Complete Hausa Novels

Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel

Reading file: Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel.docx

Chapter 23 of 28

Chapter 2️⃣3️⃣ Ya Tuna Komai 💋🧍🏻‍♂️❤️🧍🏻‍♀️

SHARE SHARE SHARE 💃💃💃💃💃

Ta tilasta ƙafafunta su motsa. Da duk wani ƙarfin hali da ta iya tattarawa, Aleena ta juya tana nufar ƙofar fita kai tsaye. Ba ta son ci gaba da tsayawa a wajen ko da na second guda ne. Domin duk lokacin da ta tuna abin da ya faru a daren jiya, sai ta ji zuciyarta ta kasa samun nutsuwa, tana dab da wucewa ta gefen sofa ɗin, sai muryarsa ta dakatar da ita. Muryarsa a sanyaye cikin nutsuwa kamar da gangan. Amma kuma tana ɗauke da wani irin iko da ya sa takunta ya tsaya cak.

"Aleena." Omar ya kira sunanta yana miƙewa tsaye a hankali. Kamar kullum, ko da tafiya yake yi, akwai wani irin kwarjini da ke tare da shi. Ya ɗauki briefcase ɗinsa daga gefen kujerar da yake zaune, sannan ya nufi inda take ba tare da ya ƙara cewa komai ba.

Nan take bugun zuciyar Aleena ya fara ƙaruwa.

Shin zai dauko maganar abin da ya faru jiya ne? No, she can't... Dole ne ta yi duk abin da za ta iya domin ya manta. Kamar yadda ita ma take ƙoƙarin mantawa.

"Ki duba schedule dinki, sannan ki sanar da ni ranar da za ki iya ɗaukar hutun rana ɗaya. Muna buƙatar zuwa Antalya." Muryarsa ta zo daga bayanta cikin sanyin da ya saba amfani da shi idan yana magana kan aiki.

Aleena ta juya a hankali tana kallonsa, nauyin kalamansa ya tsaya a tsakaninsu. "Antalya?" Ta maimaita cikin murya mai cike da rashin fahimta.

Omar ya gyada kai kaɗan. Sai kuma ya kau da idonsa daga kanta na ɗan lokaci.

Ba tare da ta shirya ba, Aleena ta ji wani irin numfashi mai sauri ya kubuce mata. Abin mamaki kuwa shi ne, dalilin hakan kasancewar bai kalle ta kai tsaye ba. Kamar shi ma yana kokarin kaucewa wani abu.

A nutse ya zaro sunglasses ɗinsa ya saka. Sannan ya gyara jakarsa cikin kwarewa da kwarjinin da suka zama wani ɓangare na halayensa, kamar babu wani abu da ya taba faruwa a tsakaninsu, kamar daren jiya bai taba faruwa ba.

Shiru ya mamaye dining area ɗin. Sai muryarsa ta sake karya shirun.  "Akwai wani abu da ya kamata ki sani. Team dina sun gano wani kamfani da zai iya kera mana wasu components din T-Phone."

Aleena ta ɗaga gira cikin mamaki. Ba ta fahimci inda maganarsa ta dosa ba. Shin yana nufin zai daina aiki da Khan Electronics ne? Bayan duk abin da suka tattauna? Bayan duk ƙoƙarin da ta yi? Kwanaki kaɗan da suka wuce ma ta sanar da shi cewa Khan Electronics za ta iya ƙara production capacity ɗinta zuwa kusan units ɗari biyar a rana. To me yasa yanzu yake neman wani kamfani daban? "Me kake nufi, Omar?" ta tambaya cikin nutsuwa. "Na gaya maka cewa Khan Electronics za ta iya kara production capacity dinta. Me yasa kake wannan maganar yanzu?" Ta yi iya kokarinta wajen boye takaicin da yake tasowa a zuciyarta saboda bata san yaga abin ya dameta. A matsayinta na CEO kuma businesswoman, ba ta san abubuwan da suke kama da sauya alkibla ba tare da wani bayani mai karfi ba. Bayan duk wata gardama da tattaunawa da suka yi a baya, ta dauka sun riga sun samu mafita. Amma yanzu ga shi ya sake bullo da wani sabon abu da ba ta fahimta ba.

