Complete Hausa Novels

Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel

Reading file: Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel.docx

Chapter 13 of 28

Chapter. 1️⃣3️⃣ Matar Omar, 💍❤️‍🔥Masoyiyar Emir🥀💔

SHARE SHARE SHARE 💃💃💃💃💃

Zoben da ke yatsan Aleena ke kyalli yana kama hasken rana da ke shigowa ta buɗaɗɗen ƙofar falon zaman makoki. Zoben auren da bata so ba amma yanzu gashi nan, a yatsanta. Shaidar alkawari da aka ɗaura a gaban granny.

Aleena tana zaune cikin shiru, amma duk da haka, hawayenta kamar suna bushewa ne tun kafin su sauko.

Yau sati biyu ke nan da rasuwar granny.

Amma har yanzu, Aleena bata jin komai.

Ganin Aleena har yanzu bai dawo daidai ba idanunta suna ganin duhu lokaci-lokaci, hankalinta yana yawo, Mutane sun yi ta zuwa suna tafiya suna mika mata ta’aziyya, suna furta mata kalmomi masu kwantar da hankali, suna karanta addu’o’i da suka saba maimaitawa cikin waɗannan kwanakin.

Yau ranar kwana sha hudu ce, amma duk lokacin da Aleena ta ɗaga hannun ta domin yin addu’a, zuciyarta sai ta ji kamar ba daidai take yi ba—saboda addu’ar da zuciyarta ta ke yi daya ce: Allah ya dawo mata da granny.

Nisa best friend dinta ta zauna agefen ta, ta miƙa wa Aleena kofin tea. Aleena ta karɓa ba tare da dubawa ba kallonta bai ɗaga ba.

“Aleena…” Nisa ta ce a hankali yayin da Aleena ta kurbi tea kaɗan.

Aleena tayi hum don amsa.

“Kina jin sauki?” ta ci gaba.

Aleena ta gyada kai a hankali.

Mariam, dake zaune a ɗayan gefen nata ta miƙa hannu tana dafa kafadarta. tace, “Leila dani muna bukatar komawa office,” ta faɗa lokacin da ta rungumi Aleena.

“Nima haka, Aleena.” Nisa ta ƙara, tana girgiza kai. “Ina bukatar in tsaya a cafe. Ki kira ni idan akwai wani abu da kike buƙata.”

Aleena ta sake gyada kai, sannan ta kalli su biyun, har da Leila, wadda tuni ta mike tsaye jakarta a kafaɗarta.

“Lafiya lau nake,” Aleena ta rada da kyar da ƙarancin sauti. “Na gode. kun kasance tare dani a kowace rana.” And I meant it. Truly.

Nisa da Leila da Mariam basu taba barin gefen Aleena ba tun rasuwar granny sun kasance akanta acikin komai tsawon sati biyu yanzu.

Sun san komai yanzu—game da auren. Aleena ta fada musu washegari bayan rasuwar granny lokacin da Omar da mahaifinsa suka ɗauki nauyin jana’izar. Aleena abun yayi mata yawa baza ta iya dauka ba, da kyar take iya rike kanta.

Sun tambayi dalilin da yasa Thorne suka dauki nauyin jana’izar da komai. Kuma Aleena ta faɗa musu gaskiya.

Sun yi mamaki a zahiri. Sun so su ji ƙarin bayani—amma basu matsa ba. Saboda yanzu ba lokacin hakan bane, kuma sun fahimta.

Ɗaya bayan ɗaya suka tattara kayansu suka bar falon idanunta yana binsu har zuwa ƙofa, amma hankalinta sai ya tsaya akan Omar, wanda yanzu ya tsaya yana magana da wasu daga danginsa Tsayuwarsa cikin nutsuwa kamar babu abinda ya faru a cikin sati biyun daya wuce.

Sati biyu, Babu kalma ko guda daya da ta shiga tsakaninsu.

Tun daren nan a asibiti—lokacin da Omar ya rungume Aleena yayin da ta karye cikin kuka, lokacin da hawayenta suka jiƙa rigarsa. Lokacin da bakin ciki ya damƙe zuciyarta.

Omar bai tambayeta ba. Kuma bai matsa mata ba. Ya bata lokaci kawai.

