Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel.docx
Chapter 22 of 28
CHAPTER 2ï¸âƒ£2ï¸âƒ£ Ka Manta Da Daren Nan, Omar… 💋💔
Dukkan wani control da Aleena take rike da shi ya karye. Zuciyarta ta yi wani irin fashewa. Ba tare da tunani ba ta karasa kusa da shi ta zabga masa mari da karfi. Sautin marin ya cike dakin wanda ya girgiza shi idonsa yayi duhu bakinsa ya bude kadan.
"Ka tauna kalamanka kafin ka sake fada min!" Muryar Aleena tana rawa cike da kuma zafin da ke cin kirjinta. "I hate you, Omar. Go to hell!" Ta juya cikin hanzari zata fita.
Amma sai ta ji takunsa a bayanta kafin ta kai hannu ta bude kofar, Omar ya kama hannunta da karfi ya ja ta baya har tana tuntube ya mannata da jikin kofar rikonsa babu tausayawa ko kaɗan. Ba tare da ya furta kalma ɗaya ba ya haɗa bakinsa da nata wani ɗan ƙaramin iska ya kuɓuce daga bakin Aleena saboda firgicin da ya mamaye ta kiss ɗin nasa ya zo da ƙarfi da tsanani, Hannayensa suka fara yawo a jikinta cikin wani irin rudani kamar wani mahaukaci.
Aleena ta ji ɗanɗanon giya a harshensa yana gaurayawa da numfashinsa a cikin bakin ta. Nan take zuciyarta ta rikice kanta ya fara juyawa jikinta ya tsaya cak. For some seconds ta kasa motsi gaba ɗaya. Sai zuciyarta ta fara yi mata ihu da ta ture shi. Aleena ta ɗaga hannu tana ƙoƙarin ture shi, amma ya matse ta da bangon jikinsa ya manne da nata ƙarfinsa ya yi mata yawa. "Mey haka kake yi?!" Aleena ta furta acikin bakinsa da karfi tana turashi amma babu amfani.
Hannunsa ya kama fuskarta da karfi idonsa yayi jajir kallonsa yayi zurfi cikin nata kamar yana karanta duk wani tunani da tsoron da ke bayyane a fuskarta. “Kin É—auka kina da control a kaina?†Omar ya faÉ—a yana jan tsaki. Muryarsa a sanyaye ta ke amma kamar guba. “Baki da wani aiki sai zagina kamar ni ne akarkashin ki? God damn you, Aleena… me yasa kike tunanin kina da power a kaina?†RiÆ™onsa ya Æ™ara tsananta. Ya Æ™ara rage tazarar da ke tsakaninsu, lips É—insa yana gab da gogar nata again. “Duk yadda na so da naji dadin rayuwata, amma sam na kasa saboda ke. Amma ke kina yin duk abin da kika ga dama a gidan nan? Why?â€
Aleena ta ji ta kasa numfashi komai ya tsaya cak. Duk wata kalma da take son furtawa ta makale a maƙogwaronta kafin ta iya ɗaukar wani mataki kawai sai ji tayi Omar ya sake haɗa bakinsa da nata cikin sauri. Aleena ta shiga yaƙin ƙoƙarin janye fuskarta.
Amma hannayensa sun kame ta tun daga kai har zuwa kafaɗunta ya riƙe ta gam yana tilasta mata karɓar kiss ɗinsa. Harshensa ya fara tsotsan lips dinta na ƙasa a hankali, da gangan.
Tunanin Aleena ya gushe daga kanta gaba ɗaya jikinta ya fara daukan rawa , wata rawar sanyi ta ratsa ta tun daga bayan wuyanta har zuwa cikin ƙashin bayanta, yayin da zuciyarta ke bugawa da ƙarfi a cikin kirjinta. Tsoro da wani yanayi da bata iya fahimta ba suka gauraye a cikinta. Duk wani hankali da tunani nata yana yi mata ihu da ta dakatar dashi, ta ture shi, ta guje masa, Amma ta kasa yin hakan hannayenta suka fara rawa sosai ta kasa ture shi jikinta ya ƙi ba ta haɗin kai. Kuma duk yadda take yaƙar hakan, ta kasa hana kanta mayar masa da martani. Kafin ta ankara, Aleena ta ji tana kissing dinsa back. Kiss ɗin ya ci gaba da zurfafawa, cike da wani irin zafi da tsanani.
