Complete Hausa Novels

Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel

Reading file: Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel.docx

Chapter 12 of 28

Chapter.1️⃣2️⃣ Mrs. Aleena Ali Thorne. 👰🏽‍♀️🤍

SHARE SHARE SHARE 💃💃💃💃💃

Hasken fitilun injunan asibitin suna kyalli da ke bada haske mai tsoro a kan gwangwanin Monster Energy lemon da ke cikin hannun Omar. Ya dan kurbi kadan, dacin lemon ya sare makogwaronsa da kaifi da zafi—kamar yadda rikicin da ya fada a daren nan ke ci masa zuciya.

Ba don yana jin kishirwa ba. Bai ma damu da lemon ba; kawai ya rike shi ne saboda yana bukatar wani abu da zai riƙe—a daidai lokacin da yake jin kamar komai a rayuwarsa yana zamewa daga yatsunsa.

Ya matse gwangwanin ba tare da ya sani ba, gabobin yatsunsa suka yi fari daga karfin daya sa. Aluminum din ya murkushe da sauri, amma matsar da ke cikin kirjinsa bai sauƙaƙa ba.

Yau rana ce da ta rusa duk wani mafarkin cewa yana da iko akan rayuwarsa, kuma yanzu dole ne ya fuskanci wannan rikici tamkar mai kallo a cikin labarinsa.

Bai san inda Aleena da Emir suka tafi ba. Amma a yanzu, ko kadan bai damu ba. Saboda Omar ji yake komai yana rugujewa ne a kewaye dashi. Komai yana juyawa - da sauri, da yawa. Yana jin guguwar motsin zuciyoyin da suke bugawa daga kowane kusurwa.

Bai yi tsammanin wannan ba.

Bai yi tsammanin zai tsaya a nan ba, a cikin asibiti, yana jiran wannan wasan kwaikwayon na aure ya faru kafin tsohuwa ta ja numfashinta na ƙarshe ba.

Ya damke idanunsa yana cewa kansa;

Wannan ba game da kai ba ne, Omar.

Kuma yasan hakan.

Yasan wannan ba game dashi ba ne.

Wannan game da kakar Aleena ne, game da burin ta na ƙarshe, game da tabbatar da cewa Aleena ta sami wanda za ta dogara dashi lokacin da ta tafi.

Omar sai yaji shi, taɓawa mai ƙarfi akan kafaɗarsa.

Baya bukatar ya duba, yasan wane ne. Kasancewarsa ko yaushe yana da hanyar tilasta kansa acikin waje, kuma koda yaushe yana jinsa a waje kafin ya yi magana.

Papa.

Omar ya ja numfashi yana tilasta yanayinsa ya zama mara nuna damuwa, Amma Papa ya sani. Ko yaushe ya sani.

“Tunda za mu yi hakan,” ya ce, muryarsa a ƙasa a tsaye, “Toh dole mu yi shi da kyau, Omar.”

Omar ya kyafta ido yana ƙoƙarin girgiza zafin da ke cikin kwakwalwarsa.

“Me kake nufi Papa?”

Papa ya kalli zuwa corridor da ke kai dakin kakar Aleena. Idanunsa suka daɗe a can, cike da wani abu mara iya karantuwa, kafin ya juyo ya fuskanci Omar.

“Yanzu na gama waya,” ya ce a sauri.

Omar yana fama da fahimtar kalmominsa lokacin da nauyin su ya buge shi kamar babbar mota. Cikinsa ya fara juyawa.

Ya dubi agogonsa. 10:25 PM.

“Papa wai da gaske kake?” muryarsa ahankali da kyar ta fita kamar rada. “Ba dole bane muyi hakan yanzu yanzu ba, Papa. Kuma dare yayi ma. Za mu iya musayar alkawari kawai, kai da Mommy za ku zama shaida. Gobe sai mu halatta shi a masallaci. Don Allah Pa…”

“A’a.”