Wannan auren aiki ne kawai—kuma hakan suka sani tun farko. Ba su taba tunanin jituwa ba. Ƙiyayya itace tushen da suka gina auren akai kuma har yanzu, har acikin wannan yanayin babu abinda zai canza hakan.

Aleena da Omar ko batun zama basu yi ba, Misali, Aleena tana zaune a Thorne family house. Omar kuma yana kuma yana zaune a gidansa nesa da gidan iyayensa. Aleena baza ta iya komawa gidan su ba saboda baza ta iya zama tana ganin rayuwar da tayi ita da granny a cikin gidan ba, kuma iyayen Omar sun dage sai ta zauna anan Thorne family house. Kuma su ne suke kula da ita.

Tsawon kwanaki goma sha huɗu, babu faɗa, babu maganganu masu zafi tsakanin Omar da Aleena. Shiru ne kawai. Wani irin zaman lafiya mai rauni da ya fito daga sati biyu.

Saboda wani lokaci Aleena ta kanga alamun damuwa sosai a idanunsa.

Omar shima zuciyarsa tana ƙuna a sirrance, kamar yadda ta Aleena take ita kuma a bayyane.

Don haka suka bar yaƙin ya huta.

A yanzu dai.

Amma wutar da ke cikin ta ba ta mutu ba. Idan akwai wani abu sai ma karuwa da tayi, hankalinta yana neman wanda zata dora wa laifin komai da ya faru kuma koda yaushe kan Omar yake dawowa. Saboda rushewar rayuwarta, rasuwar granny da kuma rashin Emir. Duk hakan ya faru ne saboda mutum daya, Omar.

Emir…. ya kasance yana zuwa gidan makokin kowace rana. amma sau ɗaya kawai ya taba zuwa kusa da Aleena ya bata gaisuwarsa.

Babu runguma. Babu kiss agoshi yanda ya saba.

Sai wata murya mai laushi mai nesa wacce kamar ba tasa ba ce. Yace, Aleena ya karin hakuri? Allah ya ji kanta da rahama yasa ta huta, I hope you will be strong.

Strong? Kalmar ta tokare Aleena. Emir bai sani ba daya rungumeta a lokacin wataƙila da ta samu ƙarfin da take nema. Amma a’a, bai yi murmushi ba. Idanunsa sun zama fanko, cike da baƙin ciki da wani ciwo mai zafi, kuma ya guje hada ido da ita tsawon lokacin.

Duk da haka, Emir yana zuwa kowace rana. Amma bayan haka, ya yi nesa, yana halartar addu’o’in cikin shiru.

Ba tare da ya kalli Aleena ba, bai sake kusanto ta ba, Ko yaushe yana zaune cikin falon agefe, sannan kafin komai ya ƙare, yake tashi ya fita cikin shiru ba tare da kalma ba.

Aleena bata san mai ke faruwa ba kawai dai taga Emir yana magana da Omar, Bata ji abin da suke cewa ba, amma tashin hankalin dake tsakaninsu ya bayyana fili. Aleena ta matsa zuwa gare su da sauri, amma kafin ta isa kusa dasu, Emir ya lura da ita nan da nan ya juya ya tafi. Aleena ta tsaya cak zuciyarta ta sake tarwatsewa a karo na biyu. Omar kuwa, ya mayar da glass dinsa ya koma cikin falo.

Emir ya koma cikin falo ya zauna, amma da ya lura da kallon Aleena akansa, sai ya miƙe cikin nutsuwa, yana tunkarar ƙofar fita. Amma wannan karon, Aleena jikinta ya motsa kafin tunaninta ya fahimta. Ta taka zuwa gare shi, ta tsayar da shi kafin ya wuce.

Daga gefen ido Aleena ta ga Omar yana kallonsu, amma hankalinta dukka yana kan Emir kawai.

Aleena ta mika hannunta mai laushi ta rike hannun Emir. muryarta da kyar kamar rada tace, “Za mu iya magana?”

Emir ya tsaya kamar bai da tabbaci. Ya kwace hannuwansa suka haye saman kirjinsa, muryarsa cikin sanyi tare da gyada kai yace, “Game da me?”

Aleena ta ja numfashi zuciyarta tana bugawa kamar ƙaho.

