Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel.docx
Chapter 19 of 28
Chapter 1ï¸âƒ£9ï¸âƒ£ Somun Tabun Fara Kishi da So🔥â¤ï¸
SHARE SHARE SHARE 💃💃💃💃💃
"Ka kira aminanka, kuma sai gamu mun zo,"
Kemal ya faÉ—a kamar mai sanarwa yayin da yake shiga cikin office É—in Omar, babu knocking, Ali ya biyo shi ta bayansa.
Ba wata-wata, dukansu biyun suka zube kan dogon sofa na office É—in Omar.
Omar ya miƙe yana gyara rigarsa, ya wuce wajen other seat kusa da sofa ɗin da suke zaune.
"Meysa ka ce mu zo yanzu?" Ali ya tambaya. "Saboda wallahi na gaji sosai daga zaman hanya, kuma ga meetings ba adadi da muka sha a can Antalya. Idan so kake muyi magana akan results É—in, don Allah ka bari gobe, Omar."
"I know, and I'm very sorry, Ali," Omar ya ce yana gyada kai, duk da muryarsa ta yi sanyi sosai kamar ba tashi ba. Damuwa ta bayyana atare dashi, Ya kalle su yace, "Ali, me zai hana mu je mu sha drinks a club É—in Hasan?"
"Shan drinks kuma? Wait..." Kemal ya ce yana dariyar tsokana, yana duba agogon hannunsa. "Karfe 6:00pm fa yanzu, wani irin zuwa shan drinks kake nufi?"
Ali ya daga gira yana É—an hararar Omar kaÉ—an. "Something is wrong. Kana cikin bad mood daga ganinka. Saboda ace har yanzu kana cikin office a wannan lokacin? Omar, me ke faruwa? Aleena ce again? Akan tomatoes ne?"
Omar ya gyara zamansa, ya ji sabon bacin rai yana dawowa masa.
"A'a," ya ce murya cikin sanyi. "Ba tomatoes bane. Amma abubuwan da Aleena Khan takeyi gaba É—aya suna cin raina yau tun safe. Na ganta da Emir yau, kuma hakan gaba É—aya yasa raina cikin kunci."
Omar ya jingina jikin sofa, bacin ran dake ransa yana ƙara girma.
Ali da Kemal suka kalli juna cikin rashin fahimta. Omar ya cigaba,
"Sun zauna kusa da juna sosai, kuma Aleena ta san da aurena kanta, amma ta bar Emir yana kissing goshinta da hannunta a gaban jama'a a restaurant."
Kemal "hmm" kawai ya iya furtawa, yana sauke idonsa ƙasa.
"So, kenan ka barta tayi duk abinda ta ga dama kenan? Laifin ka ne."
"Nasani. Tabbas laifina ne da tun farko na barta take yanda take so. Amma dole na nuna mata ni nake aurenta, ba ita ba. Saboda idan iyayena suka taɓa sani ko ganin hakan, tabbas zai lalata komai."
Kemal ya gyada kai cikin fahimta.
"Sai kuma ka je ka yi mata magana a gaban mutane akan hakan? Dai dai na canka?" Ali ya fada yana kallon Omar.
Omar ya gyada kai. "Yes. Kuma wannan shi ne last warning da zan kara mata. Idan har ta cigaba, har iyayena suka gani—Allah ma ya kiyaye su gani—toh wallahi bansan irin hukuncin da zan mata ba ni kaina," Omar ya ce.
Ali da Kemal suka kalli juna wani irin kallo mai sa mutum tsarguwa, sannan suka kalle shi. Wannan yasa Omar ya daga gira. "Me yasa kuke kallona haka?"
"A'a, bakomai," Kemal ya fada yana dariya. "Amma dai ku ukun bakuyi fada ba ko? Saboda hakan ba zai yi kyau ba—dukanku CEO's ne a manyan kamfanoni."
"No," Omar ya ce da muryar gajiya yanzu. "Kasan ni ba haka nake ba. Kawai na bata warning, sai na tafi. Amma yanzu haushin Aleena nake ji sosai, fiye da lokacin baya kafin na aureta."
"You should try being nice to her. Ka nuna mata kana so ku fahimci juna," Ali ya ce, yana bashi shawara da wata murya kasa mai nufi da wata boyayyar manufa. "Who knows, Omar? Watakila ka fara son ta duk da halinta da yake baka haushi."
Idon Omar ya bude cikin mamaki. "Na fara son Aleena Khan? Yarinyar da ko ganin mutuncina batayi? Bata respecting dina, fah! Allah ya kyauta. Soyayyar da na yarda da ita a rayuwata ita ce ta iyayena. Wani abu bayan haka? Banjin zan taba yi."
"Aleena yarinya ce kyakyawa, really sweet," Ali ya cigaba cikin nutsuwa, kamar wanda ya dade yana nazari. "Tunda har tasa ka kake kishi, Toh hakan ba komai bane—illa cewan ta samu special waje a zuciyarka ba tare da kai ko ita kun sani ba. Omar, shawara zan baka: kaje ka yi tunani sosai akai. Watakila zaka so fiye da abinda kuke yanzu—ba kawai kalmar sunan aure ba, amma ku zauna matsayin miji da mata."