Amsar Papa a tsaye cike da yanke hukuci.

“Na aika direba ya dauko Imam Qazi da mutane biyu shaida su zo yanzu,” ya ci gaba. “Wannan ba abu mai wahala bane bare idan kasan mutanen da suka dace.”

Ya ja numfashi da ƙarfi. “Wannan ba don show ba ne, Omar. Muna magana game da Sunnah… Aure. Idan za mu yi shi, Toh lalle zai zama na gaske.”

Na gaske.

Kalmar ta zauna kamar guba acikin kirjin Omar.

Ya kamata ya yi gardama. Ya kamata ya yi musu da shi game da hakan. Ya kamata ya ce a’a.

Amma bai yi ba.

Saboda Papa ba irin mutumin da ke barin abubuwa rabi da rabi bane. Kuma a Turkey, idan kana da haɗin gwiwar da ta dace, Toh abinda ba zai iya yiwu ma ba yana yiwuwa.

Yanzu, so yake ya tabbatar da cewa wannan auren ba kawai kalmomi ne da aka furta a dakin asibiti agaban tsohuwa mai shirin mutuwa ba.

Yana mai dashi ne halal na har abada. Babu hanyar fita.

Yana jin kallon Papa akansa cikin shiru amma mai ratsa rai.

Sai Papa ya sake magana muryarsa a nutse amma ko da yake akwai gaggawa a cikin ta. “Mahaifiyar ka zata dawo nan bada daɗewa ba. Ta tafi gida ne. Don ta shirya kawo kayan da Aleena zata canza da kai da kuma za ta kawo sadaki da zoben da kakannin ku suka ce abaku. Omar nasan wannan ba kamar yadda ya kamata bane.” Papa ya dan dakata kallonsa ya tsananta yayin da ya haɗu da idanun Omar.

“Tafi ka nemo Aleena. Kakarta tana nemanta.”

Bai jira Omar ya ce komai ba. Ya tafi kawai, kamar an riga an yanke hukunci. Saboda an yi.

Ya tsaya yayi shiru nawani dan lokaci yana jin nauyin komai da yake rufewa akansa.

Komai ya riga ya ruguje.

Amma dole ya kammala aikin da Papa ya basa. Don haka, ya jefar da gwangwanin lemon cikin shara, ya mike kafaɗunsa ya ja numfashi na ƙarshe don karfafa kansa game da abin da ke gaba.

Shima baya son yin abun nan. Bai son komai daga cikin wannan hadin. Amma ba shi da zaɓi.

Kuma yanzu task din sa Papa ya fada masa a bayyane - ya tafi ya nemo matarsa wadda ba shakka yanzu haka tana cikin zance mai raɗaɗi, mai zafi tare da mutumin da take yiwa so na gaskiya.

Ya cusa hannuwansa cikin aljihunsa ya bar corridor.

Lokacin buga nashi role din yazo ko yana so ko baya so. Duk da bai san me zai faru ba. Amma ya san abu ɗaya - wannan ba zai ƙare da kyau ba.

Don wasu dalilai, ƙafafunsa suka kai shi baya zuwa matakalar gaggawa - inda Aleena ta gudu lokacin da ta fara jin maganar auren su da aka shirya.

Omar yana buɗe ƙofar sai ya sankare yayin da ya ji ihun muryoyi biyu cike da zafin zuciya. Ya gane muryoyin nan da nan.

Ya kalli ƙasa ya gan su, sun tsunduma cikin fada mai tsanani da sautin da ke cikin muryar Emir Batuhan - wanda bai taɓa ji ba. Sannan Aleena Khan kukanta ya karade matakalar.

“You have one week! Aleena kina da sati daya amma baki gaya min ba!” muryar Emir yana rawa cikin fushi. “Amma kika zaɓi ki ɓoye min!”

Omar yana ganin Emir yana ƙoƙarin ’Kwace hannunsa daga rikon da Aleena take kai masa.

