Complete Hausa Novels

Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel

Reading file: Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel.docx

Chapter 27 of 28

Chapter 2️⃣7️⃣ Shameless 😭❤️😂

Katotuwar Rolls Royce ce ke jan hankali yayin da take kutsawa a hankali cikin cunkoson titunan Bursa. Agogon da ke manne a jikin motar ya nuna ƙarfe 6:12 na yamma, amma duk da haka babu wani alamar motsi a gaban su. Traffic ɗin garin ya cika titin har ya zama kamar wani dogon layi na motoci marasa ƙarewa. Omar yana zaune a kujerar baya, ƙafafunsa a nade ɗaya kan ɗaya. Wayarsa na hannunsa, yatsunsa na ta zirga-zirga a saman screen ɗin ba tare da wani dalili na musamman ba, fa ce don kashe lokaci. Ta cikin madubin gaban motar, idanunsa su ka sauka kan direbansa ya ga yadda yatsunsa su ke ta bugawa a hankali kan steering wheel. Yadda yake leƙa hagu da dama, yana neman wani kafa da zai kutsa domin su tsallake cunkoson. Takaici ya cika Omar. Da ya sani ma, bayan ya koma office ɗinsa, bai ce direbansa ya tuƙa shi ba. Da shi yake tuƙin yanzu, da tuni ya nemo hanyar tsallake wannan cunkoson.

Sai dai kuma... Ba ya jin kansa ne. Tun lokacin da ya bar ofishin Aleena, zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa. Tunani daban-daban ne kawai ya ke kai-kawo a kansa. Ko aikin da ya kamata ya kammala ma kasa yi ya yi. Hakan ya sa ya É—auko Zera tare da shi.

Zera tana zaune a gaban mota yanzu, laptop a buÉ—e a cinyarta tana cigaba da aikin da ya kasa kammalawa. Ya riga ya umarci direba cewa da zarar ya sauke shi gida, sai ya ajiye ta.

"Go-slow É—in yau ya fi na kullum, Mr. Omar," direban ya faÉ—a yana karya shirun da ya mamaye motar.

"Hmm." Abin da Omar ya amsa da kenan kawai. Saboda shi ma ya san hakane. Bayan wasu sakanni, motar ta sake tsayawa gaba É—aya. Ba ta motsi ko na inci É—aya. Mintuna kusan biyar suka shuÉ—e suna nan cak. Omar ya saki tsaki cikin takaici. "Ka fita ka duba. Ka ga motoci nawa ne a gabanmu."

Direban ya gyada kai cikin girmamawa ya buɗe ƙofa ya fita. Bai jima ba ya dawo. "Kamar wata babbar mota ce ta samu matsala, Mr. Omar," ya faɗa yana sake leƙawa ta madubi. "Mutane suna ta taruwa a gaba."

Omar ya shafa haɓarsa. "To meye sabon abu a ciki?" Ya faɗa cikin rashin haƙuri. Saboda tabbas yasan abu  ɗaya da zai faru shi ne. Akwai yiwuwar za su jima a nan. Kuma ya riga ya fara gajiya. Ya sake buɗe wayarsa yana yawo a social media ba tare da neman wani abu ba. Sai kwatsam... Wani suna ya bayyana a screen dinsa. Aleena Khan. Snapchat suggestions. Saboda ya yi saving number ɗinta. Nan da nan wani irin murmushi ya bazu a fuskarsa. Murmushin da yazo ba tare da izini ba. Idan ya san kansa da kyau, ya kamata ya ji haushi saboda makalewa da ya yi a traffic. Amma maimakon haka... Tunani ɗaya ne ya fara yawo a kansa. Ita ma yanzu haka tana cikin wannan cunkoson. Tun lokacin da ya bar ofishinta bai samu damar tura mata da ko saƙo ɗaya ba... Bai samu damar tsokanarta ba, aiki ne ya yi masa yawa. Ko kuma aikin da ya kasa yi saboda ita. Amma sai dai tunda yanzu ba ya komai, To yanzu shine perfect time da zai tsokaneta. Sannan kuma wannan shine zai zama maganar su ta farko awaya. Omar ya ɗan girgiza kansa. Wani mugun tunani mai cike da fitina da sa nishadi ya faɗo masa. Ya ɗaga wayarsa ya ɗauki hoton dogon layin motocin da ke gabansu ta cikin window. Sai ya fara typing.

Omar: Kin ga ba lallai bane na iso gida a kan lokaci, darling. Don't wait for me.

Ya danna send. Ko sakan ɗaya ba ayi ba, blue tick ya bayyana. An buɗe saƙon. Omar ya ɗan daga gira. Wow... Ya furta a zuciyarsa. Da wuri haka? Murmushinsa ya ƙara faɗaɗa. Sai ya ga alamar: Aleena is typing... ta bayyana. Sai kuma saƙo ya shigo.

Aleena: Kar ka dameni.

