Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel.docx
Chapter 24 of 28
Chapter 2ï¸âƒ£4ï¸âƒ£ Ta Mamaye Tunaninsa 🤦ðŸ»â€â™‚ï¸â¤ï¸ðŸ‘©ðŸ»
SHARE SHARE SHARE 💃💃💃💃💃
Sautin vibration É—in wayarta daga cikin jakarta ne ya katse mata tunani, ya kuma dawo da ita daga duniyar da tunaninta ya nutse. Da sauri ta zaro wayar. Idanunta suka sauka kan screen É—in.
Text message ne daga Emir.
Nan take Aleena ta yi haÉ—iyar yawu.
Emir: "Good morning, sweetheart. Na yi ta fama da rashin bacci jiya da daddare saboda kewarki."
Wani irin nauyi ya zauna a maƙogwaronta. Allah sarki... Shi ma bai yi bacci ba. Kamar ita. Amma bambancin da ke tsakaninsu ya kasance mai girma ƙwarai. Rashin baccin Emir ya samo asali ne daga kewar macen da yake so. Amma nata rashin baccin... Aleena ta lumshe ido. Nata ya samo asali ne daga wani abu da bai kamata ya faru ba. Wani kuskure da take ƙoƙarin mantawa. Kuma mafi muni... Da mutumin da bai kamata ya faru da shi ba. Zuciyarta ta sake matsewa. Kafin ta samu damar rubuta masa amsa, wayar ta sake vibration. Wani saƙon ya sake shigowa.
Emir: "Zan iya biyo office dinki yanzu kafin in wuce airport?"
Aleena ta dafe goshinta da tafin hannu. Tana ƙoƙarin tara hankalinta. Tambayar a bayyane take. Amsa ma a bayyane take.
Eh.
Ko kuma a'a.
Abu mafi sauƙi kenan. Sai dai abin mamaki, ta kasa rubuta ko kalma ɗaya. Saboda a yanzu haka ji takeyi komai ya rikice mata. Tun daga lokacin da Omar ya ambaci cewa dole ne ta yanke duk wata alaƙa da Emir har zuwa watan December sanda zai saketa. Tun daga lokacin da ya tabbatar mata cewa ya tuna komai game da daren jiya. Tun lokacin da ya jefa mata zuciya cikin ruɗani. Komai ya fara gaurayewa a cikin kanta. Ta yi shiru tana kallon saƙonnin.
Wani ɓangaren zuciyarta yana son ta gaya masa ya zo. Ta gan shi. Ta yi magana da shi. Wataƙila hakan zai taimaka mata ta dawo da hankalinta. Amma wani ɓangaren kuma... Ya kasa motsawa. Ya kasa yanke hukunci.
"Wayyo Allah..."
Ta furta a hankali tana runtse idanuwanta. Da alama hankalinta yana neman fara kubucewa daga gare ta. A karo na farko cikin rayuwarta, Aleena ta ji kamar ba ta fahimci kanta ba. Ba ta fahimci abin da take so ba. Kuma ba ta fahimci abin da zuciyarta take ƙoƙarin gaya mata ba. Ta ja wani dogon numfashi. Sannan ta mayar da wayar cikin jakarta. Ba tare da ta sake kallon saƙonnin ba. Da sauri ta nufi ƙofar gidan. Tana fatan tserewa daga tunanin da ke bibiyarta. Tana fatan guduwa daga ruɗanin da ke cike da kanta.
Amma a wani ɓangaren zuciyarta... Ta san cewa babu inda za ta gudu. Domin duk inda ta je, abin da ke damunta zai ci gaba da kasancewa tare da ita.
———
Omar yana jingine jikin kujerarsa ta office. Biron da ke hannunsa yana juyawa a hankali tsakanin yatsunsa yayin da ƙarshensa ke taɓa leɓensa lokaci zuwa lokaci. Hade da wani ƙaramin murmushi da ya laɓe a gefen bakinsa mai yawa fiye da yadda ya kamata—kuma ya ƙi gushewa.
Aleena khan.
Sunanta kadai ke yawo a cikin tunaninsa kamar wani bugun zuciya. Kamar wani waƙa ne da ya makale a cikin ƙwaƙwalwarsa.
Daga ya rufe idanunsa, sai yaji taɓawar leɓenta a kan nasa—masu laushi, masu ɗauke da wani irin zafi da sha’awa da suka bar masa. Kamar wani rada ne da ya kunna duk wani wuta da ke cikinsa. Ɗanɗanon bakinta har yanzu yana manne a harshensa. A hankali ya lashe leɓensa ba tare da ya sani ba, tunanin wuyanta a ƙarƙashin haƙoransa ya sa bugun zuciyarsa ya ƙara sauri. Har yanzu yana iya jin Ɗanɗanon ta. Yadda jikinta ya fara rawa. Yadda ta bari ya ƙamo ta ya manneta da jikinsa. Kamshinta har yanzu yana manne a cikin ƙwaƙwalwarsa, yana jan hankalinsa kamar wani maye. Fatar jikinta ta amsa masa fiye da yadda ya zata.
