Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel.docx
Chapter 6 of 28
Chapter.6️⃣ Yarjejeniyar Da Aka Ɓoye 📜🔐
“Madam Aleena, baza mu iya yi ba. Sai dai idan mun ƙara ma'aikata aƙalla 20 da ƙarin injuna 5..."
Lumshe idanuna na yi yatsuna na danne gefen goshina ina ƙoƙarin takaita ciwon kai da ke tunkaroni. Adnan, shugaban ma’aikatan masana’antar, ya cigaba da bayanin sa mai tsawo wanda yanzu kalmomin sa sun fara dushe min a kunne.
Awanni biyu.
Awanni biyu na cike da gajiya da nauyi. Ni da Mariam mun shafe su a masana’antar Khan Electronics da ke gefen garin Bursa, muna fafutukar warware matsalolin samar da kayayyaki.
Jiya Leila ta kammala kididdiga. Sakamakon ya bayyana karara: ba zai yiwu ba.
Yanzu haka tana wata ganawa da wata masana’anta ta daban wata daga cikin abokan hamayyar mu don ganin ko za mu iya ba su aikin ta hanyar haya. Mataki ne mai haɗari, amma dole ne mu gwada.
Amma tambayar nan ce ke birkita ni: za su iya cika ƙa’idar ingancin Khan Electronics kuwa?
Allah ya kare kada ɗan rainin wayon nan ya gano wata matsala ta inganci saboda sai ya koma bala’in da ba a so ba.
Adnan na kallona a bakin table fuskarsa cike da damuwa. “Yaushe zamu yanke hukunci Madam Aleena? Mu ci gaba da wannan bisa ƙarfin da muke da shi… ko kuwa, Ya dakata, yana barin sauran magana cikin sarari tsakaninmu yana jiran yanke hukuncin daga gare ni.
Mariam ta rankwafa kadan, tana danna gwiwata da yatsa.
“Yaya kike gani?”
Na sauke numfashi da nutsuwa, ina gyara zamana, sannan na ce “Ci gaba. Ku tafi da ƙarfinku na yanzu, amma ku bada damar karin lokacin aiki (overtime) ga duk wanda ya amince. Babu hutun aiki na tsawon wata biyu masu zuwa. Kuma za a biya su ninki biyu na albashin overtime.”
Idanun Adnan suka faɗa. “Madam Aleena? Ninki biyu?
Wannan… mai yawa ne. Ai ko da yanzu albashin overtime ɗinmu yana cikin mafi girma a fannin masana’antu.”
Ina kallon sa kai tsaye da tsantsar nutsuwa. “Ina buƙatar raka’a fiye da 300 a rana.
Idan muka cimma hakan, duk kuɗin da aka kashe zai dawo da riba.”
Na juya zuwa Mariam.
“A sanar da sashen kuɗi. Su shirya tun daga yau.”
Mariam ta gyada kai tana rubuce-rubuce a cikin tablet ɗinta.
Na kalli Adnan.
“Shikenan. Ka sanar da ma’aikatanka yanzu.”
Adnan ya miƙe tsaye, yana haɗa tafin hannuwansa cikin girmamawa, sannan ya ɗan rusuna.
“Nagode, Madam Aleena.”
Na amsa da ɗan gyada kai, sannan na tashi na fice daga ɗakin ganawar, Mariam tana bin bayana a hankali.
Na jingina da kujera cikin mota, ina kallon fitattun titunan Bursa daga window. Hayaniyar gari na ci gaba da tafiya amma a cikin motar, shiru ne ya lullube mu.
“Aleena…” Mariam ta fasa shiru, muryarta da rauni.
Na humma kadan, ba tare da na juya ba.
“Kin ɗauki shawarar da ta dace. A yanzu, akwai yiwuwar mu haura raka’a 300 kullum. Ragowar na hannun Leila.”
Na juyo kaɗan, ina kallon ta da nutsuwa.
“Wannan shine mafi sauki. Ƙara ma’aikata da injuna zai fi mana tsada fiye da overtime.”
Ta gyada kai, tana cigaba da rubuce-rubucenta a tablet.
Sai wayata ta fara ƙara.
Na fiddo da ita cikin jakata, na kalli fuskar wayar.
“Granny?”
“Yar albarka,” muryarta mai taushi tana amsawa. “Zaki iya zuwa asibiti yanzu?”