Omar ya gyada kai cikin fahimta. "I understand." Ya faɗa cikin nutsuwa.

"Kuma kamar yadda na faɗa a baya, abin da kuka yi babban ci gaba ne." Ya ɗan dakata idanunsa suna kanta. "Kuma kin yi ƙoƙari sosai." Kalmar ta fito daga bakinsa cikin sauƙi.  "Amma wannan factory din za ta samar mana da sauran components din da ba za ku iya karasawa ba. Ta haka za mu samu adadin T-Phone Gen 6 da nake bukata kafin lokacin kaddamarwa." Ya tsaya na dan lokaci kamar akwai wani kalma da ya makale masa a makogwaro. Sannan yayi gyaran murya ya ci gaba. "Za mu iya kaddamar da shi a watan December... ma'ana wannan shine solution."

Aleena ta yi shiru, tana nazarin kowace kalma da ta fito daga bakinsa. A hankali ma'anar abin da ya fada ya fara sauka a kanta, kuma hakan ne ya ƙara rikita ta. Omar Thorne. Mutumin da ya saba samun abin da yake so. CEO mai tsananin girman kai. Mutumin da baya son a karya tsarin da ya gina. Shi ne ya dauki lokaci ya nemo wata mafita... Domin ya taimaka mata? Domin ya tabbatar Khan Electronics ba ta rasa wannan kwangilar ba? Abin ya bata mamaki sosai. Sannan kuma wani kamfani yake magana a Antalya? Musamman idan aka yi la'akari da cewa Layla ta shafe watanni tana neman irin wannan kamfani amma ba ta samu ba. Wannan ba karamin aiki ba ne. Kuma babu shakka team din Omar ta yi aiki tukuru kafin su gano wannan damar. "I understand."Aleena ta fada daga karshe. "To wannan kamfanin yana Antalya kenan?"

Omar ya gyada kai, sai kuma ya yi shiru na ɗan lokaci. Sannan a hankali ya ƙara matsowa kusa da ita.

Nan take numfashin Aleena ya ɗan tsaya, jikinta ya yi wani irin sanyi mai gauraye da daskarewar kafa. Ba saboda kalamansa ba. Sai dan saboda kusancin da ya rage tsakaninsu. Da kyar ta iya ci gaba da tsayuwa a wajen, ji tayi kamar sararin da ke tsakaninsu yana raguwa fiye da yadda ya kamata. Ga kamshin turarensa ya mamaye ta kuma mai jan hankali, ya zura hannunsa daya cikin aljihunsa ahankali kuma da gangan.

“And yes. Ina kuma san mu je tare. Akwai wasu abubuwa da ya kamata mu tattauna da CEO ɗin kamfanin. Jiya Ali da Kemal sun kasa warware su.” Ya ɗan dakata kafin ya ci gaba. “Ina buƙatar ki yi mata bayanin component ɗin da kanki domin ta fahimci standards ɗin da nake so. And zai iya ɗaukar lokaci fiye da yadda nake tunani, saboda haka ki ware cikakken rana ɗaya.”

Aleena ta gyada kai a hankali, makogwaronta ya ɗan riƙe mata. “Na gane.” Ta gyara sunglasses ɗinta tana ƙoƙarin dawo da nutsuwarta. “Zan sanar da kai idan na samu lokaci.” Ta ɗan dakata. “Watakila gobe ko kuma Friday. Amma sai na fara tabbatar da hakan wajen Mariam.”

Omar ya gyada kai sau ɗaya, bai ƙara cewa komai ba.