“Game da mu, I miss you, Sweetheart,” Aleena ta furta hakan kafin tayi tunani kalmomin suka fito kafin ta kashe su. Da gaske nake. I miss you, fiye da yadda nake so in yarda.

Sannan, Aleena ta hango mahaifin mijin ta yana tahowa wajen Omar. Wanda yasa Omar yayi sauri ya kau da kallon sa daga garesu.

Emir bai ce komai ba. Bai motsa ba. Ya tsaya cak. Fuskarsa babu murmushi, Wani shinge ne tsakanin Aleena da shi wanda bata san yadda zata karya shi ba.

Aleena ta kalli Omar da mahaifinsa sau ɗaya kafin ta ja Emir a hankali, tana nuna masa hanya zuwa wata ƙofa agefe.

Sun fita zuwa ƙarƙashin bishiyar mangwaro, inuwa mai sanyi tana basu ɗan hutu daga rana mai zafi.

“Don Allah… Kayi mun magana.” Kalmomin kusan kamar rada suke cike da rawar jiki da buƙata.

Emir ya kyafta ido cikin mamaki yayin da yake daidaita hannayensa.

Aleena ta kai ga hannunsa yatsunta suna rawar jiki yayin da suke shiga cikin nasa.

Emir ya dan firgita kadan a ƙarƙashin taɓawarta tare da shiru mai nuna rashin yarda - amma bai janye ba.

Sai idanunsa suka kalli zoben auren. Fuskarsa ta canza, kuma nan take, ya janye hannunsa daga nata kamar an ƙone shi.

“Babu abin da za mu yi magana a kai, Aleena.” Muryarsa ta fito mai ƙarfi. Tare da haɗe hannayensa a jikinsa kamar wanda ke neman rike kansa.

“Wannan auren shirya shi akayi, Sweetheart,” Aleena tace, muryarta ta kasance a hankali amma mai ƙarfi. “Ban aure shi saboda ina so ba. Ban cin amanar ka ba.”

“Kinci amana ta,” Muryarsa ta fashe yayin da kalmomin suke fita daga bakinsa, “Kin cin amana ta, Aleena. Ko mene ne dalili, ko mene ne uzurin… Ke matar wani ce yanzu. Sai in har Omar ya sake ki, to shine za mu iya magana.”

Aleena ta sake kai gare shi hannunta yana girgiza yayin da take ƙoƙarin warware hannayensa, tana matuƙar son ta rufe tazarar da ke tsakaninsu. “Wannan auren nayi shi ne saboda granny kawai, Sweetheart-”

“Ki daina kira na haka, Aleena,” ya katse ta, muryarsa babu laushi cikinta. Ya janye hannunta a hankali da farko daga ƙarshe da karfi. “Ni dake bama tare yanzu.” Don haka don Allah ki daina kirana da wannan sunan. Ke matar wani ce yanzu.

Muryarsa babu fushi ciki, babu laushi, kawai baƙin ciki mai raɗaɗi, irin wanda yafi zafi fiye da fushi.

Lips in Aleena suka fara karkarwa. Baza ta iya riƙe ciwon da zuciyarta take ba, shakewa take a ƙarƙashin nauyin komai. Hawaye sun fashe suna zubowa kan fuskarta.

Emir ya dube ta, ya dan hade rai saboda ganin hawayenta, ya warware hannayensa kuma a lokacin ne taji kukan yana fitowa da karfi. Sa’an nan, duminsa ya rufe ta. Ya fara rada mata kalmominsa masu laushi a kunne, da kyar suke shigar ta yayin da take ƙoƙarin daidaita numfashinta.

“Ki shaki numfashi mai zurfi, don Allah…” Emir yace mata, ya ci gaba da shafa bayanta. “Fito da numfashi mai zurfi, Aleena…”

Bayan ’yan lokuta, Aleena taji kanta ya kwanta kuma ta rungumesa, ta nutsu cikin hannayensa. “Karka rabu dani,” kawai abin da ta iya faɗi ke nan. Ta riƙe sa tana kama jikinsa da ƙarfi.