Numfashi ya tsaya min. Na juya gaba, na dubi direba da gaggawa. “Ka juya. Kai ni asibiti yanzu.”
“To, Madam Aleena,” ya amsa, yana canza hanya nan take.
Na damƙe wayar sosai.
“Granny, lafiya kuwa?”
“Lafiya lau, yar albarka. Amma ina son ki zo yanzu.”
Na sauke wani numfashi mai nauyi.
“Zan iso cikin minti goma sha biyar.”
“To, ina sauraren ki.”
Wayar ta katse. Amma hankalina bai daina tashi ba.
“Komai lafiya?” Mariam tana tambaya cikin damuwa.
“Ban sani ba. Ta ce lafiya, amma… wannan ba dabi’arta bace. Bata taba kirana haka kwatsam ba.”
Na sauke ajiyar zuciya a hankali, ina ƙoƙarin daidaita zuciyata."Da zarar kun sauke ni, ki koma office. Ki tabbata an gama tattaunawar kuɗi."
Mariam ta gyada kai da kwarin gwiwa.
“Zan yi hakan, Aleena. Ina fatan komai lafiya ne a asibiti.”
Na juya fuskata zuwa window, ina kallon yadda duniya ke gudana da hanzari, yayin da damuwa ke ci gaba da tattare zuciyata tamkar igiyar da ke kokarin shafe ni.
Ina ƙarasawa gaban dakin Granny, tafiyata cikin sauri, sai naji na tsaya cak lokacin dana ga wani yana tsaye a bakin ƙofar mutumin da ko ganin sa nayi jini na tafasa yake. Me wannan yake yi anan?
Wani irin ɗaci da takaici ya mamaye zuciyata.
Ya juyo daidai lokacin da idanuwanmu suka haɗu. Waya ce a kunnensa, sai murmushin sa na raini a fuskarsa. Ɗaya hannunsa na cikin aljihu, yana kallona sama da ƙasa kamar yana tantance ni da dariya. Daga ƙarshe, sai ya lumshe ido tare da jefa mun murmushin ba’a.
Seriously? Lalle ma takaici ya kara cike zuciya ta. Kallona ya ƙone cikin idanunsa yayin da muƙamuƙina suka matse har suka mun zafi. Murmushin da ke fuskarsa kadai ke kara wutar da ke tashi a kirjina. Amma kafin in faɗi ko kalma ɗaya, ƙofar ɗakin granny ta buɗe, wanda abun ya bani mamaki.
Mahaifin Omar ne. Runtse ido nayi na bude baki cikin sauri da ladabi.
"Ina wuni, Uncle Mehmet."
Na san iyayensa suna ziyartar granny lokaci-lokaci, amma da wuya mu ci karo da juna. Kuma yanzu, ga shi yana tsaye a bakin ƙofar. Daga kafadarsa ina iya ganin cikin dakin. Mahaifiyar Omar itama tana nan, Tana zaune kusa da Granny, suna hira cikin annashuwa.
Ya yi murmushi mai dadi, ya dan dafa kafadata.
“Ya’ta Aleena, Yaya kike?”
Murmushi na mayar masa dashi cike da ladabi. "Lafiya lau, Uncle Mehmet. Kana Lafiya ? Ban san zaku zo ziyara yau ba."
Murmushin sa ya kara fadadawa. Irin murmushin da na saba gani a fuskar dansa. Amma kuma nasa mai dauke da mutunci da shiga rai. Cikin wani ɗan lokaci, Omar ya ƙaraso kusa da mu wayarsa a kashe, kuma kamar kullum, yana ƙoƙarin nuna isa.
"Tabbas, baki san zamu zo ba," ya ce. "Kakarki ce kaɗai ta sani saboda itace tace mu zo jiya."
Na gyada kai a hankali—to ashe wannan shine wayan da naga granny jiya tana yi san da na nake waya da Emir.
“Papa, “Zan koma office yanzu akwai wani lamari mai mahimmanci da ya taso. Omar ya faɗa ba zato ba tsammani yayin da ya tsaya kusa da ni.
“Ka zo yanzu kuma kana cewa zaka tafi? Ka dan zauna mana Omar."