“Don Allah, kawai…”

Omar yasa tafin hannunsa akan karfen benen, jikinsa ya tsaya cak. Ya kamata ya tafi. Ya kamata ya tsaya nesa da su. Amma ya kasa. Kallon su - kallon su haka - ba abinda ya yi tsammani bane. Ya ji kamar yana kallon wani bangare a cikin film din da bai kamata ya gani ba, duk da haka, ya kasa iya cire idonsa daga kansu. Ya tsaya a sankare, Ya kasa iya ko motsi balle ya bar wurin.

“I just proposed to you, Aleena,” muryar Emir ta karye da tsananin bugun zuciyarsa. “Jiya na nemi auren ki!” Aleena shiyasa kika ki?

Idanun Omar suka kara budewa. Yaji ya kasa iya numfashi. Emir ya yi wa Aleena proposing? Ya dafe kansa yana jin nauyin lokacin yana shiga cikin sa.

’…kuma kika zauna kawai, A nan kina kallona! Baki ce min komai ba!” Emir ya dakata, muryarsa ta shake da kuka. Omar yaga Aleena tana ƙoƙarin rungume shi, amma Emir ya ci gaba da jan baya, hannuwansa suna ture ta.

“I’m so sorry,” Aleena ta rada, muryarta cike da azaba. “Banyi nufin hakan don… I… I love you.”

Shiru mai nauyi ya rataye a iska, ya tsawaita cikin matakalin gaggawa.

Abinda kadai ake iya ji shine numfashi masu tsanani da karar bugun zuciya masu ciwo.

Omar ya makale tsakanin son ya rarrashe su da kuma son ya bar wannan rikicin da bashi da hannu a ciki.

“It doesn't matter anymore,” Emir ya sake magana, muryarsa tayi kasa kamar babu komai cikin ta. “Yanzu dole ki auri Omar. Mun gama nida ke daga nan, Aleena. Ba zan iya ba… ba zan iya kasancewa a nan dake ba. Dole in tafi.”

Ya janye jikin sa daga hannun Aleena. Aleena ta fadi ƙasa kukanta ya kara tsananta.

Kallon Omar ya hadu da Emir yayin da ya fara hawan matakala. Idanunsa - cike da fushi, cin amana, da baƙin ciki tsananin kallonsa ya kona Omar.

Ya matso kusa, ’yan inci kawai yanzu tsakanin su idanunsa suna cike da zargi. Omar bai girgiza ba. Suka rike kallon juna cikin shiru, kowannen su yaki kau da kai.

Emir ya ɗaga hannu, Omar kuma ya yi tunanin zai mare sa. Amma a’a. Maimakon haka, hannuwansa suka taɓa kafaɗar Omar ahankali. Sai ya ce. “Yaya zaka sake yi mun haka na biyu kenan, Omar? Emir muryarsa yana karyewa.

Omar ya ja numfashi da ƙarfi, yana jin wani abu yana murɗewa a cikin sa.

Daga gefen idonsa, ya ga Aleena ta mike daga kasa a hankali motsin ta mai rauni yayin da take tahowa gare su. Omar ya fada ahankali da kyar kusan rada, “Ban taɓa yin tsammanin wannan ba. An rubuta shi tun muna yara. Idan kana tunanin ina son wannan, to ba ka sanni bama, Emir.”

Idanunsa suka yi duhu. “Ta yaya zan sake yarda da kai Omar? Bayan abin da ka yi min shekaru 10 da suka wuce. Ta yaya zan yarda da kai? Ban taɓa ƙin ka ba ina ganin ka kamar ɗan’uwana kanina Omar amma… ya kasa ƙara magana.” Muryarsa ta matse, kalmominsa masu daci. “Amma a yanzu, kai ne wanda na tsana fiye da komai. Fiye da duk wannan lamari.”

Emir ya sauke hannunsa daga kafaɗarsa, ya juya zuwa ga Aleena tsayuwarta cikin ciwo.