Omar ya kalli saƙon na ɗan sakan guda. Sai kuma ya kwashe da wani irin dariya mai ƙarfi yana girgiza kansa. Dariyar da ta fito masa ba tare da ya shirya ba.

Zera, wacce ke maƙale da screen ɗin laptop ɗinta, ta ɗago kai da sauri tana kallonsa cikin mamaki. Hatta direban ma sai da ya ɗan leƙa ta cikin madubi. Dukansu biyun suna kallonsa kamar suna ƙoƙarin fahimtar abin da ya samu shugaban nasu.

Omar ya jefa musu kallo guda. Nan da nan suka kau da kansu kamar ba su yi komai ba. Shi kuma ya sake sunkuyawa kan wayarsa. Yatsunsa suka fara typing akan screen É—in.

Omar: So rude. Kar ki zuba haushin go-slow a kai na. Babu abin da na yi miki banda ƙoƙarin faranta miki rai.

Ya sake danna send, amma sai dai ba ta buɗe message ɗin ba. Bayan kusan minti ɗaya, message din ya nuna blue tick alamar an buɗe shi. Amma babu wani reply da ya shigo. Minti biyu. Har yanzu babu komai. Shiru. Uh-oh, Aleena. Ya furta a zuciyarsa. Ya na murmushi da girgiza kansa a hankali. Sam ba zai bari ta buɗe saƙonsa ta bar shi a seen ba. Babu wanda ya taɓa yin hakan a rayuwarsa. Sai wani tunani ya sake faɗowa kansa. Tunani irin wanda ko da yaso ya hana kansa, ba zai iya ba. Wani mugun murmushi ya sauka kan lebensa.

A hankali ya warware maballan rigarsa guda uku. Faffaɗan kirjinsa ya bayyana, tare da siraran gashin da suka kwanta luf a fatarsa mai santsi. Hasken fitilun waje da ke ratsowa cikin motar ya sauka a kansa, yana ƙara fito da laushin farar fatarsa, da kuma alamun tsokoki da jijiyoyin da suka yi fice a kirjinsa. Wayarsa ya ɗaga.

Ya ɗauki hoto daga ƙasan lips ɗinsa da suke ɗan buɗe kaɗan, ya sauko har zuwa kirjinsa da ya bayyana, sannan zuwa cinyarsa inda hannunsa yake kwance luf cikin wani yanayi na kasala. A gefen hoton kuma, ɗan ɓangaren hannun wata mace da agogon wristwatch ɗinta ya ɗan leƙo kaɗan daga kujerar gaba. Ba tare da wata-wata ba, ya tura mata hoton tare da wani saƙon.

Omar: I'm so bored. Kuma motar nan zafinta ya yi yawa. Ko AC É—in da yake kunne ba zai iya huce zafin da nake ji a yanzu ba. Kuma ban san me yasa ba.

Yana tura message ɗin, ya rufe app ɗin tare da ajiye wayarsa a gefensa. Wani ɗan ƙaramin dariya ya saki a hankali, idonsa yana karkatawa zuwa window. Motoci sun fara motsi yanzu a hankali, duk da cewa har yanzu ba a fita daga cunkoson gaba ɗaya ba. Sai wayarsa ta fara vibrating fiye da sau ɗaya, ya juyo da sauri yana dubawa. Aleena Khan Calling.... That was quick. Ya furta a ransa tare da ɗaga gira cikin mamaki, ya dauka Aleena was tough, kuma abin da zai karya ta ba abu ne mai sauƙi ba. Amma tabbas ashe ya yi kuskure, saboda yanzu ya gane ba ta da wani banbanci da sauran matan da idan suka ga kirjinsa kadai su ke rikicewa. Call ɗin ya ɗaga ya kai wayar kunnensa, Sannan ya lumshe idanunsa yana jingina da kujerar baya.

"Yes, honey?" Ya furta a hankali.

"Dama saboda wannan shirmen ka tambayi number na, Omar?" Ta tambaye shi. Muryarta tana ɗan rawa kaɗan, sannan ta ƙarasa maganar da tsaki.

Wani munafukin murmushi ya bayyana a fuskar Omar. "No. But I am bored. Na rasa abin yi..." Ya faÉ—a muryarsa tana fita a hankali, da gangan cikin wani irin kasala fiye da da mai cike da tsokana.

"Omar—"

"Kin ga hoton?" Ya katse ta. "Ni raina ma duk a bace yake, ga zafi sosai ya isheni acikin motar nan. Ga wannan goslow ɗin ya na annoying dina." Ya ƙarasa maganar cikin wani rada mai sautin daga hankali.

Shiru ne ya mamaye layin kiran, ko numfashinta ba ya ji. Ya kalli screen din sai ya É—an yamutsa fuska ganin cewan still call din yana tafiya bawai yankewa yayi ba. Meyasa tayi shiru? Omar ya fada cikin ransa. "Aleena? Are you alive?"

