.
“Bari kawai mu bar maganar zuwa gobe.”
Na tsuke fuska, amma ban matsa mata ba. Sai kawai na bi ta da ido.
“Daga jin maganarki, kamar zaki hadu da Emir ne yau?”
“Eh… amma idan baki so in tafi, zan zauna.”
“A’a,” ta ce da sauri, kamar baza a yi musanya ba. “Ki tafi. Yau sati daya kenan baku hadu ba. kina bukatan ki ganshi. Kawai dai karki dare sosai ki dawo wuri.”
Na gyada kai da godiya. Muka koma kujerarmu, ta kunna tsohon fim a TV. Falon ya cika da dariya da nishadi. Na tsaya kallon Granny tana dariya da nutsuwa. Dadin da yake fuskarta ya haskaka zuciyata.
Na dan kau da tunanina daga kan Omar Thorne—mutumin da kullum ke cusa damuwa cikin raina.
Yau fa, ba lokaci bane na jin tsanarsa. Yau lokaci ne da zan kasance da wanda ke sa zuciyata ta natsu. Wanda yake sa duniya ta cikin sauki. Wanda nake kira da masoyi na.
💘AUREN ALEENA💘
Amal Musa ✍️
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.