Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel.docx
Chapter 11 of 28
Chapter.1️⃣1️⃣ Zan Kula Da Ita 🤍🛡️🤲🏽🫱🏽🫲🏼🫂
Omg Omar da Emir??😤😳🙆
Toh mey ya raba su??🤔😭
SHARE SHARE SHARE 💃💃💃💃💃
Omar ya kasa iya janye idanunsa daga ƙaramin glass window din room 404, inda doctors da ma’aikatan jinya suke gudu cikin tashin hankali da kewaye da ita.
Kakar Aleena tana cikin matsanancin halin yanzu.
Omar bayan cin abincin dare da yayi a gida, wani abu ya jawo shi zuwa hospital. Wataƙila saboda ya san Aleena ba za ta kasance anan ba, kuma yayi tunanin zai zama dama mai kyau ya tsere daga tambayoyin Mommy da suka yi yawa sosai.
Lokacin da ya iso a baya, kakar Aleena da shi sun yi hira ta ɗan lokaci, amma sai wani abu ya canza.
Numfashinta ya fara rashin daidaituwa, kuma nurse inta ma ta lura da haka.
Yanzu, suna jiran doctor ya zo da update.
Iyayen Omar ma suna nan. Ya kira su ’yan mintoci kaɗan da suka wuce. Papa ya tsaya da hannuwansa a haɗe, ya ƙi zama, mugun yanayi a fuskarsa. Mommy ta zauna a gefen Omar, fuskarta ta cika da damuwa.
Omar ya ja numfashi mai nauyi. Mutum ɗaya, da ya rage shi ne Aleena - tana kan hanyar zuwa hospital.
Sautin takun gudu na gaggawa ya cika corridor.
Omar ya juya cikin lokacin da ya ga Aleena ta fito da sauri daga lift, tana gudu da sauri har ta kusan wuce shi. Sai ta tsaya ba zato ba tsammani, idanunta sun kama ƙofar dakin granny kai tsaye ko kallon sa bata yi ba - kawai ta ture ta wuce tana matsar da jikin Omar kamar shi wani shinge ne kawai a hanyarta.
Omar ya bar ta.
Ba saboda ya damu ba. Amma saboda babu abin da zai iya yi don dakatar da duk wata guguwar da ke tashi a cikin Aleena.
Sai ya gan shi, Emir.
idanun su suka hadu. Omar yaji kamar an tsaga zuciyarsa, Me ke faruwa? Shin Emir Batuhan shine saurayin da Aleena take magana tuntuni? Aminina? Koda yake ina nufin Aminina a baya, Innalillahi wannan ba zai yiwu ba.
Takun Emir sun kasance cikin shakka, a hankali. Ya gai da iyayen Omar cikin ladabi, muryarsa daidai, tsayuwarsa cikin nutsuwa. Ya kalli inda Omar ya tsaya sau daya ya kau da kai ba sallama ba gaisuwa ba komai.
Da alamu Emir bai san komai ba har yanzu, Aleena har yanzu ba ta gaya masa ba kenan.
Omar ya ɗaga gira cikin wani murmushi abin yana bashi mamaki.
Saboda Emir din da ya sani ba zai taɓa yin shiru ba. Da sai ya bukaci bayani nan da nan da zarar yaji wani abu ba daidai ba.
Amma yanzu?
Gashi a tsaye a nan, Kamar rayuwarsa ba za ta juya gaba ɗaya a cikin kiftawar ido ba.
Kuma Aleena?
Aleena har yanzu ta bar shi cikin duhu.
How generous of her.
“Aleena ’yata…”
Muryar mommy ta kasance a hankali, mai tausayi, kusan kamar uwa kamar yadda uwa ke yi wa ‘yarta, yayin da ta miƙa hannu zuwa kafaɗar Aleena.
Aleena ta juya, fuskarta ta cika da hawaye. “Aunty Asiye, me yasa haka ke faruwa? Me ya faru?” muryarta ta karye da fargaba.