Jikin sa ya ƙara matsewa a ƙarƙashinta muryarsa ƙarantacciya kamar nauyi ya murƙushe shi. "It's too painful... I can't." Aleena, “Har yanzu da zafi sosai…

Aleena ta ja baya kaɗan, hannunta suna rawar jiki yatsunta da kyar suke tsayawa yayin da take girgiza kai da gaggawa. “A’a, don Allah, kar ka bar ni. Ba na son kowa, ba wannan auren ba, ba Omar ba, ba kowa ba. Ina son ka zauna tare da ni. Don Allah… Ina son ka. Ba ni da kowa.”

“Me kike son ki faɗa min, Aleena?” Ya ce a hankali, bayan jinkiri. Ya dube ta. “Kina son in zauna tare da ke, kamar ba abin da ya canza, ko ba haka ba? Amma gaskiya ita ce komai ya riga ya lalace. Kin kuwa ma san hakan?”

“Na san abin da nake yi. Ta faɗa, amma ita kanta bata fahimci abinda take fada ba. I love you, amma na rasa ta inda zan fara gyara komai, Don Allah, ka bar ni in zama mai son kaina na ɗan lokaci. Don Allah, Emir ina buƙatar ka, yanzu, fiye da kowane lokaci.”

Emir ya tsaya a nan, ya daskare. Bakinsa ya buɗe kaɗan, amma babu kalmomin da suka fito. Ya girgiza kansa a hankali, nauyin komai yana matse shi. Yace, “Ban san abin da zan ce ba kuma-”

“Ba ka sona yanzu?” Ta katse shi,“Ka faɗa min. Don Allah… har yanzu kana sona? Za ka jira ni? ko na ɗan lokaci kaɗan. Please.”

Fuskarsa ta canza ya dan hade rai kadan cike da rudani yace, “Jira?”

“Wannan auren ba zai daɗe ba. Zan nemi Omar ya sake ni. Ko wane sharuɗɗai ne na cika burin granny, amma wannan ba ya nufin dole in tsaya cikin aure da wanda ba zan iya jure shi ba. Ban damu da rasa Khan Electronics ba, Sweetheart. Ban taɓa damuwa ba. Amma kai… Ina buƙatar ka jirani, ka tsaya. Na san ba adalci ba ne, na san yana da zafi. But please wait for me, zan dawo gare ka. Ban san ta yaya ko yaushe ba, amma ina buƙatar ka jira ni,” Aleena tace murya cikin ƙarfi.

Wannan shine gaskiya…duk da ita kanta batada tabbacin hakan, bawai don tana jin tsoron rasa Khan Electronics ba, amma sede saboda bata san taya ma zata iya fara tunkaro Thorne Family da wannan zancen ba, ko Omar kansa.

Musamman, saki.

Amma a yanzu komai bashi da mahimmanci agunta. Ba halin da ake ciki ba, ba auren ba, Kawai tana buƙatar Emir ya amince da ita. Tana buƙatar ya dawo gareta.

Sauran? Zata gano su daga baya.

“Har yanzu ina cikin zafin zuciya mai radadi kuma, amma har yanzu ina son ki sosai… Don haka Kin tabbata da abin da kika faɗa, Aleena?” Emir ya tambayeta, muryarsa tana rawar jiki da cakuɗar zafi da mika wuya. Aleena tana iya ganin bangon da ke idanunsa ya fara fashewa, amma bai barta taga fiye da hakan ba.

A karon farko, ta ji nauyin dake kanta ya sauƙa kaɗan.

Ya yi laushi kaɗan.

Ta gyada kai. “Eh.”

Sai shima ya gyada kai a hankali, idanunsa cike da rashin tabbas. “Ban san ta yadda wannan zai yiwu ba. Ba game da ko jira ba, amma… Za ki zauna cikin gida ɗaya da Omar, tabbas. Mahaifiyarsa ma ta faɗa min a kwanakin baya, sanda muka yi magana, cewa sun siya muku sabon gida. Baza suyi miki da sauki ba, Aleena. Suna da abin da suke tsammani.”

Aleena ta tsaya na ɗan lokaci. Batada labarin sabon gidan. Gaskiya tana buƙatar tayi magana da Omar nan ba da jimawa ba, duk da cewa tunanin yin magana da shi ya riga ya sa taji wani irin takaici.