Duk da cewa baƙaƙen gilashi sun rufe idanunsa, amma Aleena tana jin kamar kallonsa yana kanta. Mai zurfi. Mai cike da tambayoyi. Kamar yana iya ganin duk abin da take ƙoƙarin ɓoyewa a bayan lenses din glass dinta. Ba ta san dalilin da ya sa take jin hakan ba. Amma nauyin kallon nasa ya sa bugun zuciyarta ya ƙaru. Kuma ba tare da san ranta ba, tunaninta ya koma kan daren jiya.

Idanunsa.

Lips dinsa.

Abin da ya shiga tsakaninsu.

Komai ya dawo ya mamaye zuciyarta lokaci guda. “Shi kenan, zan tafi.” Ta faɗa cikin sauri tana juyawa. Tana san kawo karshen tattaunawar kafin ta koma wani abun daban.

Amma kafin ta ƙara yin wani takun, muryarsa ta sake dakatar da ita. “Ki ba ni phone number dinki.”

Aleena ta ji kamar yanayin wajen ya sauya gaba ɗaya. Takunsa suka ƙara kusanto ta. Har tana iya jin dumin kasancewarsa a bayanta.

Ba tare da ta juya ba, ta tambaya, “Number ta kuma?”

“Eh.” Muryarsa ta zo cikin sauƙi. “Domin idan wani abu ya taso ki sanar da ni cikin sauri. Musamman idan ya shafi teamwork ko wani abu urgent.”

Aleena ta kyafta ido.

Teamwork?

Urgent?

Wani irin tunani ya ratsa zuciyarta, shin yana magana ne akan zuwan iyayensa na daren jiya? Toh ko ya tuna komai ne? Fadan su? Kiss din? Ko kuwa… A’a. Ba ta san ma ci gaba da wannan tunanin. “Ba sai na baka ba.” Ta faɗa a hankali tana kokarin testing intention dinsa don gano ainihin dalilinsa.. “Za mu iya magana a gida idan na dawo.”

“Of course, za mu iya.” Ya amsa ba tare da ɓata lokaci ba. “Amma ba koda yaushe kike zama a gidan ba.” Ya ɗan dakata. “Ina ganin zai fi sauƙi idan muna magana ta waya idan akwai wani abu mai muhimmanci. Haka kuma za ki iya sanar da ni ranar da za ki samu damar zuwa Antalya ba sai kin fuskance ni ba.” Sai ya sake yin shiru.

A karo na farko tun da suka fara wannan tattaunawar, Aleena ta ji wani irin sauƙin numfashi. Alhamdulillah. Ba abin da take tsoro yake nufi ba. Dalilinsa daban ne. Kuma abin mamaki… Dalilin nasa yana da kusan ma’ana. Saboda Omar yana da wani hanya ta musamman wajen sanya komai ya zama logical, always giving solutions… Kuma abin da ya fi ba ta mamaki shi ne, sau da yawa tana samun kanta tana amincewa da shi ko da kuwa ba ta shirya yin hakan ba. Amma a wannan karon ta girgiza kai. Ba za ta ba shi wannan nasarar ba. Ta saki ɗan murmushi kaɗan. “Mu bar maganar nan, Omar.” Ta faɗa. “Babu anfani.” Muryarta a wannan karon ta fi ɗauke da ƙarfi.

Omar ya sake matsowa kusa da ita. Iskar da ke tsakaninsu ya ƙara yin nauyi. Hannunsa ya shafi nata a hankali kafin ya sauke shi gefe. Yatsunsa suka goga da nata na ɗan lokaci kaɗan. “Da na so, zan iya samun number ɗin a wajen kowa.” ya faɗa cikin murya ƙasa-ƙasa a gefen kunnenta. “Amma ban yi hakan ba, Ba na san tambayan abubuwa irin haka idan ba daga wajen wanda abin ya shafa ba... Kuma ina san samun abin da nake so da yardar mutum.”