Mommy ta kama kafaɗarta a hankali. “Mun iso ’yan mintoci kaɗan da suka wuce tare da Papa,” ta ce a hankali.
“Wanda ya fara sani farko shi ne Ya Omar.”
A wannan lokacin, kallon Aleena ya karkata zuwa gare shi.
“Me ya faru?” ta tambaya da karfi.
Omar ya ja numfashi da ƙarfi. Yace, “Na iso kusan karfe 8 na dare, bayan na gama cin abinci a gida,” ya amsa.
“Muna cikin hira ne kawai, sai kwatsam numfashinta ya rikice. Sai ta suma.”
Kalmomin sun buge ta kamar mari lips din ta suka bude amma babu kalmomi.
Sai kuka ya zo - mai nauyi, mara tsayawa.
Ta faɗa jikin Emir, jikinta yana karkarwa da tsananin ciwo.
Omar ya damke haƙoransa. Ya saba ganin Aleena cikin nau’i daban-daban - fushi, girman kai, munafurci, har ma fake.
Amma ba kamar haka ba.
Ya kamata ya ji daɗi da ganin ta karye. Amma bai ji ba. Bai ji komai ba.
Ya juya ya nufi wajen Papa.
Papa yana kallon Omar da wannan kallon - wanda ke sa mutum ya ji kamar ya kamata ya yi wani abu ko yace wani abu, Kamar akwai tambaya a cikin kallon da shirun.
“Abokinta ne,” Omar ya rada a ƙarƙashin numfashinsa, duk da Papa bai tambaye shi ba. Amma ya san tambayar tana cikin tunaninsa.
Papa ya ɗaga gira. “Oh.” Ya yi shiru na ɗan lokaci.
Sai Papa ya ce, “Ban san Emir yana da alaka da Aleena ba.” Saboda na san ya kasance abokinka na kud da kud a baya, kuma yanzu da Aleena?
Omar ya ɗaga kafaɗa yana ƙoƙarin yin sauti mai gaskiya. “Ni ma yanzu na gano. Amma suna da kusanci sosai. Best friends.”
Papa ya ɗan gyada kai kadan. Bai kara cewa komai ba. Wani bangare a jikin Omar yaji daɗi da Papa bai ci gaba da matsa maganar ba.
Iyayen Omar ba su san cewa Aleena budurwar Emir bace, kuma gaskiya, Omar ya gwammace ya bar komai a haka. Zai fi sauƙi.
Yanayin ya canza yayin da ƙofa ta buɗe.
Lokacin da doctor ya fito daga ɗakin Omar jikin sa ya bashi cewan - al’amuran ba kyau kawai yasan abun yayi muni.
Fuskar doctor ta ja, kafaɗunsa sun yi nauyi da wani abu mara fahimta.
Doctor ya leka ɗakin da sauri kafin ya kafa idanunsa akan Aleena. “Miss Aleena,” ya fara muryarsa a nutse amma mai nauyi. "I'm afraid the situation has worsened." al’amarin ya tabarbare sosai.”
Aleena ta ƙanƙame jikinta, numfashinta ya kama a maƙogwaronta.
Doctor ya ci gaba, muryarsa a tsaye amma tana nuna tausayi.
“Numfashin kakarki bai daidaita ba, kuma yanayin nata yana ci gaba da lalacewa. Ciwon cancer ya bazu fiye da yadda muka zata sosai. Muna yin duk abin da za mu iya, amma jikinta ya daina amsa duk wani magani.”
Shiru.
Na ɗan lokaci, Aleena ta tsaya a nan cak. Babu motsi, babu sauti. Lips sun buɗe kaɗan, amma babu kalmomi.
Sai kwatsam, kamar gilashin da aka fasa, jikinta ya fara karkarwa, fuskarta ta rikice zuwa wani yanayi mai zafi da radadi ta shiga wani hali mara misaltuwa.