Atsaye nake cak, cikin rashin sanin yadda zan motsa ban san me zan yi ba. Ya kamata in shiga cikin dakin kawai, amma Uncle Mehmet yana nan tsaye a bakin ƙofar, kuma bazan iya ce masa ya matsa ba saboda yin hakan ya zama rashin ladabi. Kuma tsayawa a nan ma yana da rashin jin dadin musamman Omar da ke gefena a tsaye. Kafin in yanke shawara me zan ce, Omar ya sake magana.
"Wannan game da T-Phone Gen 6 ne. Ina bukatan in yi magana da ƙungiyar kuɗi na," ya faɗa da ƙarfi, yana haɗe hannuwansa. Har yanzu ba a kammala ba, saboda wani kamfani da ya kasa daidaita kansa. Gaskiya, ya kamata ma in katse hulɗa da CEO ɗin gaba ɗaya.”
Na juyo gare shi da sauri, muƙamuƙina suka matse. Na tilasta wani murmushi mai daci, na bada amsa, "Zan iya tabbatar maka muna magance matsalar. Da a ce Thorne Comm bai sanya waƙaƙƙen ƙayyadaddun lokaci ba ko kuma ya nemi abin da ya fi dacewa; kamfanina ba zai kasance cikin wannan matsayi ba."
Omar ya danna harshensa, leɓunansa suna murɗawa cikin wani murmushi mai ban haushi kamar yana jin daɗin ɓacin raina. "Da gaske? Kuna magance shi? Wane sakamako, a zahiri? Na ganki kamar mai buƙata... me ya faru? tsoro kike zan yanke kwangilar? Jiya, kin nuna tabbaci. Me ya canza?"
Na ja baya hannuwana sun matse tamkar zan yi faɗa dashi. Ya saba ko yaushe ya san yadda zai sa ni jin haushi.
Uncle Mehmet ya sa hannu ya dafa kafadata muryarsa mai bada hakuri. Ki gafarta wa Ya Omar, Kinji ya’ta Aleena. Yana iya zama... mai fadan kananan magana a wasu lokuta."
Na lumshe ido, na shanye bacin rai. Amma kalmar “Ya” da ya faɗa sai ta kara zafin zuciyata. Na tsani naji ana kiransa "Ya" a cikin jimla ɗaya da ni. Abin haushi ne.
Uncle Mehmet ya juyo gareshi da kakkausar fuska:
“Ka nemi afuwa Omar daga wurin Aleena. Wannan ba daidai bane abinda ka fada bai dace ba. Ka daina cewa haka game da Khan Electronics ko kuma ‘Aleena’.”
Omar ya ɗaga gira yana ƙoƙarin nuna rashin damuwa, amma tsaurarin kallon mahaifinsa ya sa ya yi shakka. Na haɗe hannuwana na daure fuska amma a raina ina cewa:
Aha! Ka ci karo da ubanka yanzu. Bari mu ga har yaushe za ka riƙe wannan girman kan.
“Meyasa? Me yasa zan nemi afuwa?” ya fadi da dan karfi. “Ni fa gaskiya na fada—kuma ita ce ta ce min jiya—”
“I don’t care,” cewar Uncle Mehmet cikin ɗaci.
Daga nesa, na hangi Aunty Asiye Mahaifiyar Omar da Granny na zaune suna kallon mu daga ciki.
“Ka ba Aleena hakuri. Yanzu nan.” ya ba da umarni.
Hah! Wannan abin gamsarwa ne.
Omar ya yi wani ɗan nishi yana gurnani a ƙarƙashin numfashinsa,
"Yi hakuri."
Na karkatar da kai, ina yin kamar ban ji ba. "Eh? Me ka ce?"
Sai kawai ya turo yatsansa ya danna kunnena, kamar wasa.
Na janye kai da firgici. Shin da gaske ya yi min haka ya taba mun kunne?!
Uncle Mehmet ya fizge hannu ya buge ƙafafunsa da dan karfi.
“Omar! Wannan wani irin hali ne? Nemi gafara da kyau yanzu!”
Omar ya ɗan firgita, yana mai kare kansa daga bugun. "Papa! Wasa kawai nake mata."
"Omar Thorne! Yaya za ka buga kunnen mutum? Ka nemi gafara!" ya katse shi, hannayensa a gefuna kuma muryarsa ba ta wasa.