Hakan ne ya sa Omar ya ɗan kau da bakinsa daga nata. Ya shiga fara manna mata kiss a wuya, a kumatu, da gefen kunne. Hannunsa ya fara ɗaga rigarta da sauri, kamar wanda ya daɗe yana jiran wannan lokacin, kamar kuma wanda yake tsoron kada ta canza ra’ayinta. Omar ya kama jijiyoyin wuyanta da lips ɗinsa, yana ta manna mata kiss ba ƙaƙƙautawa.
Ana cikin hakan ne sai fuskar Emir ta bayyana a idanun zuciyar Aleena. Nan take idanunta suka buÉ—e.
OMG…
Aleena ta furta a cikin zuciyarta. Me nake yi haka? Tambayar ta faɗo mata da ƙarfi da tsawa. Cikin gaggawa ta ture Omar da dukkan ƙarfin da take da shi. Tana shakar iska ta baki numfashinta yana hawa da sauka.
Omar ya ja baya har ya faɗa kan gadon saboda ƙarfin turawar da ta yi masa kirjinsa yana bugawa da karfi Idonsa sun ƙara yin jajir suna kan Aleena.
Aleena kuwa har yanzu jikinta rawa yake yi. Ba saboda kiss ɗin kaɗai ba… Amma sai dai saboda abin da ya faru a tsakaninsu. Bai kamata hakan ya faru ba… kuma bai kamata in ji abin da nake ji ba. Ta faɗa wa kanta a ranta. Ta juya ta kalli Omar, wanda yake zaune a kan gadon. “Kada ka sake taɓa ni.†Aleena ta faɗa masa cikin tsawa da ihu, muryarta tana rawa.
Omar ya kalleta bakinsa a É—an buÉ—e Mamaki da ruÉ—ani sun mamaye fuskarsa. Amma babu alamar nadama tare da shi.
Aleena ta goge bakinta da bayan hannunta cikin haushi da sauri ta nufi ƙofar ɗakin ta ɗora hannunta kan handle ɗin ƙofar sannan ta dakata, ta juya kaɗan ta bayan kafaɗarta, tace, “Ka manta da daren nan, Omar. This is a mistake. A big mistake, kuma ba zai sake faruwa ba.†Daga nan ta fisge ƙofar ta buɗe ta fita Ƙofar kuma ta buga da ƙarfi a bayanta yayin da ta rufe.
Zuciyar Aleena tana bugawa da sauri yayin da take hanzarin komawa ɗakinta kowane taku da take yi, nauyin kuskuren da ta aikata yana ƙara sauka a kanta. Tana shiga cikin ɗakin ta buga ƙofar da ƙarfi a bayanta sannan ta jingina da ita tana ƙoƙarin daidaita numfashinta. Kirjinta kaman zai fashe, tunani kuwa sai yawo yake mata a kanta ta ko’ina. A hankali ta zame zuwa ƙasa har ta zauna a bakin ƙofar. Idanunta ta lumshe hannayenta kuma sun kama kanta da ƙarfi. Laifi, takaici da ruɗani suka gauraye suna yawo a cikin zuciyarta. Hawaye suka gangaro masu zafi da sauri suna wanke mata fuska yayin da kunyar abin da ya faru ke ci gaba da ƙona ta daga ciki. “Me kika aikata haka, Aleena?†Ta furta a hankali tana bugun bayan kanta da ƙofar cikin takaici.