Emir ya riketa nan da nan, yana kokarin rike ta kafin ta fadi gaba ɗaya. “Aleena,” ya rada yana kiran sunanta murya mai ƙasa amma da gaggawa.
Amma Aleena bata jin shi.
Idanunta masu sheƙin hawaye sun makale akan doctor— kamar tana neman ransa.
“A’a - a’a, ba zai yiwu ba,” muryar ta mai rawa ta shake tana girgiza kanta, yatsunta suna rike da hannun Emir. “Lafiya lau take jiya. Har magana tayi dani. Har dariya… tana - tana-”
Muryarta ta karye.
Doctor ya ja numfashi, fuskarsa ta matse da tausayi. “Na san wannan abu yana da wahalar yarda. Miss Aleena,” ya ce a hankali cikin tausayi, “amma mun kai iyakar abin da magani zai iya yi. Tana ƙarƙashin kulawar palliative care, wanda zai taimaka wajen rage mata zafin ciwo da wahala ba warkarwa ba, amma gaskiya daya ce, kuma ita ce… bata da lokaci da yawa da ya rage ko muce kwanaki.”
Gwiwoyin Aleena sun kife.
Emir ya kama ta da sauri, yana faɗa mata wani abu da bazata ma iya ji ba yanzu.
Doctor ya dan jinkirta kafin ya ƙarasa. "I'm so sorry," ya ƙara da muryarsa mai nuna tausayi. "I truly am sorry, Miss Aleena."
Numfashin Aleena ya kara rikicewa ya tsananta.
Omar ya ga yadda lokaci guda - fuskar Aleena ta zama abin tsoro, sa’an nan tsoro ya zama bakin ciki.
Sai - fushi.
Kirjin Aleena yana tashi da sauri yayin da ta ja numfashi mai rawar jiki, hannuwanta sun damke agefenta.
“Kai - ka ce,” ta rada. “Ka ce-” muryarta ta karu, ta karye zuwa wani abu mai radadi. “Ka ce har yanzu akwai lokaci!”
Doctor ya sauke ajiyar zuciya. “Mun yi fatan haka,” ya amsa da nadama. “Amma cutar ta yi tsanani sosai.”
Aleena ta fashe da wani kuka, dukkan jikinta yana karkarwa.
“Ta yi rayuwa mai kyau, Miss Aleena,”Doctor ya ci gaba. “Amma jikinta ya gaji. Ina jin tsoro babu abin da za mu iya yi sai dai mu taimaka mata ta ji dadin karshen kwanakin ta.”
Aleena ta kalle shi kamar tana son gardama - kamar tana son ta yi masa ihu, ta bukaci ya warkar da ita.
Amma babu abin da ya rage na fada.
Kuma ta san hakan.
Jikinta ya saki kamar an fitar mata da rai, kafafunta kamar zasu lankwashe hannayenta suka tafi fuskarta, wani kuka mai karfi ya fito daga bakin ta, tasa yatsu tana toshe shi.
Emir ya matso ya rungume ta sosai, yana raɗa mata kalmomin kwantar da hankali a cikin gashinta.
Omar ya matse hakoransa.
Bai taba ganin Aleena haka ba. Bai taba ganin ta haka ba… a tsirare da rauni.
Kuma ya tsani hakan.
Ba don saboda yana son ganinta ta sha wahala ba.
Amma saboda hakan yasa ta zama ta gaske.
Yasa ta zama mutum.
Kuma bai san me zai yi da hakan ba.
Doctor ya bata dan lokaci, sai ya sake magana, wannan karon ya fi laushi. “Idan kina son ki yi magana da ita, yanzu ne lokacin,” ya shawarce ta. “Ina mai baki shawarar ki yi haka nan da nan.”
Aleena bata bashi amsa ba.
Ta goge hawayenta da sauri cikin karfin zuciya, ta ja numfashi mai tsanani mai rawar jiki - sai ta gyada kai.
Amma ba yarda da gaskiya bace kokarin rayuwa ce.