“Ba zan iya hana ka daga tsanata ba,” Omar yace, muryarsa yanzu kusan kamar cikin nadama. “Ba sabon abu bane.

Mutane sun tsaneni a baya.”

“Wannan zantukan suna sani ciwo,” Emir ya rada a ƙarƙashin numfashisa, yana damke hakoransa da ƙarfi da har kusan gogan juna suke.

“Nima haka,” Omar yace a ƙarshe. Ya juya zuwa Aleena, muryarsa atsaye. “Kakarki tana nemanki.”

Ba tare da wani kalma ba, ya juya ya tafi, ya bar matakalan gaggawan abayansa. Amma ko da ya tafi nauyin kalmomansa da siffar karyewar fuskarsa ta kasance tare dashi.

Ba zai iya tserewa daga gaskiyar komai ba.

Omar yace, Da kyau. Ya kara samun wani wanda ya tsaneshi, Wataƙila yanzu zai iya cike shafi na ɗari da yawan mutanen da suka tsane shi.

Iskar asibiti tana da kauri, tana matsawa - ba kawai da kamshin magani ko injinan da ke yin sauti ba, amma da wani abu daban. Da wani abu mai sarke numfashi.

Kakar Aleena ta farka amma da kyar. Yatsunta suna rawar jiki, numfashinta yana da laushi, kuma jikinta yana da rauni - duk da haka hankalinta yana tsayin daka, kamar yadda yake.

Aleena tana tsaye kusa da ita kamar gunki, fatarta ta shuɗe, lips din ta sun bude cikin mamaki, amma bana gardama ba. “Karfin granny da ke raguwa yana rataye a kanta. A sake tsara dakin.”

Mommy ta dawo da wata ’yar akwatin karammiski. Ta ajiye su a teburin gefen gado, granny tana kallon shirye-shiryen. “Good,” ta ce a hankali, Numfashinta yana fita a hankali da wahala amma tsayayye.

Zoben aure. Da wasu tufafi don Aleena da Omar, suka shiga ɗaya bayan ɗaya suka canja tufafi, kuma mommy ta taimaki Aleena ta sa doguwar riga da doguwar lullubi da ta rufe fuskarta.

“Kun yi kyau.” Granny tace ahankali.

Omar ya haɗiye, da karfi. Kirjinsa yaji yana matsewa.

Kofa ta sake buɗewa.

Wani tsoho sanye da farar tufafi da hula a kansa ya shigo ciki.

Imam Qazi tare da mutane biyu tare da shi.

Aleena dake kusa da Omar, ta girgiza yatsunta suna motsi a gefenta. Ta juya ga Omar, muryarta da kyar akeji.

“Kai… da gaske ka?-”

“Papa ne ya kira su,” Omar ya katse ta, amma kalmomin sun buge shi. “Shi ya shirya komai.”

Aleena bata amsa shi ba. Ta fitar da numfashi cikin rawar jiki, kafadunta sun matse.

Imam Qazi da zarar ya shigo Papa ya sunkuya domin gaisuwa ya ba su kujeru, Mommy ma ta gaishe shi yayin da ta ja gefe. Imam Qazi ya sunkuya da kansa kadan a gefen gadon kakar Aleena. “Za mu fara,” ya ce cikin nutsuwa. “Saboda yanayin lokaci.”

Papa ya juya zuwa ga Imam Qazi. “Mu fara.” Yace.

Ya nemi sunayensu, ya tabbatar da cewa sun shiga wannan haɗin da son ransu.

Sai yara da; Iyalan Mehmet Thorne da Ali Khan sun yarda da wannan aure, kuma miji da mata ma sun yarda da wannan aure, kuma ga shaidu biyu don wannan aure, kuma mahr yana shirye.

“Bismillahir-Rahmanir-Rahim. Zamu fara da daurin aure bisa sunnah da shari’ar Musulunci. Aure ibada ne, shi ne ginshikin zaman lafiya da rayuwar al’umma. Ma’aurata su kasance masu biyayya ga juna, da tsoron Allah.”