“Ohh, No…â€
Nan take fuskar Emir ta bayyana a cikin tunaninta. Wani sabon nauyin laifi ya nutse a cikin zuciyarta.
Ta yaudare shi.
Mutumin da take so.
Ta yaudare shi da mutumin da bata damu da shi ba.
Mutumin da ta tsana.
“Ya Allah…â€
Ta furta tana girgiza kai. Ta rufe idanunta. Amma tambayar ta ci gaba da bibiyarta ba tare da tausayi ba. Meyasa nayi kissing din sa back? Why? Me yasa na ji wani abu game da Omar?
Ya Allah…
Tunani ya ci gaba da yawo a cikin kanta, yana murɗe mata zuciya da ƙara rikita mata hankali.
A haka bacci ya yi awon gaba da ita.
Zaune a bakin ƙofa.
Har safiya.
———
Agogon bango yana ƙyaftawa yana nuna ƙarfe takwas da rabi na safe. Tun bayan asuba Aleena ba ta sake komawa bacci ba. Yanzu kuma ta fito daga wanka tana shirye-shiryenta, ta zauna a gaban madubin banɗaki.
“Menene wannan?â€
Aleena ta faÉ—a da sauri tana zubawa madubin ido.
Idanunta suka ƙara buɗewa yayin da yatsunta suka tsaya a saman wuyanta. Wani mark ta gani a wuyanta, ja mai duhu Kamar wata shaida ce da aka rubuta a jikinta. A hankali yatsunta suka shafa wajen, kamar tana fatan alamar za ta ɓace idan ta taɓa ta. Ta ƙara matsowa kusa da madubin. Idanunta sun kumbura alamar kuka mai yawa da ta yi daren jiya, haɗe da rashin bacci. Ta mari kumatunta a hankali. Zafin ya ratsata. “Good, Aleena. Yanzu kin ƙara wa kanki sabon aiki kafin ki fita.†Ta furta cikin takaici.
Ta yaya ta bari hakan ya faru? Ta rufe idanunta. Nan take abubuwan daren jiya suka fara dawo mata.
Omar.
FaÉ—ansu.
Kiss É—insu.
Nadama.
Da kuma Emir.
Ta ja numfashi da ƙyar sannan ta sake buɗe idanunta. Yanzu kuma ga wannan jan mark. Dole ta ɓoye sa. Musamman ma da za ta je office tabbas mutane za su gani. Wannan tunanin ya sa zuciyarta ƙara bugawa.
Emir ya ce zai yi tafiya kuma zai biyo ya yi mata sallama. Me zai faru idan ya lura da wannan mark? Idan ya fara yi mata tambayoyi fa? Tabbas hakan zai kawo zargi. “Wayyo Allah na…†Ta katse tunaninta komai ya rikice mata. Abin da take buƙata kawai shi ne ta guji ganin Emir yau.
Amma kuma tafiya zai yi.
Eh… amma duk da haka dole ta haƙura.
Eh.
Hakan ya fi.
Domin abin da Aleena take ji yanzu kamar ta yaudare shi ne. Kuma gaskiyar ita ce…
Ta yaudare shi.
Saboda ta bari mijinta ya kusance ta. Mutumin da ta rantse ta tsana. Wata murya a cikin kanta ta ci gaba da tunasar da ita hakan. Aleena ta girgiza kai cikin sauri tana ƙoƙarin korar tunanin. Ta fita daga banɗakin ta nufi wajen madubin daki. “Mu gama da wannan kawai, Aleena.†Ta furta tana ɗaukar kayan makeup. “Ki ɓoye komai. Ki ɓoye yadda rayuwarki ta rikice.†Da ta gama shirinta, ta sake kallon kanta a madubi.
Komai ya yi kyau.
Kayan jikinta a shirye.
Jakarta a hannu.
Makeup ɗin ya zauna da kyau. Mark da ke wuyanta ma ya ɓace a ƙarƙashin makeup.
Yauwa… good.