Ba tare da wata kalma ba, ta juya ta nufi dakin granny. Emir ya bi ta, takun sa cikin shakku a hankali - kamar ya san abin da ke shirin zuwa masa amma bai shirya fuskanta ba.
Omar ya kalli iyayensa da suke musayar kallo da juna da ya cika da shiru mai fahimta, kafin mommy ta taba hannunsa a hankali. Alama mai cewa; Go… shiga dakin.
Don haka Omar ya gyada kai ya shiga.
Lokacin da suka shiga ciki dakin sautin na’urar injunan bugun zuciya ta cika sararin— wani irin kida mai tunatarwa da yadda dan lokaci ya rage. Kamshin hospital din ya matse su mai karfi da kuma shakewa.
Kakar Aleena tana kwance a cikin wani farin bargo numfashinta ba shi da zurfi amma tsayayye - a yanzu.
Aleena ta matsa a hankali ta durƙusa kusa da gadon, yatsunta suna rawa yayin da ta mika hannu zuwa hannun granny. “Granny…” muryarta tana karyewa, da kyar ta ji. “I am here, Granny sweetheart din ki Aleena gata nan.”
Yatsun granny masu rauni suka lanƙwasa kaɗan kusa da nata, lips suka karkata zuwa murmushi mai gajiya amma cike da kauna. Tace, “’Darling… My beautiful Aleena,” ta rada, muryarta mai laushi kamar gashin tsuntsu. “Kar ki yi kuka, ’Darling.”
Amma Aleena ba ta iya tsayawa ba.
Hawaye su ka ci gaba da zubowa.
Omar ya tsaya a dayan gefen gadon, mommy da papa kusa da shi suka yi shiru suna jin zafin al’amarin.
“Dole ne ki zama mai karfi, Aleena,” granny ta ci gaba da magana cikin rauni. “Wannan ba makawa ne…”
Aleena ta girgiza kanta, kukanta ya karu da gaggawa.
“A’a,” ta yi kuka, ta damke hannun granny mai rauni da karfi, kamar za ta riƙe ta, kamar riƙewa da karfi zai iya canza kaddara. “A’a, don Allah…”
Mommy ta matso bayanta, tana shafata a hankali da taɓawar hannunta a bayan Aleena. Emir ya yi hakan shima, tafin hannunsa ya kwanta a kafaɗar Aleena, yatsun sa suna matse ta ahankali kamar yana kokarin dawo da ita cikin numfashi.
Amma Aleena da kyar take riƙe kanta.
Jikin ta karkarwa kawai yake.
Tana girgiza sosai. fuskarta ta matse cikin katifa yayin da take kuka. “I can’t do this,” ta rada, muryarta ta lalace.
Numfashin hankali.
Idanun granny masu gajiya suka kyafta tsakanin Aleena da sauran yan dakin kamar tana so ta tabbatar da wani abu.
“Ina da buri na ƙarshe,” ta rada.
Dakin ya yi shiru gaba daya.
Aleena ta tsaya, yatsunta sun lanƙwashe cikin bedsheet. “Fadi me kikeso, granny,” ta yi alkawari, muryarta mai neman jinkai. “Gaya min ko mene shi.”
Granny ta ja numfashi, kamar tana tattara karshen ƙarfinta. Idanunta masu gajiya sun yi kyaftawa zuwa gare shi.
“Ki aure shi, ’Aleena.”
Yatsun Aleena suka daure cikin hannun granny.
Numfashin gaggawa, ba da gangan ba.
“Ina son ki auri Omar yanzu,” ta ci gaba, muryarta ta fi laushi yanzu, amma ba ta canza ba. “Kuma cika alkawarin.”
Me?
A’a.
Bazai yiwu ba… a’a.
Shiru ya kara tsanantawa.
Jikinta ya zama mai tauri. Rikon Emir ya sassauta daga kafadarta.
Omar kuwa? Sai ya ji dariyar daci tana barazanar ta tashi a makogwaronsa.