Shafa kunnena na yi a hankali da wani irin motsi kawai don in nuna ban ji dadi ba na dan lanƙwasa kaina ina matse dariya da ƙyar. zuciyata cike da farin ciki, Na ɗan sauke muryata, cike da taushin da na tsara da gangan.
“Uncle Mehmet… ba komai. Kawai abin ya zo ne ba tsammani.”
Na lura da haushin da ke cikin idanun Omar, ya harare ni da wani mugun kallo amma ya kasa cewa komai.
Uncle Mehmet kuwa bai sassauta ba, yana fuskantar shi da zafin rai.
A raina kuwa, nayi dariya sosai.
“Ki yi hakuri da halinsa, Aleena,” Uncle Mehmet, ya ce. “Yana iya wuce gona da iri.
Omar, Amma gaskiya ka ba ni kunya sosai.” Ya fada masa.
Omar Thorne, duk girman kai da mulkin zuciyarsa, yana da rauni guda daya: Tsananin kauna da gudun bacin ran Papa.
Tunanin Omar ɗan shekara 13 yana kuka da fuskar sa ja, bayan ya yi fitsari a wando. Wannan nasara ƙarama ce ta yara. Wacce saboda wasu dalilai, ta tsaya tare da ni duk waɗannan shekarun. A lokacin ban fahimci ko kalma ɗaya daga cikin yarensu na Turkiyya ba. Amma na fahimci abu daya: yana buƙatar yin fitsari da gaggawa.
Meyasa na yi abin da na yi? To ni fa shekara shida kacal nake da ita. na shiga cikin tunanina na zama gimbiya mai mulkin daula, na batar da kaina a duniyar 'yar tsana ta. Ya shigo cikin wasana yana firgitani, kuma a cikin tunanin yaranta, na yi tunanin ya cancanci a "hukunta" shi saboda ya katse min wasa.
Kallon rashin jin daɗi daga iyayensa bayan abinda ya faru? Ya fasa shi gaba ɗaya. Shekaru da yawa bayan haka, ga shi yanzu yana sake fuskantar irinsa a ƙarƙashin rashin amincewar mahaifinsa. Kuma a wancan karon, ni ce a wurin, kamar yau kuma wa ina kallo.
Na yanke shawarar kawo ƙarshen wannan al'amari, na ce, "Uncle Mehmet, zan iya shiga ciki?"
Ya kalle ni kamar wanda aka farkar daga tunani. Sai ya ja gefe da murmushi, yana nuna min hanyar shiga.
Na jefa wa Omar wani ɗan dariyar nasara. yayin da nake wucewa a gabansa. Fitilar hallway na asibitin na haskaka fuskarsa, yana nuna fushin da ya tattara a idonsa. Kallon gefe da ya jefa min kamar wuka ne, amma na ci gaba da tafiya. Raina na cike da jin daɗin wannan ƙaramin nasara.
Granny na ɗaga gira da fara’a lokacin da na shiga dakin.
Na ƙarasa inda Aunty Asiye ke zaune, na gaida ta da girmamawa, sannan na jingina da gado na rungumi Granny da kyau. "You little troublemaker," ta ce da murmushi, tana dukan tafina a hankali. “Menene duk wannan hayaniya da nake ji a waje?” Na yi ɗan dariya yayin da nake janye wa daga rungumar. “Ai kamar yadda kika sani ne, Granny. Dama drama ba ya karewa. Amma me yasa kika kirani? Lafiya kuwa? Doctor ya ce wani abu?”
“Lafiya lau, Aleena,” Granny ta ce tana sauke numfashi.
Ta gyara zama ta sauko daga gado a hankali. Na miƙa hannu ina son taimaka mata, amma sai ta girgiza kai da alama zata iya da kanta. Yau ta fi rauni fiye da jiya. Na san wataƙila sakamakon maganin da ta sha da safe ne, wanda ya sa na ji damuwa game da yawan motsinta.
Mahaifiyar Omar ta miƙe itama, tana biye da Granny har zuwa kujerun da ke gefe. Ni kuma na zauna a bangarenta, yayinda mahaifiyar Omar ke zaune a ɗaya ɓangaren. Bayan yan lokaci Omar da mahaifinsa suka shigo dakin. Fuskar Omar har yanzu cike da bacin rai ne, yanayinsa yana nuna cewa bai bar abin da ya faru a wajen ɗakin granny ba.