Kowane taɓawa.
Kowane motsi.
Kowane numfashi.
Da kuma yadda jikinta ya karɓe sa. Bai san mene ya hau kan shi a daren jiya ba. Amma daga zarar sanda leɓunansu suka haɗu, ji yayi babu wani abu da zai iya dakatar da shi.
Takaicin da ya tara tun daga abin da ya faru a restaurant ɗin. Fushin da ya yi ta dannewa tsawon yini. Duk sun taru ne a lokaci guda. Duk lokacin da ya yi ƙoƙarin shagaltar da kansa da wasu abubuwa, baya taba yin tasiri. Fuskarta ce kawai ta ke ci gaba da bayyana a gabansa. Kuma taki barin cikin tunaninsa.
A nan kawai yaji ya kasa haƙuri. Or maybe fadan da suka yi ne ta kai shi ƙarshen haƙurinsa. Ko kuma kawai nuna mata yake san yi cewan ba ita kadai ke da power ba. Omar ya saki numfashi a hankali. Ya Allah... how was i even thinking of this? Omar ya furta, Yaushe ma ya fara bata wa kansa lokaci yana tunanin Aleena haka? Shin ko ya manta wacece Aleena khan? Yarinyar da ya shafe shekaru tana bata masa rai? Domin idan akwai mutum guda a duniya da ya kamata ya nisanta tunaninsa akai, to ita ce.
Omar ya girgiza kansa da sauri kamar yana son korar tunanin, ya ajiye biron. Sannan ya ɗauki wayarsa ya fara buɗe saƙonnin da suka taru tun safe ba tare da wani dalili ba. Sai dai kawai yana son ya shagaltar da kansa da wani abu daban. Amma hakan bai taimaka ba, tunaninsa ya sake komawa zuwa safiyar yau. Wani murmushi ya sake bayyana a fuskarsa ba tare da ya sani bama.
Yatsunsa suka tsaya cak a kan screen ɗin wayar. yana tuna yadda ta rikice lokacin da ya tsaya kusa da ita. Yadda ta ƙi ba shi phone number dinta. Tsoron me ta ke? Omar ya kasa fahimta. A wurinsa yana da dalilai guda biyu kacal da yasa yake san number ta.
Na farko, bayan zuwan iyayensa jiya ba tare da sanarwa ba, ya fahimci cewa suna buƙatar kyakkyawan communication tsakanin su.
Na biyu kuma... Ya É—an yi murmushi yana kallon screen É—in wayarsa. Yana san ya ci gaba da tsokanarta. Musamman ta waya. Domin a nan yake jin kamar yana da iko.
And Mene ne dalilinsa? Shi ma bai sani ba. Amma sai dai kawai ya san hakan yana cikin wasan da yake yi da ita don ganin ya takura mata. Kuma hakan yana masa daÉ—i fiye da yadda ya zata shima. Saboda Omar ya saba da irin waÉ—annan wasanni na jan hankalin yan mata.
Wasannin kawo sha’awa.
Jaraba.
Da kuma iko.
Tunaninsa ya sake komawa kan daren jiya, ji yayi murmushin da yake fuskarsa ya bace. Ya tuna yadda ta ja baya bayan kiss ɗin. Yadda nadama ta bayyana a idanunta. Yadda jikinta ya dinga rawa. Kuma hakan kaɗai ya ɗan taɓa wani wuri a zuciyarsa. Yadda bai yi tsammani ba. Maybe ji tayi kamar ta ci amanar Emir. Amma Kuma ai gaskiya ne. Ta ci amanar tasa.
Amma shi? Bai ji nadama ba. Kuma bai ji yayi laifi ba. Aleena da kanta tayi kissing dinsa back, itama she felt it, and ta kuma mallaka masa control alokacin. Yadda jikin ta ya amsa masa. Ta kuma bashi kanta…. Wannan kuma zaɓinta ne. Don haka bai ga dalilin neman afuwa wajen ta ba.
Abin da yake tambayar kansa yanzu shi ne me zai biyo baya. Watakila har yanzu tana jin tsanarsa. Amma kuma yana da tabbacin cewa bayan tsanar akwai wani abu da dole ya sauya a ranta game dashi yanzu. Shi kansa bai san menene ba. Amma ya san akwai canji.