Omar ya ji zuciyarsa tana bugawa kamar ana matse shi daga ciki. Ya buɗe baki – wataƙila yace yaƙi, wataƙila ya yi karamar dariya – amma muryar bata fito ba.
Saboda Aleena ta fara magana.
“Granny, ni-” muryarta ta karye, idanunta suna yawo tsakanin ita da granny da ke kusa da ita. “A’a. A’a, ba zan iya ba-”
Yatsun granny suka matse nata. “Na san wannan yana da wahala, ’Aleena,” ta rada, muryarta mai kwantar da hankali, kamar ba tana neman wani abu mai wuyar gaske ba. “Amma don Allah… ina bukatar ganin hakan. Kafin in tafi. Ina bukatar ganin kin samu rayuwa, tare da wani wanda zai tsaya miki har karshen rayuwar ki.”
Dukkan jikin Aleena ya shiga girgiza. Ta juya zuwa ga Emir nan da nan, tana neman wani abu - amsa, dalili, mafita.
Amma Emir bai bata ko daya ba.
Maimakon haka, Sai ya fara ja da baya. Hannunsa da ya riƙe Aleena mintoci yanzu sun sake ta.
Yanayinsa babu komai da farko - amma daga baya sai fuskarsa ta canza ta bayyana; -
Cin amana.
Bakin ciki.
Zafi mai radadi, ba tare da tacewa ba.
“Wait-” Aleena ta matso zuwa gare shi, muryarta tana karyewa.
Amma Emir ya girgiza kai. Da kyar. Hakoransa ya damke, numfashi mai zurfi - kamar yana tilasta kansa kada ya karye a nan, a gaban dukkansu.
Omar ya yi tsammanin Emir zai ce wani abu. Ya yi hayaniya, Ya bukaci bayani.
Amma bai yi ba.
Maimakon haka, ya ja numfashi da karfi, idanu suka yi kyaftawa zuwa ga Omar da wani zargi a cikinsu sai ya juya ya fita.
Aleena ta motsa gaba. “Emir!”
Riƙon granny mai rauni akan hannunta da yasa ta dakata na dan lokaci.
Idanunta sun yi kyaftawa baya zuwa granny da tayi rauni kwance kan gado da zuwa kofar da mutum daya da take son ta aura ya fita.
Ta kara shiga wani yanayi.
“I’m sorry, granny,” ta rada. “Dole in-”
Granny kawai ta yi murmushi da fahimta, kamar ta yi tsammanin hakan. “Tafi,” ta rada. “Amma ki dawo gare ni.”
Aleena da kyar ta gyada kai kafin ta fita da gudu, muryarta tana sauti a corridor yayin da take kiran Emir.
Tunanin Omar kuwa?
Ya kamata ya barsu su tafi.
Ya kamata ya tsaya a wurin, ya rufe bakinsa, ya barsu su narke ba tare da shi a cikin lissafin su ba.
Amma wani abu a cikinsa ya motsa.
Wani abu mai rashin hankali, wani abu wai shi tsoma baki, wani abu da yasa yake son bin su- don ganin yadda ginin soyayya ke rushewa akan idonsa.
Amma sai-
Taɓawa mai rauni, mai rawar jiki ta tsayar dashi.
“Omar…”
Omar ya daskare anan tsaye.
Yatsunta sirara kamar takarda kuma suna rawa, suka lanƙwasa kusa da hannunsa. Ya juya.
Lips din granny suka karkata zuwa wani abu karami da ke ɗauke da murmushin da ya san komai.
Omar yayi ajiyar zuciya da Karfi. Sai ya sunkuya a hankali yatsunsa suna shafa hannunta mai rauni. Lokacin ya ji kamar ba gaskiya ba.
“Kai yaro ne mai karfi, Omar,” ta rada, muryarta da kyar akeji. “Kuma na sani… na san baka da dalili yin wannan auren. Amma Aleena… za ta bukaci wani.”
Ya damke hakoransa.