Ƙirjin Aleena ya matse. Kalaman nasa sun shiga cikinta fiye da yadda ya kamata.

“Amma tunda kin dage ba za ki ba ni ba, na fahimta,” Omar ya ci gaba. Yatsunsa suka sake gogan nata. Numfashinsa mai ɗumi ya sauka gefen kunnenta. “Ba zan matsa miki ba.” Sai kuma ya ɗan yi murmushi. “Wata rana da kanki za ki ba ni, Zan jira har sai ranar ta zo.” Ya ɗan dakata. “Saboda ba za ki iya jurewa na dogon lokaci ba.”

Aleena ta ji nauyin kalamansa yana nutsewa a ranta. OMG...Ya tuna komai. Shikenan wallahi ya tuna komai da ya faru jiya da daddare. “M-me kake nufi? Na ba ka mai?... Mene bazan iya jira ba... me?” Da kyar ta iya furtawa muryarta tana karyewa.

Omar ya yi wata ƙaramar dariya. Mai sanyi. Mai cike da nishaɗi. “Phone number ɗin nake nufi, Aleena.”

Nan take ta ji fuskarta ta yi zafi, ta matse haƙoranta. “Ba zan ba ka ba.” Ta faɗa cikin nutsuwa. “Saboda babu wani amfani.

“To shikenan.” Ya ce kai tsaye. Muryarsa tana ɗauke da wani abu da ba ta iya fassarawa ba.

Aleena ta gyada kai. “Good.”

Na ɗan wani lokaci shiru ya sake mamaye tsakaninsu. Sai ta ji kamar yana san ya ƙara faɗar wani abu. Amma bai yi ba. Maimakon haka, sai ya kara yin murmushi, Murmushin da ya sa cikinta yin wani irin faɗuwa. “Nice makeup.” Ya faɗa cikin kasala. Yatsunsa suka taɓa gefen wuyanta a hankali. Wurin mark din da ya bar mata wanda ta ɓoye shi a ƙarƙashin concealer. “Dole kin sha wahala wajen ɓoye shi. Ki dai yi fatan babu wanda zai lura da shi.” Ya ɗan karkatar da kansa. “Me kike tunanin Emir zai yi idan ya gan shi ko yan office? Tabbas matsala ce babba, ko ba haka ba? Ina san na baki hakuri amma kuma na mai? Saboda dukkanin alamu kema kin ji dadin sa, Idan aka yi la’akari da irin sautin da kika saki a kunnuwana jiya da daddare. Such a sexy thing.”

Aleena ta tsaya cak, baki a bude ta daskare inda take kawai ta tsaya tana kallansa. Omar kuwa ya wuce ta, ya nufi ƙofar fita. Sautin takunsa suka gushe, ba da daɗewa ba ta ji sautin motarsa. Injin ya tashi. Tayoyin suka fara motsi a harabar gidan. Sai kuma shiru. Ya tafi. Kamar babu abinda ya faru.

Leben Aleena ya fara rawa. Ta lumshe ido tana ƙoƙarin dawo da nutsuwarta amma abin ya gagara. A ƙarƙashin baƙaƙen gilashinta, komai ya yi mata nesa. Ya yi mata duhu.

Aleena ta kasa magana. Gabanta ya shiga faɗuwa yanzu kam babu sauran shakku. Omar ya tuna. Ya tuna komai da ya faru jiya da daddare. Wannan kaɗai ya isa ya rikita mata duk wani tunani. Ya Allah. For some seconds ji ta yi ta kasa jan numfashi yadda ya kamata.

Bacin rai ne?

Tayi ihu ne?

Ko kuma ta ƙara nadamar abin da ya faru fiye da wacce take yi yanzu?

Ta kasa gano amsar.

Abin da kawai ta sani shi ne… Zuciyarta ba ta cikin yanayin da za ta iya fahimtar kanta a wannan lokacin.

💘AUREN ALEENA💘

Amal Musa✍️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.