“Waliyyin amarya Mehmet Thorne, ka yarda in daura wannan aure tsakanin wannan bawan Allah Omar Thorne da wannan baiwar Allah Aleena Ali Khan akan mahr ɗin da aka ambata?”

“Eh na yarda” Papa ya ce.

“Kai Omar Thorne ka yarda da wannan aure da wannan baiwar Allah Aleena Ali Khan da aka baka a aure?”

Omar ya yi shuru, idon papa ya kalle shi sai cikin sanyi ya ce “ehh na yarda.”

An tambayi Omar sau 3 kuma ya ce eh.

“Shaidu, kun ji da kunnuwanku?”

“Eh, mun ji.”

Imam Qazi ya ce Omar ya ɗauki hannun Aleena.

Hannun Aleena yayin sanyi lokacin da Omar ya kama yaji kamar kankara.

Akwai shiru. Sannan…

Imam Qazi ya ce, Omar za ka maimaita bayan na.

Muryarsa ta fada cikin shiru da farko. Sai yace,

“Ni, Omar Thorne, na ɗauke ki, Aleena Ali Khan, zaman matata ta halal. Don tsayawa kusa da ke, don kare ki, don girmama wannan alkawari. Don riƙe alkawarin dana yi a yau.”

Imam Qazi na gaba ya ce maimaita bayanni ya kalli Aleena;

Aleena ta ja numfashi da karfi, numfashinta yana rawar jiki. Idanunta sun yi kyalkyali da wani abu - tsoro, nadama, ko kuma kawai nauyin komai.

Muryarta ta yi rawar jiki lokacin da ta yi magana, amma ta yi magana. “Ni, Aleena Ali Khan, na ɗauke ka, Omar Thorne, zaman mijina na halal. Don cika duk wani hakki naka… da kuma girmama alkawarin dana dauka.”

Aka shafa FATIHA…

Makogwaron Omar ya matse.

Mahaifiyar Omar ta matsa gaba, akwatin karammiski ta buɗe a hannayenta. Ta ciro zoben - masu kyau na zinari.

Lokacin da ya ɗauki zoben - lokacin da ya zura shi a yatsan Aleena mai rawar jiki - kuma lokacin da itama tayi mishi hakan…

An gama. An rufe. An kammala.

Imam Qazi ya ajiye mahr a gaban Aleena da dukan shaidu biyu.

Sannan ya ce; “Alhamdulillah. Aure ya kammala. Allah ya sa albarka. Allah ya baku zaman lafiya, ya baku zuriyya ta gari.”

Kakar Aleena ta fitar da numfashi a hankali, idanunta suna kyalkyali da wani abu mai zurfi. Wani abu mai farin ciki.

Ta miƙo hannu ta rike hannayensu, ta matse da rauni, murmushi mai laushi a lips din ta.

“‘Ya’yana yan Albarka,” ta rada, muryarta ta cika da soyayya da farin ciki. “Kun yi kyau.”

Aleena ta ja numfashi da karfi tana shanye kukan dake fitowa.

Sannan, granny ta juyar da kallonta zuwa Omar.

Ta yi murmushi, mai rauni amma da dumi, kuma a wannan lokacin, ya ji kamar duniya ta tsaya na ɗan lokaci.

“Ka kula mun da Aleena, Omar.” ta rada, muryarta mai rauni amma a fili.

Numfashinsa ya makale a makogwaronsa.

Yatsun Aleena suka yi motsi a cikin hannun Omar dake damke dana granny, kuma a wannan lokacin, Omar ya kasa iya ganewa shin yana yin hakan don kansa ne, ko don alkawarin da yayi wa kakarta?

Amma ba tare da ya fahimci dalilin ba, ya gyada kai.

“Zan yi.”

Yayin da kalmomin suka bar bakinsa, sai ji yayi kamar duniya ta riƙe numfashin ta.