Ajiyar zuciya ta yi daga ƙarshe sannan ta amsa shi. "Omar, na goge hoton da ka turo min yanzu daga gallery ɗina. Kuma kamata ya yi ka ji kunya! And naga ba kai kaɗai bane a cikin motar. Har da wata...! Look, karka kara tura min abu irin haka again. And I don't like it. Saboda ko kaɗan bai burge ni ba, tsantsami ma ya bani!" Ta ja numfashin takaici.

Murmushi ya yi. Lallai Aleena ta iya ƙarya saboda daga yadda take magana cikin sauri da yadda muryarta ke rawa ya gaya masa fiye da abin da kalamanta suke faɗa. "Oh, alright. But no, Aleena. Ban ji kunya ba sam. Dalili kuwa daga ni sai direbana da sakatariyata, sannan kuma na saba turawa yan mata abubuwa irin haka koda yaushe don taimaka musu wajen yin baccin dare cikin sauki."

Wani tsaki Aleena ta saki a matsayin amsa, sannan tace. "I don't care-"

"Ina da wani idea," ya katse ta, murmushin ketarsa yana ƙara faɗaɗa a kan lebansa. "If you don't like it, maybe za ki fi son wanda za ki iya taɓawa da hannunki, ba kallo kaɗai ba ko? Kamar irin wanda kika yi last night? Come on, tunda kinsan yadda yake a hannu..."

Shiru ne ya sake sauka. Shiru mai nauyi wanda ya mamaye tsakaninsu gaba ɗaya. Omar ya juya wayarsa zuwa camera ta baya, sannan cikin sauri ya sake ɗaukar wani hoton. Amma a wannan karon ya sake balle maballi biyu na rigarsa, yana cikin irin pose ɗin da ya yi ɗazu. Sai dai yanzu ya ɗan miƙe jikinsa sosai a zaune kan kujerar, abin alfaharinsa da yake cikin wandon suit ɗinsa ya fara tashi daga bacci. Cikin sauri ya latsa send ya sake tura mata. Daga nan ya mayar da wayar kunnensa. "Ki duba, na tura miki message," ya faɗa yana jin motsinta, alamar tana dubawa.

Sai kuma ya ji ta sauke wani irin doguwar ajiyar zuciya.

Da sauri Omar ya cije leɓensa yana ƙoƙarin danne dariyar da ta taso masa, kafin muryarta ta fito da ƙarfi, kusan kamar tana yi masa ihu a kunne.

"Stop it, Omar! For God's sake, dan Allah ka maida maballan rigarka sama! Sakatariyarka na nan, direbanka na nan! Meyasa kai kwata-kwata ba ka da kunya ne? Tell me, why are you so shameless? Ka rufe kirjinka yanzu! Damn you!" Ta faÉ—a cikin tsawa da faÉ—a.

Wow. Ranta ya ɓaci sosai. Damn it, Omar. Ya faɗa wa kansa yana jin wani irin abu kamar lantarkin wuta yana ratsa shi. Ya san Aleena tana da zafi, amma bai taɓa sanin tana da irin wannan zafin fushin ba. Yadda ta yi ihun har ya fi zafin wuta. Har cikin jikinsa ya ji tasirinta.

"Kana saurarona?" ta sake cewa.

Omar dariya ya sake yi, don ƙara sata magana.

"Omar—"

"No. Ba zan rufe ba. Idan har kin damu haka, ki zo ki rufe min da kanki. Ko kuma mai zai hana kawai na buɗe sauran maballan? Na san za ki so gani." Daga nan Omar ya kashe wayar. Ya mayar da wayarsa cikin aljihunsa sannan ya ɗan miƙe, yana jin wani cikakken gamsuwa da nishaɗi suna mamaye shi. Damn you, Aleena. Ya faɗa a ransa. Idan cikin kwana biyu bai same ta a kan gadonsa ba, to ba sunansa Omar Thorne ba. Yana girgiza kansa ya kalli wajen window, wani irin excitement yana ci gaba da shiga jikinsa. Ba tare da ya sani ba, wani murmushi irin na yan wanda suka fara faɗawa cikin soyayya ya mamaye fuskarsa, yayin da yake maida maballan rigarsa kamar yadda Aleena ta ba da umarni  ya rufe su tas. Kamar yadda ya saba yanzu, zuciyarsa ta sake komawa kan tunanin daren yau.

Aleena za ta dawo gida yau da daddare. Zai tabbatar mata cewa abin da yake faÉ—a mata gaskiya ne kuma itama tana jin hakan. Kuma zai sa ta haÉ—iye kalamanta da kanta na cewa tana tsantsamin sa.

Kuma zai tabbatar ta amince cewa lalle ta ji daÉ—in kiss É—insu na daren jiya kamar yadda shi ma ya ji daÉ—insa.

Just wait, Aleena.... You... just wait.

A/N: Dan cigaba da karantawa ku nemeni a wannan number dan shiga group dina 09133523119

First book dina ne kuma free book 📖💃🥰😘

💘AUREN ALEENA💘

Amal Musa ✍️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.