Omar ya jefa masa mugun kallo. Amma Ali ya yi saurin karawa yana murmushi. "A gani na, wannan ba kawai game da tsoron kar iyayenka su ganta da Emir bane. Hakane? Ko dai kishi ne, Omar?"
Omar ya yi wata dariyar takaici, haushi na dukan kirjinsa. "Kishi? Ni? Akan Aleena? Wannan tunanin ma haushi yake kara mun, wai me yasa kowa yake dagewa kishi nake saboda Allah, fah!"
"Ni fa na yarda da maganar Ali," Kemal ya tsoma baki fuskarsa cike da zolaya da dan tausayin Omar. "Inda nine kai, wallahi bazan bata lokaci ba. Zan yi duk abin da zan iya don in sa ta fara sona. Ka daina rike wannan tsanar da kake mata. Na tabbata ba ita ce a zuciyarka yanzu ba. Me yasa zaka bari mace kamar Aleena ta kubuce maka? Look at the situation now, hirar kadai tana neman samun ciwan kai."
"Alhamdulillah ni ba daya daga cikin ku bane," Omar ya ce kalmomin suna subucewa daga bakinsa kafin ya danne su. "Bazan biye wannan shawarar taku ta kishi ko soyayya ba. I'm just worried about my parents, that's all. Kawai yadda take yawo da masoyinta kamar wannan auren namu ba komai bane awajenta—abun yana bata mun rai."
Ali ya gyada kai ahankali. "Na fahimci damuwarka, Omar. Amma wannan auren, a wajenka wani abu ne?"
"Ba haka nake nufi ba, Ali. Fuck, kaga bana son wannan maganar—mu barta kawai. I'm done with both of you," Omar ya ce da haushi. "Jin hirar nan ma kara mun gajiya yake."
Ali da Kemal suka kwashe da dariya, suna jin dadin yadda yake reacting.
Bayan yan seconds, Kemal ya daidaita dariyarsa. "Alright, karka ji haushin mu. Kawai muna hangen abinda kai kaki yarda ka gani ne. Yaya maganar drinks da ka fada dazu?"
Omar ya yi dariya. "Zan kira Hasan. Idan akwai masu rawa sai muje kallo, zan kama mana wajen dukka. Ina bukatan na manta bacin raina—na dade banyi nishadi ba."
Ali da Kemal suka sake dariya. Ali yana gyada kai. "Sai da kai, abokina."
Dare ya yi, lokaci yana kirga 10:30 pm.
"Welcome," Hasan ya faÉ—a yayin da suka shiga cikin wajen. "Lallai ashe da gaske kake da ka ce zaka zo, ba da jimawa ba, Omar."
Suka shiga ciki su uku. Cikin wajen wasu red, blue, and dark lights suna haskakawa, tashin music mai bugu yana tashi. Kamshin drinks kala-kala masu tsada yana cike wajen.
Idon Omar suka faÉ—i kan stage inda 'yan mata suke rawa.
The Temptation. A VIP strip club like no other. Bai taba disappointing É—insa ba.
Hasan ya nuna musu hanyar VIP su zauna. Cikin authority ya É—aga gira zuwa ga workers nasa, ya ce: "Ku kawo su yanzu, gaba É—ayan su."
Omar murmushi ya fara fito masa, idonsa ya sauka kan wasu 'yan mata da suke rawa, wani farin ciki ya fara bayyana a fuskarsa — yadda suke rawar yana birgeshi.
Bayan seconds kaÉ—an staff suka zo don nuna musu hanya. Suka tashi suna haura upper floor babba, wanda yake cike da duhu mai É—an laushi da golden private rooms.
Nan da nan numfashin sararin saman wajen ya canza. Kamshi da sautin waka — wanda bai kai na ƙasa ƙara ba — suna cike da nutsuwa. Sabon VIP ɗin da Hasan ya sake ginawa a upper floor kenan. A tsakiya akwai five polished poles a ƙasa, shirin entertaining mutanen wajen.
"Make yourself comfortable," Hasan ya ce, murmushinsa yana ƙaruwa. "I will have your drinks prepared. And of course... da kuma entertainment ɗinku." Daga nan ya tafi, ya barsu suna settling kansu.
Omar ya fito da hannunsa daga aljihu yana shafa kan leather seats ɗin. Ya cire suit jacket nasa daga kafaɗa ya ajiye gefe. Ali da Kemal suka zauna, kowannensu a seat ɗinsa, dim lights ɗin suna ƙara musu nutsuwa.
Moments later.
Kofa ta buɗe sai gasu sun shigo — six beautiful girls. Suna tafiya cikin taku mai tsokana da jan hankali. Hudu suka makale idonsu cikin kallon Omar, suna juya jikinsu da gangan. Guda biyun kuma idonsu sun sauka kan Ali da Kemal.
Show É—in ya fara.