Wani bangare nashi yana son ya ja baya. Wani bangare nashi yana son ya gaya mata cewa Aleena bashi take bukata ba. Yana son ya ce mata shi ba mutumin daya dace da Aleena bane.
Kuma yace mata shi baya son zama wannna mutumin da take masa kallo.
Amma sai idanunsa suka kyafta zuwa siffarta mai rauni, kumatunta, nauyin rayuwa da ke zamewa a gabonsa.
Amma wannan kamannun dake fuskarta ya san shi sosai. Ya san shi sosai. Ya taba kasancewa a nan a baya. Shi da kakarsa.
Ya ja numfashi da karfi, yatsu suna matse nata.
Ya rabbi… Zuciyarsa tana bugu har hakarkarinsa kowane bugu yana duka tare da gaskiyar zahiri dake shiga cikin kashin bayansa.
Sa’an nan, kafin ya dakatar da kansa, kafin ma ya yi tunani, kalmomin suka zame daga lips din sa.
“Zan kula da Aleena.”
Muryarsa cikin kusan rada. Da kyar shi kansa ya yarda ya fadi hakan.
Amma granny kawai sai ta saki murmushi, lips din ta suka bude kamar tana tsammanin wannan tun farko.
“Kar ki damu game da ita,” ya ci gaba, alkawarin yana zama da nauyi akan harsensa. “Baza ta taba zama ita kadai ba. Ko yaushe za ta kasance tare dani.”
“Kayi alkawari Omar?” ta rada da rauni.
Omar ya haɗiya da kyar, ya tilasta kalmomi na karshe. Yace, “Nayi miki alkawari Gradma Halime.”
Nan take mommy tayi ajiyar zuciya a hankali tana matsowa kusa dani.
Omar bai kuskura ya dube ta ba.
Amma ya ji idanun Papa a kansa. Ya ji yanda yake alfahari dashi a cikin shirunsa.
Kuma Omar ya ji nauyin kalmomin sa suna yawo dashi cikin wani abu da bai gane ba.
Idanun granny masu gajiya sun haskaka da wani abu mai dumi, mai farin ciki.
Ta nuna masa ya matso kusa. Omar ya yi shakku da farko.
Sai ahankali ya sunkuya zuwa gare ta.
Hannunta mai rauni ya kai sama taɓawarta da kyar yayin da ta manna lips din ta a goshin sa kiss din mai dumi mai laushi.
Omar ya rufe idanu yana jin nauyin lokacin yana zama cikin kirjin sa.
Ya ji hawaye suna fitowa daga idonsa.
“Na gode, Omar,” ta rada, muryarta tana dauke da wani abu mai laushi sosai, mai fahimta wan da yasa makogwaronsa ya matse. Granny ta sake cewa, “Ban yi kuskure ba. Kai mutum ne nagari… Don Allah, ka kular min da Aleena.”
Numfashi mai rawar jiki ya fito daga gare shi. Ya ja baya kawai don ya hadu da kallonta, amincewa da yardar da tayi masa ta bayyana a idanunta wanda ke zama yanzu a cikin zuciyar Omar, Nauyi ne wanda bai bukace shi ba - amma wanda ya yarda ya dauka.
Sa’an nan, a hankali, ya gyada kai.
Yayin da ya mike, ya ji Papa ya matso kusa dashi amma har yanzu Omar bazai iya hada ido dashi ba.
Omar ya cire hannu a hankali kamar zai karya wani abu mai rauni idan ya yi saurin barin wurin.
Sa’an nan - ya juya zuwa kofa.
Zuwa hargitsin da ke jiransa.
Zuwa rikicin da ya yi alkawari bazai taba bari ba.
Alkawari cikin shiru. Alkawarin da bai san ko zai iya cikawa ba. Amma rantsuwa ce ya riga ya dauka.
Kuma Omar bai taba karya alkawarinsa ba. Koda sau daya a rayuwarsa ba.
A/N: 🥺💔….. Emir da Omar 🙆♀️
💘AUREN ALEENA💘
Amal Musa ✍️
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.