“Sweetheart. Ka saurare ni.” A ƙarshe ta yi magana, muryarta ta kasance a hankali amma mai ƙarfi. “Wannan auren na granny ne kawai. Ba zan taɓa zama tasa ba. Har yanzu taka ce ni gaba ɗaya. Zan tabbatar da haka. Ko da muna zaune cikin gida ɗaya, ka yarda dani. Babu abin da zai faru tsakanina da shi. Na tsane shi sosai.”

Emir ya ja numfashi sosai, sannan ya share makogwaronsa, ya juyar da fuska na ɗan lokaci. “Na yarda da ke. Amma ban yarda dashi ba.”

Aleena ta ɗaga gira. “Saboda ba mutumin kirki bane shi?”

Emir ya sake kallon ta, amma a wannan karon akwai wani abu a idonsa. “Ina jin wani abu,” ya ce, muryarsa ta ragu, “ina jin… Ban sani ba. Kawai…”

Aleena ta saki baki cike da ruɗewa. “Me kake nufi, Sweetheart?”

Ya ja numfashi, idanunsa cike da rashin tabbas. “Kawai ina jin tsoron cewa ke da shi za ku iya fara san juna.” Aleena ta buɗe baki don ta yi magana, amma bai gama ba. “Baza ki sani ba. Tunda har yanzu baku fara zama tare ba, kinga kawai ina anfani da hankalina ne, Kina da kyau, Aleena. Kuma Omar…” Emir ya tsaya. “Yana da kyau mata ma jefa kansu suke gareshi.”

Aleena tayi wata yar dariya karama mai takaici. Tace, “Don Allah kar ka faɗi haka. Don Allah! Ba zan taɓa ba. Ta damke zuciyarta, Sweetheart. Ni. Ba. Zan. Taɓa. So Omar Thorne ba.”

Emir ya dan cukule ya fada a ƙarƙashin numfashinsa da kyar ake ji kamar har yanzu bai yarda ba. “Allah yasa.”

“Sweetheart, please. I love you. Sau nawa zan ce maka hakan? Don Allah, ka yarda da ni-”

Aleena tana shirin cewa wani abu, sai daga kusurwar idonta, ta lura da mahaifiyar Omar tana matsawa zuwa kusa da ƙofar da ita da Emir suke tsaye. Tana magana da wani. Aleena tayi shiru tana juyawa tayi ido biyu dashi da sauri ta kau da kai.

Omar.

Ya kalle ta, kuma na ɗan lokaci kaɗan, idanunsu suka kara haɗuwa. Amma wani abu ya bambanta a kallonsa. Babu laushi ko tausayi kamar kwanaki sha hudu da suka wuce.

A’a, ya yi tsauri. Mai kaifi. Da sanyi.

Aleena ta ji kamar kallonsa yana yanke ta, taji kamar ta daskare, Omar ya rike ta da wani kallo wanda yasa taji gaban ta yana fadi na rashin dalili.

Yayi sauri ya wuce gefen Mommy wacce ta bi shi kamar inuwa.

Omar ya ji komai. Kowace kalma guda. Omar ya ji dukkan maganar su.

Tambayoyi sun taso a ran Aleena yayin da take kallonsa yana tafiya nesa. Meyasa Omar yake kallon ta haka? Meyasa kallonsa take jinsa kamar keji? Kuma Don meysa zai tsaya sauraron zancen ta da Emir? Meyasa ya damu?

A’a. Dole ya shirya wani abu. Kuma tana jin hakan.

Tasan halin sa bazai bar abinda yaji ya wuce haka kawai ba. Tana bukatar tayi wani abu akan hakan.

Sulhun da ke tsakaninsu da rashin shiga rayuwar juna tun bayan rasuwar granny taga alamar ya fara karyewa, kuma daman tasan Omar sai ya nemi wata hanya don karyawa.

Wani sanyi mai tsoro ya gangaro cikin kashin bayanta yayin da take tsaye a daskare a nan, tana kallonsa yana tafiya, tana jin kamar tazarar da ke tsakaninsu ta zama mai haɗari sosai ba zato ba tsammani.

Bata san dalili ba, kuma bata san taya zata fada cikin kalmomi ba, amma koma mene aran sa tasan yana tare da rashin kwanciyar hankalin ta sosai.

💘AUREN ALEENA💘

Amal Musa ✍️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.