Shi kuwa fa? Gaskiya bai sani ba idan har yanzu akwai irin tsanar da yake mata ba. Sannan dai abu É—aya ya sani. Shine cewa gaskiya bazai iya ci gaba da jin haushin ta ba kamar da ba, Aleena tana da wani irin jan hankali da ke kutsawa cikin tunaninsa. saboda koda kiss ne kadai ya hada su amma ta riga ta mamaye masa tunaninsa gaba daya. Kuma ba tare da izinin sa ba. Kuma ba tare da ya shirya ba. Kuma hakan ya dame shi.
Saboda wannan yanayin da yake ji yasa yanaji kamar bashi ba, kuma baisan har zuwa yaushe zai daina jin hakan ba, saboda ko kallanta yayi kamar dazu da safe da suka tsaya kusa suna magana kadai, abinda kawai kwakwalwarsa ke sarrafa masa kadai cewan ya janyo ta kusa dashi yaye wannan kayan da tasa mai daukan hankali da kyauta daga jikinta ya biya sha’awarta da yake anan take kan sofa kujerar. Wannan sha’awar da yake ji sabuwa ce, saboda shi bai taba jin hakan ba akan duk wata ya’mace da ya taba sani ba, don ji yake kamar bazai iya controlling kansa ba, inda wasu ne da tuni ya dauki abinda yakeso babu tsayawa saboda mata ma da kansu suke masa tallan kansu, amma da Aleena zai iya tsayawa nesa da ita ko wucewa ma kadai still yaji yana neman rasa hankalinsa.
Ya kalli agogon wayarsa.
12:51pm na rana. Lokacin cin abincinsa yayi har ya kusa wucewa. Tun da ya bar gida bai ci komai ba. Gashi yanzu yana zaune an office dinsa. Ba tare da wani dalili mai mahimmanci ba, duk da dai saboda tunanin Aleena ne ya ƙi barin kansa. Ya shafa gefen kansa yana ƙoƙarin mayar da hankalinsa kan aiki. Nan take tunaninsa ya koma kan daukar Aleena zuwa Antalya. Dole ne su yi wannan tafiyar cikin gaggawa saboda project din baya bukatan bata lokaci. CEO din kamfanin da za su je gani itama sai tambayar sakatariyarta take game da lokacin ganawarta dasu, saboda ba yar ƙasar Turkiyya ba ce, dole ne ta tsara komai tun da wuri da kuma gyara schedules dinta.
Omar ya lumshe idanunsa. Ali da Kemal sun je factory ɗin jiya domin ganawa. Kuma sun dawo da wasu matsaloli. Duk da cewa wannan kamfanin shi ne mafi kusa da abin da suke nema, har yanzu akwai gyare-gyaren da ake buƙata. Ba su gama fahimtar yadda technology din take ba. Har bayan an basu samfarin da aka kawo daga kamfanin Khan Electronics. Amma Har yanzu suna fuskantar kalubale wajen samar da prototype ɗin yadda ya kamata. Shiyasa ya yanke shawarar zuwa da kansa. Kuma Aleena ce kadai mutum ɗaya da ta fi fahimtar wannan bangaren. Maybe ma fiye da shi. Yana buƙatar ta kasance tare da shi domin ta yi musu bayanin abin da suke buƙata. Da fatan hakan zai taimaka musu su daidaita komai yadda ya dace. Sai dai duk da haka... Wani irin rashin nutsuwa da bai saba ji ba ya fara kutsawa cikin zuciyarsa. Kar kuma Aleena taki dawowa gida yau, yazo ya kasa sanin yaushe zata bisa Antalya din. Omar yaja dan baya kan kujerarasa tafin hannunsa akan desk dinsa tambayoyi suka shiga cika masa kai. Har yanzu Aleena zata dinga kin dawowa kwana gida? Zata cigaba da kwana wajen su leila? Bayan duk warning din da yayi mata da hukuncin da ta fuskanta jiya da daddare?
Omar ya shaki numfashi yana kokarin dakatar da gudun tunanin da suke masa yawo, shi yanzu haka ma bazai iya jiran amsarta ba don haka tashi zaiyi daga masallaci zai wuce straight kamfanin Khan Electronics ya samu amsoshinsa akan zuwa Antalya daga bakinta da Kansa. Watakila ma su samu damar yin magana akan sharudan daya kafa mata kafin kiss din jiya ya faru. Da wannan tunanin, ya miƙe tsaye. Ya tattara abubuwan da yake buƙata sannan ya ɗauki car key ɗinsa daga kan tebur ya fice daga office ɗinsa.
Yana fitowa idanunsa suka sauka kan Zera, sakatariyarsa. Kamar tana jiran fitowarsa ne daman. Nan take ta miÆ™e tsaye. Wani murmushi mai laushi ya bayyana a fuskarta. “Mr. Omar.â€
Omar ya gyada kai ta gefen fuska kadan cikin sauri,. “Zera, zan je Khan Electronics for some business. Amma zan dawo anjima. If anything urgent comes up, ki tura mun ta email dina.â€
Ta gyada kai cikin sauri murmushinta ya ƙara faɗaɗawa, "Of course, Mr. Omar Adawo lafiya." Ta fada tana gyara fuskarta, yatsunta suna shafa gefen desk ɗinta a hankali sai ta dan ciji lebenta sannan ta sauke kallanta kasa.