Kemal ya ja numfashi a hankali cike da jin daÉ—i.
"I like this," Kemal ya ce, muryarsa ƙasa saboda sautin waka da ya fara ƙaruwa.
Omar ya yi dariya lokacin da waiter ya ajiye musu drinks.
Karar glasses ta nutse cikin sautin waka. Omar ya ɗaga glass ɗinsa, cikin kurba ɗaya ya shanye. Yana ƙoƙarin juyar da hankalinsa nan.
Ali bai ɓata lokaci ba — ya ja 'yan mata biyu, ɗaya tana gabansa tana rawa, ɗaya kuma tana gefensa tana shafa shi. Yana tantance wacce zai dauka.
Omar ya kalle shi daga nesa, ya yi dariya. Lallai Ali a kan kaya yake yau.
Kemal ya É—auki É—aya, ya nufi wani É—aki. "Ni na tafi," ya ce. Omar ya yi dariya yana gyada masa kai.
Kyakyawar yarinya ta matso kadan tana rawa cikin salo da jan hankali, tana da dogon wuya, faɗin kafaɗa, bata da kiba, gata doguwa fara amma ba sosai ba — mace irin type ɗinsa.
Omar ya sa hannu yana tafawa kan cinyarsa, alamar iko da izini. Idonsu ya haÉ—u, yarinyar ta fahimci nufinsa.
Ta taso tana tunkaro shi cikin tafiya mai rikitarwa. Omar ya riƙe hannunta yana kallonta yayin da ta sunkuya ta hau cinyarsa. Da zarar jikinta ya taɓa shi, jijiyoyinsa suka fara tashi.
Hips ɗinta suna motsi kan cinyarsa, fatar jikinta laushi — it was impossible for Omar to resist her. Ba tare da sun daina kallon idon juna ba ta karɓi glass ɗinsa, ta sha kurba biyu, ta ajiye. Sai ta fara motsa jikinta a hankali, tana ƙara nutsar da shi.
Zafin jikinta Omar ya ji yana shigar shi. Hannunsa ya fara yawo jikinta. Ta sunkuya, bakin ta a gefen kunnensa, cikin murya mai dumi da tsokana ta ce:
"Mey kake so a daren, yau?"
Omar ya yi dariya, yatsunsa suna sauka a bayanta, yana danna su, ya ce:
"Zaki sani nan ba da jimawa ba."
Ta ja baya kaɗan, idonsu ya haɗu — kamar silent challenge. Jin daɗi ya bayyana a idonta ganin ta samu control akansa.
Omar ya kai hannunsa kan ass ɗinta, ya damƙe, ya juya ta sosai da ƙarfin sa. Numfashinta ya kame jin karfin damkarsa.
Omar ya dan ja baya, lips ɗinsa suna shafar kafaɗarta, ya ɗan zame rigarta. Ta ƙara motsi, suna kallon juna.
Sai gashi Omar ya tsaya cak — idonsa suka buɗe cikin shock.
"Dakata... W-wait. What the—"
Aleena ya gani a idonsa. Wannan murmushin nata mai kyau, idanunta masu girma, dogon wuya, da faÉ—awar saman kirjinta mai zurfi.
"I'm sorry, Mr. Omar. Nayi kuskure ne?" yarinyar ta faÉ—a, fuskarta cikin damuwa.
Omar ya girgiza kai yana ƙoƙarin korar hoton Aleena daga cikin kansa. Amma hoton ya tsaya masa cak.
Ya É—auki wani glass, cikin kurba É—aya ya shanye. Yarinyar ta matsa gefe.
Me yake damuna? Mene matsala ta wai? Ko dai drink É—in ne? A cikin ransa ya yi tambayar. Amma ai ban bugu ba, kadan kawai na sha drink din fah!
Omar ya juya zuwa ga yarinyar, sai ga fuskarta ta canza zuwa tsoro. Ya ja numfashi mai nauyi. Damn it.
Ya yi ƙoƙarin yin murmushi amma ya kasa. Duk da haka ya janyo yarinyar a kan cinyarsa, amma tunanin Aleena bai bar shi ba.
"Let's continue," Omar ya ce mata, duk da zuciyarsa ba nan take ba.
Yarinyar ta miƙe tana kallonsa. Omar yana ƙoƙarin sa hankalinsa kanta, amma duk motsinta sai ya ji kamar Aleena ce kan cinyarsa. Kansa ya fara juyawa, ya kasa nutsuwa.
Ta yaya hakan yake faruwa? Meysa na kasa cire ta daga cikin kaina?
Cikin bacin rai ya miƙe, ya kalli yarinyar:
"Kiyi hakuri, amma ba zan iya ba."
Ali ya hangoshi yana kokarin fita.
"Omar! Omar! Lafiya?" muryar Ali ta ketar cikin wajen.
Omar ya daga masa hannu cikin sauri:
"Zamu yi waya, bro. Gida zan tafi."
Daga nan ya fice, ya barsu.
A/N: Yawan comments yawan typing da update kan lokaci.
💘AUREN ALEENA💘
Amal Musa âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.