Mahaifinsa ya zauna a gefen kujera, kuma Omar, da alama cikin rashin so, ya zauna kusa da shi.
Granny ta matsa tana radawa mahaifiyar Omar abu a kunne wanda ni ban ji ba. Mahaifiyar Omar ta gyada kai, sannan ta tashi ta nufi teburin kusa da gado, ta ɗauko wani bakin akwati na gane Akwatin ita ce granny ta nuna mini jiya. Lokacin da granny ta karɓe shi, ta buɗe akwatin ta fitar da wasiƙar da aka rufe da na sani daga baya.
“Na gode da zuwan ku, musamman kai Omar,” Granny ta fara, tana dafa takardar a cinyarta. “Na san kana da ayyuka da yawa Dan Albarka. kuma kasancewar ka anan nasan yana cinye maka lokaci mai yawa, ko?"
“Grandma Halime, ba komai," Omar ya amsa nan da nan, muryarsa cikin sanyi cike da murmushi na gaskiya. “Ina da lokacin ki ko yaushe.”
Wannan shine karon farko dana ga murmushinsa; ba irin na rainin hankali ba.
Granny ta gyada kai cike da jin dadin, sannan ta kalli mahaifiyar Omar. "Wataƙila ya kamata ki fara," ta ce, tana mika rufaffen wasikar zuwa gare ta.
Wani irin rashin kwanciyar hankali ya ratsa jikina. Wani abu game da wannan lokacin yana da nauyi - nauyi sosai.
Na dora hannu a hannun granny, ina ƙoƙarin ɓoye tsananin damuwata. "Me ke faruwa, granny?"
Ta taɓa hannuna a hankali, yanayinta mai nutsuwa amma mara fahimta. "You will understand now... Duk mun kasance a nan saboda wannan," ta ce, tana nufi ga envelope da wasikar ke ciki a hannun mahaifiyar Omar.
Cikina ya kara murdewa.
Na gaya miki jiya, ko ba haka ba? Granny ta ci gaba, muryarta ta yi laushi yanzu. "Kakan ki ne ya rubuta wannan wasiƙa lokacin da kike shekara bakwai. Ana buƙatar karanta shi yau. Na ji tsoron bazan rayu in karanta miki ba a ranar birthday ɗin ki na 27.”
Na girgiza kai da sauri. "A'a, granny. Na ce miki ki dena irin wannan kalamai-"
"Aleena," ta katse ni, da kakkausar murya mai cike da so. “Kiyi hakuri. Ki saurare ni.”
Numfashinta ya yi rauni. Kalamanta sun shiga zuciyata tamkar ɗan shuka. ya kashe duk wata ƙin yarda cikin rashin so, Na gyada kai a hankali.
Mahaifin Omar ya kalli dansa. “Omar, ka saurari wannan da kyau. Wannan umarni ne daga kakanka.”
Omar ya juya da mamaki, yana kallonsa. Sai kuma ya juyo ya kalle ni — kamar ya fara gane inda lamarin ke dosa.
"Haka nan kuma umarni ne daga kakan Aleena. Alkwari ne daga kakanninku ku biyu,” Uncle Mehmet ya ƙara da cewa. Dukkansu sun so wannan ya faru, don girmama yarjejeniyar da ke tsakanin iyalanmu da kuma Ƙarfafa dangantakar dangi."
Dakin ya zama kamar ƙanƙani iska ta yi kauri da shaƙa.
Na kalli Omar. Idanunsa suka haɗu da nawa kuma na ga hasken fahimta a yanayinsa alamu ya nuna mini cewa shi ma yana fahimtar abin da ke faruwa.
Ƙarfafa dangantakar dangi?
A'a…ba dai..
Wannan yana iya nufin.?
"Zan karanta wasiƙar," mahaifiyar Omar ta sanar, muryarta ta yanke shirun. Ta bude envelope a hankali ta mikar da wasiƙar.
Na matse tafin hannuwana yatsuna na huda cikin fatar tafin hannuna da ƙarfi yayin da muryarta ta fito.
"Ga ƙaunatattun jikokimmu masu daraja, Omar da Aleena. ta fara karantawa da murya mai ƙarfi. “Lokacin da kuke karanta wannan, zaku kasance cikin shekarun da muke ganin ya dace ku fara gina rayuwa tare…”
💘AUREN ALEENA💘
Amal Musa ✍️
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.