Omar ya kalleta meyasa take behaving haka, lafiya kuwa. "Is something wrong, Zera?" Ya tambaya yana É—aga gira.
Zera ta kyafta ido cikin sauri. "Aa... bakomai." Sai kuma ta yi shiru, kamar tana san faɗar wani abu amma ta kasa. “Daman...†Ta sake yin shiru.
Omar ya ɗan matsa kusa yana jiran ta ƙarasa.
Amma da alama kalmomin sun ƙi fitowa. “Nothing, Mr. Omar.†Ta Kara faɗa cikin sanyin murya. “Daman...†idanunta suka sauka kansa.
Omar ya ɗan yamutsa fuska. "Just say it, Zera. Mene ne?" Ya katse ta cikin rashin haƙuri.
Zera ta ciji leÉ“enta again. Kunyar da ke fuskarta ta Æ™ara bayyana. Daga Æ™arshe ta sauke kanta kasa. “Daman...†Ta yi gyaran murya. “Na sa wannan dress É—in da kace kana so ne yau.†Ta É—an yi murmushi. “Kana ganin har yanzu tana yi min kyau?â€
Omar ya tsaya cak, na dan seconds ya kasa cewa komai. Idanunsa suka sauka kan rigar. Sai kuma wani tunani ya bugi zuciyarsa, hakika ya san rigar. Kuma duk lokacin da Zera ta saka ta, kusan koyaushe yana yaba mata, amma ya akayi bai kula ba gashi ga ita kuma? Ya sake kallonta. Sannan ya sake kallon rigar. Kai... Wai me yake damunsa ne a kwanakin nan?
Zera ta lura da rikicewar da ke fuskarsa. Nan take ta yi Æ™aramin murmushi. “I’m sorry, Mr. Omar.†Ta faÉ—a cikin sauri. “Zan koma kan aikina yanzu.†Tana jan kujerarta ta zauna. “Duk abin da ya taso zan tura maka shi ta email.â€
Omar ya buɗe baki kamar zai ce wani abu. Amma babu kalmar da ta fito. Sai kawai ya juya ya nufi elevator. Har lokacin kuma tunanin bai bar shi ba. Da zarar ƙofar elevator ɗin ta rufe, ya saka hannunsa cikin sumar kansa. Yana jin kamar ba shi ba ne. Kamar wani abu ya sauya masa lissafi gaba ɗaya. Kai Omar Thorne... Ta yaya bai lura da rigar da ya saba yaba wa ba? Me yake damunsa ne? “What is wrong with me?†Ya furta a hankali. Sannan ya lumshe idanunsa yana kokarin kore duk wani confusion da yake damunsa. Maybe I was just distracted.
Yeah.
That's it.
Ya faÉ—a a ransa. Amma kafin ya gama tabbatar wa kansa hakan, wata murya daga cikin zuciyarsa ta sake bugunsa. Ko kuma... Yanzu babu wata mace da idonka yake gani sai Aleena khan? Idanunsa suka buÉ—e da sauri.
“Damn it!†Ya faɗa ba tare da tunani ba. “Of course that's not true!†Ya fada da ihu mai karfi a daidai lokacin da kalmomin suka fita daga bakinsa... Ƙofar elevator ɗin ta buɗe. Kai tsaye zuwa lobby. Shiru ya mamaye wajen. Omar ya tsaya cak. Mutane suma suka tsaya cak. Ma’aikata. Baƙi. Wasu kuma suka firgita ganin CEO guda yana ihu haka. Omar ya yi haɗiyar yawu. A hankali ya gyara suit ɗinsa. Sannan yayi gyaran murya. Kamar babu abin da ya faru. Ya fara tafiya cikin nutsuwa. Mutane suna masa sallama da gaisuwa cikin girma. Shi kuma yana amsawa kamar komai na tafiya daidai. Sai dai yana jin yadda idanunsu ke binsa har ya wuce. Har ya fita ta babban ƙofar glass ɗin kamfanin.
Da zarar ya isa wajen motarsa, ya saki wani numfashi mai nauyi. “Damn it...†Ya furta yana girgiza kai, yanzu zasu fara tunanin CEO Thorne Comm ɗinsu ya hadu da ciwan kwakwalwa. Well, watakila hakane ta wani bangaren. Ya fada yana buɗe ƙofar motar ya shiga.
💘AUREN ALEENA💘
Amal Musa âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.