Shirun dakin yayi kauri, kamar iskar ita kanta tana jiran wani abu ya faru, tana jiran wani abu ya karye.

Cikin mintuna hannun kakar Aleena mai rauni wanda ya riƙe nasu ya zame kasa.

Idanunta wadanda suka kyalkyal da farin ciki nan da nan suka rasa hankali.

Kirjinta wanda ya kasance cikin wahala don tashi da faɗuwa ya tsaya.

Murmushin ta ya shuɗe, sannan kuma ɗan dumin da ya kasance a can ’yan mintoci da suka gabata ya mamaye da sanyi.

Injinan da ke yin sauti wadanda suka zama akai-akai, Basu sake yi ba.

Omar yaji yatsun Aleena suna rawar jiki a hannunsa, amma lokacin da ya dube ta, ta riga ta sunkuyar da kanta, jikinta yana rawar jiki, numfashinta yana zuwa cikin kuka mai tsanani. Omar ya kasa iya jan ta gare shi, ya kasa iya rarrashin ta kamar yadda yake so yayi, Saboda shima ya sankare. wannan duk yana faruwa da sauri sosai. Kwatsam. Kuma basu shirya ba.

Babu ɗayansu da ya shirya.

Kakar Aleena ta bar su.

Haka kawai.

Omar yaji mommy ta ja numfashi da karfi kusa da shi, nutsuwar sawukan ƙafafu na Papa yaji ya jingina gaba, fuskarsa ta murɗe cikin wani abu mai ciwon rai.

Amma Omar bai iya cire idonsa daga kan Aleena ba, wacce yanzu kukan ta ke karuwa cikin sauti mai radadi da ratsa zuciya. Kukan yafi karfin kirginta da yake fitowa.

Duniyarta ta farfashe.

“Granny…” Aleena ta rada tsakanin ja numfashi da kyar, muryarta tana karyewa.

Omar ya kasa iya magana. Makogwaronsa ya matse, kirjinsa ya cika sosai.

Imam Qazi, wanda ya kasance tsaye shiru kusa da su, ya ce “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.” Yayin da ya fara matsawa kusa da ita ya rada wasu addu’o’i a kunnenta. Ya ja taki da shakku ya koma. Ya tafi saboda lokacin ya yi nauyi sosai. Babu sauran alkawari da za a yi yanzu, sai zaman makoki.

Ba da daɗewa ba, doctor da ‘yan ma’aikatan jinya suka shigo, amma Aleena ba ta motsa ba, ko da yake suna kokarin cire hannayenta a hankali daga gawar kakarta.

“Fita da ita waje,” Mommy ta ce a hankali.

“Aleena,” Omar ya rada, muryarsa tana rawar jiki. Ya kara matsa gaba, ya miƙa hannunsa gare ta, amma ta janye daga gare shi.

“A’a, ni… Bazan... Bazan iya barin ta ba,” ta ce cikin numfashi da kyar, muryarta ta cika da bakin ciki, hawaye suna shafe kalmominta. “Ina bukatan zauna tare da ita. Bazan iya barin ta ita kadai ba.”

Omar ya san wannan ba lokacin bin ta da kalamai a hankali ba ne. Tana bukatar fiye da kalmomi; tana bukatar ya taimaketa ta tsere daga tashin hankalin cikin dakin nan.

Yana kusa da ita yanzu, muryarsa a tsaye amma a hankali. “Dole ne ki zo tare da ni.”

“A’a,” ta rada da tsanani, jikinta yana girgiza don bakin ciki. “Bazan bar ta ba, Bazan bar ta ita kadai ba.”

Ya sake miƙa hannunsa gare ta, wannan karon ya kama hannayenta da karfi fiye da yadda yayi niyya. “Don Allah, Aleena,” ya ce, muryarsa ta cika da damuwa cikin matsanancin bukata. “Dole ne ki sake ta.”