Ta sake kallon idanunta. Kumburin ya ragu. Sai dai har yanzu ba su dawo yadda suke ba. Ta buÉ—e wardrobe ta É—auko glass É—inta.
Ta saka.
Sannan ta sake kallon kanta a madubi. Yanzu komai ya yi daidai. Ta ja dogon numfashi. Ta juya ta fita daga É—akin. Idan har ta haÉ—u da Omar yau, abu É—aya kawai za ta yi. Za ta yi kamar babu abin da ya faru.
Babu magana.
Babu gardama.
Babu wani abu.
Aleena ta yi tunanin ko ta tsaya ta yi juice na tumatir kafin ta fita. Sai kuma ta girgiza kai.
A’a.
Za ta wuce office kai tsaye kawai. Kar ta sake neman wata matsalar. Ba ta ma san abin da zai faru ba idan suka sake haÉ—uwa yanzu. Don haka me zai sa ta sake tunzuro shi da sassafen nan? Ta bar hakan zuwa wani lokaci.
Idonta ya tafi kai tsaye zuwa ƙarshen corridor inda ɗakin Omar yake. Sai ta sauke idonta kan agogon hannunta. Ƙarfe tara da minti goma sha biyar na safe.
Ya farka kuwa?
Ko ya riga ya fita?
A wannan lokacin ai ya kamata yana dining area yana cin breakfast kafin ya tafi office.
Ko kuwa har yanzu yana É—akinsa?
Yana lafiya kuwa?
Ko kuma har yanzu yana fama da buguwa saboda giyar daren jiya?
Aleena ta tsaya cak. Wani tunani ya faÉ—o mata.
Ko ya kamata ta shiga ta duba shi?
Don tabbatar da cewa bai…
mutu ba?
Aleena ta haɗiye yawu… “No, no… stop.†Da sauri ta girgiza kanta cikin takaici sannan ta nufi hanyar stairs.
“Me yasa ma nake tunanin duba shi?†Ta furta wa kanta a hankali.
Amma kafin ta sauko mataki na gaba, sai ta tsaya cak. Zuciyarta ta yi wani irin bugawa lokacin da ta hango shi.
Omar.
Zaune yake a kan sofa cikin suit ɗinsa mai tsari, kamar yadda ya saba kasancewa koyaushe. A nutse yake, kamar ba shi ba ne na daren jiya. Bayansa a miƙe tamkar an zana shi da ma’auni. Wayarsa na hannunsa, yatsunsa na saurin rubutu a kanta. Idonsa suka ɗago zuwa gare ta na ɗa second kaɗan kafin su koma kan screen ɗin wayar.
Amma Aleena ta hango wani abu a kallon nasa. Wani yanayi da ta kasa fassarawa.
Daga nan sai ya ɗan yamutsa fuska yana shafa gefen kansa, kamar yana ƙoƙarin rage wani ciwo ko nauyin buguwar daren jiya.
Babu fushi a idanunsa.
Babu haushi.
Babu takaici.
Sai dai wani irin shiru da babu komai a cikinsa.
Good. Watakila bai tuna komai daga daren jiya ba. Aleena ta faÉ—a a ranta. Ko da yake ba ta sani ba, tana fatan hakan alama ce mai kyau. Saboda ba ta san yadda za ta iya fuskantarsa ba idan ya buÉ—e maganar kiss É—in da ya faru.
Abin kunya ne sosai.
Ta tilasta ƙafafunta su motsa cikin duk wani ƙarfin gwiwar da ta iya tarawa. Ta nufi ƙofar fita kai tsaye.
Amma tana dab da wuce sofa É—in, sai muryarsa ta dakatar da ita.
Muryarsa a sanyaye, cikin natsuwa kamar da gangan. Amma tana É—auke da wani irin isa da ya sa takunta ya tsaya cak.
“Aleena.†Omar ya fada yana miƙe wa a hankali.
💘AUREN ALEENA 💘
Amal Musa âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.