Idanunta suna budewa, cikin tsoro - sun cika da hawaye, Hannayenta suna rawar jiki yayin da suke riƙe gefen gadon, dukan jikinta yana rawar jiki, tana kokarin riƙe kadan na duniyarta da ya rage.

Amma Omar bai sake ta ba.

A hankali, a hankali, ya janye ta daga gadon, ya kai ta zuwa kofa. Taki yarda da farko tana jan baya da kowane taki, amma nauyi da bakin ciki ya mamaye ta ya fi karfinta baza ta iya gardama da Omar ba.

Har yanzu, bai tsaya ba. Ba zai iya barinta ta nutse cikin wannan shirun da ke shake numfashi ba. Don haka, ya ci gaba da tafiya da ita ajikinsa.

Ta kara fashewa da kuka tana fada kusan cikin rada, "I can't. I can't leave her, Omar.”

Omar ya nannade hannayensa akanta, yana jan ta kusa jikin shi har suka fita daga dakin. Aleena ta riƙe shi kamkam da karfi, ta manne kanta jikin sa kamar zai iya kare ta daga tashin hankalin.

Omar bai san dalilin da yasa yake yin hakan ba, amma yaji wani abu a cikin sa ya fashe. Kuma ya rasa inda hankalinsa ya tafi ya manta da ƙiyayyarsa da ƙyamar da yake ji mata.

Abinda ya sani shi ne Aleena ta karye, ta farfashe gaba ɗaya saboda ta rasa wacce ta fi so duk duniya. Omar yasa hannunsa yana shafa bayanta, yana jin rawar jikin ta kamar igiyar wuta.

Dukka su biyun basu ce komai da juna ba.

Amma Omar yaji yatsun Aleena sun matse kewaye da rigar sa, kukan ta yana shiga cikin kirjinsa, ya kasa iya jure sautin zafin kukan ta. kuma yana jin rigar sa tana jiƙewa yayin da ta danna fuskarta cikin kirjinsa.

Kukan Aleena ya cika hallway din, sautin sa yana amsawa a cikin sararinsu yayin da ta kara dunkulewa a jikin Omar, hannunta kamar baƙin ƙarfe a kugunsa. Omar ya riƙe ta sosai, saboda yasan cewa babu wata magana da zai sauƙaƙa mata zafi da radadin da takeji, kuma babu abin da zai iya yi don ya kawar mata dashi.

Amma sai kallonsa ya juya.

Omar ya gan shi.

Emir.

Ya jingina da bango, ’yan taki daga gare su.

Ya haɗa ido da shi, kuma wani abu ya murɗe a kirjin Omar, ya kasa iya juyar da idonsa, Idanunsa sun yi duhu da wani abu ciwo, zafi, da bakin ciki. Da kyar yake riƙe kansa, kuma Omar shima yana jin nauyin hakan.

Emir ashe har yanzu yana nan. Bai tafi ba. Kuma ya ji komai. ya san yanzu Aleena matar Omar ce. Ya ji Aleena ta karbi auren kuma ta dau alkawari.

“Ta tafi, Omar! Granny ta… ta tafi!” Aleena ta shaƙe a rigar Omar, ta riƙe shi da karfi sosai, kalmominta suna fita cikin kuka.

Omar ya kwantar da hannunsa zuwa bayan kanta, yana shafa gashinta a hankali, dayan hannunsa yana riƙe ta kusa sosai.

Sannan, saboda wani dalili da Omar bai sani ba, ya sunkuyar da kansa yayi wa Aleena kiss acikin gashin ta da saman fuskarta, yayi hakan ba tare da kalmomi ba. Amma yayin da yayi hakan, kallonsa bai bar idon Emir ba.

Sannan, Emir ya juya.

Ya tafi takunsa a hankali wanda ko waiwaya bai ba.

A/N: Allah yaji kan granny 💔💔🥹🥹 yasa ta huta

💘AUREN ALEENA💘

Amal Musa ✍️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.